← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 162 OF 163

Sashe 162

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lakatan hancin ta yayi da hannun sa yace " zan kamaki ai" sannan ya bar jikin ta ya sau'ka daga gadon ya nufi wajen Annur dake 'ko'karin tahowa inda suke, Abbas 'daga shi yayi sama yace " Oyoyo my boy na dawo bangan ka ba"
Dariya Annur yayi masa yana jan hancin sa duk da kuwa bai warware daga baccin daya tashi ba amma yanda yake son Abbas 'din ya sanya shi 'dan warwarewa dan sosai Abbas ke yi masa wasa idan yana gida shiyasa suka sha'ku hatta Teemah 'yar kallo take zama idan Abbas na gida wa'kan da yake yi masa ma yanzu har Annur 'din ya iyata dan sama zai idaga shi yana dariya yana cewa " wah...wah...waladin...Muhammad Nury waladin...., yaron Daddy waladin, yaron Mummy waladin, mai sunan Daddy waladin"
Annur ya rin'ka dariya kenan idan yaji wataran kuwa hannayen sa yake kamawa kamar sa'ani suyi ta wa'kar su a tare.
Haka hatta wanka shike yi masa idan yana gida ya kuma bashi abinci sannan ya kaishi 'dakin dayake kwana yayi masa addu'ah yana lalla6asa har sai yayi bacci.
Sau tari Teemah sai dai ta ta binsu da idanu ko kuma tana rakashi musamman idan zai kaishi bacci sai ta bisu abaya ita kanta tana jinjina wannan sha'kuwar cuz idan kaga Annur ya manne mata to Abbas baya gida ne in kuwa yana nan kallo ma bata ishesa ba.
Sha'kuwa ce mai mugun 'karfi a tsakanin su hatta yawo wataran fita suke yi su biyu su barta agida wani sa'in ne idan zasu fita Annur sai ya je ya janyo mayafin da duk yagani a fili ya kawo mata yace " mummy let's go"
Abbas idan ranar baiyi niyyan fita da ita ba sai yace "ah ah banda mummy, ita ta ta zauna a gida zamu kawo mata abin da'di".
Cuz wataran office suke zuwa wataran kuma yawo kawai zai kaishi, wani gyaran kai da Abbas ya kaishi akayi masa wai wanda yagani, Annur yaro ne amma ba laifi yana da suman kai sosai, hakan yasa Abbas yake kulawa da kan nasa kamar wani babba yasa akai masa low cut aka gyara gashin kamar ba 'dan hausawa ba, kafin Abbas ya zama ma aikacin soja ba irin gyaran kan da baya yi, amma tunda ya shiga aikin sai ya zamana gashin ma ba bari yake ba shikuwa yana da masifar son tara gashi shiyasa ma daga ya 'dan 'dauki hutu zaka ga har ya tara suma ya kuma gyara shi gwanin birgewa kafin cikar hutun Teemah kanta yana bata sha'awah da zarar hutunsa ya 'kare kuma shikenan zai je ya cire su, wannan dalilin ne yasa yake yiwa Annur dan shi bai da damar yin hakan, shi mutun ne mai son cika BURIKAN SA, sai dai baya binsu a gaggauce cikin natsuwa take binsu shiyasa idan bai samu daman yin abu ba sai ya 'dorawa wani nashi burin, kamar yanzun burinsa na son Teemah ta zama doctor wanda ta'ki bai yi fushi ba sai ya 'dauke burin daga kanta abin na nan a cikin ransa amma sai ya bari akan 'yarsa idan har Allah ya bashi....ita zata cika masa wannan burin.

Yanzun kuwa da Annur yake ri'ke a hannunsa sai yake ta faman jan hancin Abbas yana dariya, Abbas kuma yana kaucewa tare da mai wasa acikin sa da bakin sa da yake jikinsa babu riga illah pant ne kawai so idan ya hura cikin sai yayi 'kara wanda yake matu'kar sa ka Annur dariya idan yayi masa hakan.

