← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 143 OF 163

Sashe 143

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda an lallasheta ta'ki ji kawai sai abarta, dayawan mutane ma ai sunyi surviving batare da sunyi karatun ba, so ba matsala bane dan ta 'kiyi rayuwa duk tacgaji haka, wani zaka yasamu amma yana 'kinyi yayin da zakaga wani yana fafutuka da 'karfin sa da komai dan kawai yaga yasamu, wani kuwa duk ma sai kaga babu damar, domin bai samucgatan ayi masan ba kuma shima sai kaga Allah bai bashi hanyar da zai nema da kansa ma ba sanadin haka dole sai kaga mutun ya ha'kura gaba 'daya, amma duk hakan ba laifi bane face salo na rayuwa kawai domin kowa da kalar tashi 'kaddarar.

Balle ga ita data ke matsayin 'ya mace ai zaman auren shine gaba ayanzu, matu'kar zata zauna a hakan cikin kwanciyar hankali ta bautawa ubangijinta ta kuma yiwa mijinta biyayya to shi bashi da matsala da ita burinsa dama tayi farin ciki.

Abbas Daddy ya 'kira yayi masa bayani tare da bashi ha'kuri akan maganar yace ya 'kyaleta kawai tunda bata yi ra'ayi ba, wata 'kila watan wata rana ta nemi yi dakanta lokacin da ra'ayin hakan ya shigeta.

Abbas bai so hakan ba amma ya ha'kura shima ya bar zancen kawai, amma sosai ya jinjina wa kafiya irin tata, ace mutun karasa abokin gaba sai karatu.....gaskiya abin da mamaki, yasha jin labarin irin dramar da ake sha da mata akan karatu amma nata salon daban ne, maimakon tayi fitinar an hanata yi ah ah sai ma fitinar ita bataso.......ha'ki'ka duniya kowa da kalan halin sa, abinda kake ganin dai-dai ne awajen ka sa6anin hakan kuwa ga wani sai ya zama abin gudu da 'kyama na musamman, sosai yake 'kara jinjina mata a duk lokacin daya tuno duk lamarin hakan yafi matu'kar ri'ke ransa.

Shima kuwa Abbas sai yace in dai hakane kuwa ba ita ba zaman Abuja dole tabishi Porthacourt, wannan karan Daddyn Abuja bai hana shi ba dan yasan shi ke da iko akan iyalinsa, ko wancan lokacin ma ya hana ne dan gudun kar ya cutar da ita, amma zuwa yanzun ya fahimci akwai 'yar fahimta a tsakanin su, kuma ma idan yacigaba da shiga tsakanin zaman nasu to bazasu ta6a sabawa da juna ba musamman idan akayi la'akari da yanayin aikinsa ba ya basu damar da zasu sake da iyalansu kamar kowa, kuma kusancin da ke tsakanin su shi yafi komai muhimmanci, abinda Ummah tayi ta 'ko'karin fahimtar da shi kenan tun a wancen lokacin amma yakasa fahimtar ta son 'yar sa da gudun kar a cutar da ita yayi wa zuciyarsa 'kawanya a lokacin ya hana shi ganin gaskiya.

Teemah bata damu ba sai ma da'di da taji coz ko itama yanzun baso takeyi take yin nisa da mijinta ba ko dan ma ta cigaba da faranta masa, saboda ita ka'dai tasan halin da ta shiga wancan lokacin daya tafi ya barta.

Ko ta je Rivers 'din kuwa bai nuna mata 6acin ransa ba koka'dan akan abinda yafarun duk ya fitar aransa dama dan ita ne to ita wacce za'a yi domin tan kuma tace bata so to shi miye na shi.
Itace ma take 'dan jin fargaban ha'duwar su saboda tasan bata kyauta masa ba dole ransa zai 6aci da ita amma da suka ha'du ta gansa wasai sai itama ta saki ranta.

Abbas rungumar matar sa yayi cikin walwala da farin ciki suka cigaba da rayuwar su.

Amma Teemah kasa daurewa tayi sai data bashi ha'kuri daga baya domin guilty conscious ya kasa barin ta sai take ganin tamkar kawai yana kallon ta ne da abin aransa batare da ya furta ba, ga mamakinta kuwa sai yace mata ai bakomai karta damu komai ya wuche shi awaken sa.
Sosai Teemah taji da'din hakan har cikin zuciyarta.

Cikin cinye-cinyen Teemah kuwa babu abinda ya ragu aciki Abbas har ma ya saba da komai yanzu kuma ko damuwa ba yayi da canzawar ta balle yayi wani tunani akai, kawai ya bari akan lokacin cin abincin nata ne yayi shiyasa abinda kawai yasa aransa kenan duk kuwa da yasan cewa sam ba halinta bane hakan amma baya damuwa, ga wani shegen son sex daya shigeta yanzun, wannan ne ka'dai ya tsaya aransa, shi kansa yanajin da'din kasance wa da ita sosai fiye da baya har ma hakan yasa baya ta6a gajiya da kasancewar ta su be it shi ke so ko ita ta nema sam baya ta6a 'kin amincewa da hakan, sai dai wani lokaci takanyi ciwon mara, akan hakan ne yaso suje ganin likita amma tsoron kar ayi mata allura yasa ta'ki bashi ha'din kai.

Abbas hankalin sa sai yakasa kwanciya da hakan sai ya shirya mata wani shiri batare da ta sani ba akan tunda bata san clinic ba anan garin da wayo zai kaita asbitin yasan in sun riga sun isa dole ne ta tsaya a dubata dan gudun kar ya cigaba da biyeta yana bin ra'ayin ta kuma abubuwa su zo su girmama su fi 'karfin tunaninsa a 'kurarren lokaci duk dama ba'a fatan faruwar wani mummunan abu amma wai akace maganin kada ayi toh fa kada asoma shi yafi.

