← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 132 OF 163

Sashe 132

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ranar da zai dawo ya sanar da ita da safiyar ranar bayan har Hannah ta wuce makaranta.

Ranar kuwa Teemah sam bata jin da'din jikinta sai dai bata ko sanar da Hannah ba dan kar tace bazata je school ba saboda hakan, jitake kamar anyi mata dukan tsiya a ga6o6in ta duk nayi mata ciwo.

Da 'kyar ta samu ta shiga 'dakin sa dan yau 'din ko le 'kawa batayi ba, babu ma wani 'kura da yake kullun tana gyara shi yau ne kawai bata yi ba, amma duk da haka sai ta daure ta fara da tsabtace bathroom sannan ta dawo 'dakin ta share ta kunna burner tare da canja bedsheet 'din dake kan gadon ta fito ta jawo 'dakin yana tashin dadda'dan 'ka
mshi.

Kitchen ta shiga inda sai data samu wuri ta zauna tukunna ta 'dan huta harda maida numfashi, zazza6i ne take jin kamar zai kamata.

Adaddadfe ta ha'da masa lafiyayyan abinci irin na hausawa wanda yaji kayan lambu dan ita yanzu sune cimar ta bata son ganin abinci batare da veggies ba.

Juice 'din zo6o ta ha'da masa mai 'dan karan santi ta sashi a fridge abincin kuma ta kai su dinning, tana dafe kai dan sosai take jin ba da'di a duk ilahirin jikinta, gajiya take jin na damunta.

Koda ta koma 'daki ma da 'kyar ta samu ta watsa ruwa tana yi tana hutawa yau ka'dai sai data fita a hayyacin ta, shirin ta tayi cikin wata doguwar rigar atampa data kama ta sosai daga 'kirji, ganin rigar zai takurata ne yasa ta cire ta canja da wata mai 'dan fa'di marar nauyi maroon colour sai ya 'kara fito da hasken ta afili.

Duk yanda take jin jikinta kuwa hakan bai hana ta neman abincin ba saboda mur'dan yunwan da cikin ta keyi mata.

Sosai ayyukan suka ja mata lokaci, tana idar da sallar la'asar tajiyo 'karan door bell, zuwa tayi ta bu'de 'kofan da fatan Allah yasa shine kowani wanda zai iya taimaka mata dan tasan Hannah kam da sauran lokaci tace ma zata bi gidan Ummah kafin ta dawo so zuwan ta yanzun da 'kyar ne.

Cikin sa'a kuwa shi'din ne, tana bu'de wa taganshi tsaye kafa'darsa rataye da jakar sa, fuskarsa ba yabo ba fallasa koda ya gantan beyi wani reaction ba sai ma ya tsaya yana mamakin canjywar ta na yanzun.

Teemah kam gaba 'daya sai tayi loosing control tasaki murmushi sai sannan ya maida mata martanin murmushin nata, dan farin ciki ma har bata san lokacin data fa'da jikinsa ba sai kuma tafara hawaye a tun safen da take jin ta wani iri 'din batayi kuka ba sai yanzu da ta ganshi, a hankali ta furta " _sannu da zuwa Yayah_ "

Abbas kam fuskar sa ba yabo ba fallasa sa6anin zuciyar sa dake cike tab da farin cikin ganin ta.

Bai amsa mata sannun data masa ba sai hannun sa 'daya dayasa shima ya rungume ta, jikin ta babu zafi illah 'dumi da yayi shiyasa ko'ka'dan Abbas be fahimci yanayin datake ciki ba.

Dayaji sau'kan hawayen ta a'kirjin sa ne ma sai ya 'kara sakin murmushi, zaton shi duk kukan na ganinsa ne.

