← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 154 OF 163

Sashe 154

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da idanu yayi mata nuni da kujerar data tashin nufin sa ta dawo.
Teemah kam tuni har ta fara sau'ke hawaye haka ba dan taso ba ta dawo ta zauna tana mai share hawaye.

Kanta a 'kasa hawayen nata na ci gaba da sau'ka tana aikin sharewa Abbas kam ko 'kala bece da ita ba kawai ya zuba mata idanu ya kasa tuno abin da ya sata fushin ma gaba 'daya.

Teemah kuwa jin be kulata ba ya sanya ta 'daga kai ta kalleshi fuskarta cike da hawayen sai suka ha'da idanu take sai ta tashi da sauri ta dawo 6angaren daya ke 'din ta rungume shi ta baya sannan ta saki kukan mai sauti.

Sosai ta bawa Abbas tausayi musamman yanda tayi abin tamkar 'yar yarinya 'karama wacce tayiwa mahaifiyar ta laifi.
Badan kuka takeyi ba da babu abinda zai hana shi yi mata dariya amma sai ya basar kawai ya yi 'ko'karin dawo da ita ta gaban sa sai ta no'ke kanta a arms 'din sa tana sake yin kukan.

Lallashin ta yafara cikin hankali amma sai ta 'ki daina kukan har se da ya daka mata tsawan "nace ya isa ko?"
Kafin tayi shiru.
Bai sake magana ba sai da yaga ta nutsu tana sau'ke numfashi sannan ya 'dago kanta yace " me ya faru ne wai ?"
Cikin shagwa6a tace " ba kai bane"
Abbas da mamaki yace " Ni kuma Zahra yau kuma me nayi?"

Sai ta tura baki tace " ai baka so na kullum sai baby kake so"
"Shine kike kishi da babyn ?"
Shiru tayi kawai ta kalleshi cikin idanu sannan ta kawar da kanta.
Abbas sai yaja kumatun ta da duka hannayen sa biyu sannan yace " 'yar 'kauye da babyn naki kike kishi? Ke da zaki rin'ka goya babyn kullum kina bashi mama kina yi masa wanka miye abin kishi kuma?"
Wasa kawai takeyi da hannayen ta kanta na kallon 'kasa.
Sai yake fa'din "...owk..nagane...nima kina so idan lokacin yayi nayi kishin ko?"

Sai ta jijjiga masa kanta alamar ah ah.
Yace " zanyi mana, ai ni ya kamata ma nayi kishi dan baby zai kar6e min abuna dayawa dake wajen ki, kinga zai 'dauke min hankalin ki ki nasan da 'kyar ne ma idan baki daina kulawa dani ba, zaki iya daina tayani wanka, zai kar6e min abinda nafi so ma a jikinki kinga ai dole zanyi kishi"

'Daga kai tayi ta kalleshi da zararren ido alamar tambaya sai yayi mata nuni da boobs 'din ta da idanun sa itama sai tabi wurin da kallo take sai ta gane mai yake nufi sai yaci gaba da fa'din " abin tausayi zan zama may be ma ki daina bani abinci kin ga ai ni ya kamata nayi kishi ko? sai dai kinsan wani abu?"
Kai ta jijjiga masa sai yaci gaba da fa'din "amma kuma ni bazan yi kishin ba saboda nasan lokacin sa ne kuma zai wuce idan yayi wayo ma shikenan ni 'din ne kuma za'a dawo ma wa domin ni 'din special ne kuma na har abada......kamar yadda kike a cikin rayuwata, in banda shirmen ki ma a ina kika taba jin anso baby an 'ki uwar da babyn ke jikin ta ke baki san albarkacin ki babyn yaci bane ma har nake kula dashi......."

Da irin wa'dan nan kalaman yayi ta lalla6a ta har ta ha'kura inda yace mata gobe zasu fita saloon.

Kafin dare ta gama sakewa ta bar fushin gaba 'daya Abbas kuwa koda suka je bacci sai da yayi ta faman tsokanan ta wai " Jealousy Mummy towards unborn"
Da 'kyar ta samu ya bar ta tayi bacci har sai data zaune shi gaba 'daya ta hau jikinsa ta 'dane tare da ha'de bakin su kafin ta samu ya yi shiru a haka har bacci ya 'dauke ta da hannnun ta kan dimples 'dinsa, daga baya ne ya gyara mata kwanciyar ta.

*****
Washe gari ya kama ranar monday, Abbas da azumi ya tashi ranar dayake yana na nafila monday da thursday, 11:00am suka isa wajen saloon 'din inda suka samu ma ba wasu mutane sosai, kitso yace ayi mata koma wani iri ne amma yace banda 'kari yace ayi mata haka da gashin ta kawai.

Teemah kam shiru kawai tashi amma tasan zata sha azaba domin rabon kanta da kitso tun kafin auren ta da Abbas tun da ta aure shi kuwa bata sake yin kitso ba har yau.

Abbas a waje ya koma cikin mota yana jiran a gama mata su wuce.

Minti sha biyar bai cika ba a wurin wata yarinya dake aiki a wurin madam 'din tazo tayi 'kiran sa.

Fita yayi da mamaki yabi bayan ta inda suka koma cikin shop 'din, yana sa kai ciki sai kuwa idanun sa ya sau'ka kan Teemah dake kuka da hawaye hannun ta 'daya akan tana bin hannun mai kitson, tun fitar shi basuyi ko 'daya ba tsagu kawai akayi Teemah ta tsaya rigima wanda hakan ne yasa madam ta aika a 'kirashi.

