← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 163

Sashe 44

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga nan tabar wurin messages 'din ta koma taga tarin missed calls 'din data tara duk daga yayanta Mahmud.

Data ta bud'e tashiga whattsap anan ma takuma cin karo da sa'konni da dama na groups dakuma na wasu contact d'inta ciki kuwa harda na Mahmud inda yake mata good wishes na gama makarantar ta, cikin sa'a kuwa sai taga yana online hakan yasa ta rubuta
" Yayah"
Tayi sending.

" Na'am, lil sis yau me nayi ne haka" ?

Tasan wannan tambayar duk bazai wuce akan tarin missed calls d'in data gani yayi mata bane hakan yasa ta bashi ha'kuri tare da yi masa bayanin rashin fita da wayar da bata yi ba ne shiyasa.

Tace sai yanzu ne dawowarta taga missd calls d'in kuma ciwon kai yasata agaba.

" eyyah sorry lil sis zakiji sau'ki kinji, ina kinsha Magani?"

" a'a mummy ta aika asiya min yanzu"

Yace
" wish u quick recovery owk".

Itakuma ta rubuta masa " Thanks".

Sannan ta 'kara rubuta " Yayah "

Shikuma yace
" Na'am 'kanwa".!

" Yah Abbas yazo yau "!

" Haba ai be gaya min zaizo ba, amma gaskiya ya kyauta sosai , ki gaishe min dashi before muyi waya".

" Ai ya riga yakoma ma "

" Ok ba matsala kinsan yanayin aikinsa ai sai a hankali".

Bata 'kara yin wata magana ba bacci ya 'dauke ta da wayar akan cikin ta, koda mummy ta zo kawo mata maganin ma tun a'kofa data hango ta tana bacci sai ta juya kawai batare da ta shigo ba.

Shima Mahmud 'din daya ga bata 'kara magana ba sai ya 'kyaleta azaton shi ko ciwon kan ne ya matsa mata, shiyasa ya barta yace ta huta .

*****
Washe gari bayan ta idar da sallahn asubah tayi addu'o'inta kamar yadda tasaba yi kullun, sai data karanto adduar safiya da maraice ta shafa sannan sai tasa hannu ta jawo wannan kwalin da nufin ganin abinda ke ciki.

Ledan dake jikin ta yage sannan tasa hannu ta bud'e cikin kwalin.

Hannu tasa ta ciro jakan dake sama aciki ta ajiye ta 'kara ciro wani tagani.

Dogin riguna ne aciki masu kyaun gaske irin 'yan italy 'din nan kusan kala hud'u wanda idan ka saka ajikinka ako'ina kowa yasan sunsha kud'i ba 'karya, sai takalma suma masu tsada guda biyu abinda kad'ai ke cikin kwalin kenan.

Ita kanta sun mata kyau sosai yayin da 'daya daga cikinsu yafi 'daukan hankalinta mai kalan coffee.

Tashi tayi ta tsaya sai ta d'aga rigar ajikin ta tana kallo kamar mai gwada tsayi nta da rigar.

Adaidai lokacin kuma sai ga mummy ta turo 'kofarta tare da yin sallama wanda tazo ne da niyyan ji da ganin jikin Teemahn ko yaya ta kwana.

Kafin Teemah ta amsa sallamar sai mummy a firgice tace.

" ke wannan fah daga ina kika samu".

"Anan na nagani nima "
tafa'da tare da nuna gurbin da ta ga kwalin a ajiye.

Da mamaki mummyn takalleta tace
"anan kuma Fateemah".

Sai Teemah ta d'aga kai alamar " ehh"

" toh wah ya ajiye"?
Inji mummyn

Sai Teemah ta jefa mata tambaya inda tace " mummy bake kika siya min bane"?.

Tayi maganar tana kallon fuskar mummyn nata.

Mummy bata kulata ba sai tasa hannu ta kar6i rigar dake hannun Teeman aranta take wassafa kyau da tsaruwar rigar, sannan kuma ga uban kud'i, idan batayi kuskure ba tace rigar tana kaiwa kusan Eighting thousand Naira (18000) akasuwa, zama tayi abakin gadon Teemahn tare da jawo kwalin ta firfito da ragowar kayan dake ciki.

