← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 163

Sashe 57

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru Teemah tayi ta kauda kanta gefe.

Hannah kuwa sai taci gaba da maganarta _" kekika sani wallahi indai juninki wai adake ki 6oye ne kin shiga_ _ukun ki,_ _Yah Abbas fah bashida kara shikan_ _babu_ _ruwansa muguntarsa intazo yinta yakeyi ako ina indai shine, kicigaba da rufa masa asiri wai ke gaki me_ _yayah ko hmm_ , _jiki_ _magayi ai_ _yarinya"__

_"ke kin kasa yadda be min komai ba_ _ko"_ ?

_" ai ko bani ba babu me amince miki Teemah"._

_"Allah kuwa Hannah babu abinda ya min idan abu yamin ai zan sanar dake kinsani"!_

" _ke kika sani fah ni babu ruwana_ "
Hannah tafa'da 'kasa-'kasa.

Teemah kuma acikin zuciyarta tace _"kanki akeji parrot_ _kawai."_

Hannah alwashi tayiwa aranta sai ta bincika ta gano abinda ke faruwa saboda tana ganin kamar Teemah na 6oye mata wani abin ne, kuma batason Teemah ta kullaci Abbas saboda idan ya kasance kullum mugunta yake mata dole zata na jin haushin sa aranta,itakuwa tana son yayan ta batason kuma taji ance anajin haushin wani abu nashi daya dangance shima ballantana shi da kanshi, tafi son taji kowa nason shi, shiyasa ko yanzun ma ta damu dataga Teemah na kuka taso Teemahn tasanar da ita meke faruwa dan tayi maganin abin, amma Teemah ta'ki.

Abbas kuwa tun kafin ya isa 6angaren da yasan zai samu Ummahn ya 'daga waya ya 'kira Mummy..............

*ACIGABA DA KAFTAWA MUTANE NAH...........*🤞🏻

*Sa'kon Ta'aziya ga 'yar uwa RAHAMA NALELE da dukkan al'ummar musulmi, Allah ubangiji ya ji 'kan magabata yasa alajanna hutu ce. Allah ubangiji ya musanya abinda* *aka rasa da alkhairi* *mafifici.*
_Sorry 4d late condolence._

_Comment_
_Vote_
_Share_

*Salmerh ce*😍
[10/2, 6:01 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_Dedicated_
_2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs._ 😍

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

We can’t solve problems by using the same kind of thinking we used when we created them.

🅿 *47*

Mummy cewa tayi ya shigo tukunna suyi sallama da mahaifiyarsa mana kafin yawuche 'din, yayi 'ko'karin ce da mummyn ta sanar da Ummahn kawai basai ya shigo ba da 'kyar mummy tayi convincing 'dinsa yashigo koda ya shigonma atsatstsaye yayi musu sallamar yawuche abinsa kafin su Hannah su shigo ma har ya wuche dukkansu sun fahimci 'yar 6oyayyiyar damuwan dake kwance asaman fuskarsa amma basu tsaya sun tambayeshi ba saboda sun san basamun amasa zasu yi ayanda suka san halinsa.

Hannah da Teemah kuwa koda suka shigo 'din ma sai kowa yabi hanyarsa, Teemah 'dakinta ta wuche wurin friends 'dinta bayan ta daidaita nutsuwa da yanayin fuskarta, Hannah kuwa kitchen ta shiga ta ajiye tray 'din da ta 'dauko sannan ta dawo wurin Ummah tazauna agefenta.

_" Ummah wallahi Yayah ko cin abincin ma beyi ba ya fito kayansa"_
tace da Ummahn cikin yanayi na shagwa6a66u.

