← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 156 OF 163

Sashe 156

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Maman Amal ma ta zo tun daga Lagos inda Teemah tayi matu'kar farin ciki, musamman da taga yanda baby Amal 'dinta ta 'kara girma tayi wayo tana gudun ta ko'ina.

Leesah ma babu ranar da gari zai waye bata zo gidan ba, wani zobe na gold ta siyo ta sawa yaron a hannu mai kyau da tsada itama kullum son Babyn na 'kara ratsa ta barin ma da taga ya na kama da baban sa ai shikenan idan tazo kuwa bata barin kowa ya ri'ke shi sai ita ka'dai.
Tun kafin ayi suna
ma Leesah tafara 'kiran sa da Annoor ta kuma ce sunan da za'a 'kirashi dashi kenan kenan.

Hannah kam bataso hakan ba dan ita da niyyar ta a k'irashi Irfan sai kuma Haleesah ta riga ta sanya masa suna dole badan taso ba ta ha'kura da nata sunan tana jin badan wani abu ba da Leesah bata isa ce zata saka wa jinjirin suna ba amma sai Hannah tayi mata kara ta bari saboda darajar abu 'daya.

Ranar suna yaro yaci sunan *Mahmud*, babu wanda bai mamakin sunan da Abbas ya sanyawa jinjirin ba, inda jama'ah da dama suka yaba masa tare da yaba irin karamcin daya yi, especially wa'danda suka ji abin a sama cewa kawai sunan marigayi mijin matar sa na baya ne, sai suke ganin kamar shi 'din halin sa daban ne dan bakowa zai iya irin hakan ba.

Wa'dan da kuwa suka san asalin zumuncin dake tsakani sai sam barka kawai suke yi, wannan dalilin kuwa ba 'karamin farin jini ya jawo wa babyn ba.

Anty kuwa har kuka tayi dan farin ciki take ta 'kira Abbah tayi masa albishir cewa an yiwa marigayi takwara, ta 'kira mahaifin ta ma ta gaya masa tana hawaye, shima Alhaji Muhammad albarka ya ta sanyawa Babyn masu yawa tare da yiwa mahaifin little Mahmud 'din fatan alkhairi mai d'orewa.

Irin 6arnar ku'din da Abbas yayi a wannan ranar abin ba'a cewa komai, dan wurin event 'din da akayi sunan idan kagani zaka saci ko wani 'kayataccen biki za'ayi a wurin, jakunkuna aka rin'ka rabawa mai 'dauke da turmin atampa mai kyan gaske, sannan ga wani jakan kuma shima mai photon baby shima ciki kayan ciye-ciye ne fal duk akayi ta rabawa mutane.
Duk wanda ya halacci taron sunan da farin ciki akan fuskarsa ya tafi domin kuwa ko ka'dan ba'a yi wani abu da zai sosa ran wani ko wata ba a wurin har taro ya watse.

Kyaututtuka kuwa da Teemah ta samu suma ba'a magana, cikin masu bada kyautar kuwa hadda Anty inda ta yiwa Baby da maman sa kaya masu yawan gaske kowa da nashi akwatin, Daddy ma ya aiko nashi kyautan da yake bai samu yazo ganin baby ba.

Ana kammala suna Abbas ya koma Rivers, haka ma su maman Amal da wasu mutanen na nesa duk kowa ya kama gaban sa suna masu farin cikin samun 'karuwar da Abbas 'din ya samu, inda aka bar Ummah da Anty har ma da Mummy suka cigaba da kulawa da mai jego har tsawon sati biyu sannan Anty ta koma Lagos da yake itama a halin yanzun abokiyar zaman ta nada tsohon ciki ne haihuwa yau ko gobe.

Mummy kam sai da ta kai 1month cif kafin ta koma Dubai, bayan tafiyar ta ne kuma Abbas yazo ya duba iyalan sa inda ya same su cikin 'koshin lafiya da kwanciyar hankali baby yayi 6ul-6ul a binshi, dan ma kullum sai sun tura masa photon shi a duk wankan da aka mishi su Hannah sai sunyi masa photo sun turawa Abbas wataran dukkan su sukeyi wataran kuwa Baby da mamar sa wataran kuma shi ka'dai.
Haka ma yana yawan 'kiran su video call a haska mishi babyn wataran ya ganshi yana bacci, wataran kuwa zai ganshi idanun sa biyu yana wasa da hannun sa abaki.
Abbas idan yaga hakan kuwa sai yace mata wato har yanzu tana masa rowan ko?"

Teemah sai tace " ah ah"
"Toh meyasa yake kai hannu baki?"
Ha'de goshi takeyi tace " Wasan shi fah kawai yake yi Yayah, kai dan baka ga yanda yake tsotseni bane shiyasa ai zaka ce wani ina masa rowa"

Sai cewa yayi " rama min yake yi ai kema kin tsotseni"
Teemah da sauri tace
" wallahi ba wani nan, to in dai haka ne ma bazan 'kara nuna maka shi ba"

Abbas ha'kuri ya bata yana dariya yace " to shikenan ya wuce, ni wasa nake miki maman Baby"

Lokacin da Abbas yazo ya gansu ba 'karamin farin ciki yayi ba har ji yake duk fa'din duniyan nan babu abinda ya kai masa farin ciki sama da su.
Wani kyau yaga Teemahn tayi masa da yake already Anty ta aiko an fara yi mata gyara ga haske datayi kamar ba mai jego ba, ko irin 'karnin nan da wasu masu jegon keyi sam bai ji a wurin ta ba illah 'kamshi daga ita har lil Mahmud 'din, da yake ma dama Teemah gwanar son 'kamshi ce kuma Anty tasa an kawo mata wasu ha'din su humra da sauran su masu bala'in 'kamshi shiyasa bata wasa da amfani dasu,
dayake kuwa bata wasa da kayan 'kamshi ciki da waje tana 'ko'karin kulawa sosai.

