← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 140 OF 163

Sashe 140

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Leesah tayi matukar mamaki sosai dan koka'dan data gansu bata ji ajikinta cewa matarsa bace dukkuwa da cewa sosai taga dacewar su ganin yanda ta ke zuba masa shagwa6a son ranta kuma yana biyeta kamar yarinya 'karama sai ta bari akan sister take awurinsa.

Yanzun kuwa dataji cewa matarsa ce Fateemahn sai ma taji ya 'kara birgeta sosai musamman idan ta tuno yanda Teemah ke yi masa sakalci da shagwa6a kuma ya kar6a mata, bakowa ke iya kar6an hakan daga wurin mace ba face cikakken namiji wanda ya san kansa yasan darajar matarsa.

Amma bata nuna hakan ya dame ta ba sai ma ta sanya musu albarka tare da basu tabbacin kawo musu ziyara idan ta samu lokaci kuma in sun bata damar yin hakan.

Tana yawan k'iran Abbas su gaisa daga baya ma har da numbern Teemah take 'kira, dan ranar da kanta tace Teemah ta k'irata da numbern ta.

Acikin kwanakin da basufi biyar ba sukayi sabo da juna dan Teemah yanzun tafahimci abota ce kawai bakomai ba a tsakanin su, duk da shi'din na yawan tsokananta game da Leesah amma sam bata wani reaction sai dai tayi murmushi.

Leesah ta 'dan girmi Teemah ka'dan dan ita 25-6yrs take yayin da Teemah har yanzu take da 19yrs.
Amma duk da haka bai sa Leesah 'kiranta da sunan ta ba dan soyayyar da tafara yi masan sai ya juye ya dawo ta abota da 'yan uwantaka, jin Abbas take yi tamkar d'an wanta na jini.

Takance dashi *bross* Teemah kuwa *sister* take k'iranta.
yayin da Teemah ke k'iranta da *Anty Leesah*, har labarin Hannah take bata idan suna waya itama Leesah na bata labarin wanta da yanzu ma baya k'asar yana waje.

*Duk naji za6in ku yanda kowa yafa'di ra'ayinsa game da ranar da za'ana update kuma na fahimce ku gaba 'daya, duk da cewa ra'ayoyi bai zo 'daya ba amma ni na* *yanke cewa zamu rin'ka posting CAPTAIN ABBAS 2-2 days saboda ganin hakan yafi ni awurina, kuma ma zan fiyi anutse, sannan kuma zakufi* *samu dayawa* .

*Wa'danda suka ce aringa yi kullun 'din nan kuyi ha'kuri dan Allah ba wai na'ki taku bane amma kunsan komai cikin natsuwa yafi.* 🤞🏻

👎🏻😰
*Sannan kuyi ha'kuri babu wuta ne a garinmu shiyasa kk jini shiru kwana 2....... kuma jiya nayi rubutu na dayawa har saura nayi editing ma kawai sai whattsap 'dina yayi clearing komai narasa chats gaba 'daya, wa'danda suka min magana basu ga amsa ta ba suyi min ha'kuri dan Allah domin bangani bane shiyasa*

_Comment_
_Vote_
_Share_

*Salmerh ce*😍
[10/13, 1:58 AM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_This page is specially dedicated_
_to my hard&die fans 👇🏼
*Mar-yerm, Mum Haidar, 🌹Tamama🌹, Mom inteesar(mai ku6ewa), Ummin Diga, Faateemaah🥰, Ummy Aliyuu, Nanerh, Hassan Adam Kagadama ('dan Nigeria* 🇳🇬 *)Fatee Duguri, Nusaibateey, Maamah love, Khadija Hussain,i Fiddausi, Bebin soo, 💅🏻Zulaihart💅🏻,Ayshah🍃 Humaira,* *mj, mom Ansar, A.S, Mum Khady, Maman Muhammad, Mumyn Minal, Aneesa, Zb, Teemah baby, Fatima2(, AMINA, Maman Arfat, Maman* *Nawwara, 💋Sheerdert💋, Khadeja Abdulhameed, Baby on top, Ummu Zahra, AbdullahiZainab, Maman Zahra, Oum Farhan, Hauwa Gulumbe, HafsatJabyr, Asma'u Usman, Maryam Wakili, Mommy F's, Zainab Bala Abubakar..........anya zan iya kuwa?🤔Allah yawa ne da ku sosai, ha'ki'ka 'kauna ta da ku ta musamman ce, daku* *dama wa'danda ban fa'de su anan ba inaso kusani cewa ur COMMENTS nd* *DU'AHS na matu'kar faranta raina, Allahu ya bar* ' *kauna ya kareku ya haskaka rayuwar ku a ko'ina kufi 'karfin ma'kiyanku......INA MATU'KAR YIN KU MUTANE NAH...........IRIN UN LIMITED 'DIN* *NAN🤞🏻.* 😍

