← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 163

Sashe 52

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kuma ako wacce wayewar gari sai mahaifinta yayi mata nasiha sosai cikin natsuwa akan rayuwar duniya iya yanda yasan zata fahimceshi, ita kanta mahaifiyar tanma yanzu ba kamar da ba, dayake girma yakama ta itama kuma sai tayi sa'a yazo mata da shiriya, wani lokaci takanji tamkar tayi kuka dan ba'kin cikin halin da akace 'yarta nayi, domin tasan komai akace maryam 'din tayi laifinta ne komai da aka 'kirga awurinta ta koya sai dai yanzu tanaji tamkar maryam 'din tafi 'karfinta tama kusan nunka mugun halin data koya agurin mahaifiyarta 'din.

Itama sosai take zaunar da Antyn duk dama bata fiya sauraranta ba domin ba 'karamin raina mahaifiyartan tayi ba, gara ma shi Alhaji tana 'dan jin shakkan shi hakan yasa dole take zama ta saurare shi ko bata so ko da ba zata 'dauki abinda yake fa'da 'din ba amma dai zata zauna dolenta, tsawon lokaci tana sauraran karatun nasa batare da ta 'dauki koda abu guda daga ciki ba.

Abinda basu sani ba ayanzun shine, Anty bata da burin daya wuche taji ance babu wannan maganar auren.

Tsana mafi girma take ji azuciyarta game da auren, tana jin koda me nene ze faru sai ta ga ta hana wannan auran faruwa.

Duk da yawan nasihar da Alhaji muhammad ke mata amma dai dai da rana 'daya tak sam
'Kudurin Anty be canja ba daga cikin 'kudurorinta na baya sai ma abinda ya 'karu domin 'karan tan da Abbah ya kawo bai gyara komai ba sai ma lalata wa dayayi.

*sharhi nake bu'kata ga duk wanda yakaranta* 🤞🏻

*Salmerh* 😍
[10/2, 6:01 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

There is no any slave of Allahwho commits a sin, then he perfects his ablution, stand b4 Allahu subhanahu wata'ala to pray 2raka'ah of prayer, then seeks Allah's 4giveness, expect that Allah will 4give him.
Abu Dawud,2/86, At-tirmizi 2/257.

🅿 *44*

Abu 'daya ke cin zuciyar Anty akoda yaushe in ta tuna shi kuma shine yafi sata damuwa fiye ma da batun auren Mahmud 'din haushin hakan kuma shike 'kara sata takae jin haushin kowa,dan tasan batun aure me sau'ki ne matu'kar tasamu ta ziyarchi gidan _'dan_ _Oga_ (boka) tasan matu'kar ta samu ta ha'du da shi to bata da sauran damuwa.

Amma prolem 'dine taya zata ha'du dashi?
Mtsalar ka'dai dake cinta kenan har azuciyarta, ita aganinta maganar auren nan dasuke ta wani 6ata bakinsu akai arana 'daya zata iya warware shi kaf kuma waru kenan, da ace ta 'dau mataki toh da dolen kowa ya ha'kura da maganar auren amma kuma sai tayi rashin sa'a 'kawarta Anty Chideh ta'ki sam ta taimaka mata akan lamarin, sai ma wasu banzayen sharu'd'da datake faman gindaya akai kafin wai tayi mata jagora zuwa wajen _'dan Ogahn_ itakuwa sam bazata iya abinda Anty chiden take 'ko'karin taga ta aikata ba, akullum tunaninta yanda zata samo mafita ne amma taras,shi 'din nan dai tafi yadda da aikinsa sai dai ta rasa yadda zatayi tunda 'kawarta ta'ki kaita , tambaya kuwa babu irin wanda batayi ba amma tarasa wanda yasan shima balle 'kauyen dayake rayuwa.
Idan ta matsa sai akwatanta mata wani wuri daban , da zumu'din ta take zuwa amma kamar ha'din baki kalaman su iri 'daya ne.

