← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 163

Sashe 70

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Jijjiga kansa yayi dan yasan 'karya take bawani sallar datayi.
_" wai laifin menayi ne haka lil sis please tell me kinji_ _banson kin......_

Be 'karasa maganar ba ta tare shi da fa'din _" bakai bane,_ _jiya ciki na ciwo yatayi dadare_ _nakasa bacci, ina ta tashinka kai kuma ka'ki ka kulani, bayan nasan kana_ _jina "_

Kansa yadafe tare da fa'din
_" innalillahi, ya akai duk bansan anyi haka ba, pls_ _Fateemah kiyi ha'kuri kinji aikinsa bahaka nake yi miki ba ko, wallahi jiyan_ _ne baccin ya min nauyi ni kaina nayi mamaki, amma insha Allahu hakan_ _bazai sake faruwa ba kinji"_

Shiru tai masa batayi magana ba,
_" bazaki ha'kura ba_ _ko Fateemah?_

Tashi yai kamar zai tafi irin yayi fushi 'din nan shima, take sai Teema ta kamo hannunsa koda ya juyo kuwa sai suka ha'da idanu, kai ta jijjiga masa sai yace mata _"kin_ _ha'kura"_ da kai ta amsa masa alamar _"ehh",_ yana ganin hakan sai yadawo gefenta ya zauna yace toh tayi dariya yagani, murmushi tayi tare da sunkuyar da kanta 'kasa shima murmushin yayi yace cikin zolaya yace _" wato dan na 'ki kulaki shine kika yi fushi kika koma parlour kika barni ni 'daya a 'daya a'daki ko?._

Dariya sukayi atare daga nan maganar ta wuche suka shiga harkokinsu kamar kullum.

'Karfe takwas 8:am na safe Mahmud ya wuche offfice tare da rakiyar Teemah har wajen da zai shiga motar sa, tana 'kara jaddada masa wai ya dawo fah da wuri dan ita tsoro take ji, kullum dama inzai fita sa'kon ta kenan, sai kuma tace ya siyo mata tarkacen fruits da har yau tafi sansu akan abinci, takan sha ko ci aduk lokacin da Mahmud ya matsa mata akan taci abinci, wani lokaci kuma sai taci abincin musamman ranar da ya 'ki siyo mata fruits 'din, yauma daya tambayeta abinda zai kawo mata sai tace masa Apple kawai takeso yau, murmushi kawai yayi ya juya ya shige mota dan baya so ta sake yin fushi dashi akaro na biyu badan haka ba da bazai siyo mata ba, dan yasan idan tana ganin fruits 'din bata ta6a waiwayar abinci akan lokaci sai ta ga dama.

Bye-bye ta masa daga nan yaja mota ya fita agidan shima yana me 'daga mata hannu.

*****
Duk wani abu daya rage na tafiyarsu Daddy yayi ya kammala komai harma yarage saura kwana biyu kacal su tafi, Mummy taso taga 'yarta kafin su tafi amma Daddy ya hana ko awaya ma yahana ta sanar da ita saboda baya so ta 'daga hankalinta, yafi son tayi zamanta hankali kwance agidan mijinta batare da sa damuwar komai aranta ba, Mummyn ma damuwarta ayanzun bai wuce tasan irin zaman da Teemahn keyi da Anty ba abinda yafi damunta kenan, dan tasan 6angaren Mahmud da sauki duk dama tana zargin bason auren yake ba, amma koda ta 'kira Teemah awaya bata samun labarin komai, Teemah bata sanar da ita matsalar dake damunta, akullun cikin farin ciki take jinta, tun tana zargin ko Teemah na 6oye mata ne har tazo ta yarda cewa Teemahn bata tare da damuwa, fatanta dai Allah yasa hakanne, Allah ya wanzar da farin ciki da zaman lafiya a tsakaninsu gaba'daya.

Wata'kila shiriyace tazo wa Antyn shiyasa ta yada makan ya'kinta ta ri'ki Teemahn amatsayin matar 'danta Mahmud.
Mummy takanyi murmushi ita ka'dai idan hakan yazo ranta domin babu abinda ya fimata da'di da farin ciki ayanzu irin taga Teemah na rayuwa cikin walwala ga dukkan alamu kuma burin ta ya cika.

Hatta Ummah da su Hannah basu sanar da ita tafiyar da iyayentan zasu yi ba, dan gaba 'daya Daddy ya hana kowa sanar da ita, bayan kwana biyu ranar wata litinin da 'karfe biyar na yamma jirgin su yatashi zuwa dubai tare da rakiyar Abbas daya baro bakin aikinsa anan cikin maidugurin dan yakusan sati anan 'din da aka kawo su, domin kwantar da tarzoma da irin matsalolin 'yan ta'adda dake addabar yankin na arewacin Nigeria musamman ma jihar Borno, koda zasu rabu ma su Daddy na ta sa masa albarka da zuba masa ruwan addu'o'i na kariya daga dukkan munafukai da mahassada dama dukkan wani abin 'ki musamman ma yanzu daya taho nan domin yin ya'ki da 'yan addacin 'kasar tamu ta Nigeria, da Ameen kawai Abbas ke amsawa dan shi kanshi yasani zuwa yin aiki a Borno a wannan zamanin shi yafi komai risk ga rayuwar duk wani ma'aikaci irin sa, zuwa borno awannan lokacin tamkar sai da rai ne, 'kalilan daga cikin ma'aikatan nasu kan ajiye aikinsu dazarar sunji cewa zasu jihar borno, masu 'karfin imani, zuciya da tawakkali sune ke aimincewa zuwan sa6anin Abbas da dakansa ya sa aka sanya sunanshi acikin jerin list 'din amatsayin jagoran batallion nasu, domin yana ganin zamansa a borno shi yafi masa dan yasan akoda yaushe zai kasance ne cikin shirin kota kwana tunaninsa zai kasance ne akan aikinsa akowani lokaci bazai samu lokacin tuna past dinsa ba yafi son yamanta da komai.

