← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 163

Sashe 71

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayani likitan yamasa game da abinda ke damunta, da kuma yadda za'a magance shi cikin sau'ki, sosai Mahmud ya fahimce shi, dan shi da farko hakan ma be zo ransa ba sam, yama manta da cewar mata na irin wannan abin lokaci zuwa lokaci, dan ko data fa'da masa cewa jiya cikinta yayi ciwo ma shi zaton shi wata matsala ce daban be kawo hakan aransa, ko data masa 'karyar tayi sallah ma yau da safe be yi wani dogon nazari akai ba dukda yana da tabbacin bata yi sallar ba.
Ya 'dauka ko abinda tasaba yi ne kullun cikin dare shiyasa ma yau daya fita ya 'kara zuwa wani 'kwararren asbitin daban domin asake duba masa lafiyarsa da kyau, yafi so yaji gamsashshiyar amsa game da matsalar dake damunsa, amma ako ina baya samun amsa mai kyau su kan tabbatar masa da cewa lafiyar sa 'qalau baya tare da wata damuwar da har zata hana shi amfanuwa, sai dai ko 'dan abinda ba'a rasa ba, ko yau 'din ma wasu magungunan daban aka sake rubuta masa tare da tabbatar masa abinda likitan daya ganshi da farko ya fa'da masa inda yabaro asbitin da zummar bada himma ga shan maganin ko dan matsalar da matarsa ke ciki domin kar ya kaita ma'kura, shikan shi yana so yaji kansa amatsayin cikakakken namiji yanaso mazantakar sa ta dawo kamar da, dukda ma acikin jikinsa baya ji kamar yana tare da wata matsala ajikinsa, jinsa yake garau, amma me yasa ba ze iya biya wa matarsa bu'katar ta ba bayan likitoci ma sun shaida cewa lafiyarsa 'kalau?
Wannan abin na 'daure masa kai ba 'dan ka'dan ba.

Baccin kimanin mintina talatin Teemah tayi sai ta farka, Mahmud tagani zaune agefen gadon da take kwance ya 'kura wa 'karfen gadon idanu, sai da ta juya ta kalli 'karfen sannan ta dawo da kallonta gareshi, _"Yayah "_! tace da dasashshiyar siririyar muryarta da bata gama warwarewa daga baccin da tashi yanzun ba.

Mahmud be ji ta ba domin be amsa sunansa data ambata ba kamar yadda be kawar da idanunsa daga inda yake kalla tun 'dazun ba.

Ganin haka yasa Teemah ta yun'kura ta tashi ahankali ta kai hannunta ta dafa kafa'darsa tare da sake 'kiran sunansa, juyowa yayi ya kalle ta take sai ya 'ka'kalo murmushi tare da dawo da dukkan hankalinsa gareta
_" kin_ _tashi?_
Ya tambayeta yana 'ko'karin kamo hannunta dake kan kafa'darsa.

Da kai ta amsa masa alamar
" _ehh_ "

" _Ya jikin naki_ ?
Ya sake tambayarta da kulawa.

Sai ta bashi amsa da fa'din

" _na daina jin komai_ _yanzu"_

Fa'da'da murmushinsa yayi tare sa fa'din
" _Masha Allah, ubangiji Allah ya 'kara sau'ki, zaki iya tafiya kuwa ko de na 'dauke ki?_
yayi maganar yana kallon cikin idanunta.

_" a'a zan iya tafiya_ _ma da kaina_ "
Teemah tabashi amsa tare da yun'kurin sau'kowa daga gadon, sai de bata kaiga ajiye 'kafafunta a'kasan ba taga gurin wayam ba alamar takalmin ta, sai ta juyo ta kalleshi tace. " _Yayah takalmi_ !

Mahmud kai ya dafe tare da fa'din
" _oups, ni ai duk ma na manta, ko tunawa banyi da batamun takalmanba garin_ _sauri, kin rikitani sosai Fateemah har ma bansan inda_ _hankalina ya tafi_ _ba"_

Murmushi tayi masa kawai dan bata san mezatace dashi ba alokacin.

