← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 163

Sashe 32

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ku gafarceni dan Allah nasan dayanku sun k'osa kuji daga gareni amma kuka jini shiru wanda hakan yasa wasunku suka bini private sukayita tambayata nasan hakan duk cikin k'auna ce wasu ko harsun gaji da zuba ido sun hak'ura
.......

duk da ban samu lokaci nayi muku abinda kuke so akan lokaci ba amma nasan kun min uzuri sosai Allah yabar k'auna.(Ameen)

*Salmerh nayi muku* *fatan alkhairi*

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

Respect people’s feelings. Even if it does not mean anything to you, it could mean everything to them.

🅿 *29*

Ajiyar zuciya Munira ta sauk'e lokacin da Mahmud ya6acewa ganinta, take kuma sai murmushi ya d'an k'wace mata data tuno da mahaifiyarta tasan bata da wata matsala matuk'ar ta furta cewa yamata.

5minutes me kyau Munira bata k'ara ad'akin ba ta fito itama, dan ji tayi zaman ya gundureta tun bayan da Mahmud yabar d'akin hakan yasa ta mik'e tafito itama.

Azaton ta zata ganshi a harabar gidan ne, amma ga mamakinta ko kalar rigarshi ma bata gani ba ballanatana shi da kansa jitayi datasan inda yayi da babu abinda zai hanata zuwa kodan ta k'ara ganinsa ma kawai koda bazaiyi mata magana ba .

Haka ta taka ahankali taje ga motarta ta tayar tayi gaba zuciyarta fal farin ciki da ganin Mahmud d'in da tayi for the first time arayuwarta domin basu ta6a had'uwa ba sai yau d'in gashi kuma akayi sa'a shid'in ya mata 100%.

Shikuwa yana fita 6angarensa ya nufa ransa a matuk'ar 6ace dan tun ganinsa da yarinyar yaji yatsaneta sam bata birge shi ba, balle data k'ura masa idanun nan nata ji yayi kamar ya hauta da duka ma sa'anta d'aya shi ba mai saurin hannu bane inbahaka ba yace da mari zata sha d'azun dan yanda tabashi haushi.

Tsaki yaja lokacin daya isa d'akin nasa ji yake kamar ta shiga rayuwarsa ne dan yana cikin hutawansa tasa ya tashi ba shiri ya fito sai ya zauna abakin gadonsa yana wani jijjiga k'afa kai kace wani abin 6acin rai irin sosai d'innan akayi masa.

Nan kuwa bahaka bane ko tsanan Muniran dayaji yanayi ya samo asali ne daga tsanar daya yiwa duk wani wanda yake huld'a da Antynsa domin acewarsa duk ba alkhairi bane yahad'a su.

Munira bata jima da barin gidan ba Anty ta dawo kuma koda da dawo d'in da bataga Mahmud ba bata wani neme shi ba sai tayi zamanta apalournta ta hakimce kamar wata sarauniya.

Tunowa datayi da sak'on da sukayi za'a kawo mata saboda abinda yasa tadawo gidan dawuri ma kenan dan kar azo ba'a sameta ba gashi har sun shiga lokacin yanzu, dayake daman sun saka lokaci koda ta dawo d'in kuma sai bata tadda kowa ba agidan da alamun kuma sak'on ma bai iso ba har yanzu .

Wayarta ta lalu6o ta nemi numbern me aiko sakon ta kirata dan taji dalilin jinkirin da aka samu d'in.

Bayan sun gaisa ne matar take ce mata ai ta aiko ma already 'yarta ta taho zata kawo mata sak'on tad'an jirata kad'an bari ta sake ta6ota awaya taji inda ta tsaya.

"Ok" kawai Antyn tace tare da cire wayar daga kunnanta numbern Mahmud tasake k'ira tabashi umarnin zuwa yasameta a palourn sannan ta ajiye wayar a gefenta.

Mahmud kamar bazashi k'iran Antyn ba amma dai ya daure yatashi yaje wayar tasan ma ad'akin yabarta domin bayyi zaton zai jima awurin Antyn ba.

