← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 163

Sashe 29

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shikuwa bai tsaya ko'ina ba sai wajen parking sai da ya bud'e motar ya shiga kafin ma ta k'araso itama ta shiga.

Ahanya ne yayi tajan ta da hira yana tsokanarta har sai dayaga ta sake gaba d'aya kafin ya kyaleta.

Koda yakaita makarantar ma dakansa yakama hannunta ya isa har office d'in shugaban makarantar yayi masa bayani tare da neman alfarma akan cewa bata jin dad'ine kuma tace zasu yi test shiyasa ya kawo ta so idan sun gama test d'in yana so ya wuce da ita clinic a dubata.

Principal d'in ne ya tambayeta sunan malamin da zaiyi musu test d'in tagaya masa, sai kawai yak'ira shi awaya ya tambayeshi lokacin dazai yi test d'in sai yace masa nan da 30mins ne.

Bayani yayi wa Abbas d'in daganan suka fito atare gaba d'ayansu sai Abbas yayi musu sallama akan cewa Teeman taje class ta jira lokacin yayi inyaso idan sun gama sai tasame shi amota.

Daga k'arshe suka yi musabiha da principal d'in yakoma office Abbas kuma ya tafi ga motar sa yayinda Teemah ta wuce class.

Tana zuwa ma bata dad'e ba akazo akayi musu test d'in
alokacin kusan 11:00am tayi, ko da suka gama sai class rep d'in su (Fauzee) da wata friend d'insu suka rakota har wajen motar.

Abbas kuwa hankalinsa naga wayarsa bai ga tahowarsu ba har sai da Teemah ta k'wank'wasa masa glass kafin ya ankara dasu.

Ahankali ya sauk'e glass d'in yana murmushi yace " lil sis yadai ko har kun gama test d'in?"
Kai kawai ta d'aga masa alamar "ehh".

" Shiga mu wuce "
Yace da ita.

Su Fauzee kam tun da ya sauk'e glass d'in suka k'ura masa idanu suna k'are masa kallo dan sosai yatafi da imaninsu.

Jin da Teemah tayi shiru bataji sun gaishe shi ba gashi har yana cewa tashiga su tafi sai ta d'an waiga ta kallo su gani tayi dukkansu suna kallonsa take sai ta ji ranta ya 6aci da hakan sai ta juya shima ta kalli 6angaren dayake taga nashi yanayin, cikin sa'a sai taga shi d'in bai masan suna yi ba dan hankalin sa ma sam baije ga inda suke ba.

Sai da ta bud'e marfin motan kafin takuma kallonsu tace musu "toh Fauzee nikam na wuce sai gobenku".

D'agowa fauzeen tayi ta kalli Teemahn sai ta kuma maida kallonta ga Abbas d'in tare da fad'in " ina kwana Yayah"

'Dago kai yayi ya kalle su dan shi harga Allah bai kula dasu awajen ba, sai lokacin da yaji Teemhn na musu sallama kuma ko a sannan bai zaci suna tsaye agurinba atunaninsa wucewa sukayi.

"Lafiya ya school " ya amsa mata dashi.

Ga mamakin Teemah sai taga
ya amsa mata wasai bawani d'aure-d'auren fuska kamar yadda yasaba fitowa a asalin millitary force d'insa ba.

Sai d'ayan k'awartasu mai suna Ameena itama ta gaisheshin kamar yadda Fauzee tayi abin mamaki bayan amsa gaisuwar harda tsokanar su yayi akan test d'in da suka yi wai ina de basu yi satan amsa ba" yanda ya sake musu fuska sai suma take suka sake dashi yayinda suka bashi amsa da fad'in " haba dai ai an girma anwuche wurin yanzu mun girmi satan amsa"

"Ohh daa anyi kenan" yafad'i da d'an zaro idanu waje.

