← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 163

Sashe 4

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka ahanzarce suka fito,dole yau sai habibu yah kaisu saboda kartayi latti,don inyace yauma da kafar zasu toh kuwa ba 'karamin latti zatayi ba.

Koda suka sau'keta gida suka dawo abinsu shida habibun batare da ko sau'ka yayi a motar ba.bye bye kawai yamata tashiga ciki.

'Karfe biyar daidai yakama hanya ya koma islamiyar don ya dawo da ita gida yanda suka saba abinsu.Dayake sai 5:30 ake tashinsu.

*****
Abbas ba'ko ne agidansu teemah watansa daya kenan da zuwa gidan yanzu.

Amma idan aka lissafa a duka duka wannan shine zuwansa gidan na uku kenan akaf din rayuwarsa.

kuma tunda yazo Habibu bai sa ke kaiwan Teema makaranta ba,haka ma dauko ta,dan acewar Abbas din ahakan ne zai ga gari da kyau,amma in amota ne wai bazai gani dakyau ba.
Teemah kuwa tun ranar farko dasuka zo daidai wajen mai kayan fruits daya siya mata babana,
shikenan tasamu abinka da yarinta wai kullum
Sai an siyah mata,kullum da kalan data ke za6a,in kuwa aka 'kii siyah toh fah ranar antaro *match*............

*****
The following day kuma takama ranar sunday ne,kuma aranar daddy yayi musu zuwan bazata.

Sosai sukayi farin ciki da zuwan nashi ,musamman ma daya cika su da tsarabobi ai sai suka sake rikicewa da farin ciki......haka suka yi ta murna da annashuwa.......

Awurin cin abinci ne bayan sun kammala da abincin Daddy yasake yimusu wata bazatar kuma...,,....

Don cewa yayi zuwa ranar laraba Abbas zai tafi makaranta.
Dama hutun J.S.C.E. yakeyi,so yanzu shima zai koma SS1,already ma daddy yace an kammala masa komai ,shi kawai yarage ya tafi.............

*Yah ne readers,* *kuma nasan daddy* *ya muku* *bazata ko?*
( *Hhhh* 😃)
*don't worry just* *keep following* *ME* ........

*YANZU FAH MUKA* *FARA* .

*Ur comments is needed* 👌🏻

nd
*Share pls*

*Salmerh md* 😍
[10/2, 5:49 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

Luv story😍

_Wattpad@_
_Serlmerh-md_

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫

~We are here to~ ~make you~ ~happy,smile,educate~ ~and to~ ~realized~ ~that we are the best~ ~among all~ .....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *4*

Shirye-shirye aka farayi na tafiyar abbas 'din makaranta,dayake hankali bai gama isan Teemah ba shiyasa bata wani damu da batun tafiyar ba har se ranar da ze tafin kafinnan, wato ranar laraba.

Dawuri yagama shirinsa don shima irin yaran nanne masu jarabar son makaranta.Baya wasa da harkar karatun shi tun asali,wannan halayyarsa ne tun yana yaro qarami.
Ballantana Yanzu da ya 'kara wayo sai ya fi jin yin karatun sosai.

11:00am ne flight dinsu,ba sassafe zasu tafi ba,hakan yasa yau 'din ma yace shi ne zai kaita makaranta.

Ahanya neh yake sanar da ita cewa shima fah zai tafi makarantarsu anjima,ko ajikinta bata damu ba illah cewa datayi "ai nima zan dinga raka ka kullum inzaka je"

Dariya ma tabashi shikam,dan shirman nata abin dariyah ne, wannan shi ne ana ce miki ga gabas kina 'kara tambayar ina al'kibla.

Sai da yayi dariyar kuwa sannan yace mata

" ke bafa anan bane makarantar,tafiyata zanyi nima,yanzu sai de Habibu ya rin'ka kawoki a mota kullum."

