← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 118 OF 163

Sashe 118

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rausayar da kanta tayi gefe tana kallon shi, Abbas baya son taga kamar yana matsa mata ne dan haka sai yace " _owk, zan barki kiyi amma make sure that mura na kamaki ba sassauci Anty nurse zan'kira ta ringa yi miki_ _injections har sai muran ya tafi...kin yarda_ ?

Tana jin haka ta karya mai kafa'da alamar bata yadda ba.
Abbas sakin ta yayi tare da nuna mata hanya yace
" _Toh oyah go inside!_ "

Dolen ta ta shigo ciki tana 'kun'kuni 'kasa-'kasa, shima Abbas take mata baya yayi bayan ya rufe 'kofar.

Teemah 'dakin ta ta wuce cikin fushin an hanata wanka inda tana komawa 'dakin ta hau cire kayan dake jikinta dan sun ji'ke sosai.

Sai da ta cire su gaba 'daya kafin ta nemi towel ta 'daura ajikin ta sai ta shiga bathroom 'din ta ta cika bathtub da ruwa ta shige ciki afili ta furta " _in ka hana wancen ai baka isa ka hanani shiga wannan ba, mutun_ _kullum sai de ya hanaka rawan gaban hantsi.....abu ka'dan sai ya wani ce injection! Wannan da ace shine yake yin alluran ai da anshiga uku nasan da kullun sai ya min goma ko.biyar dan mugunta! "_
Ta 'karshe da jan tsaki daga 'karshe.

Abbas ma a parlour ya zauna inda ya 'dau lokaci yana amsa waya sai da ya gama kafin ya wuce ciki dan watsa ruwa be ko sake bi ta kanta ba.

Teemah kuwa ta jima cikin ruwan hankalinta kwance sai da ta fara jin hanjin ta na motsi ne sannan ta fita aruwan tayi wanka mai kyau tafito.

Koda ta fito sai ta tsaya kuma ta 'debi wayarta dana Mahmud ta zauna bakin gado, layin Umar ta nema cikin wayar marigayin ta'kira shi lokacin 'karfe sha 'daya ta wuce sosai 11:42am.
Umar yayi mamaki sosai data 'kirashin ya kuma ji da'di musamman dayake shima Maman Amal na yawan damunsa
akan batun Teemah.
Nan yayi mata al'kawarin zai ha'da su da zaran ya koma gida.

Cikin hanzari ta shirya tare da kwaso wayoyin harma dana Mahmud saboda sauri ta fito dan nemawa cikin ta dake 'kugin neman agaji mafita.

Turus taja ta tsaya ganin babu komai akan dinning, bata 6ata lokaci ba sai ta wuce 'dakin sa ta same shi yana sa kaya shima.

Bata damu da yanayin dayake ba ta isa wurinsa ta ha'de goshi ta ita adole tana fushi dashi tace " _Yayah nifa yunwa nake ji kuma banga komai a dinning ba_ "!

Be kalleta ba yace " _Ya za'ayi kenan_ ? _dama nace a daina kawowa ne saboda bakya ci....._ "!

Da sauri ta tare shi da fa'din " _inaci mana bagashi yanzu ma ina jin yunwa ba_ "

Kwafa yayi yana kallon da ta gira a'dage jin yanda tayi maganar, cikin salo yace da ita
" _Harda fa'da ne kuma_ ?

Baki ta tura gaba ta kauda kanta tace " _Ni ba fa'da nayi ba ai yunwa nake ji ne shiyasa_ "!

Cigaba yayi da 6alle bottuns 'din longslip 'din daya sanya ajikinsa yace

" _Sai kije kitchen ki samu abinda zakici ko noodles ma ki tafasa kici zaifi sauri_ "

Dan haushi ma Teemah ko jira ya gama maganar batayi ba tafice abin ta, jitayi badan yunwa na damun ta ba da babu abinda zai sata shiga kitchen yanzu.

