Sashe 58
Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Inkuwa matsala ce ta kunno mata kai bata san ta tsaya ta kaiwa Allah kukan ta ba, sai de Anty Chideh, zuciyar Anty gaba 'daya ya lalace da zuwa gurin bokaye da 'yan tsibbu harma tana ganin kamar matu'kar kana da 'yan canji toh baka da matsala da komai arayuwa inhar bokaye na existing toh damuwarta ka'dan ce, bata san tasaka Allah a lamarinta ba sai dai bokaye sosai tayi amanna dasu da ayyukansu.
Wata 'kawarta ce ta ziyarce ta asatin bikin tasame ta cikin yanayi na damuwa anan tabata shawaran cewa wai tasaki ranta kawai asha biki agama lafiya duk da baso takeyi ba ta 6oye hakan aranta tunda yanzu tarasa mafita inyaso bayan bikin sai ta shi tsaye ta nemi hanyar 6illewa tayi maganin su gaba 'daya.
Aranar da matar ta fa'di haka Anty kamar zata cinyeta 'danye dan masifah, da 'kyar matar tasamu ta fita ta wuce inda ta fito tana mai dana sanin kawo wannan shawaran datayin, Anty cewa take wai dan me matar zata ce haka, tana nufin ta tsaya kenan har sai angama bikin tana kallo, tana nufin idanu zata zuba kenan tana gani 'danta ya auri waccen _banza_ _dangin mayun_ , tajima tana kunfar baki baub wanda ya tankata agidan, dayake ma Abbah baya nan alokacin, house maid ne ka'dai da ita agidan, da 'kyar Anty tasamu ta lallashi zuciyarta tayi shiru.
Sai dai wani abu da batasani duk wannan dramar da Anty keyi akunnan Mahmud kaf aka yi su har sai da yaga matar tafita sannan shima yakoma 6angarensa, dama shigowar sa gidan kenan yanufo parlour daniyar duba ta, sai kuma yaji suna wannan maganar.
Hawaye yake ta faman sharewa na ba'kin ciki da takaicin halin da mahaifiyarsa ta cusa kanta 'karfi da yaji, har yaushe Anty zata gane ta dawo kan dai dai, har yaushe zakace a kullum sai kayi jayayya da lamarin ubangiji bayan shike da kai ba kai kake dashi ba.
Hawaye Mahmud yake sharewa yake wannan tunanin, babban dalilin dayasa tun farko yanuna baya son auren nan kenan, dan bazai iya tsayawa ya juri ganin Fatima awani yanayi ba, dan yasan Anty bazata ta6a saduda taso zuri'arsu ba, wannan wani irin rayuwa ne?, karo na barkatai kenan daya ke jin irin mugun alkaba'in data ke bin danginsa dashi, bayan yasan ako ina zasu tsaya ko suje ita ce abin zagi basu ba ga duk wanda yasan halinsu gaba 'daya.
Darajar haihuwa kawai Anty take ci amma wani lokaci Mahmud jiyake tamkar ya sha'keta saboda kawai ya huta da ganin ba'kin ciki awanan gidan.
Duk da lokuta da dama yana tanka mata akan abinda takeyi 'din sai de baya jan maganar sosai sai ya 'kyaleta haushi ma baya barin sa ya 'dau dogon lokaci tare da ita, haka kuma be fiya son suna jayayya da ita ba akan abu.
Bayan fitan matar ne kuma sai Anty ta zauna tayi tunani da kanta akan maganar matar sai kuma taga hakan kuma fah yafi mata, saboda bata san ta ina zata fara ba yanzu kam amma bayan angama biki hankalin munafukai ya kwanta asannan ne ita kuma zata bayyana nata haukan.
Sosai tayi na'am da wannan shawarar da zuciyarta ta batan, takuwa bishi dan Abbah da kansa yayi mamakin yanda farat 'daya Anty ta sau'ko ta zubda dukkan makamanta na ya'ki ta kama shirin biki babu 'ka'k'kautawa, yanda ta nuna tana son auren ma har in baka sani ba zakayi zaton ko tafi Abbah ma burin son ganin anyi auren angama.
