← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 163

Sashe 102

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abbas kam jiyake kamar idan yaci gaba da zama agarin nan toh kowa ma zai iya fahimtar yanayin farin cikin dayake ciki, dan haka take ya yanke shawaran gara ya tafi kawai tunda yanzu yanada tabbacin mallakarta inyaso sai ya dawo lokacin auren.

Dama already kominsa a ha'de yake dan dama da niyyar tafiyan ya kwana,maganar daddy ne ya dakatar dashi, yanzu kuwa da ya san cewa za6in Daddyn cikar farin cikinsa ne ai shikenan, da yake dama shi ba ya yin tafiya da kayan sawa in dai tsakanin Abuja da Rivers ne sai de kayan da yasan zasu masa amfani, dangin su wayoyi, system da sauransu.

Acikin wata jaka kalar Army green ya ha'da komai, Rigarsa daya cire 'dazu bayan ya dawo daga gurin Daddyn sa ita ya maida jikinsa tare da 'daukan jakan ya rataya akafa'dan sa ya nufo palour.

Teemah na isa 'dakin ta tarar dashi tsaye agurin switch yana 'ko'karin kashewa, kafa'dar sa rataye da jaka sallamarta ne ya dakatar dashi sai ya juyo ya zuba mata idanu bayan ya amsa sallamar tata.

Itama bata ajiye abin hannunta ba sai ta ri'ke tare da yin 'kasa da kanta tace " _ina kwana_ _Yayah_ !

Be amsa ba sai ya tako ahankali zuwa inda take tsayen ya jefa mata tambayar " _Yau kuma fushin me kike yi? Me ya sameki_ ?
_Ya tambayeta tare da tsare ta_ _idanunsa masu rikitata gaba 'daya_ .

Jikinta har na rawa saboda irin kallon daya ke binta dashi.
'Kasa-'kasa ta amsa da " _bakomai_ "

Juyawa yayi ya koma gurin switch 'din da be kashe ba 'dazun, yana kashewa kuwa take 'dakin ya dawo duhu ba'ki'kirin.

Sannan ya mi'ka hannu ya kakkashe conditioners ma gaba 'daya daga nan ya sake dawowa inda take tsaye.

Yanzun kam da hasken 'dakin ya ragu har 'daga kanta tayi ka'dan ta kalleshi sannan ta kauda idanunta gefe.

" _Kunyi magana da Daddy ne_ ?

Jijjiga kai tayi sannan ta furta " _ah' ah_ "

" _Okay ba matsala, amma make sure that baki tsallake duk wani umarninsa_ _ba koda bana nan, and ki daina fushin nan haka abincin ne bakyaso ki kawo_ _min ko kuma menene_ ?

Afirgice ta 'daga idanu ta kalleshi, hakan kuwa datayi sai yasa shi saurin fahimtar ya harbo jirgin ta, zuwa inda yake ne bata so.

Murmushi yayi sai yace " _Yes, ai nasan halinki baki ta6a appreciating yin wata hidima agareni ba, nima ban son abincin ki koma da abinki am ok na hutar dake_ "

Cikin shagwa6a tace " _bahaka bane fa Yayah!_

Jakar dake kafa'dansa ya gyara
Sannan yace " _toh menene gaya min naji_ "

" _Ni....ni...nifah_ ....
Kame-kame ta hauyi ta rasa takamamman abin fa'da.

Murmushi Abbas yayi yace mata _"maganata gaskiya ce kenan_ ?

Yana gama
fa'din haka ya juya zuwa 'kofa a hankali.

Teemah kam baki ta tura tabi bayansa da kallo.

Har ya kusan rabin 'dakin sai kuma yajuyo ya sake kallanta yace " _ki saki ranki ki daina fushin nan kin manta yau Mummy na hanya_ _ko_ ?

Da kai ta bashi amsa sai yaci gaba da fa'din " _kinga nima yau ina cikin farin ciki kema ki tayani kinji_ "?

