← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 163

Sashe 6

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana fitowa kuwa wajensu daddy tafara zuwa ganin basanan sai ta nufi wajen su mummy,tana shiga da sallamarta tafara tambayar mummy "ina su daddy suka je kuma,?
harararta mummy tayi, da me zaki musu? Mummyn ta tambayeta.

sai ummah ce ta bawa Teemahn amsa da fad'in "sun tafi masallaci ne zasu sallaci jumma'ah"

"Ohh na manta ne ummah ashe fah yau Friday"

Daya taga reaction d'in mummy data shigo,mummy da harara tabita kuma tasan ma'anar hararan haka yasa yanzun bata zauna ba ta kuma ficewa daga d'akin,don tasan in bata fitan ba mai zai biyo baya anjima ko gobe,kunnan ta ne zasuji ajikinsu.

Mummy bata son wai taringa zama a inda ta ke matuk'ar tana tare da bak'i.Dan yana rushe tsarin tarbiyar yaro.Itama dayake tasan abinta sai kawai tafice can bayan gidan tayi zamanta a inda taga yafi mata da'din zama.

Da lokacin sallah yayi ne ta koma ciki dan ta yi sallahr itama.

Bayan su daddy sun dawo ne aka had'u agun cin abinci,kowa yana ci amma banda teemah da bai fi spoon biyu taci ba kawai,Daddyn abuja ne ya hankalta da ita hakan yasa ya tambayeta ko bata jin dad'in abincin ne?

Murmushi tayi masa batare datayi masa magana ba.

Daddynta ne ya bawa daddyn abuja amsa da fad'in

"da de kayan itatuwa ne da ba sai ka 6ata bakinka wurin sata ciba ,amma abinci kam ni har na gaji da yi mata magana akai ma"

Da kyar ta dage tad'an ci abincin dan yadda taga daddyn abuja yadamu da rashin cin abincin nata, bai san cewa wannan d'in ma daure wa tayi tafara ci ba dan ganin suna nan,amma in su kad'ai ne ita da iyayenta ma ko kula dining d'in batayi musamman in abincin rana neh,su har sun riga da sun saba da wannan halayyar tata.

Kwanan su Daddyn Abuja d'aya washegari suka koma Abuja,dayake daman wani abu ne yakawo su garin,shine har suka kwana.

Teemah jitayi kamar ta bisu da zasu tafin don ita akwai son mutane sosai.

Baifi wata biyu da tafiyarsu ba Daddynta ya shirya wai zasu je passing out d'in Abbas a katsina shida su daddyn Abuja,Allah ya kiyaye kawai Teemah tayi mar tare da fad'in ya gaida mata da su ummah da daddy.

Har gun mota suka rakashi
"shiga yayi bayan ya amsata driver yaja suka tafi airport.

Haka suka je lapiya qalau cikin ikon Allah.acan suka had'u da su daddyn Abujan har sun rigashi isa ma.

Abbas yayi murna da zuwan Iyayen nasa,inda suka gama abinda yakawo su cikin sa'a har zasu tafi ma sai kuma Daddn yace su jira Abbas d'in kawai inyaso su taho tare tunda shima washe gari zai tafi.

Kud'i sosai su daddy suka kashe kafin Abbas yasamu wannan matsayin,don da farko har daddyn Abuja ma yace wai sai dai Abbas d'in ya hak'ura ya bari ya nemi wani aikin,amma daddyn Teemah yace sam baza'ayi haka ba, don sanin daya yiwa Abbas tun yana k'arami burinsa kenan,Burinsa yazama sojan Nigeria,dan haka ya dage sai da yaga burin Abbas ya cika,don acewarsa rashin bada muhimmanci akan al'amarin yara yana matuk'ar affecting d'in cigaban yaran.don haka ya tsaya tsayin daka ya shiga ya fita har sai da yaga burin abbas d'in ya cika kafin ya samu salama.Dayake daddy yana da manya kuma yabi masa ta sama ne,kuma short service yaje, shima Abbas d'in ya shak'i karatu sosai shiyasa cikin sa'a yafito da babban matsayi, amma kafinnan fa aljihun daddy sai da yayi kuka.

A can katsinan aka barshi ba aka kaishi ko'ina ba amma kafinnan sai yayi hutu tukunna zai koma gaba d'aya.....