A kunnan ta ya ra'da mata " _kin koyi rashin kunya ke ma ko? Shine harda kukan farin cikin gani Yayah_ "

Duk da yanayin datake ciki amma sai datayi murmushi ta 'dan motsa ka 'dan sai ya sake fa'din " _jakata zaki kar6a nagaji sosai fah_ "

Da sauri ta tashi a 'kirjin san tana mai sau'kar da idanun ta 'kasa dan kar yayi saurin fahimtar halin datake ciki.

Kar6ar jakan tayi batare da ta kalli fuskar sa ba tana jin ta cikin wani yanayin farin ciki marar misaltuwa.
Sanyin da ga6o6in ta sukayi ma duk sai taji ya ragu batasan dalili ba.

Abbas kam 'kura mata ido yayi da mamakin yanda take avoiding ha'da idanu dashi yau 'din bai san dalilin ta ba amma sai yaji hakan ya birgeshi ganin kamar tafara yin wayo ne tunda har take kunyar shi.
Cikin hakan sai kuma ya fahimci kamar akwai abinda ke damunta.

Bayan ta yabi da kallo har ta shige 'dakin sa da jakar sannan ya 'karaso cikin parlourn inda ya yada zango akan kujera tare da 'daga kansa sama ya lumshe idanu, yana tunanin damuwar tata ko ta mecece oho.

Wani zazzafan iska ya huro daga bakin sa take sai ajiyan zuciya ya biyo baya.

Teemah bata fito ba sai da ta ha'da masa ruwan wanka sannan ta fito inda ta same shi zaune ya jingina da jikin kujera, afili ta fahimci tsantsan gajiyan daya kwaso sai taji tausayin sa sosai dan tasan irin aikin su babu sau'ki sam.

Fridge ta wuce ta 'dauko masa ruwa mai sanyi da cup ta zo gefen sa ta zauna wanda hakan yasa shi ya 'dan bu'de idanu yabi jikinta da kallo.

Sai data tsiyayi ruwan sannan ta mi'ka masa, ya kuwa kar6a ya shanye, koda tayi yun'kurin 'kara masa sai ya girgiza mata kai tare da mi'ka mata cup 'din.

Komai cikin 'karfin hali take yinsa dan bata so tabawa 'dan 'karamin zazza6in data ke ji 'din 'kofar da zai sanya har ya dawo mata babba balle ayi mata zancen injection, she hate it at all.

Cup 'din ta ajiye agefe sai ta sau'ka ta tsugunna dai-dai 'kafafun sa tafara warware igiyar boot 'din dake 'kafar sa tare da socks 'din gaba 'daya ta cire su ta matsar gefe.

Tana jin 'dan nauyin sa amma haka ta daure ta kama 'kafar tasa ta dinga mammatsawa ahankali tana mi'kar da yatsun 'daya bayan 'daya.

Sosai Abbas yaji da'din hakan sai ma yasake lumshe idanu yana jin tamkar karta daina yi masa.

Bata wani da'de a hakan ba ta tatashi ganin agajiye yake dole zai bu'kaci freshing up saboda ya'dan warware sai ta dawo ta zauna inda ta tashi 'dazu daga gefen kujera a hankali ta fara 6alle masa botilan rigar tana 'kara sau'kar da idanun ta 'kasa.

Abbas kam yana jin hannun ta a'kirjin sa ya bu'de idanu yana kallon kan fuskar ta zuwa idanun ta amma ta'ki bari su ha'da idanu.

Bai hana ta ba dan yanda yake jin gajiya bai 'ki wan kan ma ta taimaka masa ba saima yake 'kara mamakin wannan sabon sauyin dayake gani daga gareta komai ma canja masa yayi, daga ita har rayuwar ta gaba 'daya.

Idanun sa ya lumshe ya sake yin baya da kansa Teemah kam har ta ji da'di taci gaba da 6allewan cikin natsuwa bata sani ba ashe a hakan yake 'karewa halittar ta kallo.

