← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 163

Sashe 111

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunaninsa ya tsaya ne lokacin da ya bu'de 'kofan bathrum idanunsa suka sau'ka cak akan jan pant 'din ta dake shanye tun jiya abayin.

Wani 'kululun ba'kin ciki, haushi da takaici hade da kishi ne ya tokare sa, sai yanzu ne ya fahimci asalin abinda Auwal ya gani da har tunanin can yazo masa.

Tsaki yaja tare da jan 'kofan bayin ya koma parlour.

Waya ya 'dauka ya 'kira layinta ta kuwa 'dauka dan lokacin already an gama yi mata kwalliya tana zaune da wayar a hannun ta.

" _Hello_ "
tace ahankali.

" _Me kike yi_ ?
Yace da ita a kausashe.

itama tace
" _Ba komai_ "

" _maza ki zo yanzun nan karki 6ata min lokaci_ "
Be jira jin amsarta ba ya ending call din.

Teemah baki ta tura gaba ta kalli inda Hannah take tsaye tana rage kayan jikinta sai kuwa suka ha'da idanu, Hannah da bata gani tayi shiru sai tace
" _Ya daga amsa waya kuma kin fara fushi ince dai lafiya?_

Amsa ta bata da fa'din
" _Ba Yayah bane yace wai inje_ "!

Hannah sai cewa tayi
" _Dodo yayi kira kenan, sai ki tashi ki tafi ai kinsan angon naki sai ahankali inajin be gaji da ganin ki bane kika gudo"_

Kalan tausayi tayi tace
" _Dan Allah Hannah kije ko kuma 'kira shi kice masa 'kafata na ciwo....._

Tare ta Hannah tayi da fa'din
" _Ah ah sai de ince masa 'kin zuwa kikayi..._

Sake marairaicewa Teemah tayi tace
" _Haba dan Allah Hannah_ "

" _ni baruwana kinga tsakanin ku ne, yanzu fah mijinki ne kun fi kusa, daina sani a shirgin ku please_ "

Tana maganar ta nufi bathrum.

" _Hannah toh dan Allah tsaya ki raka ni mana_ "

" _Daya 'kira 'din yace miki kije ke da Hannah ne, i thought amarya_ _ka'dai ya nema_ !

Tana gama fa'din haka tashige abinta tana dariyar mugun ta.

Teemah sharewa tayi kawai ta tashi ta wuce wurin Mummy dayake dama tun safe basu ha'du ba, Mummy da bata san me ake ciki ba sai ta zaunar da ita ta ringa yi mata nasiha kawai akan biyayyar aure.

Anan Hannah tazo ta same ta dan tana gama wankan ta taho 'dakin da Mummy take anan take shiryawa tunda aka fara biki, sai kuwa taga Teemah tawani bararraje tana hira.

Hannah cewa tayi
" _har kinje 'kiran Yayan kin dawo ne_ "
Da gangan ta tambaya dan tasan it's hardly ace Teemah taje batare da tayi taurin kan nan nata ba.

Harara Teemah ta banka mata tare da ha'de ranta.

Muryar Mummy tajiyo tana fa din " _na me kenan_ ?

'Kasa Teemah tayi da kanta ta rasa me zatace dan tuni ta hango 6acin rai a fuska da muryar Mummy, gashi ita ba kowani lokaci ta iya shirya 'karya ba ballan tana ta fidda kanta.

Mummy ne tasake fa'din
" _Teemah karki kuskura kice min Ya 'kiraki ne baki je ba kika yo nan"_

"' _Karyan Hannah ne fah...Mummy naje ni... tun 'dazu"!_
Tayi maganar kamar zatayi kuka.

Mummy juyawa tayi ta kalli Hannah ta ce " _da gaske ne wai Hannah abinda ta fa'da_?

Hannah sai da ta kalle ta suka ha'da ido sai ta kawar da nata idanun tace
" _Bawani nan Mummy yanzun nan ne fa dazan shiga wanka ya 'kiratan_ "

Mummy dawo da kallon ta tayi wurin Teemah tace " _na 'kirashi na tambaye shi kin yarda_ ?