*****
Kwance take.........

👎🏻
_Ina gaida mutane na makarantan wannan littafi ina kuma yi muku albishir 'din cewa just some few pages ne suka rage mana mu kammala wannan labarin sai dai alal ha'ki'ka ni kaina bansan zuwa kwana nawa hakan zai 'dauke mu ba gaskiya, fatan dai zaku cigaba da samba'do madaran comment wanda zasu rin'ka sani yi muku typing akan lokaci koda kuwa ban shiryawa hakan_ _ba......lolz_ 🤪.....
*A KAFTAH* 🤞🏻

_Comment_
_Vote_
_Share_

*Salmerh ce*😍
[10/13, 1:58 AM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

👇🏼
Assalama Alaiki warahamatullahi wa bara katuhu. Gaskiya salma na yaba maki da wannan novel naki mai suna *captain Abbas* Allah ya kara basira ameen summa Ameen.
*From*
_Abubakar Saleh Al~Quyraemey_
*Ngd 'dan uwa, i really appreciate....nd i dash ths page specially 4u where ever u ar*👍

😍 *Dr.Khausar* Allah ubangiji ya baki lafiya ya kuma albarkaci baby ya sa ta cikin bayinsa salihai.( *AMEEEN* )

*Bismillahir rahmanir raheem*

_Every heart has a pain......only d way of expression is different.....some hide it in eyes while some hide it in their smile_ 🤞🏻

🅿 *90*

Kwance take akan kujera mai zaman mutun uku jikin ta da wata rigar bacci sharara mara nauyi, rigar 'yar 'karama ce dan ko cikin ta bai gama rufe wa ba sai 'dan wandon rigar mai d'an fad'i da ka'dan ya wuce mata gwiwa shima, sosai take jin da'din kayan dan rashin nauyin su da kuma yanda take sakewa cikin sa idan ta sanya su.

Yayin da Abbas ke zaune facing nata akan wata kujerar daban yana kallon CNN gaba 'daya hankalinsa na kai ganin an kai hari ma wani 'kauye inda aka yi musu kisan gillah manyan su da yaransu kuma gwamnati takasa yin komai akan hakan, abin haushi yake bashi na yanda ake 'daukan rayukan al'umma batare da wani 'kwa'k'kwaran dalili ba tamkar baza'a mutu watarana aje fadar Allah domin kar6an ayyuka ba, mutane mantawa sukeyi da hakan...... time to time yana sipping mango juice da Teemah tayi masa 'dazun nan.

Hannun ta 'daya na kan cikin ta sai aikin shafawa takeyi a hankali tana lumshe idanu tana feeling yanda cikin nata ya 'dan d'ago ka'dan wanda tun ba yau ba ta fahimci hakan, hatta Yayah ma sai da ya tsokane ta akai last three days wai Fatee bombom mai tummy, ta kuwa ji haushi sosai dan ranar kuka ta ringa yi masa kafin da 'kyar ya daina tsokanan nata amma sai ya cigaba da yi mata dariya.

Ita kanta ma ba so take yi ba abin na bata haushi sosai, musamman da yake tasan cewa ba komai ne ya jawo mata hakan ba face yawan cin abincin nan da take yi.
Murmushi tayi lokacin da ta tuno yanda kwa'dayin awaran 'kwai ya sa ta a gaba 'dazu da rana lokacin ita 'daya ce a gida Abbas na office, sai ta tashi taje ta ha'da komai ta yanyan ka 'kwan bayan ta dafa shi sannan ta sake ka'da wani 'kwan ta wadata shi da albasa da da 'dan maggi dan yanzu bata fiya son taji 'dan'danon gishiri abakin ta ba, tafiya son tajishi da nisa sama-sama, in abinci ya kasance hakan kuwa har wani santi yake sata tana jin da'din sa sosai.
Dududu da 'kwai biyar tayi amfani har ta gama.

Sauce tayi na zallan attaruhu da shima yaji albasa na fitan hankali da spices ta harhad'a abinta a plate tazo ta ajiye, bata ma tsaya a parlour ba sai ta wuce 'dakin ta da abincin, bata bu'katan wani juice a lokacin ruwa kawai take jin ya isheta dan haka sai ta 'dauko mai 'dan sanyi ta shige ciki.

Har Allah-Allah take yi taji shi cikin bakin ta dan yanda take jin kwa'dayin nasa abin har na bata mamaki.

Bata 6ata lokaci ba ta fara aikawa dasu bakin ta inda da'din sa ke ratsa mata har cikin zuciyar ta tare da sauk'ar mata wani nutsuwa na bam mamaki irin rai ya samu abinda ke so d'in nan kuma at d right time.

Ci takeyi a hankali tana korawa da ruwan sanyin ta, in kaga yanda ta nutsu take cin abincin har zakayi zaton ko shine abu na farko da yafara shiga bakin ta a yau 'din.

Sai dai bata ko ci rabin sa ba taji lokaci d'aya amai ya yun'kuro mata, ido ta zaro ta tare da gumse bakinta da k'arfi tana mamakin silar faruwan hakan sai taji ya sake yun'kuro mata da karo 'daya ai bata san lokacin da ta ajiye plate 'din agefe ba tayi cikin bathroom, amai ta ringa kwarawa har sai da ta amayar da duk abinda ke cikin ta a lokacin sannan ta fara sau'ke numfashi.

Sosai taji ta galabaita sai ta jingina bayanta da jikin sink 'din tana maida numfashi bayan ta tsabtace wurin.
Chapter 143 · 0% Book details