*Salmerh* 😍

share pls👌🏻
[10/2, 5:50 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh md*

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

Dedicated
2
_my family_ 😍

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

Why do we often feel like we can speak with authority on someone’s life? How can we when we’ve not experienced what the other person has; we’ve not walked in their shoes. We have the tendency to stereotype people and think like we know it all.
*The* *truth is we don’t!*

🅿 *6*

Da zasu dawo su baro katsinan Abbas bai bi su ummahn sa zuwa Abuja ba sai yabiyo daddyn Teemah suka taho tare.

Yanda yatarar da gidan ya matuk'ar birgesa,musamman yanda aka canja tsarin gida ya koma na zamani,hakan ya k'ayatar dashi.Aransa yakejin ai hakan yafi da ace ana ta canje canjen muhalli ana bin zamani ai gara ka renovating wanda kake dashi in hakan zai yiwu.

Sosai yaji daddyn ya burgesa da irin yadda ya maida gidan "so take away😘
Bakamar daddynsa da kullum cikin canja muhalli suke ba.

Lokacin da suka dawo Teemah na school,bayan ta dawo ne ta tarar da daddyn ta ya dawo,murnar kamar tacinye sa d'anye.Inka ganta sanda ta ke murnar zaka zaci tafiyar shekara guda yayi,nan kuwa kwanansa uku kacal da barin gidan.Sai data gama murnar sannan daddy yace toh taje ta gaida yayanta,shima yazo yana d'akinsa,Zaro ido tayi waje sannan tace "daddy wani yayannawa?"

"Abbas neh angel ,Abbas na Abuja."
Daddy ya bata amsar tambayar data yi.

"Owk"
Tacewa daddyn
Sannan ta k'ara da "amma daddy barinje incire uniform d'innan tukunna"
Tafad'a tana kallon fuskar daddyn nata.

"Uhm,jeki cire abinki"
Daddyn ya bata amsa da haka.

Tashi tayi ta sannu ta d'auki school bag d'inta,harta fara tafiya sai kuma tace ''daddy ina mummy fah"

"sai yanzu kika ga daman tambayar inda nake ko?

"Wato dan kinga daddynki ko?

Muryar mummy tajiyo tana fad'in hakan,yayinda daddy yafara dariya k'asa 'kasa.

Waigowa Teemah tayi nan ta hango mummyn awajen dinning tana k'ok'arin daukan abu.

Karakata kai tayi gefe .

Mummyn ko kulata ma batayi ba,data d'auki abinda zata d'auka ficewarta tayi tabarta a inda ta ke tsaye.

Daddy ma kauda kai yayi kamar bai san meke faruwa ba.

Ganin haka yasa ta fice kawai daga parlourn, d'akin ta ta nufa,kamar yanda tasaba sai da tacire uniform d'in kaf,kafin nan tanemi towel ta d'aura ajikinta.

Toilet tashiga ta watso ruwa tare da d'auro alwala,Shiryawa tayi cikin wata gown na material marar nauyi,d'inkin ya mata kyau yayi cifcif dajikinta wani k'ara min gyale ta d'auko wanda bai ma fi ak'ira shi da d'ankwali ba,ta yafa akanta.

Parlourn ta koma ,dan ita kwata-kwata tama manta da batun wani yayah,amma haka sai tana jin ranta wani iri sai taji bata da nutsuwa.

Daddy tasamu still azaune yana kallon news d'in rana,aranta tace

"daddy da news badama."

Shiganta keda wuya tun ma kafin ta zauna kamar had'in baki sai ga mummy ta 6ullo ta itama har tayi wanka tacanja sutura.

muryar Mummyn tajiyo tana fad'in "yauwa Teemah yiwa yayanki magana kinji,lunch is ready".

Dum taji zuciyarta ta amsa,bata san dalili ba,amma tafi kyautata zaton k'ila dan ta jima bata had'u dashi bane shiyasa.

Dayake daman bata kaiga zama ba,sai kawai tajuya ahankali ta fara tafiya dan zuwa aiken mummyn.

"Ni kinma je kin gaidashi kuwa?"
Tasake jin muryar mummyn tafad'I.

Kai ta jijjigawa mummyn batare data waigo ba dan duk jitayi jikinta yasaki.