Tambayarta ya sakeyi da fa'din
_" yanzu ya za'ayi ne_ _toh ?_

sai tace yakoma gida ya 'dauko mata kawai sai yazo su tafi.

Ido yazaro waje yace
" _kina nufin wai har gida zan koma in kuma sake dawowa nan?_

Da kai tabashi amsa alamar _ehh_ , jijjiga kai Mahmud yayi tare da fa'din se kace bani da hannaye, yana maganaar yana 'ko'karin cicci6anta, be zame ko'ina ba, sai inda ya faka motarsa, daya ke already likita yariga yagama dasu yagama sallamarsu
,dama Mahmud zaman jiran farkawanta kawai yake su wuche gida.

Dakansa yasata acikin motan sannan yazaga 'dayan 6angaren yashiga.

Tun kan ya 'karasa daidai ta zamansa tafara fa'din
_"alluran da wannan likin yamin fah akwai zafi sosai "_ tayi maganar tana kaiwa hannuta wurin da aka mata alluran tare da langa6ar da kanta .

_"Eyyah sorry , very soon zaki daina jin zafin ai"._

_"Ni de karka 'kara_ _kawoni gurin nan Yayah ..........!_

_"Bana ma fatan 'ki 'kara yin ciwon har_ _abada"!_
Ya tari bakin ta da fa'din haka.

Sai itama tace _"Ameen Yayah, Allah mutumin mugune, ai har nayi niyyan cizon shi danaga ya 'dauko allura kawai de_ _nabarshi ne yamin dan yanda cikina kemin zafi sosai, amma fah har guda biyu yamin dan mugunta"_

Murmushi yayi mata kawai tare da shafo fuskanta sannan yace " _Alluran ai shine daidai baki ga acikin 'kan'kanin lokaci kin samu lafiya ba"_ .

Dai-dai wani babban store Teemah tace ya tsaya tana son ta siyi abu, kallonta Mahmud yayi da sauri yace _" ina fatan de ba dangin su choculates bane, dan doctor yace ki rage shan su saboda ciwon cikin nan naki"._

_" ah ah Yayah basu bane wani abu daban nake so"_

Sai da yayi parking agefe kafin yace ta fa'da toh yaje yakawo mata yanzu sai su wuce gida dawuri ko dan tasamu ma ta'dan huta gashi maghrib takusa.

Teemah kuwa cikin shagwa6a tace masa.
_"Ni fa zan sayo dakaina "_

Kwafa yai yana kallon ta da mamaki, ganin ta'ki ta fa'da masa abinda take so 'din sai yace mata _" ba_ _takalmi ba mayafin zakije "_

Jijjiga masa kai tayi tare da fa'din masa yanda za'ayi.

Tana gama masa bayanin yafice amotar batare da yayi magana ba.
Minti goma me kyau be yi ba yadawo da leda ya mi'ka mata, kar6a tayi ta ciro takalmin ta sanya a'kafarta dayake ya san size 'din 'kafar ma sai ba 'a samu wani kuskure ba, 'dan 'karamin mayafin dake cikin ledar takuma cirowa ta yafa shi akanta.

" _Muje toh_" tafa'da tare da bu'de bangaren data ke zaune, shima fita yayi ya bi bayanta bayan ya dannawa motar lock.

Dakanta ta 'debi duk abinda takeso Mahmud na gefe yana kallonta sai da aka zo wajen biyan ku'di kafin ya ga abubuwan da ta kwaso, harara ya doka mata sai ta kauda kai tare da yin fi'ki-fi'ki da idanu, tasan daman ai hakan sai yafaru shiyasa ma tace da kanta zata shigo dan tasan inshi 'din ka'dai ne yazo 'kin siya mata zaiyi.

Be kulata ba yabiya ku'din tare da 'daukan ledan itama sai bishi abaya suka fito suka koma mota, har suka isa gida be 'kara yi mata magana ba.

Data ga haka sai ta dawo kusa dashi lokacin yana zaune akan cough a palourn su, _" Yayah_ _inkawo maka ruwa kasha_ ?

