← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 163

Sashe 104

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da daren ranar kuwa sai Daddy ya 'kira Teemah yafara da bata ha'kuri akan tafiyarsu Dubai batare da ta sani ba, da kuma lokacin rasuwar Mahmud da be tsaya ya tausheta ba be wani ke6e da ita a matsayin sa na uba ya bata baki ba wanda shi kanshi yasan be kyauta ba, sai de alokacin tsananin tausayin ta da yakeji ne yasa hakan, ya kara da fa'din mata batun gadon ta wanda aka bata cewa komai a hannun Abbas sai yanda sukayi, yana cikin maganar ya shigar da batun auren da ake kai ayanzu, inda yaringa 'ko'karin fahimtar da ita cewa bawai rashin gata ko so bane yasa duk hakan ke faruwa face tsananin son da ake mata.
yace
" _duk abinda zanyi ina yi ne Fateemah saboda ke da farin cikin ki, abaya ni na za6a miki mijin aure wanda Alhamdulillah kin cika 'ya ta gari Fateemah da_ _kika yi min biyayya wanda har shi Marigayin_ _ya koma ga mahallici banji wata sa6ani a tsakanin ku ba, naji da'din haka_ _sosai da kika amince da za6ina Fateemah yau ga ni na sake dawowa da_ _wani 'ko'kon barata, kuma mai girman gaske ban sani_ _ba ko zaki iya tayani cika shi!, a karo na biyu Fateemah na sake za6a miki mijin aure wanda na yadda da nagartar sa, nasan yanzu 'yancin kine ke keda wannan damar kuma addini ne yabaki, amma na shiga gabanki_ _na tauye ki, kiyi ha'kuri Fateemah ki ya femin sannan_ _kimin uzuri ki kar6i za6ina, duk abinda zanyi ina 'ko'karine inga na baki abinda nasan ya dace_ _dake domin na tabbata ba zakiyi kuka dashi ba ba zakiyi dana sanin amincewa da za6ina ba insha Allahu_ "

Fateemah kuka takeyi sosai amma na zallan hawaye, hawayen ta ya kasa tsayuwa, kuma ta kasa bu'dan baki tayi magana aranta take fa'din " _na amince Daddy na amince da za6inka, ni 'yarka ce kaine ka haifeni kabani dukkan gata insha Allahu bazan ta6a_ _baka kunya ba, bazan ta6a bijirewa umarnin ka ba, bazan ta6a cewa_ _me yasa ka aikata hakan agareni ba_ "

Hakan takeso ta furta amma bakinta yayi mata nauyi ga kuka daya ci 'karfinta sosai har sai da Daddyn Abuja ya sanya baki shima yayi ta rarrashinta kafin tayi shiru ta tsagaita kukan amma dayake daga zuciyarta kukan ke tasowa sai hawayen ta ya kasa tsayuwa gaba 'daya, dole cikin kukan ta tabbatar wa Daddy amincewar ta.

A tare suka ha'da baki wajen sanya mata albarka da kuma haske mai 'dorewa har 'karshen rayuwarta sannan suka sallameta.

Tana jin 'kunci, takaici da ba'kin ciki ga memories 'din Mahmud da ya dawo mata sabo yabi ya cika mata zuciya tab amma ko dan irin yadda taga farin ciki kan fuskar iyayen nata ma dole zatayi musu biyayya dan kawai ta faranta rayukansu kuma taci gaba da ganin hakan har abada hakan ma ka'dai ya isheta.

Kwance take akan gado amma hawayen ta duk yabi ya ji'ka pillown jagab kamar wanda ruwa ne ya zuba akai, ita kanta tana so ta daina kukan amma hawayen ta yakasa tsayuwa.

