Sashe 110
Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
" _Kai ka bari kawai maza sai a hankali wallahi, amma gaskiya ni banji da'din abinda kamin ba, ya za'a yi auran ka amma kawai sai de inji anyi ba wani labari_ !"
Shafo kansa yayi tare da fa'din
" _ohh sorry Saleem abin ne yazo unexpected in just 1 week Daddy ya yanke lokacin shiyasa, amma agafarce ni"_
Saleem cemasa yayi
" _Bakomai Cpt. yawuce girman kane ai, me ake shirya mana ne ina fatan za'a yi Sword_ _crossing kasan mu ta nan muka fi 'karfi_ "
Juya kai Abbas yayi yace " _gaskiya bawani COS da za'a yi nima yaushe na nutsu Saleem, an shirya a Rivers amma inajin ba zai yiwu ba dan bazan samu zuwa ba. Amma may be ayi dinner yau in ya yiwu a nan Abuja inaga shi ka'dai ma ya isa nagaji da hayaniyan nan Allah gaba 'daya Saleem_ "
" _Haba mana Captain......ko da yake bari sai na iso kawai nima da yaddar Allah yau_ _zan shigo_ "
Cewar Saleem.
Abbasa ma sai yace masa
" _okay, ba matsala, sai ka iso_ "
Yana cire wayar a kunnen sa yaja tsaki aransa yace " _bawani crossing na sword da za'a yi, haka kawai gardawa daku_ _ku saka yarinya atsakiya kuna faman 'karewa halittar jikin ta kallo_ _a banza_ "
*****
Ba Teemah ta tashi daga baccin ba sai 'karfe tara na safiya ta gota, tana tashi kuwa Anty kamar jira take tazo ta ha'da mata ruwan wanka na ha'din turare tace tayi dashi.
Zama tayi bayan shigan Teemah wurin wankan ta tallafi kanta da hannayen ta duk biyu tana tunani.
Anty na jin 'kunci azuciyar ta fiye da zaton mutun musamman da tasan cewa yau Abbah zai yi aure abinda be ta6a ko kwatan ta zancen shi ba tun farkon rayuwar su har Allah ya kar6i ran Mahmud sai gashi Allah cikin ikon sa rana tsaka kamar wasa ana shirin 'daura auren sa da wata daban.
Bazata ta6a fasa yi musu fatan alkhairi da zaman lafiya ba, dan koma menene yafaru laifin tane, she caused everything, dan haka ita a yanzu bata da wani buri illah taga 'karshen rayuwar ta tayi kyau kawai fatan ta Allah ya fe mata kurakuran ta na baya.
Tana zaune tana tunani har Teemah ta fito daga wanka bata sani ba.
Teemah tayi mamaki sosai da taga ta 'kira ta har sau biyu amma bata amsa ba hakan kuwa yasa ta matso dab da ita ta furta " _Anty_ "!
Da 'dan 'karfi.
Firgigi tayi tare da sakin ajiyar zuciya kana tace
" _har kin gama wankan ne? Kinyi da kyau kuwa?_
Tayi maganar tare da 'kwa'kulo murmushi ta sanyawa fuskar ta.
Cikin sanyin jiki Teemah ta amsa mata da fa'din "eh _h nayi mei kyau, Anty me yafaru ne naga kinyi shiru kina tunani?_
" _Hmm, bakomai Fatee na kawai ina tuna halin rayuwa ne yanda duniya ke juyawa damu, yau gashi Fateemah na ta sake zama matar wani karo na biyu"_
Anty ta tayi maganar tana mai sunkuyar da kanta kasa bata so Fateemah taga rauninta koka'dan musanman da yanzu ta tuna da marigayi gudan jininta Mahmud.
Teemah kam tsayawa kallon ta tayi kawai dan sam bata yarda hakan shine a zuciyan Anty ba, domin 'karara damuwar ta ta nuna a fili kan fuskar ta.