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

_We are all here for some special reason......Stop being a prisoner of ur past..... Become d architect of ur future_ .

🅿 *89*

Anty Leesah nada mutunci sosai dan ko ka'dan bata sanyawa ranta 'kiyayyar Teemah ba sai ma 'kara janta a jiki da tayi tana kula da dukkan al'amuran ta tamkar sistern ta na jini, Abbas kansa najin da'din yanda take bi da Teemahn sosai hakan ya 'kara mata fada awajen sa kuma dalilin kenan daya sanya shima yake girmama zumuncin dake tsakanin nasu.

*****
Satin sa biyu da dawowa Abuja sai ya 'kira layin Umar sukayi magana akan zuwa katsina da ke gabansu, har suka shirya batun tafiyar ma bai sanar da Teemah ba Coz da farko be yi niyyan tafiya da ita ba amma da kansa kuma daga baya sai yaga dacewar zuwa da itan ko dan cika niyyar marigayi Mahmud ma tunda da ita uayi planning zuwa kafin rasuwar sa.

Duk da haka sai ana jibi tafiyar sannan ya sanar da ita, Kwana biyu kacal yace zasu yi acan dan haka bata sha wani wahalar shirya musu kaya ba da kanta ta za6a musu harda shi ma kayan da zai yi amfani dasu har su dawo gida.

Washe gari gidan Ummah suka wuce inda suka yi mata sallamar tafiyar ta su da yamman ramar Umar kuma ya iso Abuja inda yazo wa Teemah da tsarabar sirri daga Maman Amal, Abbas binta da idanu ya rin'ka yi Teemah kam idan sun ha'da ido sai ta murgu'da baki ta yi kamar bada shi take ba, duk yana kula da ita, kuma itan ma tasan kallon na menene shiyasa take ta kakkauda kanta gefe.

Kamar jira suke Umar ya wuce sai Abbas yace dole sai ta nuna masa abin yagani dan bai yadda da wannan sabon salon 'kawancen ba, haka ya dage akan shi bai yadda ba sai yaga menene abin da aka kawo mata.

Teemah kam tashi tayi da sauri ta koma daga bayan kujera tare da yin baya da hannun ta ta 6oye laidan sai 2seatern dake parlourn yazama atsakanin su, tana tsayen itama tace ai kuwa ba zai gani ba ai sirri ne aka kawo mata kuma babu kyau gulma da sa ido"

Abbas najin tace gulma da sa idon nan sai ya zabura da sauri zai kamo ta ai kuwa tayi 'dakin ta da gudun gaske tana dariya ta shike dayake shine akusa da ita bai kamata ba kuwa, tana shiga sai ta datse 'kofan harda murd'a lock sanna tafara maida numfashi sama-sama.

Sai data gama sau'ke numfashin kafin ta tashi taje ta 6oye shi inda ba zai ma gani ba koda kuwa ta bashi garin nemowa.

Soasai taji 'kishin ruwa na damunta
dan haka bata 6ata lokqci ba ta sake bu'de 'kofan ta fito tazo tasame shi zaune akan kujera ya na'de 'kafafu.

Jikinsa ta fa'da tare da furta "ruwa"!
Baiyi wani musu ba ya tashi da kansa bayan ya gyara da kyau yaje fridge ya 'dauko mata ruwan da kofi.