Sai suka d'anyi dariya su Fauzeen

Shikuwa cewa yayi
" toh Allah yasa dai hakan ne", bari mu wuce kunga lil sis d'ina ba lafiya ina so in kaita clinic yanzu"

Har karo muryoyinsu sukeyi wajen fad'in " toh Allah ya kawo sauk'i yayin da d'aya ke fad'in Allah ya sawwak'e .

Jinjina kai yayi kawai tare da d'aga musu hannu daga nan yaja motar suka tafi.

Sosai su Fauzee suka ji Abbas d'in ya yak'ara birgesu.

Sai da ya hau titi kafin ya kallo Teemahn jin tayi shiru tun d'azun, sai yayi gyran murya ita kuwa fuskanta na saitin gabanta amma sai ta fahimci da it hakan dayake yana kallonta yayi.

Sai juyo itama ta kalleshi yayin da shi kuma yariga da ya maida hankalinsa ga tuk'I.
" wai dama kasansu ne yayah?
Ta jefa masa tambayar tana kallonsa.

" shi kuwa murmushi yayi mata dan dama abinda yake so kenan, amma sai yace mata " me kuma yafaru?,ko laifi ne dan mun gaisa dasu?

" a'a" tace ahankali tare da kawar dakanta gefen hanya.

Sarai ya fahimci damuwarta kishin Teemah sam baya iyah 6uya, he can recalled that lokacin daya zo gidansu batason ko gaishe shi ma tayi balle magana ya had'asu, haka ma da Mahmud yazo tai tayin rigima dan dai mahmud d'in ba irin sa bane da yasan har lokacin barinsa gidan bazasu yi wani shirin arzik'i dashi ba, kuma duk hakan yana faruwa ne sanadiyar son kanta sam bata so wani yafita ko kuma afifita wani akanta tafison a kullum ta zama tasha gaban komai akuma ko'ina ta kasance A.

Bai sake kulata ba har sai da suka zo daidai wajen mai saida kayan itatuwa harma ya d'an gota shi sai kuma yadawo da baya.

Fita yayi bayan yai parking sai yaje ga mai saida fruits d'in yasayo da d'an dama kuma kala-kala sannan yadawo motar aka zo aka sa masa su a boot daga nan yaja yafara tafiya yanzun ahankali yake tuk'in har suka zo gida suna yin parking yace mata "ki bud'e baya ki shigar da kayan can na ciki, "toh tace tana k'ok'arin fita ya kuma cewa " kinsan mai yasa na saya?

Da kai ta amsa masa alamar "a'a".

" toh tuna baya nayi ko kin manta?

Murmushi kawai tayi dan tasan labarin baya d'in kaf abakin mummy, shima sai yafara gaya mata irin abinda take masa abaya d'in lokacin tana k'arama da irin muguntar datake masa da rigimar sai an saya mata fruits kullum.

Dukkansu abin sai basu dariya sai ta bud'e motar tafito shima ya fito suka nufi bayan atare shi ya bud'e ita kuma tasa hannu ta d'auko ledar, tana fitarwa tayi saurin dire shi ak'asa tana nishi

" miye kuma" ya tambayeta da mamaki.

Karkata kai tayi gefe tare dayin
k'walk'wal da idanu tana kallonsa.

" gara ma ki zage ki d'auka domin ni nayi nawa tun abaya yanzu kuma lokacin kine kema"
Yana rufe boot d'in yake maganan.

Cikin shagwa6a tace " Allah akwai nauyi sosai yayah"

" koma menene fah sai kin d'auka yau d'in nan dan na fahimci ba k'aramar raguwa bace ke d'in kina nan kullum sai surutu amma ba amfani."

Baki ta tura sannan azuciye ta cicci6i ledan tayi ciki da shi, shima bayanta yabiyo hannunsa rik'e da wayarsa da kuma key d'in mota.