" _Uhmm_ "
Tace masa

Shi kuma yasake fa'din " _natafi_ "

" _Allah ya tsare_ "
Tace ahankali shima asaman la66ansa ya amsa da " _Ameen_ ".

Daga nan yafice abinsa be sake juyowa ba.

Teemah ma tsayuwa taci gaba da yi agurin tama rasa mai ke damunta, jitake kamar tafiyar tasa ne bata so amma sam tarasa dalilin hakan, yau ka'dai sai taji tamkar zatayi missing 'dinsa idan ya tafi.

Komawa tayi kitchen ta ajiye kayan kafin ta wuche 'dakinsu ta kwanta agado tayi luf abinta.

Hannah ma a 'dakin ta sameta wanda barinta gun su Ummah kenan bayan wuchewar Abbas.

Tana barin gurin su, Ummah ta bawa Anty labarin abinda ke faruwa.

_Comment_
_Vote_
_Share_

*Ur comments are gating very low gaskiya kuma banajin da'din hakan harga Allah.*

~Mabiya Labarin *CAPTAIN ABBAS* kuyi min uzuri najina da kukayi shiru kwana biyu abubuwa ne sukayi yi min yawa amma yanzu kam insha Allahu nadawo da 'kafafuna, insha Allahu zaku rin'ka jina akan lokaci.~

*Salmerh ce*😍
[10/2, 6:03 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_Dedicated 2 my_ ❤

*Bismillahir rahmanir raheem*

_Silence is the best answer of all questions nd Smile is the best reaction in all situations............ Unfortunately both never help in VIVA & INTERVIEW_ .

🅿 *74*

Anty taji da'din hakan sosai tace kamar an shiga ranta anga ni, dama ita ta jima da ganin dacewar hakan, tace ai kuwa zama be kama ta ba, shiri ne gagarumi ya kusanto ta dan ma abin yazo a 'kurarren lokaci ne in ba dan haka ba ai da bikin sai ya zama bikin 'yar gata wanda aka da'de ba'ayi irinsa ba, duk da haka de tace bazatayi 'kasa agwiba dole ne tafitar da 'yarta yanda zata zama abin kwatance.

Ummah ce ta dakatar mata da tunaninta ta hanyar shigo da 'korafi akan rashin sanar da Fateemah da Daddy be yi ba inda tace da Anty
" Sai de ina ganin kamar fa ba'a kyautawa yarinyar ba, saboda bada yaddan ta mahaifinsu ya yanke wannan hukuncin ba, ina tsoron kar a shiga hakkinta sosai dan kinsan yanzu tana da daman da zata za6i miji da kanta ba sai an za6a mata ba musulunci ne dakansa ya bata wannan damar, duk da cewa za6a matan ma ba haramun bane amma naso da an nemi yardan ta tukunna"

Murmushi Anty tayi tace " karki damu da wannan dan Allah, ni nan nasan halin Fateemah bazata ta6a yin musu ba, shima mahaifin nasu yana da tabbaci akanta ne shiyasa kika ga ya yanke hukuncinsa kai tsaye batare da wata fargaba ba saboda yasan dukkan su zasu yi masa biyayya shiyasa be damu ba, kuma yawanci idan kinga mace tayi jayayya da iyatenta akan maganar aure toh already zaki samu tana da wani me daban, Fateemah kuwa ai nasan bata da wani manemi daban ko akwai?
Anty ta ta'karasa maganar tata da tambaya.

Jijjiga kawai Ummah tayi tace "
Bana tunanain haka gaskiya"

"Toh kin gani, insha Allahu bazata damu koda ta damun ma zata sakko da yaddar ubangiji"

Shiru Ummah tayi tana tunani aranta, ita aganinta duk da haka ya kamata Teemah tasan me ake ciki, kafin lokaci yazo ya 'kure yakamata aji nata ra'ayin, ita Ummah 'daukan alhaki ne take tsoro shiyasa ma ta damu sosai, wanda tunanin nan yayi mata karan tsaye a zuci ya hanata sakat dan haka sai ta yanke shawarar samun mahaifin nasu da batun.