Mahmud ne ka'dai yasan dalilinta shikuwa akullum addu'ah yake kar Allah yabata sa'an cutar da kowa, dan yasan ha'ki'ka sihiri gaskiya ne, tsafi gaskiyar mai shi.
*INAJIRAN GANIN MUHAWARAR KU READERS.........* 🤞🏻
👎🏻
_Comment_
_Vote_
_Share_
*Salmerh ce*😍
[10/2, 6:01 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕
By
*Salmerh MD*
Luv story😍
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*
_Dedicated_
_2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs._ 😍
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
_Happiness is not a goal, but a way of life._
🅿 *48*
Anty da kanta ta 'dauki driver suka je da Abbah gidan abokin Abban ta sake duba kayan da aka harha'da 'din, anan ta nuna cewa wasu abubuwan ai sunyi ka'dan ya kamata a'kara gaskiya saboda wannan bikin na _kai_ _da kai ne_ .
Speechless Abbah ya zauna yana kallon iyayin da Antyn keyi, take kuwa ta sake tura ku'di wa Hajiya Aisha tace a'karo kayan tanaso bikin 'danta ya kasance fitattace wanda za'a jima ana kwatancensa aduniya.
Hajiya Aisha kanta tayi mamakin yanda abin ya dawo, domin ba haka labari ya iso mata ba da farko ganin alokacin Abbahn shine tsaye akan komai, sosai tayi mamakin yanda Mum Mahmud 'din ta canja cikin 'kan'kanin lokaci, dan akwanakin baya ka'dan kafin zuwan yau akullum in suka yi duba da yadda Abbahn yayi ruwa ya kuma yi tsaki akan lamarin auren ba sa cewa komai sai dai suce Allah ya shiryi Mahaifiyar Mahmud 'din, Allah da ikon sa kuwa ashe shiriyar tata na kusa yanzu kam sai dai suce _"ALHAMDULILLAH"_ dan Mum Mahmud tabawa kowa mamaki alokacin da basu zata ba.
Aranar Anty bata koma gida ba kasuwa ta wuce tayi siyayyah sosai ma kanta, kaya tsadaddu ta siya ta bada 'dinkin express a inda tasan bazasu bata matsala ba, bata damu da tsadan 'dinkin ba ita damuwar ta tasamu adai dai lokacin da zata bu'kace su.
Ta dawo gida da sauran ragowar siyayyan data yi ni'ki-ni'ki a hannu.
Tun daga ranar Anty bata 'kara nutsuwa guri 'daya ba akullum tana hanyar fita, kasuwa da sauran abubuwa.
Haka duk mutanen data san zata gayyata duk ta gayyace su daga 6angarenta, 'kawayenta ma wasun sunyi mamakin canjuwarta ta amma koda sukayi magana sai tabisu da murmushi kawai batare da ta basu gamsashshiyar amsar da suke son ji ba.
Akwana biyu kacal da sa'k'kowar Antyn har gida yafara cika da wasu daga cikin 'yan uwa da abokan arzi'ki, hatta 'yan uwan Abbah da suke 'kauye 'kalilan daga cikin su sun samu sun zo hakama yan uwan Antyn.
Abin mamaki Anty duk ha'dasu tayi tai musu sau'kar bangirma, bata nuna mugun hali ba koka'dan bata bari sun samu 'kofara da zasu zageta da ita ba wanda hakan duk yana cikin target 'dinta ne nagaba.