A wannan halin Hannah ta shigo ta same ta tana kan kukan, tana jin motsin Hannah kuwa ta taso ta taho gurinta ta rungume ta sai yanzu ne sheshshe'kan ta ya bayyana, Hannah ma duk jikinta yayi sanyi sai de bata raba 'dayan biyu cewa maganar aurenta taji shiyasa take kuka, dan haka sai ta bata chance sai da tayi kukan ta isheshshe sannan ta fara bata ha'kuri wanda da 'kyar tayi shiru har sai da Hannah tace zata je ta sanar da su Mummy cewa tana kuka kafin ta 'dan sarara ta sanar a Hannah meke faruwa.

Hannan bata yi mamaki ba danta riga ta sani dan haka sai ta ringa lallashinta tana bata ha'kuri har ta samu tayi shiru.

Abakin Hannah taji labarin cewa Yayah Abbas shine mijin da za'a aura mata nan da kwana biyu, zuwa lokacin kuwa zuciyarta da idanunta sun riga sun bushe ta fawwalawa Allah komai, ta fahimci cewa duniya dama kowa da kalar 'kaddarar sa da Allah yake jarabtarsa dashi wata'kila nata kalan 'kaddarar kenan na fannin aure, shine *auren za6in iyaye* , hakan ma ta gode Allah tunda nata iyayen na raye kuma tasan son da suke yi mata ne duk yasa haka, tasan dayawan mutane na son su kasance tare da iyayensu ko dan su ri'ka yi musu biyayya ma amma babu su basu samu wannan damar ba kuma sunyi ha'kuri, balle ita da nata iyayen na raye toh me ze hana ta yin biyayya agare su ko dan gudun dana sani agaba ma dole zata basu farin ciki koda kuwa wani iri ne indai har tana da daman yin hakan zatayi shi koda menene kuwa.

Yanzu ne ta fahimci manufar komai, yanzu ne tagane cewa gyaran amare akeyi mata wanda wasu lokuta ake ha'da ta da Hannah ayi mata a fahimtar ta dan kar tunaninta ya yi tsayi ne shiyasa ake yin hakan.

Ke nan kowa ma na farin ciki da wannan auren, kowa murna yake yi akan zatayi aure shiyasa tun ranar da taga aka fara yi mata gyaran farin ciki ya sa'k'ko cikin gidan nasu, zuwan Mummy ne ma ta 'dan ga canji daga gareta dan ita Mummy bakace ga damuwar ta amma tana yawaita tunani wanda ita kanta Teemah abin na damunta.
Yanzu ne ta fahimci manufar maganan Hannah da tace *nata mijin dodone* !
Tare da tunowa da kalaman Yayan ranar da zai tafi inda yake cewa ta tabbatar tayiwa maganar Daddy biyayya koda baya nan.

Tarasa ina tunaninta ya tafi tun farko da batayi noticing komai akan lamarin ba.

Aranar kasa bacci tayi tunanain Mahmud duk ya dameta gaba 'daya baccin da ya kamata tayi ma kasawa tayi, har kusan 2:00 am idanunta biyu.

Tunowa tayi da wayarsa dake cikin kayanta tayi sai kuwa ta tashi da sauri taje ta lalu6o wayar.

Tayi 'ko'karin kunnawa amma wayar akashe dan haka sai ta jona a charge ta zauna tayi tagumi agabanta.

Shawara ta yanke dan haka sai ta mi'ke ta nufi bayi ta 'dauro alwala tazo ta tada sallar nafilfili bayan ta idar ta ringa jero addu'o'i sannan ta shafa.

Tana idarwa kuwa sai ta fara jin bacci dan haka akan sallayar bacci yayi awon gaba da ita.

Ba ita ta farka ba kuwa sai da Hannah ta tasheta cewa ta tashi tayi sallah lokaci ya 'dan ja.

Hannah na idar da sallah ta tafi gurin Mummy ta sanar da ita abinda ya faru na cewa Teemah tasan da batun auren ta yanzu, Mummy cewa tayi " _dama mahaifinku yace idan yazo shi zai sanar a ita da kansa ai_ "
Mummy taji da'din haka dama ita tafison asanar da ita barinta cikin duhun bashi da amfani sam.

