Sashe 117
Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zuwan wayar ne ya 'dan sanyaya mata rai ta 'danji dama-dama sai duk ta bi ta sanya su a chaji gaba 'daya.
*10:12am*
Abbas ya buga mata 'kofa amma be jira ta bude ba kawai sai ya juya zuwa dinning.
Tana kwance tana faman chatn jin an buga mata 'kofa yasa ta ajiye wayar ta fito sai ta hango shi zaune yawani hakimce yana amsa waya.
Tasan shine ya buga 'kofar dan haka sai ta isa dinning 'din itama.
Bata zauna ba sai ta koma kitchen ta 'dauko su plates da cups ta dawo tayi serving nasu kana ta zauna bayan ta tura masa nashi gabansa.
Abbas na lura da ita amma be kulata ba dan yasan halinta sam magana be sata cin abin sai in har tayi niyyah sa6anin haka kuma sai de in kai ne zaka'dauki nauyin bata da hannunka dan haka be ma 6ata bakinsa ba, yasan idan taji yunwa zataci ne dolen ta ai tunda ita yunwa ba sabo ne da ita ba.
Har suka 'kare cin abincin be ce da ita komai ba haka itama.
Ranar kam Abbas be fita ko'ina ba har aka 'kira sallar azahar yana gida, sai de duk da agidan yake amma kowa na 6angaren sa babu wanda yaje wurin kowa.
Kafin azahar 'din Teemah tayi wankan tsarki ganin cewa period 'din ta ya 'dauke, dama 4days takeyi.
Shi kuma lokacin da yayi alwala zai fita sai yabi ta wurin ta inda yazo dan sanar da ita fitar sa sai kuma ya tarar da ita tana sallah, be jira ta idar ba ya wuce kawai abinsa dan ba yaso jam'i ya wuce shi.
Bayan sun fito ne ya 'kira ta awaya dayake yasan wayar natare da ita yace mata shi yafita kuma ba zai dawo yanzu ba, yace m za'a kawo mata abinci sai ta kula idan taji door bell taje ta anso kuma ta tabbatar ta rufe jikin ta da mayafi kafin ta fitan kuma bece ta fita ko da harabar gida bane.
Daga 'karshe dan ya sake tunzura ta sai yace " _zanje in dubo Zahra ta ne kwana biyu bana samun ta_ "!
Teemah ta6e baki tayi tare da fa'din
" _uhumm sai ka dawo_ "
Koda ya yanke 'kiran kuwa abin yaso ya dameta dan sosai ya tsaya mata azuci amma sai ta tambayi kanta dalilin damuwar sai ma taga laifin tane na shishshigin damuwar, miye ruwan ta toh da al'amarin sa ai yace itace farin cikinsa toh ita miye nata.
Tilastawa kanta tayi 'karfi da yaji ta ya'ki zuciyar ta dole ta kawar da tunanin Zahran Yayah aranta sai de duk da haka lokaci zuwa lokaci tana sake tunawa.
Kamar yanda ya fa'da mata haka tayi domin tana jin 'karan door bell tafita bayan ta zun6ula hijabin ta wadatacce babbah da take sallah dashi.
Driver ne yakawo sai ta kar6a bayan ta gaida shi tare da kawo masa coolers 'din safe sannan tace da shi kar ya kuma kawo wa anjima wannan ma ya isa.
Ciki ta koma tana me jinjinawa 'ko'karin Ummah sosai gashi kullun abincin yawa yake yi musu idan sunci ne ma sai Abbas yayiwa mai gadi magana yazo ya tafi da sauran gaba 'daya ko ya yake yi dashi ma oho, ita dai nata kawai wanke warmers 'din ne.
Zama tayi a parlour kawai tare da 'kiran layin Ummah tayi mata godiya da kuma bayanin abincin sannan ta yanke 'kiran.
Bata ko sake bi takan abincin ba taci gaba da duba wayar ta.
Abbas kuwa har se da yamma ya dawo gidan ya kuwa zo mata da fruits masu yawan gaske.
Daya duba abincin shima sai yaga ko ci batayi ba, yariga yasan hakan amma na yau 'din sai yayi tunanin ko harda fushin Zahra ne, dan gudun kar ya shiga ha'k'kin ta da yawa daya watso ruwa bayan ya shirya sai ya fito yace tazo tayi serving nashi abinci.
Sai da ta wuche kitchen ta 'dauko plates 'daya da table spoon 'daya sannan ta dawo ta zuba masa abincin dai-dai shi tare da 'dauko masa lemonjuice da ruwa harda fruits 'din da ta gama yanyan kawa tasa afridge ya 'danyi sanyi domin kanta duk ta kawo masa ganin fried rice yau aka kawo kuma nada mai'ko sosai.
Tana shirin mi'kewa yadakar da ita inda yayi mata nuni da kujera.
Sam batada ra'ayin cin abincin musamman data ga ma cewa shinkafa ce wannan kuma bata cikin ra'ayin ta shiyasa koda zauna 'din ma sai ta na'de hannu kawai tayi shiru tana tunanin 'kila so yake ta taya shi zama.
Spoon 'daya, biyu yakai bakin sa na ukun da ya 'debo sai ya nufo bakinta dashi.
Teemah cikin idanunsa ta kallah sai yayi kamar be ganta ba hakan yasa ta dawo da idanun ta kan hannun sa dake ri'ke da spoon 'din tare da bu'de bakinta ta kar6a.
Sai da yaga ta ha'diye sannan yace " _bakya son cin abinci ko? Idan Zahra ta tazo raina ki zatayi dan kuwa ita_ ' _katuwa ce nikuma babu ruwa na_ "
Take tayi fushi ta tura baki harda 'dan hararan sa ka'dan.