Ganin da Anty tayi Teemah tayi shiru sai ta kamo hannun ta dawo da ita gaban mirror ta zaunar da ita kan stool tare da fa'din
" _Zo zauna in gyara miki gashin kin nan kafin mai kwalliyar ki tazo_ "
Teemah yanzun ma shiru tayi ba ta furta komai ba damuwar ta be wuci ganin sauyin yanayin Anty datayi ba, tana so tasan ainihin dalilin hakan amma tasan Anty idan ba tayi niyyah ba bazata ta6a sanar da ita ba, inda tayi niyya ne da tun ma kafin ta tambaya da da kanta zata sanar da ita.
Tsinkayar muryar Antyn ta tayi tana fa'din " _Yarinta ta girma 4d second time, nauyin auren ya sake hawa kanki, amma kin san me nake so dake Mamana_ ?
Kai Teemah ta jijjiga mata ahankali alamar " _ah ah_ "
Rage murya Anty tayi yanda bakowa ne zaiji su ba sai in kana kusa cikin natsuwa tace
" _Kinsan Yayanki Abbas shine mijinki ko?_
Ahankali Teemah ta bata amsa da fa'din " _ehh nasani Anty_ "
Anty cewa tayi
" _Yauwa uwata, ina fatan zuciyarki ta kar6i hakan baki ji cewa an takuraki_ _ko shiga hakkin ki ba ko_ ?
" _Ah ah banajin hakan koka'dan Anty_ "
Da sanyin muryarta ta bata amsa.
" _Alhamdulillah_ "
Anty ta fada harda lumshe idanu dan yanda taji da'di da kar6an auran da Fateemah tayi.
Afili kuwa Antyn cewa tayi.
" _naji dadi Fateemah, nayi farin ciki sosai, ni kaina na rigaki kar6an auren nan tun ma kafin a ha'da shi, da kaina Fateemah na hangi 'kauna_ _da kishin ki tattare da Abbas kuma nasan da iznin Allah_ _rayuwar auren ku sai ta bada sha'awah watarana!, inaso koda kin koma gidan auren ki dan Allah Fateemah ki ri'ki_ _ibadar ki kinji, ki ro'ki Allah akan komai zai miki maganin koma menene, karki yadda ki kai kukan ki wurin kowa koda kuwa meze faru dake domin kuwa Allah kadai_ _ne mai taimakon da babu wanda ya isa ya miki makamancinsa_ _sai shi din nan dai Allah mabuwayi, Fateema rayuwa ta aya ce awurin_ _ki ai nasan kinsan duk abinda yafaru dani, 'karshe wa gari ya_ _waya?_
_Niice da kaina nayi dana sani nayi Allah wadai da halina!Mijin ki mijinki ne Fateema kuma_ _sirrin kine, 'yan uwan sa kema nakine dan ma kinga ai duk dangin_ _mijinki jininki ne dole ne ma ki so su koda babu aure a tsakanin ki da Abbas ballantana_ _kuma aure ya 'kara ha'da ku, ki so su ki kauna ce su sosai, ki girmama 'karfin_ _zumuncin dake tsakanin ku kar kiyi watsi da shi"._
" _Nasan auren ku auren ha'di ne na iyaye wanda za'a ce dukkan ku ba shiri yasame ku, amma dukkan ku kunyi_ _biyayya kuma na matukar jinjina muku, amma ki sani dole ne sai kinyi ha'kuri dan auren ha'di na tafe ne da wasu irin rikitattun abubuwa_ _wa'danda sai wanda ya ta6a faruwa dashi ne ka'dai zai gane su, ba zance bakwa son junanku_ _ba dan ban shiga zu'katan ku nagani ba amma nasan dole ne sai kin fuskanci wani 'kalubale daga mijinki wanda ha'kuri ne ka'dai_ _zai iya magance miki su, Fateema kiyiwa mijinki biyayya, bansan taurin kai da rashin kunya banda_ _musu da jayayya dashi kinji? na tabbata idan kika ya'ki zuciyar ki kika kuma dogara ga_ _Allah komai zai zo miki da sau'ki amma sai kin daure sosai kinji?_
Ahankali ta 'dagawa Anty kanta dan duk kalaman Antyn sun sa jikinta yayi sanyi matu'ka, duk abinda Anty ta fa'da gaskiya ne sai dai ita can 'kasan zuciyarta take jin ta shiryawa zama da shi a kowani irin hali.