Gurin da Teemah take ya koma da shi yana fa'din " Annur baya son zama da kaya agida da alama halin ki yayo"
Teemah kam murmushi mai sauti kawai tayi batare da ta tanka masa ba sosai take jin da'din yanda Abbas yake kulawa da Annur duk kuwa da abubuwan dake gaban sa amma sam bai sa sun rinjayi tattalin iyalinsa ba, sosai yake 'ko'kari akan hakan har tausayi yake bawa Teemah wani lokacin idan taga Annur na ma'kal'kale masa, ita kanta tana so suna 'dan barinsa yana samun natsuwa, sau tari sai dai in tana son ya barshi sai ta yi masa wayo tace "bamboo Annur, come on zo in goya ka kayiwa Daddy dariya" Annur idan yaji goyon ne kafin yake zuwa ya bar Abbas 'din, wataran ma har datse 'kofa take yi da key dan ya samu yayi bacci, tun Annur bai gano ba har ya gane so idan baiga Daddyn nasa ba kuma yaga 'kofa arufe sai yaje yayi ta bugawa yana 'kananun kuka tare da 'kiran "Daddy"!

A gefenta Abbas ya zauna inda ya maida idanunsa kan fuskar Annur batare da ya kalle ta ba ya fara yiwa Annur wa'kansa ta waladin " wah...wah...waladin....
Annur kam sai dariya yake yi Teemah kuwa binsu take da kallon 'kauna tana murmushi, tasan idan kowa irin Abbas ne to da babu macen da zatayi 'korafi akan raino amma ina tasan bakowa ke sa'an samun hakan ba dan hgaka sai ta furta " Alhamdulillah" da dacen samun miji nagari da tayi mai son ta mai kula da dukkan al'amuranta, mai baiwa bu'katun muhimmanci uwa uba kulawa da ahalin gidan sa.

Sai da ya gama wa'kar tasa kafin yace da Annur " Yaron Daddy... you need a baby sis to play with right?"

Annur sai ya 'dage kai sama tare da fa'din " yes Daddy just like Anty Ummah's baby" yana washe fafaren 'kananun ha'koran sa waje.
(Anty Ummah wata mata ce a block 'dinsu data haihu sati biyu yanzu da suka je da Teemah ta 'dauki babyn shine ya 'kare mata kallo harda wasa da 'kafafuwan ta ).

Abbas kam kamar Annur ya ziga shi sai ya ya sake fa'din " Oyah tell ur mum that u want ur baby sis from her like Anty Ummah's baby.."

Annur kallon ya dawo da shi kan Teemah data zuba musu idanu tana murmushi cikin maganar sa da bata gama mi'kewa ba yace
" yesh Mummy ...i wan my lil prinshesh right away"

Teemah zaro idanu tayi tace " see u, right away 'din 'kaniyar ka a ina zan samo maka yanzun?"

Abbas kam murmushi yayi ya bashi hannu tare da kama chicks 'din sa yace " That's my boy, we need our princess right now ko ?"

Kai Annur ya 'daga masa yana washe baki, Abbas kam yana murmushi yayi pecking 'dinsa a goshi.

Teemah kuwa tashi tayi da sauri ta fita taje 'dayan 'dakin ta 'dauko teddy bear 'din sa da yake wasa dashi ta kawo masa tace " ga lil princess 'din taka....bana son damuwa ni"
Tana maganar tana cusawa a tsakanin sa da Abbas.