Kanta ta lan'kwasa gefe 'dayan kafa'darta tare da fadin
"hum um-hum um"
harda bubbuga kafafunta a'kasa irin na shagwa6a66un yaran,sannan tace ni banaso.
Kallonta yayi sosai dan so yake ta fahimci maganar tasa sosai amma yarinta bazai barta ba sai kawai yace mata

"dolenki ai yarinya,inkuma bahaka ba sai de ki rin'ka zuwa ke ka'dai."Kinga habibu ma huta da zirga- zirga.
Kuka tafara masa na rashin dalili,ehh mana rashin dalili,daga cewa habibu ne zaina kawota makaranta kuma sai kuka,toh danma bataga yatafi yabarta ba kenan daya zatayi. abin dariyah wai
cewa tayi .
"sai na fa'da ka da Daddy"

Batasan cewa daddyn shi ne jagoran tafiyan ba.kiyi ha'kuri karki fada ni da daddy ya fa'da da sigar yanda itama tayi magananta,ta ke kuwa yabata dariyah."me zan siyo miki idan naje makarantar ya tambayeta."ai nima binka zanyi inzaka tafin,irin yanda kake rakani,a'a nawa nikai zanje bawanda zai rakani kuma idan natafi zandade bandaqo ba.amma wannan karon bata kulashi ba don yafara bata haushi.sai kuma ta tuna fruits 'dinta
Kai ta 'daga ta kalleshi,hannunta na ri'ke cikin hannunsa suna tafiyar.sai tace toh yayah idan katafi wazai dinga siyamin Apple da pineapple harda babana ma?
Habibu zaina siyamiki kinji? Yabata amsar tambayarta ta cikin sauri. Kuka tafara masa wai ita bata son na habibun nashi take so.

suna tafiyah tana kuka,tausayinta yakeji dan yasan dolene daman taji ba da'di,shikansa ma bada'din yakeji ba don sosai sukayi sabo fiye da zaton mai karatu.

Da 'kyar ya lalla6eta tayi shiru sai da yace mata dawasa yake mata babu inda zaije.Kuma shine zai na siyamata apple 'dinta kullum.
tana jin haka kiwa kuka ya 'dauke cak.
Haka ya rakata makarantar dai dai zata shiga ya miqa mata lunchingbox 'dinta yace ta shiga class dinsu banda wasa,harta fara tafiyah sai ya 'dan 'daga 'kafa ka'dan ya iso gareta,dayake bata wani yi nisa da inda yake tsayen ba,hannunta yakamo sannan ya tsuguna dai dai tsayinta.

Sake daidaita mata 'dan Hijab 'din uniform 'din dake kanta yayi,wanda dudu-dudu bai wuce iyah kafa'dunta ba.

Kallon cikin idonsa tasa keyi itama,sai yayi murmushi ya kamo kumatunta duka biyu ya 'dan jijjiga mata fuskar

"Smile mana kin wani 6ata rai kamar an dokeki"

Dariyan kuwa tayi masa.Tana sa ke kallonsa.

"Silly girl"
Yace ahankali
yana murmushi

Hannunta ta 'dago ta danna saitin dimple 'dinsa.

Bawani zafi amma dan kawai ya 'dauke mata hankali yasa shi cewa

" kai kai,Allah yarinyan nan kin iyah mugunta"

Sai yayi kamar zaiyi kuka tare da kama gurin data danna 'din.

"Sorry yayah"
Tafada tana turo baki gaba

Sake 6ata rai yayi sannan ya ce.

"Zan ha'kura amma sai naje anmin allura idan ya daina zafi toh shikenan zan han'kura amma idan bai daina ba toh shikenan bazanma dawo ki ganni ba.

Kin yadda?
Ya tambayeta.

Kai ta 'daga masa alamar ehh tayadda.

Tashi yayi tsaye sannan yace toh ki je class,"
"barinje amin allauran ko?

Sa ke 'daga masa kai tayi

"ko zaki rakani?ya sake tambayarta

yanzunma kai ta kuma jijjigawa alamar a'a.

"To kije class anjima habibu zaizo ya 'dauke ki kinji.

Duk da kai take bashi amsa.
Sannan tajuya tanufi cikin makarantar shima bai tafiba tsaya wa yayi yana kallon bayanta harta isa bakin class din su sai ta juyo kamar tasan bai tafinba.

Hannu ta 'dago ta mai bye-bye.

Shima 'daga mata hannun yayi.
sai da yaga ta shiga class kafin shima yajuya ya kamo hanyar gida.awurin mai kayan fruits ya tsaya,alokacin ma mai kayan bai gama kintsa wurinba,haka Abbas yajirashi tsaye agefe har ya kammala gyara wurin ya kik-kintsa fruits 'din kowanne a muhallinsu kafin abbas ya matso yasiyah matah,wanda tafi ra'ayinsu daganan ya isa gidan.
Yana shiga yasamu mummy zaune aparlour tana kallon wani series,binsa tayi da kallo dan ganinsan datayi ri'ke da leda a hannu.