A parlour ta ziba wayoyin dake hannun ta sannan ta wuce.
Koda ta shiga kitchen 'din kuwa sai ta wuce fridge ta 'dauko fruits ta gyarashi ta hau sha har da zaman ta kan stool 'din dake cikin kitchen 'din.

Sai da ta 'danji dama-dama acikin ta kafin nan ta kunna gas ta dafa indomien ta dai-dai cikin ta tajuye a plate tarufe da wani plate 'din harda 'dora forkspoon 'din ta akai, sannan tayi mixing fruits tayi juice 'din ta 'dan dai-dai a 'kasan glass jug da extra cup 'daya batare da wani 6ata lokaci ba kuwa ta kammala duka tafito.

Kan dinning taje ta ajiye su sannan takoma kitchen 'din domin kimtsa shi dan bata son idan tafita tasake dawowa dan kim tsawa ba.

Batafi 9mins a kitchen 'din ba ta kammala tafito da ruwan ta mai sanyi a hannunta kawai sai idanun ta ya sau'ka akan Abbas yana siffing mata drink 'din data ha'da cikin kwanciyar hankali kamar ance shi aka ajiyewa abincin.

Ga plate 'din abincin ta ma bu'de a gabansa da ga dukkan alamu yana kan ci ne.

Turus taja ta tsaya dan haushi ma sai tarasa me zata ce dashi, shima sai yayi tamkar beganta ba yaci gaba da cin abincin cikin natsuwa.

Data ga haka ne sai ta taho da sauri har idanun ta na tara ruwa dan takaici sai ta tsaya agaban sa tace " _Yaya abinci na ne fah_ !

Gira 'daya ya 'dage ya kalle ta sai ya kuma kallon abincin yace " _really!_ ?
_Ai ban sani ba ne i thought nawane kika ajiye min ai_ "

" _Ai baka ce min zaka ci ba_ "!

'Da, zaro idanu yayi yace
" _Au sai ma na fa'di zanci kafin adafa dani_ ?

Shiru tayi masa bata yi magana ba sai hawayen ta da suka gangaro, harga Allah yau 'din yunwa takeji sosai kuma tayi niyyan cin abincin ta sosai take son jin wani abu acikin ta.

Ganin tafara kukane yasa yayi murmushi tare da janyo hannun ta ya zaunar da ita kan kujerar kusa dashi, be yi magana ba sai kawai ya 'debo abincin ya nufo bakin ta dashi.

Babu musu Teemah ta bu'de bakin ta ta kar6a.
Sai yayi mata murmushi aransa yace da din waya gaya miki Borno gabas take? ai yunwa maganin kowani fitinanne ne yasan badan taji yunwa ba da yau 'din yanda tayi fushi dashi 'din nan dako kulashi ma bazatayi ba sai gashi kuma har abinci yabata abaki kuma ta kar6a, afili kuwa sai yace da ita" _ni ban ta6a ganin inda mata ta hana mijin ta abinci ba sai_ _yau awurin ki! wato cikin ki ka'dai kika sani ko?_ "

Shiru taui kamar bada ita yake ba sai ma kauda kanta da tayi gefe, Abbas sai ya sake 'dibowa ya mi'ka mata itama sai ta bu'de baki ta kar6a.

Sai daya bata kusan spoon biyar batare da yaci ko 'daya ba data kar6i na biyar 'din ne sannan cike da tsokana yace da ita " _cinye abinki tunda bakya so inci nima zanje wurin Zahra ta ta dafa_ _min_ "

Tsayawa tayi tana kallonsa shima kuma haka dan kawai ta tabbatar da abinda yace 'din, ganin hakan shima ya tsare ta da idanu sai ta kauda nata idon ta maida shi gefe, duk iskancin ta da rashin jinta bazata ta6a iya kallon kallo da shi na tsawon lokaci ba, sosai kwarjinin sa ke karya mata zuciya, tsawon mintina kusan biyu babu wanda ya furta komai acikin sannan Teemah ta ha'diye abincin dake bakinta ahankali.

