← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 116 OF 163

Sashe 116

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari da asubah daya tashi yau kam dabaibaye shi tayi, yajima da farkawa sai yajita ajikin sa amma beyi ko motsin kirki ba gudun karya tashe ta, 'kiraye-'kirayen sallah ne yasa shi motsawa tare da yun'kurin tashi wanda hakan yasa ta bu'de idanu.

Jin kamar tana jikin mutun yasa ta 'dago idanu da sauri ta kalleshi sai ta kuma komar da kanta 'kasa saboda ta 'dan ji nauyin hakan dayafaru, shikuwa ganin alamar kamar bata da niyyan barin jikinsa sai ya ce da ita
" _Madam 'dagani zanyi sallah ne, ko tashin ma sai na 'daga ki kafin ki tashi dan na_ _ga alama naki son jikin na musamman ne_ "

Jan jikin ta tayi ahankali ta bar jikinsa tare da juya masa baya tana 'ku'kk'uni.

Sarai yajita amma be kulata ba saboda hanzarin karya makara yin sallah ,sai da ya mi'ke kafin yace " _shine azhkar 'dinki na tashi daga shimfi'da ko?_

Shiru tayi masa aranta tayi tsuka sai ayyana irin yanda ya takurata takeyi, kullum baya barinta tayi bacci mai kyau in badan ma tana jin tsoro ba da ina zai ganta ma balle ya dame ta.
'Dan 'karamin tsaki tasake ja tare da gyara kwanciyar ta da kyau dan taji da'din yin wani baccin.

Ita kanta tasan tana da birgima dan ko Hannah nayi mata complaint akan hakan watarana wasu lokuta idan suka tashi daga bacci amma ita baya damun ta kamar yadda bata kula Hannah koda tayi mata mitan dan kuwa ita bata san ta yadda zata daina ba.

Ko da datake gida ma gadon ta babban size daddy ya sai mata da mummy tagaya masa cewa tana da birgima, bata son taji ta takura idan zata kwanta shiyasa ma take birgimar ta son ranta, duk kuwa wanda yace zai kwanta gado daya da ita sai ya dasawa zuciyar sa ha'kuri sa6anin hakan kuwa sai de kai kayi ta annabawa ka bar mata gadon.

Tunanin ta tsayawa yayi cak lokacin data jiyo muryar sa yana rero karatun littafi mai tsarki cikin dadda'dan sautin sa me sa nutsuwa ga fidda dukkan 'kal'kala da dokokin karatu, tana jin fitsari amma ta'ki tashi taje tayi dan kawai kar ta yanke jin karatun.

Har ya 'kare karatun tana nan kwance, tana ji har ya gama gaba 'daya ya mi'ke tsaye.

Tana ganin ya mi'ke agurin itama sai tayi hanzarin mi'kewa da saurin gaske ta shige bayi ko tura 'kofan ma batayi ba dan yanda fitsarin ya matsata ta ke saurin sau'ke shi.

Abbas da idanu ya rakata har ta shige bayin sannan ya jijjiga kansa afili yace " _Allah ya shirya_ " sannan ya dawo da hankalin sa ga abinda ke gaban sa.

Yau 'din bacci yakeji saboda baccin sa na daren jiya ka'dan ya samu yayi dan haka yau ko news 'din safe ma be tsaya gani ba kishingi'da.

Teemah brush kawai tayo tafito dan tafi son tayi wanka a'dakin ta saboda zatafi sakewa acan kuma ma ko dan saboda kayan dazata saka ma.

Inda yake tazo ta tsaya har bacci ma ya 'dan fara 'daukan sa, sai yaji alamun ta akusa dashi, share ta yayi ya cigaba da baccin sa sama-sama sai ya jiyo ta tana 'kiran sunan shi a hankali.

Idanun sa ya 'dan bu'de sai ya sau'ke su akanta, suna ha'da idanu sai tayi saurin fa'din " _ina_ _kwana Yayah_ "

" _Lafiya lau_ "
Yace da ita sai ya sake maida idanun sa ya rufe zaton sa ko dama gaisuwar ce.

Ganin haka sai tayi saurin sake furta " _Yayah_ !

" _wai me zan miki ne_ ? Yayi maganr a'dan tsawace.

Teemah sai ta nutsar da muryarta cikin natsuwa tace " _Yayah wayar ka zaka 'dan ban aro in 'kira su Mummy tun fa dana zo nan gidan ban 'kara_ _waya dasu ba_ "!

idanun sa still arufe yace
" _Ina taki wayar_ ?
Ya sake tambayarta sai tace " _ni bangani ba bansan ko tana gida ba_ "

Baya son dogon surutu dan haka sai ya nuna mata wayar tasa inda take.