Sai Ummahn tace mata
_" 'kila baya tare da yunwa ne shiyasa "._

'Kasa-'kasa tayi da murya dan kar kowa yajiyo ta tace _" Ummah kinsan wani abu"?_

Kai Ummahn ta girgiza mata alamar _a'a_ sai ta cigaba da fa'din
_" kukafa nasamu Teemah nayi a'dakin nasa na tambayeta kuma ta'ki ta sanar da ni_ _abin da yasameta"._

_" nasan za'a rina"_
Mummy tace azuciyarta.
dan duk 'kasa-'kasan da Hannah tayi da muryarta sai da Mummy tajiyo ta batasani ba, dah ita a shirmenta wai ba'a jiyo ta Ummah ce ka'dai kejinta, wannan karan Ummah mantawa tayi da sirrin 'karyar da Hannah take so suyin tace
_" toh me yasame_ _ta"?_ da 'dan 'karfi tayi maganar.

_" oho nima bansani ba, amma inaga itada yayah ne"!_
Hannah ma dolenta ta dawo da muryarta daidai yayin fa'din hakan dan Ummah tariga ta tona ta.

Mummy naji amma bata tanka ba sai da taga Ummah taciro waya sannan taso saka baki amaganar duk da bata so haka ba amma sai taga yazama dole ne tayi maganar, tana shirin yin magana sai Hannah ta rigata tambayarta abinda Ummah zatayi da wayar ganin tana shirin nemo wata number, afirgice tace da ita _"wa kuma zaki 'kira Ummah da wayar"?_

_"Abbas mana, tambayarshi zanyi abinda yarinya nan tayi masa ya daketa"_

Hannu Hannah tasa tana 'ko'karin kar6ar wayar tace _"kai Ummah bazaki ci ribar zance ba kekam, daga magana sai ki 'kirashi kalan yazo yaci 'kaniyata yace ni ce nafa'da miki".?_

_" Toh me yasa zai daketa yatafi abinsa, daga zuwa gaishe shi dan_ _neman fitina da rashin ha'kuri sai yakama ya doketa, yarinyar da ake shirin taron bikin ta shine zai daka tsabar shi_ _ishashshe ko me?"_

Sai yanzu mummy tasamu damar saka baki amaganar tasu ganin Ummah ta 'dau zafi tace.

_" dama kin hutar da bakinki da zuciyarki akan yaran nan, indai Teemah da Abbas ne toh wallahi_ _gajiya zakiyi da magana har bakin ki yayi tsami, haka suke kullum cikin abu 'daya"._

_" toh ai wannan duk rashin ha'kurin na sa ne, taya zai rin 'ka biyewa yarinya 'karama har haka"?._ _mthewww_

Ta 'karashe da yin tsaki sannan ta da dawo da kallon ta da Hannah tace " _kinga Hannah je 'kiramin ita Fatiman, maza yi_ _sauri"._
Tafa'da tare da 'dago hannayen Hannah sai da taga ta tashi tsaye kafin tasake ta.

_" ki sauri mana"_
Ta 'kara cewa da Hannah ganin tana 'daga 'kafa ahankali kamar ba son zuwa take ba.

_" hmmm"_ kawai mummy tafa'di a'kasan ma'koshinta, ganin ko'karin Ummahn takeyi ita.

Ko bayan fitar Hannah Ummah cigaba tayi da surutu tana mita akan lamarin mummy ce ta dakatar da ita da fa'din

_" wannan abinda kike yi fah duk abanza ne inde akan yaran nan ne, kuma nasan babu_ _wani dukanta da Abbas yayi dan tunda muke dashi agidannan banta6a ji ko ganin yasa hannu ya_ _ta6a_ _lafiyarta ba duk kuwa da irin rashin ji da Fateema keyi_ _agidannan, ko yanzun ma nasan iskancin Teemah ne kawai ki rabu dasu."_ !

Kauda kai Ummah tayi gefe kamar bataji ba ga dukkan alamu maganar mummyn be wani shiga kanta ba, sai mummy ma tayi murmushi kawai ta ta tashi ta bata wuri.

Da Teemah ta tashi zuwa 'kiran da Ummah keyi matan gaba 'dayan su suka taho da sauran friends 'din nata dan cewa sukayi suma zasu wuche gida ganin lokaci ya 'dan ja.

