Sashe 37
Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Haka ahankali har yak'araso k'ofar parlournsa, key hondern dake tare dashi yaciro ya lalu6i makullin da zai bud'e masa d'akin yasaka ya bud'e yashiga ciki.
Sake tura k'ofan yayi ya rufe abinsa tankar ma ba'a bud'e ba.
D'akin ma ashare tsab bawani datti dayake duk bayan kwana biyu Anty take sawa a share masa koda ma bayanan so bashi da matsala da wannan, kawai sai ya ajiye jakar kayansa tare da rage kayan dake jikinsa.
Bayi ya shiga ya watso ruwa tare da d'auro alwala yazo ya tada sallah ya rama wanda yawuche shi tare da sallatar wanda tagabato adai dai lokacin.
Yana idarwa ya d'auki wayarsa ya k'ira mummy ya sanar da ita isowanshin lafiya harma suka d'anyi hira da Teemah kad'an basu wani d'au lokaci ba yace mata bacci yakeji he need to rest, sallama tayi masa tace idan yatashi yak'ira zata bashi wani labari, " toh kawai yace mata atakaice dan yasan babu wani larin da zata bashi k'aryace kawai da kuma son yak'iratan datakeyi. daganan ya kwantaa bayan ya maida wayar a silent da niyyar kishingid'a, kamar wasa kuwa sai bacci ya d'auke shi suka tafi.😜
Antynsa bata san ya iso ba, kuma duk k'iran data ta yi masa aranar ko guda d'aya bai d'auka ba hakan kuwa bak'aramin
6ata ranta yayi ba amma sai ta kyaleshi da niyyar duk lokacin data sameshi awaya sai taji dalilin hakan inma zigashi ake yi yamata rashin kunya toh duk zataji.
Bashi ya tashi ba sai da aka k'ira sallar maghrib,koda yatashi alokacinma sai yaji gaba d'aya kansa yamasa nauyi,hakan ya sa yad'an 6ata lokaci abayi yana cikin ruwa da kyar yasamu yafitoh.
Sallar maghrib d'in yagabatar tare da zaman jiran lokacin isha'i yacika itama ya gabatar da ita, baya son yaje masallaci su had'u da Abbansa ne shiyasa baije ba amma da farko harya yi niyyan zuwa sai fasa.
K'arfe takwas da rabi daidai tayi masa ne ak'ofar babban parlourn Anty.
Hannu yasa yatura ahankali tare da yin sallama ciki ciki.
Suna can wajen cin abinci dan haka basu ji sallamar tasa ba amma sunji k'arar k'ofan.
Jin k'arar dasukayi yin ne yasa suka maida hankulansu wajen k'ofar shiru sukaji babualamun mutun kuma domin daya shigo tsayuwansa yayi awuri d'aya shiyasa basu kuma jin motsinsa ba.
"Waye ne?
Abbah ya tambaya batare da ya mik'e ba.
Ahankali yah amsa da " nii neh" kamar dole aka saka shi.
Suna jin muryarsa suka mi'ke atare suka nufo shi tare da ambatar "MAHMUD" alokaci guda.
" Mahmud kani da daren nan?
Abbansa ya tambaya cikin mamaki.
Kai ya d'agawa Abban alamar ehh
Hannunsa yakamo suka koma gurin cin abincin dukkansu nan take Anty ta had'a nasa nasa plate d'in ta tura masa shima.
Dayake daman yunwa yakeji sai be wani yi yanga ko gardama ba ya bud'e ciki ya kwashi abincinsa sai da suka gama kafin Abbansa ya tambayeshi meyasa yayi tafiyar dare?
" bayanzu na zo ba Abbah"
Yabawa Abban nashi amsa .
Ido Abban ya ware "bayanzu babana tun yaushe kazo?
" Tun da rana".
Salati Anty tasaka takama baki sanna tace " yanzu Mahmud tun da rana ka iso amma kak'i zuwa inda muke sai yanzu".
Abbane ya d'aga mata hannu yana murmushi yace " pls barshi Maryam may be yagaji ne shiyasa......
" amma me yasa bazai ko sanar akan yana hanya ba.....
Anty ne tasake fad'in hakan.