Anty kuwa baruwanta da'di
taji dajin wannan labarin sai de kuma wani 6angaren tana tunawa da marigayi Mahmud, amma bata bari hakan ya nuna afili ba sai kawai ta takaita tunanin da ro'ka masa addu'ar dacewa wurin mahalicci.

Sai da ta koma 'daki sannan tasha kuka har ta godewa Allahn ta, babu wanda yasani, dan haka da kanta ta ha'kura tayi shiru.

Ayanda akasa ranar bikin Abbas 'din zai kasance kwana 'daya tsakaninsa da na Abban Mahmud domin shi nashi ranar Saturday ne sa6anin na Abbas daya kasance ranar Friday.

Da yamman ranar Mummy ta iso su Hannah murna kamar zasu ha'diye ta baran ma Teemah da tayi matu'kar missing 'dinta sosai kuka ta sanya ta rungume ta da 'kyar Anty ta lallashe ta tayi shiru.

Mummy kam dataji labarin bata wani damu ba dan ta riga da taji abakin Daddy tun a Dubai, sai de tana tunanin ko shi Abbas 'din baze amince ba tunda yanzu Teemah matsayin ta daban, bazawara ce ayanzu.

Abinda kenan ya tsayawa Mummy ama'koshi ya kuma hanata jin da'di.

Amma ganin yanda kowa ke farin ciki da al'amarin musamman Anty dan kane-kane tayi ta hana Fateemah zuwa ko'ina bayan ta nemo matar da zata ringa yimata komai, hakan ne yasa Mummy ta saki jiki tabi ayari aka cigaba da hidima da ita.

Ummah tasamu Daddy da abinda ya dameta amma shima nuna mata yayi ba komai shikansa yanaso yayi mata maganan amma yafi son idan Yah Kabiru ya iso, dan shi ka'dai bazai iya ba yarinyar na matukar bashi tausayi ganin bataje ko'ina ba amma rayuwa ya gwara kanta, kuma yana tsoron kar jin labarin ya dawo mata da past 'dinta baya.

Babu wanda ya sanar da Fateemah cewa auranta za'ayi kowa kawai harkar gabansa yakeyi, su Mummy tunanin su wai kar atuna mata da baya kuma ta 'daga hankalin.

Ummah cema ke yawan yawan damun Daddy akan asanar da ita saboda kar garin neman gira kuma a rasa ido, ita kullun damuwarta gudun shiga hakkin yarinyar, ganin ba'a bata daman daya kamata abata ba aka hau shirin 'daura mata aure.

Daddyn kansa abin na damunsa amma jiran Yayah Kabiru yakeyi idan yazo sayi maganar tare, yanada tabbacin cewa Fateema bazata ta6a gujewa umarninsa ba, dama Abbas ne matsalan dan kuwa har yanzu be san inda al'kiblarsa take ba akan auren, duba da yanda ya tattara yayi tafiyarsa duk da kuwa yasan cewa auren ya iso, hakan kuwa dayayi sai Daddy ya bari akan rashin son auren ne yasa, shi kuwa bayajin akwai abinda zai hana auren nan yiyuwa koda ma Fateemahn tace bata so toh dole sai tayi ha'kuri tunda ita da Abbas 'din 'yan uwan junane, saje can su 'karata.

Idan yaga akwai cutarwa ne sannan zai 'dau matakin daya dace akan Abbas 'din.

Tuntuni su Teemah sun can cewa Yayansu zaiyi aure amma kuma hakan ba dalili bane da zai sa har a tsare ta a'daki da gyaran jiki ,wata rana kuma harda Hannah akeyi musu, hakan da aka mata kuwa sai ya dinga tuna mata da lokacin aurenta da Mahmud wancan ma kusan hakane yafaru.

Bata san dalilin daya sa za'a ringa yi mata gyaran jiki ba, dan wani zaiyi aure amma dayake gwanar son kwalliya ce ita sai kawai ta basar da zancen ta saki jiki aka cigaba da gyara ta.
Chapter 102 · 0% Book details