← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 163

Sashe 22

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ai tana jin haka tayi saurin mik'ewa tsaye ta tattare plates d'in ta fice da sauri, shima bayan ta yabi da kallo aransa yace

"mara kunyan banza kawai, nida kene ai a gidannan".

Tana fita ta wuce kitchen ta ajiye plate d'in sai ta wuce d'akinta,tana shiga kuwa tafad'a kan gadonta taringa kuka mara dalili amma deep down tana tunawa da Mahmud ne dan tasan da yana nan da hakan bai faru ba, da shikam tayata ci zaiyi ya,a bata abaki amma wannan shi sai bala'in mugunta.

Washe gari ma da aka zo cin abincin haka mummy tayi ta kwalla mata k'ira dolenta ta fito tazo tasami mummyn.

Mummyn cewa tayi

"yiwa yayanki magana maza yazo yaci abinci"

Baki ta tura gaba tayi kamar zatayi kuka, mummy kanta ak'asa yake bata ma lura da abinda TEEMAH tayi ba.

Ganin haka yasa Teemah juyawa tanufi d'akin nasa ranta amatuk'ar 6ace.

Knocking tai tayi daga waje shikuwa yana zaune agaban d'an k'aramin madubin d'akin yana jinta ya k'i kulata dan yasan itace inba ita ba babu mai mar irin wannan iskancin.

Ganin ank'i kulata ne yasa ta tura k'ofar ta shiga a hankali, take taja ta tsaya dan ganinsa datayi zaune akan kujera yana gyaran fuskarsa, sai jin haushin ta ya k'aru fiye dana d'azu, a tunanainta barci yakeyi aai kuma taganshi a zaune.

Azuciyarta take ayyana "dama yana jina yak'i kulani dan salon wulak'anci kenan, dayake gani k'aramar danga amma daya je wurin waccen yarinyar ai tana fitowa shima ya fice ya tareta ahanya irin ma kar ya 6ata lokaci ranta ya 6aci d'innan"

Haushi ne ya k'ara kamata sai ta kalleshi dayake bayansa take iya kallo sai kawai ta banka mar harara.

Karaso wa tayi kusa da shi,ta tsaya

"Yayah ina yini"
tafad'a tana wani kauda kai.

"Banganshi ba" yabata batare da ya kalleta ba.

Juyowa tayi da mamaki ta kalleahi dan ita tasan ba wani abu ta tambaya ba, giransa d'aya ya d'aga mata sama sai taga ya bala'in yi mata kyau take abinda ke ranta d'in ya kau ta hau wassafa kyaun sa aranta, dan d'an zaman da yayi agidan har fuskarsa tafara tara gashi, kuma ya mar kyau dan sanda yazo gidan babu komai akansa da fuskarsa amma yanzu kam duk sun fara fitowa kuma sosai suka masa kyau.l suka kar6esa.

Sosai taji ya birgeta musamman data ga shima hankalinsa nakai alamar shima yanason abin.

Ta6e baki tayi ta maida idonta gefen madubin sannan tace

"mummy na k'iranka"

Juyowa yayi kamar baisan da tsayuwarta agurin ba tun farko.

"Baki iya sallama bane?

Ya tambayeta idonsa k'ur akanta.

Kasa tayi da kanta da wuri batare da ta k'ara yin wata magana ba.

Bayyanan niyar murmushi yayi wanda azahiri sautin ya bada
"hmm"

sannan ya juya yaci gaba da abinda yakeyi "kije in abinci ne ki had'o ki kawo min nan d'aki"

Tana jin haka ta juya ta nufi hanyar fita aranta ta ce

"Nikam na shiga uku na, yau kam Allah yasa bani zai sa cin abincin ba"

Haka taje ta had'o tana ta farga ba jikinta har rawa yakeyi tsabar tsoron kar yasata cinyewa sai tasaka abincin d'an dai-dai.

Yaukam cikin sa'a sai yace mata ta zauan tajirasa idan yaci sai ta wuce da plates d'in.

Tasabar farin ciki har sai da tayi murmushi duka yana lura da ita.