Murmushi Abbas yayi kawai amma na gefen baki be kulata ba yanzun dan so yake ta 'dan ci abincin koma ka'dan ne shiyasa kawai ya shareta.
*****
Washegari da asubah da ya tashi sallah sai itama ya tashe ta ganin tafara yi, amma Teemah ta'ki ta tashi sai ta ringa juye-juye.
Har yaje yayo alwala ya fito bata tashi ba da yaga zata 6ata masa lokaci sai ya sa hannu ya 'dago kafa'dun ta ya ta data zaune wanda hakan yasa dolen ta tashi tare da bu'de idon ta.
Sai yace " _ki wuce kiyo alwala idan kika 6ata min lokaci Allah zan 6ata ranki kema_ "
Tanajin haka dolen ta ta mi'ke tana gunguni bata da'de abayin ba tafito bayan ta 'dauro alwalan.
Abbas ne ya mi'ka mata hijab babbah daya 'dauko a'dakin ta ta kar6a ta sanya tare da bin bayan sa yajasu sallar asubah tare da 'daukan dogon lokaci yana addu'o'i tun kan su shafa Teemah take layin bacci suna shafewa kuwa ta koma gado ta du'kun'kuna cikin hijabin ko cire shi batayi ba sanadiyyan sanyin da ke tashi ka'dan-ka'dan da safiyar.
Abbas kam Al-qur'ani ya 'dauko ya 'dora da karatu tsawon lokaci sannan ya kammala.
Zuwa lokacin kuwa ruwan sama ya sa'k'ko sosai ganin hakan shima sai ya kishingi'da ya lumshe idanu yana me tasbihi ga mahallici.
'Karfe takwas da 'yan mintina Teemah ta farka daga bacci, jin ruwa na sau'ka yasa ta yin luf sosai take jin sha'awar shiga ruwan amma tarasa yanda zatayi dan tasan Abbas ba barinta zaiyi ba, juyawa tayi ta kalleshi sai taga kamar yana bacci ganin haka yasa da sauri ta fincike hijab 'din dake kanta ta ajiye.
Cikin san'da ta ta kama hanyar barin 'dakin dama Teemah gwana ce wurin son wasan ruwa Allah-Allah take tagan ta cikin ruwan nan musamman ma da yanzu ya 'dan tsagai ta ka'dan.
Abbas idanunsa biyu babu baccin dayake yi duk kuma abinda take yi yana kallon ta sai da yaga ta kama hanyar barin 'dakin ne yayi tunanin ko wani rashin ji zatayi dan haka sai ya dakatar da ita da fa'din
" *ZAHRA* !
Cak ta tsaya a inda take amma bata juyo ba shima kuma be sake magana ba idanunsa yasake lumshewa tamkar wanda ba shine yayi maganar ba.
Teemah kam jin be sake magana ba yasa ta waigowa sai taga still baccin sa yake yi sai tayi tunanin 'kila ko cikin baccin ne yake 'kiran Zahran sa amafarki murgu'da baki tayi.
Taso ta koma ta tashe shi a baccin kodan ya daina mafarkin Zahran ma dan ta 'dan ji wani iri sanadin hakan amma jarabar son ta shiga ruwan sai ya fi rinjayar ta kawai ta juya.
Abbas ma sai ya 'kyaleta kawai tatafi.
Cigaba tayi da tafiyar ta ta isa har kofan parlourn ganin a kule da security lock yasa ta koma tabi ta baya tafita ta 'kofar kitchen.
Da farko hannayen ta tasa tana taran wanda ke sakkowa daga bakin roofing tana tara tana watsa shi afuskan ta tana murmushi, data ga hakan baze mata ba sai kawai tafara 'ko'karin shiga gaba 'daya.
Caraf taji an ri'ke mata hannu daga baya wanda ya matu'kar firgita ta domin bata ji zuwan mutun ba ita.
Arazane ta juyo sai taganshi take kuwa ya janyo ta zuwa jikin sa yana kallon cikin idanun ta yace " _Kinyi ajiya aruwan ne_ ?
" _Umm- umm_ "
Tace da shi tana 'kif-kif da idanu.
" _Toh me zakiyi_ ?
Yasake tambayarta.
In ina tafara tarasa me ma zata ce dashi sai yace " _ina jinki_ "
Ahankali tace " _wanka... zan..yi ne fah....Yayah_ "!
" _Shower ya lalace_ _ne_ ?
Ya tambayeta
Jijjiga mai kai Teemah tayi ranta har yasoma 6aci dan tasan ba barin ta zaiyi ta shiga ruwan ba tunda ya fito.
Sai ya sake fa'din.
" _bathtub fah_ ?
Da muryar shagwa6a tace
" _Yana nan_ "
" _Bazakiyi ba toh, wuce muje bana son rashin ji_ "
Kalar tausayi tayi tace " _Ayyah Yayah ka'dan fah zanyi.........._ "
Kafin ta rufe baki ma ya tare ta da fa'din " _i said bazakiyi ba ko?.....ko ni sa'an ki ne dazan na magana kina jayayya dani_ ?
_Comment_
_Vote_
_Share_
*Salmerh ce* 😍
[10/13, 1:56 AM] 🌸Salmerh🌸: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕
By
*Salmerh MD*
Luv story😍
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*
👎🏻
Wannan page 'din naku ne 'yan group *CAPTAIN ABBAS FANS 2* Allah sosai nake jin da'din Comment da conversation 'dinku ina matu'kar jin da'di, koda ace my ka'dai nake dashi nasan labarin CAPATIN ya isar, wannan page 'din naku ne kuyi yanda kuke so dashi..
🥰
*Bismillahir rahmanir raheem*
_Never expect things to happen. It’s better to feel surprised than to feel_ _disappointed_ .
🅿 *81*