Abbah da kansa ya nemawa Mahmud 'din gida flat house mai kyan gaske ya kuma zuba komai na bu'kata dai-dai da zamani sai 'dan abinda ba'a rasa ba, sai dai gidan babu nisa da gidan Abbah yake duk a area 'daya suke, da farko ma Anty takawo shawarar cewa wai ko a side 'din Mahmud za'a kawo amaryar, har Abbah yaso ya amince domin shi be kawo komai aransa ba game da canjawar Antyn zatonsa shiriyah ce kawai tazo mata daga Allah, amma da aka sanar da Mahmud shi kam sai cewa yayi a'a shi ba zai zauna a nan ba gaskiya sai de anemo wani guri daban, jin hakan yasa Abbah ya yarda da batun Mahmud 'din dan shi lalla6a shi yake yasamu yaga de an 'daura auren yasan daga lokacin komai zai wuche yazama tarihi.
Hakan yasa ya nema masa gidan da kansa ya biya ku'din lokacin ma Mahmud 'din be sani ba sai daga baya Abbah ya 'dauke shi ya kaishi gidan dan yaga yanayin gidan ko ya masa.
Shikanshi Mahmud ya yaba da tsarin gidan, dan shi dama yafison gida flat mutun yafi sakewa aciki sai dai kuma duk da haka sai da yayi wa Abbah complaint cewa wai ai sun yi kusa sosai shi fah bahaka yaso ba yafison yayi nisa dasu.
Ido Abbah ya kwalalo yana kallonsa da mamaki " Mahmud wai lafiyarka kuwa"?
Abbahn ya tambayeshi.
Baiyi magana ba illah 'dago hannunsa dayayi yana duba tsadaddiyar agogon dake 'daure atsintsiyar hannunsa.
Cigaba da magana Abbah yayi.
" Babana dan zakayi aure shine zaka guje mu gaba 'daya har baka son zama kusa damu?"
"Bahaka bane fah Abbah"!
Kwafah Abban yayi kana yace "toh menene?"
Shiru Mahmud 'din yasake yi ya sunkuyar da kansa 'kasa.
"Mahmud karfa laifina ni danasa ka kayi aure alokacin da baka shirya ba yashafi wata daban, inaso kaji tsoron Allah Mahmud adukkan lamuranka , wallahi idan ka kuskura ka cutar da yarinyar nan azaman aurenku da ita bazan ta6a yafe maka ba, sanin kanka ne ni...nine na nemi ha'din auren nan da kaina, kuma kasan inde har hakane kuwa bazai yiwu in zuba ido inga ancutar da ita inakallo ba batare da nayi magana ba, dole zan 'dauki mataki matu'kar hakan yafaru koda kuwa waye ne yata6ata"
Mahmud kansa ya 'dago ya kalli Abbahn nasa sannan yace
"Abbah nifah bani da burin 'kuntata wa ko cutar da Fatima arayuwata ko ka'dan............"!
" toh menene "?
Abbahn yatari maganar Mahmud 'din da sauri.
" Tausayinta nakeji ni Abbah "
" you see......,"Abbahn yafa'di tare da nuna Mahmud da yatsansa yakuma cigaba da fa'din.
"Ai shi yasa nake ce maka akullum kaji tsoron Allah, ina son ka sani cewa daga ranar da akace an 'daura maka aure toh nawi ne babba ya hau kanka bana wasa ba, daga ranar amanar Allah ta hau kanka duk abinda ka aikata kai da mahallici ne kar kayi zaton ko babu wanda yaganka, idan tausayin nata kakeji da gaske tun yanzu zakayi 'damar zama da ita idan kuwa tausayin ta dan zata auri wanda baya son aurent ne toh kasanar dani inji...."
Shiru Mahmud yayi yana sauraran maganganun Abbahn, shi kanshi yasan gaskiya Abbahn yake fa'da masa amma shi koka'dan abinda ke ransa beyi matching da na Abbahn ba, taya Abbah zaiyi tunanin shi zai cutar da Fatima dan kawai ansashi ya aureta bada son ranshi ba, ai ko da ace yana bacci ne aka tashe shi aka ce ga matarka an aura maka ita bazai cutar da ita ba ballantana kuma Teemah,! yasani daman idan yace be son zama guri 'daya dasu dole daga Abbahn har Anty sai sunyi tinani daban kowa da abinda zai zo cikin ransa,shi kuwa manufarsa tayin hakan daban ce da tasu.