Cikin sassarfa ya 'karaso gaban ta ya tsugunna ya 'dan ha'de rai yace " kuka kuma Zahra kitson da zafi ne?"

Sai tayi saurin 'dage kai wani sabon hawayen na sake sau'ko mata.
Da rawar murya tace " Kace....mata ta dai....na yi min mai zafi.... to".
" Naji shikenan to share hawayen ki wani iri kike so ayi miki?"
Ya tambaya yana share mata hawayen.
"Chukwun ibra zata yi min amma zafi yake min sosai ni bana so".

Da kansa ya sake za6a mata wani kitson kalba yace ayi mata shi 'din 'kila ba zaiyi mata zafi ba daga nan yafita ya bar su.

Sun kai 1hr suna kitson kafin suka kammala ta fito idon ta jajur da 'dan kwalin ta a hannu ta fito veil ne kawai ta bari akan nata ko kunya bata ji tasha kukan kitso da girman ta.

Abbas ne ya koma ya biya balance sannan ya dawo cikin motan ya so suje yawo amma ganin ta kamar ba'a nitse ba yasa kawai ya maida ta gida.

Suna isa barrack gaban block 'din su yayi parking Teemah fita tayi ta shige ciki da sauri.

Abbas kuwa ganin Sam abokin sa ne yasa shi tsayuwa a wurin sa dan su gaisa.

Tana shiga ciki ta zame veil 'din tare da cire pencil skirt 'din dake jikinta ya rage mata 'dan guntun wandon skinny wanda yake iya gwiwa da rigar 'dinkin 3quarter atamfar ta bari kawai ajikin ta.

Bedroom ta shige domin ajiye kayan sannan ta wuce wurin mirror ta na kallon kitson.

Duk da bawani style mai kyau bane amma ita kanta tasan ta canja sosai goshin ta ya fito har iska takeji yana shigan ta.

Tana tsaye gaban madubin tajiyo muryar sa yana 'kiran ta sai ta fito a hankali tamkar bata son yin tafiyar ta nufo shi.

"Zo inga kitson naki mana kuma".
Yace da ita yana murmushi sosai ya shirya tsokanan ta a yau 'din.

Itama kamar ta sani sai ta shirya dakewa a zuciyar ta dan tasan sai yayi mata dariyar tayi kukan kitso.

Kusa dashi tazo ta zauna tana wani shan kunu ita a dole zata tsare.

Abbas murmushi yayi yace " kitson fa nace zan gani kika wani ci magani a can "
Matsowa tayi tare da 'dora kanta akan cinyar sa ta kwanta sannan tace " gashi nan ka gani".

Murmushi yayi ya shafo kitson yace "gaskiya matar nan ta taimakeki, jibi fah yanda kan naki yayi kyau shine ko kunya baki ji baby na kallon ki kika ringa rusa kukan kitso ko?"

Baki ta tura gaba sannan tace " ai wanan 'din da zafi ne shiyasa".
Hannun na kan nata yana ta shafa kitson yace
" Ke de kice baki so kawai amma miye abin kuka a kitso".

"Allah Yayah da zafi ne rabona da kitso fah tun kafin auren ka".
Da mamaki ya tambayeta
"Aure na kika ce ? to ke kuma fa banda ke ko?
'Kasa-'kasa tace " har da ni mana"
Abbas sai yace
" to tun kafin auren mu zakice not me alone.......kinje kina ta kukan fisabilillahi yanzu idan kika haifi baby girl kuma zakiyi mata kitson ko ?....ni kam idan kika dukar min baby akan kitso ni da kene a gidannan....ai na riga naga sirrin"

Shiru tayi masa itama tana tunani bata yi magana ba har bacci ya yi gaba da ita.

Da yamma ta shirya masa 'kyataccen girki na gaban kwatance sosai kuwa yaji da'din hakan inda ya ringa saka mata albarka yanaci yana yaba mata.

Teemah bata tashi sanin tsananin son kitso da Abbas keyi ba sai da sukaje bacci yanda yarin ga yabon kitson yana shafo wa abin har mamaki yaso bata, dan tunda suke dashi bai ta6a nuna mata yana son kitso ba ko yanzun ma tasan ya kaita kitson ne dan yawan 'kai'kayin da kan ke mata kuma wai dan kar tsefaffen gashin ya ringa damun ta.
Amma ba wai dan ra'ayin kansa ba.

Sosai take jinjina wa miskilancin sa a hakan ma ita bai fiya yi mata ba sosai yake sake mata fuska har take sanin wasu abubuwan sa, in kana son ganin asalin halin sa to ka tsince shi cikin uniform kaki a lokacin ne zaka tabbatar da ko shi waye amma banda cikin gidan sa.

Duk kuwa wannan abinda ke faruwa Abbas be sanar da kowa ba, ko su Ummah be iya 'kira ya sanar dasu ba, ya dai sanar da Leesah inda tayi matu'kar farin ciki ta taya shi murna, Teemah kuwa wa Maman Amal ka'dai ta sanar mawa.

Tanas o ta bawa wani daga cikin dangin ta labarin abin farin cikin daya same ta amma ta kasa gaba 'daya kunya ya ishe ta ganin shi da yake namiji ma bai fa'da ba sai ita toh ta ina ma zata fara.

Watarana da suna waya da Anty sai tayi tunanin sanar da ita don tasan yanzun Anty ta canza ba kamar da bane, bayan sun gama gaisuwa da 'kyar Teemah ta harha'da kalaman tace
"Anty ba.... da cikina na motsi ba sai mukaje wurin Doctor Yace mana...wai....wai...."
Sai ta kasa cigaba da maganar nauyin kalmar take ji.
Chapter 154 · 0% Book details