Da sauri ta jijjiga kanta alamar " ah ah"ta 'kara da fa'din " _Allah Mummy Yayah allura yake sawa ayimin fah_ "

" _Bana son maganar banza Fateemah alluran saboda lafiyar waye akeyin ta?_

Shiru Teemah tayi ta sunkuyar da kanta 'kasa tana ta juya hannayen ta cikin juna.

" _Ina tambayarki_ "!
Mummy ta daka mata tsawa.

Afirgice tace " _saboda... nii....ne_ "

" _Toh 6ace min a'daki na tunda ke kullum kunnen ki bana jin magana bane kije kiyi tayi, kuma saura inji cewa baki jeba_ "

Tashi tayi sum-sum ta kama hanya tana bankawa Hannah uban harara kamar idanun ta zasu fito.

Hannah kam sai gwalo take yimata tana 'karawa har suka daina ganin juna.

Aranta tace " _kiyi ha'kuri 'yar uwata ina sonki sosai kuma inason ganin kina farin ciki, amma nasan matu'kar kika ci gaba akan haka toh bazaku shirya da Yayah ba ni kuwa *BURINAH* inga kun gyara auran ku kun rayu kamar kowa"_.

Fitan Teemah kenan sai ta ha'du da Anty, take ta jefa mata tambayar ina zata kuma haka?

" _ba Yayah bane yace wai inje kuma fah Anty allura yake sawa ayi min_ "
Cikin shagwa6a tayi maganar tana turo baki.

Murmushi Anty tayi tace da ita
" _Habah kuma yarinyata da akeyi miki alluran bakiga kin fi samun sau'ki bane, maza kiyi_ _sauri kije kar ki 6ata masa lokaci_ "

Haka ta juya ta tafi tana 'kun'kuni har ta isa.
Ciki-ciki tayi sallama haka kuma shima ya amsa mata ahankali.

'Karasowa ciki tayi sai ta tarar dashi hakimce a kujera tamkar wani sarki, ba 'karamin kyau yayi mata ba amma sai ta ta6e baki tare da kawar da kanta gefe.

Inda yake ta'karaso ta ce " _ina kwana Yayah?_

Abbas kam wani yanayi na 'kauna da shauki ne yayi nisan tafiya da shi hakan yasa be ma ji lokacin da ta gaishe shin ba, ita kuwa bata 'kara ba sai ta ci gaba da tsayuwan ta.

Tunaninsa na dawowa sai ya kauda da kansa batare da ya sake kallon ta ba yace " _kinyi breakfast ko_ ?

" _Uhmm_ " tace dashi.

" _Me kika ci_ ?

" _Chips da...._
Kafin ta 'karasa ma yatare ta da fa'din " _D'auko maganin ki ki kawo ingani_ "

Wucewa tayi cikin bedroom 'din nasa ta 'dauko maganin saman drawer ta kawo masa.

Maganin ya 6alla ya bata ta kar6a tasha, har zata tafi ma ganin cewa dan maganin ne ya kirata kawai sai taji yace da ita ta wuce bathrum ta 'dauke wannan abin nata da bari kuma karta kuskura ta sake amfani dashi, in kuwa ta 'kijin magana shi da ita ne.

Zuwa tayi ta dudduba dan shaf ita ta manta da pant 'din ta nan, tana gani kuwa ta hau gungunin " _ina ruwansa da abuna toh, dama me yakai idonsa wurin da har ya gani._ ?

Haka tazo ta wuce shi tana tura baki.

Shima binta yayi da kallo harta fita, sai ya jijjiga kansa.

*****
'Karfe 11:07am na ranar aka 'daura auren Abbah da amaryar sa Halimatus Sadiya, 'kanwa ga Hajiya Aisha matar abokin sa da tayi siyayyan kayan auren Mahmud.