Daga 'karshe Daddy yace masa
_"Nabar Fateemah agidan mijinta bai san awani hali take ciki ba, yace Abbas_ _duk lokacin daka samu lokacin zuwa Abuja ka daure ka 'karasa ka dubo_ _min ita amma bawai nace dole sai kaje bane karka takura kanka sai in_ _kaga kana da lokaci sannan,"_

_" bakomai daddy insha Allahu zan 'ko'karta inje da iznin Allah."_

" _Yauwa Babana Allah ya ma albarka yabaka sa'a_ _adukkan al'amuranka "_

_"Ameen Daddy_ _nagode sosai"_

Kallon daddy yayi da kyau sannan yace
" _Inason zuwan farko da zan sakeyi awannan 'kasar yakasance taron daurin auran_ _Babana nazo"_

Mummy najin haka ta dawo da kallonta ga Abbas din sai kuwa taga yayi shiru ya tsurawa Daddy idanu amma ga dukkan alamu hankalinsa da tunanainsa ba akan daddyn yake ba, sai daddyn ya dafa shi kafin ya dawo dai dai.

_"Tunanin me kakeyi kuma ?,ina fatan dai kaji abinda_ _nafa'da"._

_" ehh naji daddy insha Allahu zan_ _'kokarta."_
Jinjina kai daddy yayi cikin farin jin kyakykyawar amsa daga bakin Abbas .

Abbas sai da yaga tashin jirginsu kafin yajuya ya tafi yakoma bakin aikinsa yana me alhinin rabuwa dasu tare da tunanin dalilin dayasa su irin wannan tafiyar _.(safe trip mummy and Daddy)._

Daddy ya yanke wannan shawarar ne sanadiyyar tashe-tashen hankula da suka yi yawa a jihar yobe, har ya kasance akullum ba'a kwana atashi cikin kwanciyar hankali harin kullun da kalan yanayin sa, so 'yan uwa da dangi duk sun masa cha akan yabar garin ko dan yawan hare-haren da ake yawan kaiwa, da farko ya yi biris da maganar amma daga baya da yaga abin na neman yin yawa kawai da kansa sai ya aminche.

Daddy ya shirya musu komawa Dubai 'din ne tun kafin ayi zancen auren Teemah, da maganar auren yataso ne kuma sai ya danne nashi 'kudurin azuciyarsa har sai da aka kammala komai ya mi'ka Teemah gidan mijinta kafin nan.

*Ur comment is getting low, I feel like nima in 'dan huta, saboda gaskiya banjin dadi'n hakan da* *kukeyi* 😭.

_Agyara pls_ 🤞🏻

_Nasan ana yi but_ _anunka_ 👌🏻

*inason ganin sharhinku kalakala ne dan idan ina karantawa ji nake kamar kar in daina wlh, INAYINKU IRIN......,,,,,,,,,,,,'Din nan .*

👎🏻
_Comment_
_Vote_
_Share_

*Salmerh ce* 😍
[10/2, 6:02 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_Dedicated_
_2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs._ 😍

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

_Never argue with a fool because People might not know the difference....._

🅿 *57*

Ciwon cikin Teemah da yamma ya 'kara dawo mata sabo fil, gashi ita ka'dai ce agida kuma har alokacin bata sha magani ba, data rasa yanda zatayi sai kawai ta fara kuka tana mirgine-mirgine dan tayi iya 'ko'karin ta dan ganin ta danne ciwon amma sai da ya fi 'karfinta tafara kuka.

Acikin wannan halin Mahmud ya dawo gida ya sameta, ai kuwa jifa yayi da jakar dake hannunsa arikice ya kinkimeta yayi waje da ita be ma tsaya tambayarta dalilin kukan ba saboda yaga tana ta ri'ke cikinta tana mur'kususu, be manta ciwon datace cikinta yamata jiya cikin dare ba, shiyasa yana ganin ta awannan halin kawai ya nufi asibiti da ita.

Allah ma ya taimaka ba wani nisa sosai ne tsakaninsu da asbitin ba, dan haka be 6ata lokaci akan hanyar ba, duk dama zuwa lokacin hold-up yafara taruwa amma dai yasamu ya isa akan lokaci, kanta ko mayafi babu lokacin da suka isa asbitin, amma duk wannan be zo kan Mahmud ba shi dai damuwarsa aduba masa lafiyarta a kuma bata magani.

Cikin sa'a ma sai yasamu wani likita ya duba masa ita akan lokaci tare da yimata allurai guda biyu, cikin ikon Allah kuwa daga nan tasamu bacci ya 'dauke ta.
Chapter 70 · 0% Book details