Yana shirin 'kara 'debowa sai ta yi sairin rike mai hannu, bata kalle shi ba koda yabi ta da kallon mamaki ma bata san yayi ba, dan ita plate 'din abincin take kallo.

Kar6i spoon 'din tayi ta 'dibo abincin tayi dauriyan kai masa bakin sa batare da ta sa idanun ta cikin nasa ba, Abbas kuwa sai ya'ki bu'de bakin sai ma kauda kansa gefe da yayi.

Hakan ne yasa ta kalli idanunsa sai ya'ki bata hankalinsa.

Cak ya mi'ke tsaye ya koma cikin 'dakin sa domin tsabtace bakinsa.

Teemah tamkar statue haka ta zauna ri'ke da spoon a hannu sai ta rasa me yake mata da'di, Abbas be da'de da shiga 'dakin ba ya fito hannunsa ri'ke da makulli ko kallon inda take be sake yi ba ya kama hanyar barin 'dakin.

Ganin haka yasa Teemah ta mi'ke da hanzari cikin sassanyan murya ta ce da shi " _Yayah wurin Zahran zaka tafi_ ?
Da " _umm_ " kawai yabata amsa batare da waigo ba, yana me cigaba da tafiyar sa ahankali.
" _Nima zan bika_ "
Ta sake cewa da shi wanda jin hakan ne yasa shi waigowa ya kalle ta dai-dai lokacin kuma sai waya ta 'dau 'kara daga cikin parlourn dukkan su sai hankalin su ya koma wurin.

Teemah ce taje da sauri dan tasan ita ta ajiye waya a parlourn, hannu tasa ta 'dauki wayar hannun ta har na rawa dan yanda zuciyar ta ta tsinke tun daga jin 'karan ringing 'din dan tasan ba wayar ta bace ta kuma riga tasan kalan ringing 'dinsa tun yana raye, gani tayi number ce ba suna.
Aduk lokacin data ga wani abu daya danganci Mahmud sai ta tuna da shi balle wannan daya kasance 'karan wayar sa ne da ta saba ji atare dashi tuni sai ya sa zuciyar ta bugu cikin sauri.

Kafin tayi wani yun'kuri har wayar ta tsinke.

Abbas ma ganin wayar da kuma yanayin data shiga yasa hankalin sa ya dawo kanta shima ahankali ya dawo baya ya tsaya nesa da ita ka'dan yana sake karantar yanayin ta, be san wayar waye ba ce kuma yasan ba tata bace dan yariga yasan nata dayake shine da kansa ya canja musu bada jimawa ba ita da Hannah iri 'daya.

Take wayar tasake 'daukan wani 'kara wanda yasa Teemah sai da ta danganta jikinta da kujera kafin ta iya amsa 'kiran tana me danne hawayen ta ta kai wayar kunnan ta da rawan jiki.

Shiru tayi tana sauraran me ake fa'da mata wanda tuni hawayen tan suka kasa tsayuwa suka gangaro kan kuncin ta.

Ganin haka yasa Abbas ya 'karaso kusa da ita ya kai hannu ya cire wayar akunnan ta ya ha'da ta da kunnansa.

Yin hakan keda wuya sai Teemah ta fa'da jikin 'kafafunsa ta rungume 'kafafun tana mai cigaba da kukan ta.

Yana sada wayar da kunnan sa yaci gaba da saurara batare da ya furta komai ba.

Sai yaji ana fa'din"............ _kullum na'kira bana samunka yalla6ai_ _sai yau dan Allah kazo ka duba aikin daka bani, inaso in gaya maka cewar Innah_ _na cikin farin ciki yanzu ha kama yaranta kuma tanaso ta gode maka bisa_ _taimakon dakayi mata amma bama samun ka shiyasa ta damu, ni ma_ _kuma ina so kazo kaga aikin daka bani jagoranci bansani ba kona yi_ ' _ko'kari"_ __ !
Chapter 118 · 0% Book details