Be yi magana ba sai ya jawo ta zuwa gabanshi ya nuna ta yatsa yace _"wato_ _ke ba kya ji_ _ko?,_ _ciwon cikin be ishe ki ba ko"_

Hannayenta ta 'da go tarufe gefe da gefen fuskarta dan zaton ta marin ta zaiyi yanda taga yake maganar sosai yaso ya firgita ta.

Ledar ya sa hannu ya janyo ya ajiye agabanta yace
_" oyah fara ciro su 'daya bayan 'daya kina min bayanin su"_

Haka ta yi kamar yanda ya bu'kata amma sai da ta ciro su pads 'din data siya da farko ta ajiye ta ciro wani turare ma ta ajiye sannan ahankali tana kallon fuskarsa tafara ciro dangin choculate 'din data ta jida kusan kala hu'du.

Harara ya doka mata yakai hannu zai kamo kunnanta take tayi saurin matsawa baya tace _" Allah Yayah sunmin kyau ne shiyasa fah na 'dauko, kuma fah sabon product_ _ne baka ta6a kawo min irinsu ba shiyasa ne 'debo, bama yanzu_ _zan sha ba sai na sami sau'ki"_

_"Waye yace miki sabo ne "_ ?
Yafa'da atsawace

Sai Teemah tace " _ni ai ban ta6a gani_ _bane"_

Mahmud 'kyaleta kawai yayi ya tashi ya wuche ciki domin ya watsa ruwa ajikinsa dan yasan inya biye wa Fateemah har ciwon kai sai ta sashi abanza.

*Bayan kwana biyu*
Mahmud sosai ya dage yana kula da shan magungunan sa akan lokaci saboda shi kansa ya 'kagu yaji shi cikin 'koshin lafiya, hakan yasa sam baya wasa da lokutan shan maganinsa ko agida ko a office baya ta6a sa6a lokaci.

Acikin kwanakin kuma Anty Chideh ta ziyarci Teemah inda tasameta ita ka'dai agida saboda Mahmud na office ita ka'daice gida.

Alokacin ma Teemah na kwance tana ta trying layin su Mummy taji baya shiga abin sosai yadameta ya 'daure mata kai, dan ko no. 'din Daddyn ta ma baya shiga a'yan kwanakin, kuma kullum haka takeji in ta 'kira su Hannah da Ummah kuma sai suce mata wai sede in matsalar network ne amma su kam wai suna 'dan yawan gaisawa da mummyn ko basu kira ba ita tana 'kiran Ummah su gaisa.

Mamaki yakan cika wa Teemah zuciya, tarasa meyasa se da ita hakan zai faru, takan yawaita tambayar kanta _"toh me yasa Mummy zata 'kira kowa amma ni ta manta dani, ko dama in akayiwa mutun aure shikenan kowa agidansu mantawa yake da shi?........_

Tana cikin wannan halin taji door bell na kara, tsaki taja ta share kawai, sai da akayi tayi kusan sau uku kafin azuciye ta tashi taje ta bu'de sai taga wannan 'kawar Antyn ce tsaye ita ka'dai, dariyar ya'ke ta 'dan saki tare yi mata maraba da zuwa sannan ta bata hanya ta shigo ciki.

Anty Chideh na gaba Teemah na biye da ita abaya, sai ta ta6e baki tare da 'karewa shigar Anty Chidehn kallo.

Sanye take da wani ba'kin mini skirt wanda be ko rufe gwiwarta ba hakan ma da 'dan tsago ka'dan daga baya wanda hakan ya taimaka wurin ganin fararen cinyoyinta afili, sai wata riga wanda ta wadaci jikinta domin bata kamata sosai ba, yadin rigar kamar yadin material ne da zanen 'kananun flowers ja, kanta kuwa yasha fixing na ba'kin attachment irin wanda kana gani kasan hula ne ba gashinta bane ba.

Duk cikin 'yan da'ki'ku tayi wannan lissafin sai ta ta6e baki tare da 'fa'din _" arnanci de beyi ba, har yaushe zaka rin'ka yawo da_ _irin wannan 'dan iskan kayan acikin gari kamar baka da mafa'di."_
Chapter 71 · 0% Book details