Tafiya kad'an ce ta iso dashi inda take tafita da k'yar kamar zata fad'i, tausayi tabashi da ganin yanda take kokuwa da ledan sai alokacin kuma ya tuna da bata da jin dad'i ma ashe sai yasa hannu ya kar6i ladan ya rik'e ahannunsa " muje intayaki d'auka kafin ki fad'i wa mutane".

Yaryarfe hannu ta fara bayan ya kar6a d'in ita adole wai zafi, yana tafiya tana binsa abaya har suka isa kitchen sai da ya ajiye ya juya kafin yace mata " inkin gama ki had'a min fruits salat ki kawo min"

"Ayyah yayah kamanta banda lafiya ne " Tafad'a kamar zatayi kuka dan harga ita bacci takeso tayi.

" kin warke ai naga."
Yana kan tafiyar ya bata amsa atak'aice.

Ita kuwa haushi ne ya cikata daman ba barinta zaiyi ta huta ba shine ya hana zama a school?

Cewa Baabah Lami tayi ta zuba su acikin fridge ita kuma tafice daga kitchen d'in.

Gurin mummy ta koma dan sanar da ita akan sun dawo amma koda taje sai bata tarar da mummyn ba hakan yasa ta wuce d'akinta ta sauya kaya kafin ta dawo kitchen d'in dan had'a masa abinda yasata.

*****
Acikin kwana ukun daya rage wa Abbas ya tafi ba k'aramar sakewa da Teemah yayi ba hakan kuma shi ya kawo shak'uwa mai k'arfin gaske atsakaninsu yakan 6ata lokaci yana mata hira da labarai na ban dariya, wani lokaci ya k'ira mata Mahmud awaya suyi ta hira dashi Abbas yana jinsu sai dai yayi ta murmushi in kuma sunyi abin dariya shima sai ya dara, yawo sukanje kusan kullum dashi hakanan yakan kaita islamiyah da boko ya kuma dawo da ita gida hatta muhibbat sai da suka kai mata ziyara tare da Teemah, anan ne ta fahimci ashe ma ba budurwarsa bace wacce abokinsa zai aura ne wato Saleem.

Ita kanta wani lokaci takanyi mamakin al'amarin takance ashe dama Yah Abbas ya na da fara'a da sakewa haka?, amma mai yasa bai ta6a gwada min asalin halinsa ba sai ya ari wani hali ya ya6awa kansa, kodan shi soja ne shiyasa yake mugun hali oho.

Mummy kanta taji dad'in wannan sauyin domin dama can bata son wancen d'abi'ar tasu ta rashin jituwan nan, kawai dai bata da yadda zatayi ne, kuma ganin hakan ne yasa ta manta da fushin datakeyi da Teemahn akan abinda tayiwa Abbas d'in saboda sosai hakan ya 6ata ran mummy aganinta raini ne kawai ke damun Teeman tunda shi Abbas d'in ai ba abokin wasanta bane.

Cikin wannan kwanakin ne kuma Fauzee ta takura Teemah akan al'amarin Abbas d'in yayinda abin yake matuk'ar k'ona ran Teemah fiye da zaton mai karatu, tun daga ranar da Abbas yakai Teemah school har suka gaisa shikenan kullum sai sun rakota in sun tshi zata koma dan kawai su ganshi, wani lokaci har 6uya take yi dan kar su ganta, hakan bazai hana washegari su kuma tambayanta abu akansa ba most especially fauzee tafi damuwa dashi sosai.

Bata kula ta haka take danne ranta har sai inta dawo gida sannan ta yi ta masa mita da fitina akan hakan shikuwa da bama sanin kirki yayi musu ba yadai san sun ta6a gaisawa da k'awayenta amma yanzu koya gansu he can not even recognize them amma duk da haka dan ya k'ara bata haushi sai yace " wai har yanzu bata daina damunki ba, jiya fah da mukayi waya nace mata karta na sakoki akan maganar amma bataji, kiyi hak'uri lil sis ki barni da ita zanyi maganinta"
Chapter 29 · 0% Book details