Teemah kuwa Tunda ta idar da sallah ta gama addu'o'in ta shafa sai ta 'dauko wayar Mahmud ta kunna tare da kwanciya akan gado, Gallery ta shiga ta dinga bi 'daya bayan 'daya tana kallon pictures kala-kala nashi dana wasu da bata sansu ba, sai nasu da suka 'daka tare ita da shi tare wani suna dariya wani kuma ma ba'a gida sukayi ba.

Sosai pictures 'din suka tuna mata da baya ta ringa gani tana 'kara maimaitawa, sabo fil Mahmud ya dawo mata, haka mutuwar sa ma sai ta ke jin tamkar yau ne suka rabu.....

Takai 1hr da wayar a hannnunta sosai ta shagala da kallon pictures 'din dama tun rasuwar sa bata 'kara bi takan wayar ba sai yanzun shiyasa duk hankalin ta ya 'dauku ga kallon hotunan kawai sai taji wayar ta 'dauki 'kara.

Firgita tayi har sai da ta tashi ta zauna tarasa yanda zatayi har 'kiran ya yanke bata 'daga ba wanda atake wani 'kiran ya sake shigowa a karo na biyu duk numbern 'daya ne da na farkon kuma babu suna yafito.

Daurewa tayi ta 'dauka da niyar sanar da me 'kiran cewa me wayar ya rasu 'kilan bashi da masaniya ne shiyasa.

Receive ta danna tare da bu'de speaker, bata 'kai wayar kunnan ba sai ta ri'ke ahannu.

Tanajin yanda me 'kiran ya furta _Alhamdulillah_ daga 'daya 6angaren ga dukkan alamu 'daukan da akayi ne yasa shi jin da'di.

" Assalamu alaikum, Yalla6ai Rabi'u ne daga Katsina, kullun munata neman layinka bama samu sai yau 'dinnan, wallahi duk na damu akan baka zo kaga aikin da aka yi agidan ba, gashi da sauran ku'din ma har na sa Meram a makaranta tafara zuwa ga.....
Ko sallamar be bari ta amsa ba yaci gaba da koro bayani.

Cikin rawar murya Teemah ta tare shi da fa'din " _bashi bane, shi 'din ya rasu tun wata hu'du da suka wuce_ ......
Kuka ne ya kubce mata tana jin yanda me 'kiran yafara jero salati sai tayi saurin kashe 'kiran tare da kashe wayar ma gaba 'daya.

Sai yanzu tunanin waye Rabi'u yazo kanta, yanzu ne ta tuna da labarinsu.
Ranar 'karshe ranar da Mahmud zai rasu ma sunyi magana da shi akan komawa katsina kamar yanda yayi al'kawari.

'Kiran da Rabi'u yayi mata ne yasa kukan ta ya kasa tsayuwa ta ringa zubda hawaye tana tuna baya, dama tana tunanin Maman Amal (matar Umar) kullum, yanzu da abubuwa sukayi mata yawa kuwa jitake bau wanda tafi bu'katan ha'duwa dashi sama da ita gashi bata da contact 'din ta batada na Umar ma, cikin haka Hannah tazo tayi 'kiran ta akan cewa wai Anty ne 'kiran ta, dayake yanzu kullum da safe ne ake yi mata wankan turaren sauran duk abinda za'a mata already an gama shi tun jiya sai de abin da Anty ke bata kullun tana sha ne har yanzu bata daina bata ba.

Tashi Teemah tayi tana wani kauda kanta wai dan kar Hannah ta ga hawayenta, amma tuntuni Hannah tasan kuka takeyi amma bata kulata ba, dan ita kanta tana jin tausayin ta ahalin yanzu.

*****
Ana gobe 'daurin auren ne Abbas ya iso da 'karfe bakwai na dare, sai da yayi alwala ya sallaci sallar maghrib kafin ya shiga cikin gida domin gaida iyayensa da burin ganin ta azuciyarsa.
Chapter 104 · 0% Book details