Sashe 90
Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hakan nema yasa da 'kawata ta nemi ha'din kanta izuwa aikata alfasha nice na tsaya tsayin daka wajen ganin faruwar hakan, akan haka Mahmud yazo yau 'din nan dasafe yana kuka Khadija, yana hawaye yake ro'kona akan meyasa nayi haka, meyasa zan bada irin wannan gudummuwar wa rayuwarsa, banji komai araina ba face 'karin haushin matarsa araina hakan yasa nafa'da masa maganganu son raina wanda be kamata ni in fa'da masaba amatsayina na mahaifiyarsa,
Kinsan me yace min ?
"Cewa yayi zai 'dauke matarsa su bar min garin yace inyafe masa in Abbahn sama yadawo ince ya yafe masa laifukan daya masa daga nan yatafi yana share hawaye, ashe 'karshen Mahmud kenan, 'karshen rayuwarsa kenan, ban masa adalci ba koka'dan amma duk da haka yace ya yafemin yace in yi masa addu'ah kawai Mahmud yatafi ya barni da ba'kin cikin rasashi da muguwar dana sanin da bazata ta6a amfanata da komai ba, kaicona nikam wallahi dana kasance me tsananin son kaina, inama zaka dawo Mahmud mu sake rayuwa dakai da sai na so ka na sada ka da 'yan uwanka na kula da kai yanda se ka zama abin kwatance zan zame maka uwa yanda kowa sai ya yi sha'awar rayuwarka, da kai kanka sai kayi alafahari da kasancewata uwa agareka, amma babu dama, ni da kai na nasan ni ba uwa tagari bace, ban kasance acikinsu ba face masu cika rayuwar 'ya'yansu da 'kunci, wahala da azaba gashi ni da kaina nayi sanadin rayuwarka.. inasonka yarona, inason ka Mahmud bansan me ya 'dauke hankalina na manta cewa kai 'din amana ne agurina ba, amanarka Allah ya bani gashi sanadina kabar duniya da tarin ba'kin ciki azuciyarka, Allah kaji'kan yarona kayi masa rahama, Allah ka hasakaka kabarinsa kasa shi 'din me rabone"
Ta 'karashe da kuka me ciwo tana dafe 'kirjinta, kusan dukkan wa'danda ke cikin 'dakin sai da suka zubda hawaye tsaban yanda Anty tacika zuciyoyinsu da tausayi.
Cikin kukan tace
"Khadija dan Allah ku yafemin, tun da sauran rayuwata, Mahmud ya tafi ya barni batare da yabani damar da zan ro'ki yafiyar sa ba wanda inajin ciwon hakan har azuciyata nasan wannan nawin baze ta6a barina in rayu cikin salama ba, Khadija idan ke ma kika 'ki ki yafeni bansan ya 'karshen rayuwata zata kasance ba, na tabbata nayi babban hasara dana 'dauki tsana mafi girma na shinfi'da atsakaninmu, gashi nan shine sanadin komai nice nayi hasara arayuwata gaba 'daya, Fateemah ki yafemin kinji dan Allah ku yafe min ko Allah ze ji tausayina "
Mummy kuka take tayi harda sheshsheka har maganar ma kasayi tayi gaba 'daya jikinta yayi sanyi da al'amarin Anty duk da yake dama ita bata wani ri'keta da haushi azuciya ba, kullum addu'ah take faman yi akan Allah ya shiryata yasa tagane cewa ita 'din bata nufinta da komai, tagane cewa 'dan uwa ba abin yarwa bane, amma hakan be samu ba har se da rai yabi al'amarin kafin nan, yanzu kam se fatan Allah ya jikan Mahmud yasa aljannah itace makomarsa muma Allah yasa mucika da imani Allah yasa kalmar shahada itace 'karshen kalmarmu.
(Ameen).
Kafin Mummy ta bu'di baki tayi magana sukaji anyi sallama ashe har anfito daga masallaci, anzo fita da gawa, cikin masu shigowan harda Abbas aka shigo.