Aranar da yazo 'din kuwa Teemah da kayar ta sha, duk da tana yi masa tuni da cewa gidan Ummah ne ya bari fah kar tazo amma Abbas bai saurare ta ba yaci gaba da abinda yakeyi har sai daya gama rikita mata lissafi da salon wasannin sa cuz he really missed her a lot ji yake kamar ba zai sake iya 'daukan lokaci ba tare da ita ba, Teemah kuwa duk da ranta ba'a sake ba amma yanda yake sarrafatan yasa har ta fara 'daukan layi itama.

Kukan da Annur ya saka lokaci guda ne ya ceceta domin kuwa da sauri ta 'kwaci jikin ta tafi ta 'dauki 'danta ta rungume tana jijjiga shi.

Abbas kam tana barin jikin sa yayi baya ya kwanta tare da lumshe idanu a fili ya furta " Uwa! Uwa kenan!"
Wannan shine step na farko dake raba soyayyar mace ga mijinta domin matu'kar ta samu Baby to dole ne soyayyan babyn sai ya rinjayi na kowa ciki kuwa har da mijinta duk da dai baza'a ta bar son shi ta komawa danta ba amma na 'dan sai yayi rinjaye fiye da komai.

Abbas tashi yayi ya zauna yana kallon yanda take faman jijjiga shi da dukkan kulawa sai yaui mirmushi a hankali yace da ita " ki kaishi wurin Ummah mana please sai ki dawo "

Sai cewa tayi " ah ah Yayah barshi kawai ai zai yi shiru, Ummah ta gaji dayawa yau 'din duk a wurin ta ya wuni tun da rana"

"Hmm" kawai yace tare da 'ko'karin sau'kowa daga gadon, sai daya sau'ko da 'kafar sa 'kasa sannan yace " wato dai kince Annur ya fini ko?"

Da sauri ta furta " ah ah fa Yayah ai kaga d'azun kuka yake yi ne shiyasa"

Tana maganar tana tahowa inda yake ta zauna daga gefen sa tare da raba Annur 'din daga kafa'dar ta sai ta ri'ke shi a cinyar ta, Abbas ne ya 'dauke sa ya 'dagashi sama yana jijjiga shi yana murmushi, yaron ma kallon fuskarsa yake yi kamar an ce masa mahaifin sa ne.

Abbas yana murmushi yace " Ai dama na gaya miki, idan kin haihu nasan guduna zakiyi ki tattare duk ki komawa 'dan ki, kika 'ki yadda, ni kuwa nasan hakan dama sai ya faru gashi tun ba'aje ko'ina ba zance na ya tabbata gaskiya"

Murmushi tayi ta koma daga bayan sa ta rungume shi tare da fa'din " afuwan Yayah ba haka bane fa, banaso yayi kuka sosai ne har Ummah taji kuma tazo kaga da kunya sosai hakan ai"
Yana kallon babyn yace " to ni sai yaushe kenan za'a kulani... kin san fa gobe zan koma akwai aiki a gaba na, ko zamu je can 'daki na mu kwana?"

Kanta ta kawo gefen fuskar shi tace " da sauran lokaci fa Yayah,kuma ma ni gaskiya ina jin kunya ace daga zuwan ka har na bika 'dakin ka?"

'Dan b'ata rai Abbas yayi yace " bana son fi'ili ni, yau kika fara kwana acan 'din ne ko kuma yau ne kawai kunyar tazo miki?, ke 'din nan naga alama kin gama gaji dani ko? shikenan bakomai i know what to do kar ki damu"
Ya 'karashe maganar cikin basarwa kamar wani da gaske.

Ita kuwa jin yanayin da yayi maganar ne yasa ta sanyaya murya dan sai taji ba da'di cikin sanyin jiki tace " me zakayi Yayah?"
A tsare yace " amarya zanyi wacce bazata gaji dani ba"

Cike da firgici ta saki wuyan sa tare da juyawa ta koma ta jingina bayan ta da nashi tana kuka tace " an gaya maka ni 'din gajiya nayi da kai ne?"

Sai yace "ah to nima na sani ne? In kina son in yarda baki gaji dani ba then tashi mu tafi "

Kuka ta sanya mishi tana hahharba 'kafa tace " Ni dai kagaya min in kaine ka gaji dani...ai ni ban fa'da ba.

"Ban yi tunani akan hakan ba tukunna"
Ya fa'da cikin halin ko in kula.

Shiru tayi mata yi magana ba, sai ta cigaba da kukan ta, shi kam tashi yayi ya nufi 'kofa da babyn a hannun sa ba tare da ya sake kallon inda take ba.

Bai damu ba yasan ko badan bayn bama dole zata biyo shin idan ya tafi ko dan rigimar ta ma dan haka hankalinsa kwance ya fice a 'dakin.

Dan haushi ma ita yana fita sai ta ta shi kamar an tsikare ta ta shige bayi, bata san me ya kawo ta bayin ba dan haka sai ta watsa ruwa kawai ta fito, tana fitowa sai suka ci karo da Hannah da shigowan ta 'dakin kenan itama.

Kau da kai Teemah tayi tamkar Hannah ce tayi mata laifin sai ta nufi gaban mirror tana goge jikinta dake ji'ke da ruwa.

Hannah ta6e baki ganin bata ko kula ta ba itama bata damu ba dan tasan bazai wuci fushin Yayah bane take yi da har itama ta samu rabon ta.
Chapter 156 · 0% Book details