Annur yana ansa sai yayi jifa dashi gefe tare da fa'din
" Not ths mummy i want d yeal one"

Dariya dukkan su suka sanya ilah Annur, Teemah kam harda zama Abbas yana cikin dariyar yace
" yaro na na son d real princess ba fake ba sai ki shirya kar6an lil sis 'din Prince 'dina an jima "

Kafa'da ta no'ke tace " ni dai ah ah...Allah Yayah duk kai kake koyawa yaron nan iyayi.....har da wani now sai kace an gaya masa haihuwan sau'ki ne dashi, nawa ma yake shi'din 19months ne fa yake har yanzu dan Allah, ni dai gaskiya ba yanzu ba....kuma ya dameni da zancen babyn nan zane shi zan fara ni kam"

Abbas sai yace
" Kina ta6a min yaro to kuwa sai kin haifi triplet ba ruwana "

Sai tayi saurin no'ke kafa'da kamar 'yar yarinya 'karama tana tunzura baki gaba.

Abbas ma sai yace " do ur worst 'yan mata zaki kuwa sha mamaki...yaron da nake planning kai shi school kwanan-nan 'din ne zaki ce min bai kai ya samu sister ba?
Kin ma yaudari kanki yarinya is better ki fara shiri ma cuz next year like ths insha Allhu i'm with my 2 kids".

Jikin sa ta fa'da tana kukan shagwa6a tare da kaimar bugu a 'kirjin sa shikam dariya ma ta bashi da shegen tsoron nata Annur ma ganin yana dariyar shima sai ya bu'de bakin sa da 'kananun ha'koran sa guda 12 yana taya Abbas 'din dariya.
_They live happily ever._

*ALHAMDULILLAH WASSALATU WASSALAMU ALA NABIYUL KAREEM*.

Anan na kawo 'karshen littafin *CAPTAIN ABBAS*
Wanda na 'dauki tsawon lokaci ina rubuta shi amma bazan iya fa'da muku tsawon lokacin ba gaskiya dan kar kumin dariya🙈.....lolz

*Yabo da godiya sun tabbata ga Allah ma'daukin sarki mai kowa mai komai wanda* *ya kawo mu har wannan lokacin muna cikin rayayyu.*

Fatan darasin dake cikin labarin ya isar, wanda suka ha'da da tsoron Allah, ha'kuri, da kuma tawakkali...ha'kurin ma dai shine kusan mafi rinjaye cikin labarin so ina fatan zaku fahimci manufata duk da nasan bakowa ne zai fahimci hakan ba amma ko da tsirarune daga cikin makaranta labarin idan suka fahimta toh Alhamdulillah *BURIN SALMERH* ya cika...... rayuwar d'an Adam de dukkanin ta aya ce mai girman gaske... nasan munsan hakan, sai dai still bamu fasa aikata son zuciyar mu ba, musamman idan mukayi duba da yanda rayuwa take tafiya a wannan zamanin, mafi yawancin mu mu muna aikata abinda ran mu yake so ne koda kuwa munsan ba akan dai-dai muke ba amma sai zuciyoyin mu su rinjaye mu sai muna ganin kamar dai-dai muke aikatawa azahirance, wanda bazamu tashi yin Allah wadai da hakan ba har sai ranar da Allah ya nuna ikon sa akan mu alokacin ne dayawan mutane ke gane kuskuren da suke aikatawa.
Son zuciya, son kai, buri da kaiwa kanmu inda Allah bai kaimu ba shima babu amfani tunda kunga yanda rayuwar Anty, Munnira da kuma Anty Chiddy ya kasance saboda son zuciyoyin su daga 'karshe kowa sai da ya yi nadaman halin sa wanda tun farko rashin ha'kuri ne ya haifar da shi....Yayin da ha'kurin Mahmud yasa ya amsa 'kiran mahaliccin sa ayan yardajje cikin natsuwa.
ALLAH UBANGIJI KA KASA MU GANE GASKIYA GASKIYA CE KUMA KABAMU IKON YIN AIKI DA SHI.

....fatan zaku fahimce ni....kuraren dake cikin labarin kuma ku yafemin dan Allah kar ku tuhumeni akan hakan ayi min uzuri saboda littafina na farko kenan duk dama bashi na fara rubutawa ba amma dai kusan zance shine farko tunda al'kalamin sa ya kai 'karshe.
Chapter 162 · 0% Book details