Tun da ya fara ci bai d'ago ya kalleta ba, kansa da hankalinsa ya tattara gaba d'aya ya bayarwa abincin.

Kamar wasa ya fara ci sai gashi kuwa yacinye tas.

Kuma sai daya cinye d'in kafin ya d'aga daidai ta kalleshi sai suka had'a idanu sai abun yabasu dariya gaba d'aya amma murmushi suka yiwa juna.

Yana murmushi yace " kinga ai yau d'in na rowa kika sako min gashi yamin kad'an"

Sai kuma yafara yunk'urin mik'ewa
yana fad'in
"jeki k'aro min"

Ai kuwa da rawar jiki tatafi k'aro wan takuwa d'ibo yanzun harda na mugunta ganin d'azu bai sata taci ba shine ta k'aro da farin cikinta.

Koda ta dawo sai ta sameshi atsaye yana 6alla botton d'in rigar jikinsa.

Shigowa tayi ta ajiye masa tana shirin shirin juyawa ya dakatar da ita akan cewa ta tsaya ta daman wannan nata ne shi ya riga da yaci nasa.

So wannan nata ne kuma tayi da wuri dan fita zaiyi yana da gurin zuwa,irin najiya yace maza tacinye tas.

Sai ta d'ago da sauri ta kalleshi,da alamar mamaki "uhhhm" yace mata da alamar shima amsar mamakin nata yabata.

Sai itama tace
"Abincin fah yawane dashi yaya"

"Ahakan nan kuma zaki ci 'yan mata"

Fuskar tausayi tayi zata fara magana ya dakatar da ita da fad'in "hurry up pls nace miki zan fita ko"

Sai tace
"Toh kaje abinka yayah Allah zanci"

"Gani yaro ko Teemah"
Yafad'i yana kallonta

Jijjiga masa kai tayi da sauri sannan tafara chin abincin dan taga kamar tafara k'ureshi.

Haka tafara tura abincin da kyar data k'oshi sai ta karkata kanta gefe tana kallonsa da ido ruwa-ruwa.

Ji yayi ta bashi tausayi gashi kuma shima yana da uzurin fita sai kawai yace
"tashi kije"

Yauma da sauri ta tattare ta fice daga d'akin nasa amma koda taje kitchen d'in sai ta samu wuri ta zauna tana maida numfashi dan gaba d'aya taji ta wani iri kamar ba ita ba abincin data ta turawa ne suke sata jin numfashinta yana sama-sama.

Baabah Lami ce ta tambayeta " wai lafiya kuwa Fatu"?

Kallon Baabah Lami d'in tayi batare da tayi magana ba.
Illah kauda kanta gefe datayi sannan tace
" Baabah Lami keda Yah Abbas ne kad'ai bakwa k'aunata agidannan"

Zaro ido Baabah Lami d'in tayi tare da fad'in "haba ke kuwa k'auna gaba d'aya?

"Ehh mana kullun sai kin k'irani da sunan da bana so shi kuma duk abinda banso shi yake sani yi kullun"

"Toh kiyi hak'uri an daina insha Allahu"

Baabah Lami d'in tafad'a tare da ficewa ta k'ofar baya.

Da kyar taji ta tayi d'an daidai sai ta tashi ta lalla6a tawuce d'akinta taso taje wurin mummy tace mata tayi masa magana ya daina sakata cin abincin dolennan amma sai ta tuna mummy ma ba goya mata baya zatayi ba.

Sai kawai ta wuce d'akinta tana rage kayan jikinta sai taji kawai tana son shiga bayi.

Da sauri ta wuce ta shiga bayin aikuwa bayan gida mai taurin tsiya ne ya matsa ta.

Da kyar tasamu yafito har sai da idonta ya cicciko da hawayen azaba.

Koda tafito sai ta kwanta agado tana maida numfashi.

Afili tace
"Gab ake da kashe miki y'arki mummy amma nasan kona gaya miki bayansa zaki bi bani ba"

Sai data huta kafin taje tawatsa ruwa tazo ta kwanta take kuwa bacci yayi awon gaba da ita.