Gani yayi ta ko'de sosai farin ta ya 'karu, ga wani 'dan 'kiba datayi hips 'dinta ma suka 'kara fitowa sosai, aransa yace " _sam bata damuwa da rashina ji yanda tayi kyau ta 'kara 'kiba abinta ta manta dani da rayuwata."_

Har ta gama 6alle bottles 'din yana karantar yanayin ta, sai data gama kafin tayi 'karfin halin 'dago idanu ta sau'ke su akan nasa sannan tace " _Yayah saura kayi wanka ko sai kaci abinci tukunna_ ?"

Bakin ta kawai ya tsaya kallo harta gama maganar bai ko yi yun'kurin nuna alamun yaji bama balle tasaka ran samun amsar ta, aransa yake tunanin.....how on earth zai gaji da kallon wannan yarin yar? Angel 'dinsa, kyautar Allah, amanar sa, matar sa, kuma 'kanwar sa, his first and last lover wacce yake fatan ta kasance uwar 'ya'yan sa gaba 'daya kuma 'kar'kashin ikon sa har abada.

Acikin muryar ta ya 'dan fahimci damuwar dake tare da ita inda ya gaskata zarginsa saboda muryar ta kansa fizo shi takeyi ta harha'da kalaman data furta masa.

Tana shirin mi'kewa yasa hannun sa ya janyo ta sai ta fa'do jikinsa, zafi taji acikin ta dan yanda ta tafi ba shiri da sauri ta yamutsa fuska sannan tace " _awwshhh....Ya...._

" _.......Tell me! Me ke damunki_ ?"
ya tare ta da fa'din hakan.

Take sai ta tura baki dan bata san me zata ce dashi yake damun ta ba.

Turo bakin datayi ne yasa shi ya kai yatsan sa 'daya kan bakin ya shafa slowly tare da 'kara rage 'dan tazaran dake tsakanin su sannan ya sake fa'din
" _gaya min mana inji me yake damunki ko ciwon rashin Yayah ne ya shige ki sosai haka_ ?"

Goshi ta ha'de tare da niyyan fara gunguni sai yayi saurin 'daura bakin sa akan nata wanda hakan ya tilasta mata nutsuwa.

Passionate kiss ya bata wanda ya matu'kar ratsa ta har cikin jikinta tare da sake matso ta zuwa jikin sa sosai.

Door bell ne ya fara 'kara wanda yasa ta tafara mutsu-mutsun 'kwace jikin ta, ganin hakan sai Abbas ya sake mata bakin amma be raba jikin sa da nata ba, taga kamar baida niyyan 'kyaleta ga door bell nata bada sauti sai ta juya ta kallo 6angaren 'kofan tare da da dawo da kallon ta gareshi duk yana kallon ta.

Bu'dan baki tayi zatayi wata maganar sai yasa 'dan yatsan sa akan bakin nata hakan sai yasa tayi shiru tabi hannun da kallo sannan ta kuma maida kallon nata kan fuskar sa.

Sake matso da kansa yayi yabata wani peck a tsakiyan goshin ta wanda yasa ta har sai data lumshe idanu sannan yaraba jikinsa da nata sai ta mi'ke tsaye ahankali ganin ya sake ta shima take ya mi'ke tsayen kamar yanda tayi ya nufi 'dakinsa.

Teemah binsa tayi da kallo har ya shige sannan tasa hannu ta 'dauki
mayafin ta ta rufe kanta dashi ta tafi ta bu'de 'kofan.

Tana bu'dewa Hannah tace " _hala bacci kike yi da la'asar 'din na ko, tun 'dazu fah nake ta faman aikin danna bell amma shiru_ "?

_Comment Vote and Share_

*Salmerhn ku ce* 😍
[10/13, 1:58 AM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

~Dedicated to my family~ 🥰

*Bismillahir rahmanir raheem*

_Never be afraid to help others in their time of need. You never know when you may need that_ _shoulder to lean on_ .

🅿 *86*

Muryar ta ciki-ciki tace da Hannah " _har kin dawo_ "?
Chapter 132 · 0% Book details