Anan ne kam koke-koke ya 'karu dan Anty da Teemah kukansu nin kuwa yayi fiye dana baya, banda su Ummah ma da sauran mutane suma sai share hawaye sukeyi.
Anty kam ri'ke shi tayi tana sake zubda hawaye tare da dana sanin abubuwan duk data aikata abaya.
Abbas ne yace su 'dauka su tafi kawai kukan bashi da anfani tunda ba addu'ah zasuyi masa ba.
Haka suka 'dauke shi suka fita dashi zuwa waje.
Teemah kam cak kukanta ya tsaya tabisu kawai da idanu har ta daina hangosu, babu wanda ya lura da ita sai Ummah, itace tazo ta mi'kar da ita tsaye sannan suka koma gefe suka zauna taringa yimata nasiha tare da bata baki har ta nutsu.
Agurin Abbah aka ajiyeshi yayi masa addu'ah sosai hakama Alhaji Muhammad (kakansa mahaifin Anty).
Daga nan akayi masa sallah aka sada shi da makwancinsa na gaskiya.
Abbas kam suna dawowa daga ma'kabarta be wani da'de ba bayan yasamu ya isar da ta'aziyarsa ga su Abbah kawai ya wuche abinsa, dan baze iya shiga cikin gida gurin matan ba a wannan lokacin, bayaga haka ma shi sam ya tsani ganin fuskar Anty ayanzun.
Yana komawa kuwa ya tarar komai ya kammala sai kawai suka 'dau hanya.
Niyyarsa idan yakoma 'din ze nemi pass ne sai yasake dawowa gurin rasuwar amma kuma koda suka koma sai suka tarar da wani mummunan hari da aka kawo, an kashe dayawan sojojinsu aranar, ka'dan ne suka samu rauni inda 'kalilan daga cikinsu kuma suka tsira da rayukansu da 'kyar.
Washegari sauran 'yan uwan su dake 'kauye suma suka iso da 'yan uwan Anty inda so rin'ka tunawa da alkhairin da Mahmud ya musu kwanaki ka'dan da suka gabata, suna jinjina halin rayuwa ha'ki'ka rai ba'a bakin komai yake ba.
*****
Abin ya matu'kar 'kona ransa yanda 'yan ta'addan ke faman wasa da rayukan mutane batare da damuwar komai ba, sun maida rayukan al'ummah tamkar ran kiyashi, son ransu suke 6arna agurare batare da damuwar komai ba, haushin hakan yasa ya manta da batun mutuwar Mahmud kawai yafara tunanin neman mafita.
*BAYAN SATI 'DAYA* .
Kafin a'karo musu wasu sojoji Abbas da kansa yayi shiri sosai jin inda ma6oyar 'yan ta'addan yake acikin garin daga wani majiyar sirri sai ya yi shirinsa sosai musamman dayake akwai kayan aiki agurinsu sai sukayi amfani dasu tare da taimakon wa'dan da suka rage daga cikin battalion 'dinsa suka tunkari wajen da harin ko ta kwana.
Yariga yasawa ransa cewa ze yi ya'ki dasu da dukkan 'karfinsa da zuciyarsa hakan yasa be ji ko 'dar ba ya tunkare su da zuciya 'daya Allah kawai ya mi'kawa dogoransa, abu 'dayane dama abin tsoron shine mutuwa shikuwa be dame sa ba, yasan ko mutuwa yayi awanan halin Allah yasani, bashi da alhakin kowa dan haka no retreat no surrender.
Basu fi su goma ba, ha'di da armourtank guda biyu suka tunkari sansanin.
Allah cikin ikonsa kuwa gaba 'daya suka tada gurin suka 'kona komai, kafin hakan sai da yayi ko'kari wajen ganin ya kama director 'din su dake gurin araye, sai de kuma shima Abbas 'din an kashe kusan bakwai daga cikin sojojin nasa befi su biyar bane suka tsira da rayukansu.
Wannan abin da Abbas yayi ba 'karamin girma ya 'karawa hukumarsu ba, dan kuwa aganinsu yayi abinda bakowa ne ze iya yi ba sosai sukayi farin ciki tare da alfahari dashi, hakan yasa duk su biyar 'din da suka rage aka yi musu albishir na 'karinum girma.