"baki san yazo bane?
Mummyn tasake tambayarta.

Ynzun kam saida ta waigo kafin tace "nasani mummy,d'azu daddy ya fad'amin,daman inada niyyar zuwa"
Kai alanga6e tayi maganar kamar zatayi kuka.

"Hmm"
kawai mummyn tace,daganan bat qara kallon inda Teemahn ta ke ba.

Daddy kam k'ala bai ce musu ba.
Juyawa tayi taci gana da tafiya,koda taje k'ofar d'akin nasa ma jitayi kamar karta shiga,amma data tuna cewa mummy ce ta aiketa aikawai sai tayi shahada ta tura k'ofar ahankali tashiga sannan ta maida k'ofar ta rufe,gani tayi d'akin duhu bak'i k'irin ba haske,neman inda switch yake tayi ta danna,amma still ba haske.

Hakan ya tabbatar mata da cewa bulb d'inne suka lalace,kuma dayake ba'a cika amfani da d'akin ba shiyasa babu wanda yabi takansu,ballantana a canza su.

Ahankali ta k'ara cikin tsakiyar d'akin jitayi shiru ba alamar motsi,sai de uban k'anshin turaren da yau ne farkon fara jinta dashi,da kyar ta tattara la66anta ta harhad'a sunansa.

"Yah....yah Abbas"!
Shiru taji

"Yah Abbas"!!

Ta sa ke maimaitawa amma still no answer.Juyawa tayi tafita daga d'akin,taje tasanar da mummy akan bayanan Yah Abbas d'in.

"Babu inda Abbas yaje Teemah,k'ila ko zuwa bakiyi ba"
Cewar mummy

Teemahn ne ta kar6e da fad'in.....

"Allah naje mummy,kuma fah d'akin duhu ba haske".

D'auki wayata ki haska,maza kije ki dubo minshi, inaga ma bacci yake saboda gajiya"

Tana d'aukan wayar tace "mummy harfa k'ira nayi amma babu wanda ya kulani"

"Shine ai nace ki duboshi in bacci yake karki tasheshi,ki dawo kawai"k'ila ma dakika ga duhun k'in shiga kika yi ko?

Kwa6a fuska tayi
"Nashiga mana mummy "

"Naji toh ni sauri ki dawo"
Mummyn tafad'a sannan takawar da kanta gefe.

Fita Teemah tayi ta nufi d'akin Abbas d'in,data isa bakin k'ofa zai ta tsaya ta kunna hasken wayar kafin ta tura k'ofa tashiga.

Ko sallama batayi ba don ita azatonta babu kowa ad'akin kamar yanda ta tarar dashi d'azu.

Saida ta maida k'ofar ta rufe kafin ta d'aga hasken hannunta haska,Hasken ya gama haska ilahirin d'akin ,don wayar mummyn badai haske ba.

Mutum ta hango a tsaye dogo mai d'an hasken fata,k'ugunsa d'aure da towel,wuyansa ma wani towel d'inne rataye kuma duka farare,hannunsa d'aya riqe da man shafawan daya d'auko da niyar shafawa, jin an6ud'e masa k'ofah batare da neman izini bane yasa ya tsaya,dan yaga wani gwani ne wannan.

Ko tsoro bataji ba tasake daidaita hasken asaitinsa a k'ok'arinta naganin wannan mutumin da akace wai shine yayanta.

Hannunsa d'ayan ya d'aga ya kare hasken dashi,dan ta saita masa ne afuska,sannan ya mik'a d'ayan hannun ya ajiye man shafar.

Kallon mai haskashin yake da mamaki,so yake yaga waye wannan d'in,amma dayake hasken ahannunta yake sai hakan ya hanashi ganinta dakyau.

Takowa yafarayi zuwa inda ta ke tsayen,amma still bai sauk'e hannun daya d'aga dan kare hasken dashi ba.

Bata motsa ba,kamar yanda bata kawar da hasken daga saitinsa ba,sai da taga yakusan cimmata kafin tajuya bayan ta yada wayar agurin,ta nufi k'ofa da gudunta.

Tsayawa yayi cak,daga inda yake tsayen, sai ya kama kunkumi da dukka hannayensa biyu gefe da gefe,yabi bayanta da kallo,harta k'arasa bakin k'ofar.
Chapter 6 · 0% Book details