" yah salaam "
Tace aranta
" toh daga ina haka"

Ta sake tambayar kanta.

tace kuma ba daddyn Teemah bane ya kawo domin shi tasan yariga yabata gift 'dinta tun lokacin daya dawo daga tafiya and she believe that matu'kar zaiyi abu toh sai ya sanar da ita.!

" toh wannan daga ina haka!".?

Zuwa Teemah tayi ta zauna akusa da mummyn saboda yanayin dataga mummyn tashiga itama kuma sai alokacin tunani wanda ya kawo kayan ya shige ta musamman data ga duk hankalin mahaifiyarta ya tashi da ganin kayan ,sai ta dafa ta tace " mummy wani abu ne?".

" a 'a ina tunanin ta inda kayan nan suka fito ne"!

Daga nan mummy n tasake yin shiru tana kallon Teemahn badan tariga tasan halin 'yarta ta ba da sai tace tasan daga inda kayan suke tunda har acikin 'dakinta aka gani, amma kuma ahalayyar Teemah babu 'karya sai dai uban rashin ji da taurin kai sannan bata 6oye gaskiyarta ko kad'an ita.

_ABBAS_ shine ya fad'o ran mummy atake wanda hakan yasanya ta sauke sassanyar ajiyar zuciya tare da hamdala acikin zuciyarta.

Domin da farko har kanta yafara caji hankalinta ya d'an soma tashi narashin sanin asalin takamamman inda kayan suka fito.

Amma tuno cewa Abbas yazo ayau d'in duk sai wad'ancan abubuwan suka kau, mussamman data tuno lokacin data ganshi ze shiga parlour hannunsa rik'e da wani abu wanda tun alokacin bata 'kara tunowa da neman sanin miye abin ba, zaton ta jakar kayansa ne tagani ahannun nasa , sai kuma yanzu tafahimci menene abin tunda shi da be zo zama ba ina yaga ta shigowa da jaka har gida.

Murmushi tayi abayyane data tuno halayyar Abbas d'in shi sam baya son inzaiyi abu wani yasani komiye dalili oho, sai dai hakan da yakeyi d'in ita kanta yana birgeta domin halayya ce tagari ga dukkan wani musulmi abin kwaikwayo ga kowa.

Kallon Teemah tayi da tun 'dazu ta zuba mata idanu tun sanda tafara murmushin nan tace
" inajin Abbas ne yakawo dan naganshi da kaya 'dazu dayazo lokacin hankalina nakan aiki".

Sake 'daga rigunan mummy tayi tare da jujjuya takalman ahannunta tace " size 'dinki ne kuwa beyi kuskure ba".

Kar6an takalmin Teemah tayi tana 'ko'karin gwadawa a'kafarta.

Yayinda mummy taringa sanya masa albarka, fatan alkhairi, da kuma fatan gamawa da duniya lafiya da ganin haske adukkan al'amuransa.

Acikin zuciya Teemah taringa amsawa da Ameen.

Sai mummy tace
" ki ajiye bari anjima anunawa daddynki shima yagani " .

Da
" toh "
Teemah ta amsawa mummyn, kuma sai asannan ne mummyn tace " ya ciwon kan naki "

Dariya Teemah tayi tace " sai yanzu kika tuna da ni ko mummy".

" 'kaniyarki wannan 'dinma ai duk saboda kene kikaga nashiga tunani."......

Daganan suka kwashe da dariyar dukkansu har mummyn gaba 'daya.

*****
Kwana biyar bayan graduation d'in Abbah ya sau'ka a damaturu..............

_Comment,vote_
_and share_ 🤞🏻

*Salmerhn ku ce* 😍
[10/2, 6:00 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* 😍

*Salmerh nayi muku* *fatan alkhairi*

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

Don’t be ashamed to be different........ Be proud that Almighty Allah made you like no one else.