Koda tasha 'din ma sai data 'dan huta kafin taji ta dawo normal dan tsokana sai ta kalli idanunsa tayi murmushi, shims sai yace "ina kika 6oye min wato kin yadda da wasu fiye da ni ko Zahra?"
Sai tace
"Ayyah Yayah bafa haka bane kawai dai tace ne fah kar kowa yagani"

Gira 'daya ya 'dage yace "Shine harda ni? Kuma kika yadda?

"Ai bakomai idan nagani ai kamar ka gani ne ko?

Cewa yayi " ni fah kin san ba na son shirgin 'yan Lagos 'din nan kin manta abinda sukayi miki ko?

Ahankali tace "ah ah ban manta ba ai wannan 'din daban ne"

"Nine dai ban yadda nuna min inga ko menene"

Rungumarshi tayi ajikinta tana murmushi ta 'dage masa kafa'da tare da fa'din bazai gani ba tunda ya koyi gulma shima"

Yanda yaga ta dage akan bazai gani 'din ba yasa dole ya ha'kura da ganin.
Amma da shara'din idan tayi amfani da wani abin dake ciki har ya samu nasaran cutar da ita toh yayi mata al'kawarin har ita kanta bazata tsallake wa hukuncin sa ba" Teeemah tace " ehh ta amince"
akan haka maganar ta 'kare.

The next day suka 'dunguma garin Katsina bisa jagorancin Umar dayake shine ka'dai yasan asalin inda suka dosa.
Umar sosai yaji da'din yanda Abbas ya cire lokaci musamman dan ganin ya cika wa marigayi Mahmud burin sa da kafin cikarta Allah ubangiji ya kar6i ransa, yasan ko ba komai hakan ma na 'daya daga cikin halin girma, sosai Abbas ya birge Umar, baran ma daya ga yanda ya ri'ke Fateemah da kyau yake kula da ita sai yaji ya 'kara birgeshi, saboda yasan banda wahala da rashin kwanciyar hankali babu abinda ta tsinta agidan auren ta da Mahmud amma Allah cikin ikon sa sai ya musanya mata da wani mai so da tausayin ta wanda duk a yanayin su ya fahimci haka.

Koda suka isa Katsinan kuwa Umar mamaki yayi na yanda ska tarar da gidan Innah gaba 'daya ya canza dan yasan shi ada, sa6anin su Abbas kuwa da basu san komai ba nasu sai dai ido ne kawai.

Duk kuwa da cewa gyaran ba wani na kirki bane amma cikin rufin asiri akayi komai kuma bu'kata ta biya, gidan Innah ya canza sosai haka ma yaran ta dan wannan dattin nasu ya 'dan ragu ba kamar da ba, duk dama zuwa yanzun sun 'dan fara shiga wani hali saboda 'karewar ku'din da Marigayi Mahmud ya bar musu danma sunan da kayan abinci dai-dai gwargwado shiyasa ma abin yazo musu da 'dan sau'ki sai wahalar ta 'dan 6oye kanta.

Umar ne yayi musu bayanin rasuwar Mahmud 'din gaba 'daya a takaice inda Innah ta ringa kuka da hawaye tana binsa da kyakykyawar addu'ah.

Hatta Rabi'u sai da ya zubda hawaye duk dama ba wai yau ne ya fara jin labarin ba amma irin karamcin Mahmud 'din yasa sam bai mantawa dashi yake kuma jin alhinin rashin sa sosai.

Teeemah ma sai da ta tuna da shi itama ta taya su hawayen rashin nasa da suke yi.
Kunyar matar ka'dai ya hana Abbas rungumo matar sa ya share mata hawayen amma duk da haka bai iya jura ba sai da ya maida hankalinsa gaba 'daya kanta suna ha'da ido sai ya yi mata alamar bai son kukan ta daina.

A hankali ta yi 'kasa da idanu batare da ta daina hawayen ba dan ko tace hawayen ya tsaya ma hakan ba zai samu ba.
Chapter 140 · 0% Book details