Hutu aka basu na tsawon wata 'daya dan su koma ga iyayensu da matayensu.
*CONDOLENCE*😭
Sa'kon ta'aziya ga dukkan 'yan uwa musulmai da suka rasa yan uwansu da 'ya'ya yensu, ubangiji Allah yaji'kansu da rahama (Ameen).
Kuyi ha'kuri kuma masoyana, ha'ki'ka ni kaina naji mutuwar Mahmud sosai kamar yanda naga wasu dayawan ku ma suke fa'di , amma ya zamuyi , mutuwa dole ce akan kowa, kuma ahaka labarin yazo tun asali, kunga sai de muyi hakuri....
Dafatan zaku ci gaba da bina har akai ga ci........🤞🏻
👇🏼
Fatan zaku cigaba da min uzuri na jinkiri danake yi kafin kuga update musamman Wattpad reader's wlh abubuwa ke min yawa amma kullum kuna raina ban ta6a mantawa daku ba.😍
_Share_
_Vote_
_Comment_
*Salmerh ce*😍
[10/2, 6:03 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕
By
*Salmerh MD*
Luv story😍
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*
_Dedicated to u my lovely fans.....Allah ya bar min ku_.🥰
*Bismillahir rahmanir raheem*
_Failure is only a temporary change in direction to set you straight for your next success. Only_ _those who dare to fail greatly can ever achieve greatly_ .
🅿 *68*
Abbas ma porthacourt ya koma ya 'dan huta tukunna sai da yayi kwana biyu kafin yakoma Abuja.
Daddyn Abuja yaji labarin abinda sojoji suka aikata a Borno akafan ya'da labarai amma be ta6a zaton 'dansa Abbas bane ya jagoranci abin har se da Abbas ya dawo gida yake sanar dasu 'karin girman da za'a yi masa.
Mamaki sosai Daddyn Abuja yayi har yake tambayarsa dama haka akeyine, daga shigan mutun sai 'karin girma yabiyo baya.
Anan Abbas yayi masa bayani atakaice akan abinda yafaru, ai kuwa anan Daddyn Abuja yafara masa masifa akan abinda ya aikata 'din yake cewa yanzu badan Allah yarufa asiri ba inda sun kashe shi awurin fa, yace shi sam baya son rigima da tashin hankali yace shiyasa tun farko ni hankalina be wani kwanta da wannan aikin ba in ban dama Yayah Kabiru ya sa baki da wallahi bazaka yi wannan aikin ba ballantana har kaje kana rigima irin wannan, 'karin girman banza da wofi salon cuta, aidan sunga kana bada rayuwarka ne shiyasa inda bakayi hakan ba da bawani girma da sazu 'kara maka"
Shiru Abbas yayi yana sauraronsa sai da yaji yayi shiru kafin ya fara bashi
ha'kuri amma kamar 'kara zugashi yakeyi sai sake 6allewa yakeyi yana bu'de sabon salon masifa ta inda yake shiga bata nan yake fita ba, shi tsakaninsa da Allah yaji haushin
abinda yafarun.
Abbas dayaga haka sai yayi shiru kawai yaci gaba da sauraransa.
Allah sai ya taimaki shi ya kawo masa Daddy Babba dayake shi be baro wajen ta'aziyar Mahmud ba sai yau kasancewar Abbah babban abokinsa ne dole ya kasance dashi a kowani irin hali.
Yana shigowa kuwa yaji me suke tattaunawa akai sai da yaji Daddyn ya kasa fahimtar Abbas ne kafin ya jefo nashi da fa'din
" _haba Hassan, ya zakayi haka kuma? dama ya shiga aikin ne dan ya zauna yaga ana abinda bashine ba_ _ya kuma sar'ke hannuwa yana kallo?_
" _Ai kamata yayi ka 'kara masa 'karfin gwiwa tare da godewa mahallici daya sanya ya tsira da ransa, bawai kasashi agaba da bambami irin haka ba, da wanne zaiji?_ "