🅿 *38*

Mummy na can uwar 'dakinta taga daddy ya 'kirata awaya akan wai tafito parlour yanzu yanzun nan.

" lafiya kuwa?"

Ta tambaye shi

Sai yace " lafiyar kenan Khadeeja".

yana gama fad'an haka ya yanke 'kiran sai kwai ta tashi ta fito parlourn domin ams a 'kiran Daddyn.

Sai dai tun kafin ta 'karaso tafara jin zuciyarta na tsinkewa, bata san dalili ba amma sai dole hakan yasa yanayin saurinta ya ragu ba kamar yadda ta farao tafiyan da farko ba.

Koda ta iso parloun ma ciki-ciki tayi sallama bata damu da ko daddyn yaji ko be ji ba domin damuwar luguden da zuciyarta keyi ne ka'dai aganbanta awannan lokacin.

Bata ankara da ko mutune nawa bane zaune a d'akin ba har se da ta iso sannan ta 'daga kai a'ko'karinta na neman inda ya yadace tazauna sai kawai idanunta suka hango mata yah yusuf zaune agefen daddy.

Yatsa ta 'daga tare da fa'dan sunan shi cikin tsananin mamaki

" Yah........... Yusuf.........kaine ko............ko.........i"adanuna ne...?

Murmushi yayi mata sannan yace " Nine nan ba idanunki bane Khadija 'Karaso ki zauna".

Ya 'karasa maganar tare da nuna mata wajen zama.

Bata 'karaso inda yake 'din ba sai zune jagwab a inda take tsayen tama kallon shi yayinda idanunta suka da'de da fara zubda ruwan hawaye.....

" Ashe zan sake ganin 'dan uwana aduniya........ashe da rabon in sake ganin ka, Yah Yusuf me yasa ka manta dani, kamanta da koni wacece agareka...ka manta da............

Daidai nan daddy ya dakatar da ita da fad'in " Khadija " !

Da 'karfi yayi maganar wanda yasa dan dolenta tayi shiru sai dai hawayenta dasuka kasa tsayuwa.

Teema ce ta taho da niytan zuwa gurin mummyn ta ta sai ta tarar dasu a parlour dukkansu shiru sai mummynta dake zaune a'kasa kamar me neman gafara tana kuma share hawaye.

A sukwane ta iso gurin mummyn ta zauna itama kusa da ita tafara tayata goge hawayen batayi magana ba amma ga dukkan alamu kukan take shirinyi itama.

Daddy da yaga haka sai ya 'kirata akan tazo wurinshi sai kawai ta kalleshi batare da tayi niyyan tashi daga jikin mummyn ba tace

" daddy me yasami mummy"?

Rashin sanin abin da zai ce da ita yasa shi yin shiru " toh me ze mata yasaka mahaifiyarta kuka?".

Juyawa yayi ya kalli Yah yusuf instead of ya bata amsar tambayar da tayi masa, cikin sa'a kuma daidai nan mummy ta dakatar da kukanta ta kamo Teemah, ta rungumeta ajikinta, tana 'dan bubbuga bayanta.

Daddy da yah yusuf ne suka ha'da baki wajen bawa mummy ha'kuri.

Sai tace bakomai ai ya wuce tunda taganshi yanzu, tace abinda yasa ma har yaga tana kukan bakonai ba ne face tunawa da tayi da Mahaifansu, ta tuna irin gwagwarmayan da mahaifinsu yasha arayuwa 'karshe kuma Allah ya kar6i abinsa, daga baya kuma mahaifiyarsu, wacce tayi iyah 'ko'karin ta wajen ganin ta kula da rayuwarsu yanda ya kama ta bayan ba ran mahaifinsu amma ita ma Allah ya kar6i ranta tun ba aje ko'ina ba.

Tace " Iyayenmu sun barmu mu biyu da tabbacin zamu had'e kanmu mu kala da kan mu da rayuwarmu, amma hakan sai ya kasa faruwa muka kasa yiwa kanmu wannan gatan, nasan da mahaifan mu na raye sai sunyi Allah wadai da faruwar wannan al'amarin"....
Chapter 44 · 0% Book details