Anty Sadiya 'yar kimanin shekaru 31,kuma bazawara ce da mijin ta ya rasu ya barta da yaranta maza biyu, bayan rasuwar sa kuwa dangin sa sai suka kar6i yaran a hannun ta suka ri'ke agurin su.

Sam bata da matsala koka'dan, tana da hankali da nutsuwa, uwa uba ilimi ingantacce ya wadace ta boko da arabi, ga ta da son mutane da kuma yawan kyautata musu, wanda wannan dalilin ne yasa Abbah da kansa yayi sha'awan auren ta domin ya sa6unta rayuwar gidan shi da ya kafu shekaru da dama da suka shu'de.

Ahalin yanzu kuwa burin Abbah yariga yacika domin an 'daura auren da Haleeman sa, bawai dan baya son Anty ba ah'ah sai dan kawai yana so shima rayuwar gidan shi ta canja.

*****
'Kayataccen Dinner aka shirya wanda tsirarun mutane ne suka halatta saboda ba gaiya sosai akayi ba, shima 'din Abbas be wani 6ata lokacin sa ya gaiyaci abokansa ba wa'dan da suke kusa dashi ne suka sani su 'din ma yawanci friends 'din sa na secondary school ne.

Daga wurin dinnern aka wuce da amarya zuwa sabon gidanta da ke.......

_Comment_
_Vote_
_Share_

*Salmerh ce* 😍
[10/2, 6:03 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_Dedicated to my fans all over media_ 😍

*Bismillahir rahmanir raheem*

_Failure is neccessary 4 any learning curve......_
_Failure makes u stronger, bolder and_ _less scared of taking risks......._

🅿 *78*

Daga wurin dinner sai aka wuce da Teemah zuwa sabon gidan ta dake Maitama.

Duk kushen mai kushe be isa ya kushe gidan Teemah ba, dolen sa sai ya bawa wannan gidan yabo ta musamman domin kuwa ko acikin ayari ba ze baka wahalar warewa ba, iya ha'duwa gidan ya ha'du matu'ka da duk wani abu da 'dan Adam yasani na more rayuwa, Ba stairs bane gidan plat house ne dan'karere, sai dai 'dakuna uku ne kacal agidan da kuma babban parlour 'daya dake tsakiya, sai babban kitchen dake daga can hanyar wani corridor da zai fitar da mutun har bayan gidan inda wani 'kayataccen lambu yake gwanin birgewa....
I can't even describ ths house 4u clearly, but u urself should imagine it, koma yaya tunanin ku ya baku just take it as if daku aka shirya komai na gidan.

Abbas da kansa ya rakata har 'dakin ta lokacin 'karfe 7:30pm ne, ko tsayawa be ba ya barta ya fito ya shiga nashi 'dakin dake nesa ka'dan da ita.

Itama binsa tayi da idanu har ya shige ciki.

Teemah kam Abbas na shigewa sai ta tura 'kofar ta ta fara cire 'kayatacciyar shigan da akayi mata na fitan dinner party 'dazu.

Sosai irin wannan dressing 'din auren suka isheta, dan kayan na takurata da nauyi, sai da ta cire gaba 'daya kayan kafin ta nutsu kuma sai alokacin ne hankalin ta yadawo jikin ta, kawai sai ta saki baki tana 'karewa ha'duwa, kyau da tsaruwan 'dakin da Yayah Abbas ya ambace shi da suna nata ne.

Tashi tayi tana juyi tare da murmushi " _wow_ " tace tare da daka tsalle dan ganin dream bed design 'din ta a'dakin kamar an shiga zuciyarta an gani, most especially colour 'din bed 'din fari ne tas sai akayi masa kwalliya da orange colour daya 'kara haska shi, colourn paint 'din entrance door dana bayi ma duk farare ne, hakama tiles 'din dake 'kasan 'dakin shima fari tas, wani shegen ha'da'd'den labile aka sanya a'dakin orange colour mai matu'kar birgewa.
Chapter 111 · 0% Book details