Da sallamarsa ya shiga d'akin yayinda Antyn ta amsa ciki-ciki kamar bata so ta amsa sallamar ko kuma kamat dole akayi mata ta amsa inba ka lura bama bazaka gane ta amsa d'in ba.

Jijjiga kansa yayi cikin takaici, sai da ya isa gefenta ya zauna kafin yace mata " wani lokaci kina abu kamar bada hausawa kika tashi ba Anty"

Ido ta zubashi mishi alamar tambaya take mishi batare data furta tambayar tata da bakinta ba.

Shikuwa sai yaci gaba da fad'in " yanzu fi sabilillahi tsabar isa sallamar ma sai kin ga dama kike amsata Anty?"

Azafafe Antyn ta amshe maganar tasa da fad'in " toh d'an ayi,ubana malam Muhammadu, kadawo kuma ko zaka fara takur min, nagade ni ce na haifeka kuma tun kan ahaifeka nasan ana sallama aduniya ko kai zaka koyamin yanda akeyi yanzu?

Murmushi yayi dan ganin yanda Antyn ta hayyak'o masa kwata kwata ya rasa matsalar matannan sam bata son gaskiya ita.

daga magana kuma Anty sai ki hau.........

Kar6e maganan tayi da fad'in ehh banaso.

Kawai sai ya bata hak'uri yana murmushi dan ya shatantar da zancen, sai yace tunatarwa ce fa kawai nayi Anty kinsan ni bakina baya shiru idan naga abu shiyasa.

Kauda kanta tayi cike da jin haushi ganin hakan yasa shima yaja bakinsa yayi shiru.

Haka sukayi zaman kurame kusan na mintina goma babu wanda yasake yiwa wani magana illah Anty dake d'an jan tsaki time to time wanda yake da harshen damo domin haushin nata biyu yazama, gana mahmud gana Matar da tasata jiran sak'o kuma tasa6a lokaci.

Harji takeyi ai badan tana matuk'an buk'atar abinba da cewa zatayi tafasa su bari kawai.

Daga k'arshe sai Mahmud ya mik'a hannunsa yajawo remote ya kunna T.V domin katse zaman shirun da sukeyi dashi da Antyn tasa.

Jiyake kamar ya bud'i baki ya tambayeta dalilin k'iran datayi masa amma ganin yanda tasha mur sai ya hak'ura da tambayar, yana matuk'ar so kuma ya tafi yabar d'akin domin akwai inda yake son zuwa sai dai ayanda yasan halin Antyn yasan bori zata masa kar kuma tace ta k'ira shi yak'i ya saurareta saboda ya rainata.......wannan dalilin ne yahanashi barin d'akin kawai ya kunna T.V duk da ransa ba son kallon yake ba amma dan dolensa ya kurawa T.V d'in idanu dukda baya wani fahimta sosai, jira yake yaji ta anbatoshi amma shiru.

Sun kai 20 minutes zaune agurin sannan yaji anturo k'ofar parlourn tare da fad'in "ex.......cuse me........."

Da tura k'ofar da yin maganan da kuma shigowan duk sun faru ne adaidai lokaci d'aya.

Da mamaki Mahmud yasake juyawa ya kallo k'ofar dan ganin waye mai wannan rainin hankalin, kawai sai idanunsa suka sauk'a akan yarinyar daya gani d'azu, shi harya manta ma da ita bacin yanzu da ya sake ganinta.

Kallon inda Anty take yayi sai yaga yanda take 6are baki tana dariya wa yarinyar kamar ba ita ce mai uban fushi da tsaki ad'an wasu takaitattun lokutan da suka gabata ba, ga dukkan alamu bak'aramin farin ciki tayi da zuwan yarinyar ba.

Mahmud sai ya jijjiga kansa kawai yakuma maida dubansa ga T.V d'in tare da fad'in " ALLAH YAH SHIRYAH".

Munira kuwa zuwa tayi ta zauna akusa da Antyn tana murmushi suka gaisa da juna bayan sun gaisa d'in ne Munira tace harfa nakusan isa gida ma sai mummyna ta k'irani tace wai kindawo in sake komowa.