Abbah kuwa cewa yayi wannan tsakaninku amma dai kibarshi kwa gama dasafe idan Allah yah tashemu lafiya".
Juyawa yayi ya kalli Mahmud yace " abana jeka huta sai da safe koh".
Mahmud da tun d'azu yake zaune kamar mutum mutumi kallon Abban sa yakeyi da mamaki, domin yajima baiga Abbansa na irin hakan acikin gidansa ba, sai yau yaga Abbansa na dakatar da Anty akan abu kuma tayishi, sosai hakan yasashi mamaki matuk'a, shiyasa be ma ji abinda Abban ya fad'a da farko ba sai da Abban yasake maimaitawa kafin ya yi firgigi.
be san cewa addu'ar da mummy keyi akullum bane yafara tasiri akan Abban.
" meke faruwa ne ?
Aban ya tambayeshi.
"Ahh bakomai Abbah "
" toh maza jeka kwanta sai da safe"
Tashi yayi tare da sake yi musu sallama ya wuche abinsa.
Anty kuwa abin ne yafara yimata yawa domin ga matsalar Mahmud daya d'an d'au lokaci aranta tana tunani ta yadda zai yadda da batun auran Munirat, sai rana tsaka kuma matsalar Abbah ta kunno kanta kusan sati kenan tarasa gane kansa, gashi duk tarasa dalilin hakan.
Koda tayiwa Anty chideh magana kuma sai ta rink'a yi mata yanga kamar ma bata son zuwa.
Itakuma vagane gurin zatayi ba yanzu kuma bata son canja wa tagi son wancan wurin d'in dasuka yi mata aikin tun farko dan sosai ta yadda da aikin nasu.
Washe gari daya zo gaida iyayen nasa sai yace wa Antyn yanso me yakoma dawuri domin akwai aikin dake jiransa acan idan wani abu take so ya mata tafad'a dawuri sai yagama mata shi ayau dan yanaso yakaoma"
Antyn kamar bazata fad'a ba dan tsoron abinda zai biyo baya kar kuma tak'i fad'a yace yau yake son komawa tunda babu abinda zai mata, sam bahaka taso ba , taso su ka6e su biyu sannan suyi maganan musamman ma dayanzu yadda yakasance Abbansa na yawan yi mata katsalandan a abu shiyasa take tsoron fad'in abinda ke ranta a gaban idanunsa.
Tunanin hakan yasata ta bud'i baki badan ranta yaso ba anan ta yada manufarta nasawa datayi yazo d'in.
Haushi Mahmud yaji sosai bayan yaji bayanan Antyn.
Dayake cewa tayi yakamata ya tsaida matar da sai aura kodan gudun lalacewar da duniya take ciki dan hakneta mtsa akan yazo gida domin su tsaida magana wuri d'aya.
Haushinsa d'aya ne dayaji wai duk wannan masifan data tayi masa d'in wai akan batun aure ne toh ni wama zan aura ?
Ya tambayi zuciyarsa.
Azahiri kuma murmushi yamata kana yace " kwantar da hankalinki Anty, nibama yanzu na shirya yin aure ba gaskiya, shiyasa ma har yanzu banda kowa da muka yi batun aure da ita kinga kuwa ai da sauran lokaci"
Abbah ido kawai ya zubawa wayarsa tamkar baya jinsu amma kuma gaba d'ayan hankalinsu da kunnuwansa na gare su ne.
Anty ne h tasake fad'in cewa " ai karka damu Akwai wata 'yar k'awata..........
sai tadakata ta kallo Abban Mahmud d'in....
" mahmud aransa yace dama nasani ai" yayinda afili kuwa kallonta yakeyi kamar wanda tana fad'an maganar zai amince.
Gani tayi Abban Mahmud d'in sam hankalinsa baya tare da su sai tayi hamdala azuciyarta.
Daganan taci gaba da fad'in......
" yarinyar nada hankali Mahmud shiyasa nayi sha'awan kai ka aureta nasan baza'a samu matsala daga gareta ba bansan dai kai ba"
Takarashe maganan da yanayin tausayi.