Dariya yayi yana kallon mummyn shima saboda irin kallon tuhumar datake binsa dashi.

"Mummy kayan Teemah ne na siyo mata don zata dawo yau bana nan"

Murmushi mummyn tayi tare da fa'din "lalle Abbas da 'ko'karinka.Kai da zak tafi har se ka biyeta kasiya mata bayan ma kawi agida.a'a mummy cewa tayi nawan tafiso." Ku kuka sani ai mummyn ta qarasa zancen nata tare da komawa ta jinginu da kujerar da take zaune akai.

"Toh kaiwa fanni tasaka mata a fridge kafin tadawo
karsu lalace dan yauma naga garin adafe yake,ragowar mafa inaga yawa ne dasu a fridge din"

Ce mata yayi
" a'a mummy wannan yafi da'di.haka yafadawa mummyn yana qoqarin barin parlourn .

"Zan gani ai idan ka tafi wa zai rin'ka siya mata mai da'din tunda namun ba da'di.
Dariya kawai yayi sannan ya 'karasa
Fita daga 'dakin,wurin Fannin ya nufa a inda yasan zai fi samunta cikin sau'ki, daga nan yawuce 'dakin Teemahn,bayan yabata ledar.

Guri yasamu ya zauna abakin gadonta ya yi tagumi.

Ha'ki'ka sabo ba da'di don yanda Abbas yakeji,jiyake kamar kar yatafi yabarta,amma bazai yiwu ba.
Sosai ya 6ata lokaci a'dakin nata amma shikanshi baisan dalili ba,illah kawai kewarta dayake ji tun kan ya tafin.

10:30 suka fita shi da daddy da mummy,Habibu ne ya kaisu airport 'din daganan ya dawo da mummy gida su kuma suka wuche Abuja.

Koda lokacin tashin su Teema yayi Habibun ne yaje ya 'dauko ta yadawo da ita gida.

Sai data gansu a 'kofar get 'din gidan habibu na danna horn kafin ta turo baki Sannan tace

"Nifah bahaka yayah yake min ba"

Juyowa yayi ya kalleta daidai anbu'de get 'din gidan.

Cewa yayi Bayan yaja motar ciki

" me yayan yakeyi wanda ni banyi ba,?
ni dama na kawoki a mota"

"shi ai yayan kullum se ya siya min fruits ahanya"
Kai kuma baka siyamin ba,ai inya dawo daga alluran sai na fa'da masa"
kuma 'dazu yace wai zaka dinga siyamin kafin yadawo"

Tafa'da masa da turarren baki irin ita adole tayi fishi 'dinnan.

"Fishi yana gaba yarinya "

habibu yafa'da azuciyarsa don yagane cewa wayo Abbas 'din yamata da sunan allura zashi.

Afili kuwa yace mata yayi " ii ha'kuri 'yar Daddy yanzu zanje insiyo miki."

"a a ni banaso na yayah nakeso ni,idan ya dawo zai siyo min ai. tafa'di hakanne bayan sun fiffito daga motan.

Aransa yace "ashe zaki jima yarinya" afili kuma ya ce mata"kinga ai kin hutar dani"

Ciki tashiga da sallamarta 'yar siririyah,bataga kowa a parlourn ba hakan yasa ta wuce 'dakin mummy.

Zuwa tayi da gudu ta rungume mummyn nata tabaya dayake atsaye take agaban ma'ajiyan kayan sawanta wata 'kila wani abun zata 'dauka ko ajiyewa dan ba kaya ta ke nema ba.

"Oyoyo mummy"
Teeman tafa'da

Itama mummyn cewa tayi "oyoyo yarinyar mummy"

Sannan ta kama hannunta tazauna akan side drawer daga gefen gado tace mata"wato yau yayah bayanan harda oyoyo na samu ko?

"Ai mummy allura yaje zai dawo yace min "

Hmm " kawai
mummyn ta ce

Rage mata kayan jikinta tayi sannan tace mata taje fanni ta watsa mata ruwa,sai ta dawo.

Fita tayi hannunta ri'ke da kayannata tashiga 'dakin ta watsa su akan gado tayi wajen fannin akitchen tasameta tana wanke wanken kayanda aka gama anfani dasu yanzu.
Chapter 4 · 0% Book details