Da fara'ah dukkansu suka shigo 'dakin saboda ragowar dariyar dasukayi duk be bar kan fuskokinsu ba, Naanah ce take kwatanta rawar da zatayi wai agurin bikin Teemah gashi bata iya rawar ba abin dariya kuma wai ita adole sai tayi ,Fauzee kuwa data kare mata kallo sai tace _wai_ _rawar Naanahn_ _tamkar agwagwa na tafiya_ hakanne yasasu dariya gaba 'dayan su shiyasa suka zowa Ummahn da murmushi akan fuskokinsu.

Ummah idanunta akan Teemahn yafara sau'ka da har yanzu takasa ri'ke tata dariyar idonta har yana hawaye tsabar dariya, aduk lokacin da ta tuno maganar Fauzee sai kawai taji sabuwar dariya ya kamata.

Mamaki Ummah tayi sosai kuma sai alokacin ta yadda da maganar mummyn data gama fa'da yanzun kafin ta tashi, yanda taga idanun Teemahn badan taga tana dariya ba da sai tace kukan dukan da Abbas din yamata ne amma ganinta tana dariya sai ya wanki ranta ta 'danji wasai.

Sallamansu kawai tayi batare da ta tambayi Teemahn abinda yafaru ba, haka suka je suka yi musu rakiya awurin gate suka musu sallama tare da godiyan ziyaran dasuka kawo musu daga nan su Fauzee sukayi gaba sukace sai nan da kwana biyu kuma idan sunzo shan shagalin biki.

*****
*LAGOS*

Mahmud kullun addu'ah yake kar Allah yasa Abbah yasake tunowa da maganar zuwa yoben nan dan shi ba son zuwa yake ba, Allah kuwa ya taimakeshi Abbah be sake bi ta kai ba, sai kawai yaci gaba shiryen shiryen dake gabansa.

Anty kuwa zuwa yanzun hankalinta inyayi dubu toh ya gama tashi, dan ganin yanda shirye-shirye ya kankama gashi Anty chideh ta 'ki bata ha'din kai suje gurin neman maganin har yanzu, ta ro'ki Anty Chidehn iya yanda zata iya amma sam ta'ki yadda har Anty ta ha'da da cewa zata iya samo mata 'yan mata duk irin wanda take so wanda suka ri'ka awannan harkar ko guda nawa ne matu'kar zata amince ta kaita wurin 'dan ogah, amma Anty Chideh ta'ki yadda tace ita kanta zata iya nemowa kanta indai tana da bu'katar su wannan ba matsalarta bane ayanzu.

Anty kuwa tace ita sam bazata iya aikata lesbian ba, bata ma son ko ka'dan taji ana labarinsa ji take yi kamar zatayi amai tun ranar data ga Anty Chideh nayi ta 'kara tsanar abun bata ma ko san tunowa dashi ballantana ita ta aikata shi da kanta, akan hakan ta gwammaci ganin auren Mahmud da ire-iren 'ya'yan Khadija ko da su nawane aduniyan nan indai har sai ta aikata lesbian zata ga rashin yiwuwar hakan.

Akan haka kullun suke dramma da 'kawarta Anty Chideh inda kowa ya kafe akan nashi ra'ayin, duk kuwa da wannan abinda Anty chidehn keyi mata hakan besa daidai da 'kwayar zarra taji haushin Antyn Chideh ba ko ka'dan, ahaukarta ita gani take kamar _so ne_ ai har yasa Anty chidehn taza6e ta akan hakan, sai dai rashin sa'ar da Anty Chidehn tayi shine ita Anty bata da ra'ayi.

Maimakon ta 'dan ja baya da Anty chideh a'a sai ma wani sake lalla6a ta data keyi akullum, saboda tsoron kar ta ce zata fita aharkanta ta rabu da ita gaba 'daya wanda take ganin kamar in hakan yafaru ba 'karamin asara tayi ba tana ganain cewa wahala zata sha in Anty Chideh bata tare da ita, gani take zata shiga uku domin Anty Chideh itace idanun ta afa'din garin Lagos, duk wani damuwarta, farin cikinta, ba'kin cikinta samu da rashin ta kafin kowa yasani sai Anty Chideh tasani.
Chapter 57 · 0% Book details