Washe gari ma data tashi sai da tayi kashi kafin anan tayi wanka " nikam Allah zai saka min wallahi, mutun wai in baiga yayi mugunta ba bai jin dad'i"

Haka ta shirya tafito dan har ta d'anyi latti ma.

Drop ur comment pls mutane na I heart u all🤞🏻

*Serlmerhn ku ce*😍
[10/2, 5:57 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO_* 😍

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *22*

Zuwa yanzun satin Abbas uku agidan su Teemah inda adaidai wannan lokacin yaci kimanin rabi da quarter daga cikin hutun da ya samu na aikinsa.

Shikansa yanzun ak'age yake ya koma ya fara aikin,har ji yake zaman gidan yafara isansa dan dama bak'aramin so yake yiwa aikin nasa ba dalilin hakan ne yasa yafara k'irga ranar tafiyarsa.

*****
Mummy ce zaune akan kujera Teemah kuwa na gefenta sai zun6uro baki takeyi gaba tana guna guni k'asa-kasa, mummy kuwa ko kallon inda take ma batayi ba kanta na gefe.

Teemah data ga mummyn bata da alamun sak'k'owa sai ta k'ara risina ta had'iye miyau tare da daidaita bakinta sannan tace " mummy dan Allah kiyi hak'uri ki barni naje mana Allah idan naje bazan dad'e acan d'in ba"
tana kawo wa nan sai zamo daga kan kujerar ta zube akan gwiwoyinta tayi kalan tausayi agaban mummyn nata, mummyn ma sai tak'i ko kallon inda take balle ta san tanayi.

"mummy please"
ta k'ara fad'i kamar zatayi kuka.

Sai a sannan mummy ta juyo ta kalleta, suna had'a idanu sai ta k'ara rausayar da kanta gefe alamar rok'o.

Sai kuwa taji mummyn tace "zan barki kije Teemah amma kuma cikin 2hours zakije ki kuma dawowa, idan kika kuskura kika wuche hakan wallahi ni da ke ne agidan".

Wani tsallen da Teemah ta buga ta fad'a jikin mummyn har sai daya firgita ta.

Sai tace " haba Teemah miyeh hakan kuma kin kuwa san yanda kika tsoratar dani?

Dariya Teemahn tayi sannan tace "duk murna ce kawai mummy"

"Hmm Allah ya shirya minke nikam Teemah"

"Ameen mummyna"

"Ki zauna kina min iyayi anan yarinya duk cikin lokacin ki ne ai ni babu abinda ya dameni"

Dawuri ai ta mik'e dataji abinda mummyn ta fad'a sai tace
"Banaje in dubo Habibu in fad'a mar zai kaini unguwa in bayanan kuma sai ki k'iramin shi awaya dan kar yayi nisa yamin cikas"
Kai mummyn nata ta d'aga mata alamar taji.

Har ta fara tafiya sai mummyn ta dakatar da ita da fad'in ta k'yale habibun kawai dan ita bata yadda Habibun ya kai Teemahn ba , domin tariga da tasan halin Teemahn tsab, acewar mummyn wai Teemah tariga ta raina Habibun kuma koda sun fita ba bin maganarsa zatayi ba sai dai nata.

Duk mummy tayi maganar ne Teeemah na tsaye a inda tatsaya tun sanda mummyn ta dakatar da ita.

Sai da taji k'arshen maganar mummyn kafin tafara tafiya ta dawo ta zauna a kusa da mummyn.

"Toh mummy idan bashi d'in wa zai kaini?
ta jefawa mummy tambayar.

Amsa mata mummyn tayi da fad'in " zan rok'i Abbas ne ya kaiki kuma zai jira ki idan kin gama zai dawo dake "

" kafad'a ta d'aga tana kallon mummyn alamar tak'i ita bata yadda ba.

"Then sai kiyi zamanki agida abinki tunda bakya son zuwa ni kinga banda problem".
Mummyn ta fad'a tana mai nuna halin ko in kula ga zancen.
Chapter 22 · 0% Book details