" kardai kice min kin zo bana nan"?
Cewar Antyn ta fad'a da kulawa

" ehh nazo mana wannan be sanar miki ba" Munira ce ta fad'a tare da nuna inda Mahmud yake zaune da idanu tana d'an satan kallonsa.

"Humm zai fad'a min ne wannan me mugun halin ?"

Antyn tafad'a tare da ta6e bakinta gefe.

Shikuwa ko kallonsu ma baiyi ba sai yayi kamar irin bai san ma dashi sukeyi d'innan ba.Amma acikin ransa bak'aramin haushin Kalmar mugun hali da Anty ta ambace shi da shi agaban yarinyar nan yajiba.

Yana gani Munira ta ciro sak'on Antyn tabata a leda bak'i, bama wani abu me yawa bane amma yaga duk farin ciki da walwalar Anty ya k'aru alokacin datayi arba da sak'on a hannunta.

Haka kawae yaji zuciyarsa taraya masa ba abun kirki bane aka kawo mata bana arziki bane abin.

Koda Munira ta mik'e da niyyar komawa inda ta fito sai Anty ta mik'e da fara'arta take tambayarta wae da abun hawa tazo ne?

Da " ehh"
Muniran ta amsa mata.

Sai Antyn tace dama wae ko Mahmud zai sauk'e tane amma tunda da mota tazo shikenan.

Yana ganin yanayin canjin fuska atake agurin Munira amma sai ta d'an basar tace " bakomai akwai wataran ai"

Amma aranta bak'aramin haushi taji ba na missing wannan damar datayi.

Acewarta aida tasan abinda Antyn zata ce kenan da bazata ce da mota tazo ba....,,..,,....(nikuwa nace ai danasani k'eyace Munirah)😜.

Anty dakanta tarakata har wurin motar tata suna takunsu kamar wasu k'awaye.

Lokacin data dawo daga rakiyar kuma bata sami Mahmud a palourn ba shima tafiyarsa yayi dayake daman hanya yake nema shima.

Koda ya koma d'akin nasa misscalleds yatarar awayarsa kusan 5 , ciki kuwa harda na Abbas guda d'aya da sauran abokanshi da kuma wanda suka yi dashi akan zasu had'u yau.

Saida yasamu yazauna duk ya bisu da k'ira kafin yayi shirin fita inda zashi d'in.

Mayafi Anty ta k'ara d'auka ta nufi gidan k'awarta Anty chideh.

Lokacin da Anty tashiga gidan shiru taji ba motsin kowa koda tata knoking sai taga ba'a amsa mata ba sai kawai tabata uzurin ko Anty chidehn na wanka ne shiyasa.

Saita turo k'ofar tashigo ciki kanta tsaye,
amma saidai me........ wani gani da Anty tayi har sai da takusan kwara amai a inda take d'in take tayi fatan kar Allah yasake nuna mata irin wannan abin har abada.

tana k'ok'arin juyawa sai Anty chidehn ta hango ta, yunkurawa tayi da niyyar tashi ta zauna sai hakan yabawa abokiyar masha'artata dama tafahimci meke faruwa dalilin d'ago kan datayi.

Sai jiyo muryar Anty chidehn tayi tana fad'in " ah' ah mum Mamud why did u stand there"?

Hankalinta akwance tayi maganar kamar ba wacce aka ganta ta ke ayyakata babban sa6o ba.

Anty kamar bazata juyoba sai ta daure ahankali ta juyo sukayi 4eyes da Anty chidehn, murmushi tayi mata yayinda Anty tasha mur sosai dan kokad'an bata ta6a kawowa aranta Anty chidehn na irin wannan harkar ba.

Tashi Anty chiden tayi ta zauna tana 'ko'karin lullu6e jikinta tace " k'araso mana "

Daurewa Antyn tayi ta k'araso chiki yayinda takasa d'auke idanunta daga kan house maid d'in Anty chidehn wacce zuwa yanzu tafahimci ba house maid kad'ai yarinyar ta tsaya ba harda........

Koda ta iso ma dakyar tasamu guri ta zauna jikinta duk yayi sanyi.
Chapter 32 · 0% Book details