Shi kanshi sai yaji tausayinta amatsayinta na uwa mahaifiya agareshi, idan har tana ganin bata da matsala da yarinyar toh why not shi data haifa kuma?
Batare da wani 6ata lokaci ba take yace mata gobe yake so ya koma amma insha Allahu kafin ya tafin zaije yaga yarinyar inyaso sai yabar komai ahannunsu.
Farin cikin da Anty taji tamkar ta goya shi haka taji kawai sai fara yi masa godiyah kamar wanda yamata kyautan wani abu.
Sai asannan kuma Abbah yayi magana inda yace " ga dukkan alamu yarinyar tatafi da hanakalinki gaba d'aya ko?
Murmushi tayi amma bata yi wata magana ba dan karta 6ata plan d'inta tunda tasamu ya amince ai shikenan.
Da yamman ranan Anty ta had'a Mahmud da drivernta dayake ahi yasan gidan sai ta masa bayanin abinda zai kaisu gidan atsanake.
Fita yayi bayan sun isa ya bar Mahmud d'in zaune acikin mota shikuma yaje yayiwa Mai gadin gidan bayani take kuwa yawuce ciki yah isar da sak'on da aka bashi.
Minti goma mai kyau bata cika sai ga Munira tafito cikin shirinta na k'asaitacciya awurin iyayenta.
Riga tasa iya gwiwanta yakuwa yi mata kyau sai dai rigarasosai yakama mata jiki dayake roba ce da dogon wando daga ciki kanta kuma wani d'an k'aramin veil me tayane kanata dashi, tana tafiya tana karairaya dayakr dama tasan da zuwansa mahaifiyarsa tariga ta sanara tun kafin ma ya iso shiyada tayi masa shiri na musamman.
Tun daga nesa Mahmud ke k'are mata kallo yana karantar yanayinta.
Murmushin takaoci yayi lokacin daya fajimci yarinyar ya kuma tuno inda yafara ganinta,sam ba irin matan dayake ao ya aura ba kenan asali ma shi baiga wani abinso tattare da yarinyar ba tun farko dahar Abty take ganin dacewansu dashi.
Tsaki ne ya subce masa lokacin daya tsinkayo muryarta tana fad'in " Hi "
Bai kulata ba sai ma kauda kai da yayi gefe kome yatuna kuma oho sai ya fito yazo tagabanta ta tsaya tare da folding hannayensa a k'irjinsa.
Gaishe shi Munirah takuma yi tare da yi masa iso zuwa cikin gida.
Bai amsa mata ba sai ma tambaya daya jefah mata nacewa " wacece ita?
Murmushi tayi tare da fad'in " ohh sorry"
Sunana Munirah kuma nice wacce Mahaifiyarka ta za6a maka atsayin mata.
" oh really "
Yafad'a da sigar rainin hankali yana kuma murmushi.
Kallonsa ta tsaya yi domin afili zaka fahimci manufarsa koda baka da wayo balle ita.
" kinsan wani abu?
Idonsa acikin nata yayi maganar sai kawai ta jijjiga kanta dan sosai jikinta yafara yin sanyi.
" ko kad'an bakiyi min ba!
Sake matsowa yayi kusa da fuskarta yakuma fad'in " kinsan dalili?
Da kai ta bashi amsa alamar " a'a".
Sai yace mata " saboda ko kad'an baki dace dani ba".
" Ki gayawa zuciyarki cewa Mahmud d'innan banaki bane, dan nasan wannan duk munafurcinki neh,ni kuma insha Allahu bazan ta6a auranki ba, mark my word."
Yana fad'in haka yajuya ya shiga mota da gudu driver yazo ya shiga shima yatada motar suka fita agidan.
Har suka bar haraban gidan Munirah bata iya motsawa ba, mintina yakai uku ta k'ara bayan fitan motar tasu daga gidan kafin ta dawo hayyacinta, gefe da gefenta ta kallah taga babu kowa da gudu tayi cikin gida tana rusa kukan takaici bata zame ko'ina ba sai gurin mahaifiyarta.
Da k'yar tasamu Muniran tayi mata bayanin abinda ke faruwa ai kuwa take ta d'aga waya ta k'ira Anty tafad'a mata abinda Mahmud d'in yai wa 'yarta.