Anty cewa ta sakeyi " _Yauwa uwata Allah ya miki albarka, yasa haske arayuwarku har illah masha Allah_ "
A saman la66a Teemah ta amsa da fa'din " _Ameen_ "
" _Bansan me yasa nake jin da'din wannan auren naku ba har azuciya ta ba, inaji ajikina da iznin Allah auren ku akhairi ne,dan haka_ _ki bawa mijin ki kulawar data dace kinji_ ?
Kai ta 'dagawa Antyn tana me sake sunkuyar da kanta.
Anty data fahimci taji kunya sai ta yi murmushi kafin tasake yin wata magana kuwa sai ga mai shirya Teemah ta iso da sallamar ta abakinta tare da wata mata abayan ta.
Amsawa sukayi dukkan su Anty sai ta mi'ke tare da gabatar musu da kayan da Teemah zatayi amfani dashi a yanzun sannan ta bar 'dakin.
Abbas wanka yayi, ya shirya cikin wani shadda golden brown, ajikin babbar rigan kawai akayi aiki da coffee 'din zare wanda ya 'kara haska kayan sosai hakama a jikinsa sai annuri yake yi da sheki sosai kayan ya kar6i jikinsa, yana shirin fita kenan sai ga abokansa sun shigo, take kuwa suka fara yi masa tsiya akan tun jiya ya tafi ya 'kyalesu ko dai amarya ce ta ri'ke shi.
Shiru yayi musu kawai har suka gama be kula su ba, dan shi be iya irin wasan nan ba be ma san me ze ce dasu ba.
Sai da sukayi suka gaji har sukayi shiru, daga baya suka fara hira normal sannan ne yasaka bakin sa aka 'dan ta6a hirar da shi.
Anan aka kawo musu kayan break fast sukaci gaba 'daya still suna masa tsiyan na gaba sai agidan amarya.
Wannan karan kam murmushi Abbas yayi dan indai akan girki ne bazata bashi kunya ba saboda yasan Mummy bata barta haka nan ba.
'Daya daga cikin su ne mai suna Auwal ya tashi ya shiga ciki dan yana so yayi using bathroom, ai kuwa anan yaci karo da pant 'din Teemah da ke shanye a bathroom 'din,
har Allah-Allah yake kuwa ya fito dan ya baza kanu, aikuwa yana fitowa yaje gurin Abbas ya bashi hannu tare da fa'din " _mazaah!!, ashe angon cewa kayi yau din shiyasa naga kana ta shan 'kamshi!_ "
Kallon _me kake nufi_ yayi masa ha'de da harara yace " _ban son iskanci Auwal toh haramun nayi? Me ma kaje yi min acikin 'daki?_
Dariya duk sauran suka kwashe dashi suna nuna Abbas 'din, sosai yaji haushin hakan duk dama abinda suke zato 'din be faru ba amma ai wannan sirrin sa ne damuwar sa ma shine ya akayi har wannan tunanin yazo ran Auwal har haka, yariga yasan kayan ta data cire jiya ba'a fili yake ba sannan shi be ga wani abu a'dakin da zai sanya har mutun yayi masa wannan tunanin ba.
Basu wani da'de bama suka tafi, Abbas be bisu ba.
Suna tafiya kuwa yayi hanzarin shiga bedroom 'din yafara investigating 'dakin, still shi be ga komai ba dan hatta su bangles da earings 'dinta da sauran su ma ba'a fili suke ba balle yace ko dan sune tunanin sa ya bashi cewa wani abu yafaru, sai dai ko in Auwal bincike yayi masa har yaga wani abin mace shiyasa yayi masa wancan tonon sililin...