Akwai wani guri da suka je da wata 'kawarta, bokan ce musu yayi wannan auren babu fashi sai anyi, the same abinda wata matsafiya ta gaya musu da suka je da mahaifiyar Munira harma da ita kanta Muniran.
Anty kamar zatayi hauka dataji abinda suke ta faman sanar dasu.

Inta matsa wai ko za'a samu wata hanya da za'a awarware maganar takance ita ko nawa ne she is ready to pay it indai auran zai fasu.
Akwai wani bokan dayace mata ehh akwai dama za'a iya warware maganar amma ba ku'di zata biya ba zata tattaro ta dawo gurin na tsawon wata guda akwai aikin daza'a yi.

Sam sai taji zuciyarta be yi na'am da wannan batun ba, auren da ake 'ko'arin yinsa nanda sati uku masu zuwa taya ya itakuma za'a ce tayi 1month tare dasu da yaushe kenan za'a warware maganar, bayan an 'daura kokuwa?
Bata manta labarin da Chide 'kawarta ta bata ba na wani daya ta6a yi mata aiki tace satin ta guda agurinshi yana faman sex da ita ba 'ka'k'kautawa sai cewa yayi wai suna 'diban abinda zasu ha'da jinin tane da mijin nata alokacin, itakuwa dayake ta 'kagu taga ta malleka shi sai bata damu ba ta daure tayi ta jure wahalhalun da bokan ke bata, tace har tacika satin ana abu 'daya, tace data koma gida sai da tayi jinya kusan na. 11days kafin nan ta warware, atlast ma kuma bata ga komai ya canja ba babi wani abinda ya faru sai da ta je gurin wani daban kafin nan tayi sa'a aikin ta yaci.

Tace ballantana ita da ba mallaka ko juyo da hankalin wani take bu'kata ba ayanzun burinta ta warware maganar ne toh dan me zata tattaro ta dawo gurin boka har na tsawon wata guda, yana nufin ita ma so yake yayi mata irin na 'kawarta kenan Allah ya kiyaye tace afili, _angudu ba'a_ _tsira ba kenan_ .

'Kin amincewa tayi kawai tayi tafiyarta.

Dama agurin Anty chiden take da hope 'din samun ingantaccen wurin da tasan za'a share mata hawaye domin itace tasan gurare da dama acikin garin na lagos, amma kuma shara'din Anty Chidehn tazo mata dashi sai ya girmi tunanin ta, sam bazata iya aikata abinda 'kawartan ta ke son ta aikata ba, how on earth ace tayi irin wannan abin....

Koda ta koma gida (Lagos) ma cigaba tayi da neman mafita amma tarasa ta ina zata fara, kullum hankalinta atashe yake, gaba 'dayan su agidan ma sai suka rasa gane kanta, Abbah kuwa ko kallo ma bata ishe shi ba, kamar yadda itanma bai isheta kallo ba , zaman gidan tamkar wasu abokan gaba aka tara aciki haka suke yinta kowa harkar dake gabansa kawai yakeyi, Anty ta 'debi abin ne da zafi 'karfi dayaji take so taga ta hana abinda Allah bai haramta ba, duk kuwa abinda take yi shiga da fitan ta da wasu abubuwan Abbah kallon ta kawai yakeyi yana mamakin taurin kanta, zai yanzu yake 'kara jaddada wa kansa rashin sa'ar mata yayi, ha'ki'ka shi kan baiyi sa'a ta wannan 6angaren ba, bayaga haka kan be sa me zai ce ba, Alhaji Muhammad mutumin kirki ne dashi kanshi zai iya bada shaida akan haka, sannan yana da tabbacin Alhaji yaja wa Maryam (Anty) kunne akan haka harma ya ha'da da tabbatar mata cewa matu'kar bata kar6i wannan auren ba toh babu ita babu shi, lokacin da Alhaji Muhammad yayi wannan maganar shikanshi Abbah bai ji da'di domin bazai so ace iyalinsa ta samu matsala da mahaifinta ta dalilinsa ba, yaso yayi magana tun awancan lokacin amma sai yayi tunanin wai ko zata yiwa kanta fa'da da wannan kalmar ta saduda ta barwa Allah ikonsa amma sam sa6anin haka yagani wanda be sani bama sai yace acan ta 'karo taurin kan da taje, ha'kika duk wanda yayi nisa da wuya yake jin 'kira koda me 'kiran ya hau kan babban tsauni ne,sai dai kawai Allah ya shiryamu gaba 'daya.(yasa mu gane gaskiya gaskiyace kuma yabamu ikon yin aikin da ita).

Shima Abbah babu abinda yasa agaba ayanzu illah yaga anyi auren nan angama shi lafiya ko hankalin kowa zai kwanta.

Abbah da kanshi yasa Mahmud agaba suka je gurin wata matar abokinsa suka yi maganar kayan lefe afa'darsa tunda mata suka suka san kayan mata 'yan uwansu, transfern ku'di kawai yayi mata masu yawan gaske yace ta ha'da masa lefe nagani afa'da yace baya san algus ko ka'dan aciki saboda yarinyar ma 'yarsa ce ahaka kawai ma zai iya yi mata ballan tana kuma ace aure ne sanadi kuma auren 'dan cikinsa zata yi.

Dariya sukayi masa sannan matar ta bashi tabbacin bashi da matsala da wannan ya kwantar da hankalinsa komai zai yi kamar yanda yake bu'kata, dayake daman tana sarin kaya tace wannan satin zata yi ordern su sauran kuma dole sai anan Nigeria za'a siya.

Godiya yayi mata sosai ,sai abokin nasa yace " ban ta6a jin inda mahaifin ango yayi kane-kane akan kayan lefe ba...............

"Akaina zaka fara gani Alhaji"
Abbah ya karasa maganar yana dariya.

"Asalin tuwona mai na 'din kenan Alai yusuf lallai zaka kafa tarihi a 'kasar nan".

"Kwarai ma kuwa ".
Abbah ya sake bashi amsa still suna dariya.

Mahmud kam tunda suka zo daga gaisuwa be sakeyin wata magana ba sai kawai ya ciro wayarsa yana danne-danne dayaga sun gama maganar sun koma hira suna dariya sai kawai yatashi ya basu wuri, binsa sukayi da kallo har ya 'karasa barin 'dakin.

Alhajin ne ya tambayi Abbah abinda ke damunsa shikuwa Abbah be '6oye masa ba yabashi labarin yanda batun auren ya kansance ya 'karasa da fa'din fushin Mahmud 'din na rashin son yin aure yanzu ne wai shi ba yanzu zai yi aure ba sai nan gaba , laifina anan shine nace yanzu zaiyi aure shikuma ba haka ya tsara wa rayuwarsa ba shine fushin."

"Allah sarki yaro kenan, inbanda abinsa ai aure bashi da lokaci"
Inji Alhajin.

" rabu dashi bazai gane hakan ba ai, amma nasan wataran dakansa zai gode min idan yafahimci banyi hakan dan na ba'kanta masa face gata da nake 'ko'karin yi masa".

Inji matar Alhajin
"Hakane kam".

Ajiyar zuciya Abbah yayi sannan yace
" Allah shi kyauta"
Tare da mi'kewa tsaye, Alhajin ma sai ya mike yamasa rakiya har inda sukayi parking motar su .

Mahmud na hango su ya tada motar kmar daman jira yake yaga fitowarsun.

Ahanya ne Mahmud yake tambayar Abbah wai kayan miye zaa siyo?

Abbah ce mishi yayi "kayan auren kane!"

"Toh ni Abbah ya baka siya min ba sai ita ka'dai"

"Abu mai sau'ki ne ai wannan babana idan kanaso zan siya maka kwantar da hankalinka."

Shiru Mahmud yayi yaci gaba da tu'kinsa har suka isa gida bai sake magana ba.
Chapter 52 · 0% Book details