Teemah 'dauka tayi ta koma parlour ta 'kira layin Mummy kamar yanda taga an rubuta awayar, bayan sun gaisa da ita sai ta ha'da ta da su Anty har ma da Ummah.

Inda duk suke 'kara yi mata tuni akan biyayyar aure da bin dokar sa, Ummah ce ka'dai data kar6i wayar taringa ce da ita tayi ha'kurin zama da mijin ta.

Cikin farin ciki suka 'kare wayar, bata maida masa wayar ba sai ma zaman ta data gyara zuwa kwanciya tayi pillow da hannun kujera.

Galleryn sa ta shige ta ringa bi tana kallon pictures 'dinsa dama wa'danda ba nasa ba.

Cikin haka taci karo da pic 'din wata mai kama da ita tana bacci, ganin kamar su da ita ne yasa ta tsaya 'karewa pic 'din kallo sai kuma tafara ganin kamar ita ce bawata daban ba, amma ta kasa tantance asalin gaskiyan waye ce a photon dan haka sai ta tashi tanufi wurinsa tana me 'kara kallon fuskan wayar domin tabbatar wa.

Data kasa fahimta sai kawai ta bari akan wata daban 'din ce ba ita ba, domin kuwa ita bata san lokacin da akayi pic 'din ba, amma bari ta tambaye shi.

Tun kan ta 'karasa cikin 'dakin tafara 'kiran sunan shi dolen sa ya yanke baccin ya sake bu'de idanun sa tare da fa'din " _ya akayi_ ?

Kamar an korota tace dashi
" _Yayah kalli pic 'din wata awayar ka me kama dani_ ?
Tayi maganar tana me sake kallon cikin wayar.

Beyi mamaki ba dan yasan yana da pix 'dinta daya dauka da hannun sa wanda ita kanta bata ma san da zaman su ba.

Amma duk da haka
Abbas sai yace da ita
" _ingani_ "!

Dayake yana kusan tsakiyan gadon ne shiyasa sai da ta hau saman gadon ta zauna kafin ta nuna masa.

Abbas be kar6i wayar ba sai ya 'dago kansa ya maida kan cinyar ta sannan ya kalli wayar sau 'daya sai ya maida idanun sa ya sake lumshe wa sannan yace " _kinsan ta ne_ ?

Amsa ta bashi da fa'din " _ah'ah naga tana kama dani ne shiyasa....! a ina take Yayah?_ Tana maganar tana sake kallon cikin wayar ita dai abin na bata mamaki matuka.

Ce mata yayi " _a_ _zuciya ta take_ "!

Teemah da mamaki ta kalleshi harda kwalalo idanu waje tace " _Zuciya dai Yayah_ _saboda me kuma_ ?

" _Saboda ita Zahra ta ce, farin cikina kuma burin raina ina matu'kar sonta sosai........inda kinsan yawan 'kaunar da nake mata nasan har zaki tausaya wannan mijin naki, kusan hauka nayi abaya da_ ' _kaddara ya shiga tsakanina da ita ya sanya narasa ta sai daga baya kuma tadawo min alokacin da bana zato bayan har na yanke 'kauna_ _da samun ta_ "

" _Ni kan ina so inganta Yayah plz ka kaini inganta even once_ "

Kai ya jijjiga mata alamar " _ah ah_ "

Sai t asake fa'din " _pls Yayah mana nice fa_ "!

Yace
" _Ke wa_ ?

Itama sai bashi amsa da " _Fateema Kabeer_ "

Cewa yayi
" _Yes ai nasani_ "

sai tace
" _Toh ka kaini in ganta mana kaji Yayah, Allah bazan 'kara yima birgima ba daga yau 'din nan_ "

Murmushi yayi dan kuwa maganar tata dariya taso sashi sai yace da ita " _bazan kaiki ba ai yanzu ma damuna kikayi kika hana ni bacci dan haka nima sai ranar dana ga dama zan kaiki_
"

" _i'm sorry toh bazan sake ba Allah na daina daga yau_ "
Tayi maganar harda kama kunnuwan ta duka biyu.

Abbaskuwa ya jijjiga kansa.
Da sauri sai tace " _Yayah toh sai yaushe kenan_ ?

" _Bayanzu ba akwai steps b4 aganta kinsan Zahra ta ta da bance_ "!

Teemah shiru tayi tana kallon fuskar sa dake kan cinyar ta yana murmushi har dimple 'dinsa na lotsawa.

Ita kam abin na birgeta har ma bata san lokacin da ta kai hannu wurin ba.

Tuna waye ne yasa tayi saurin 'dauke hannun ta tana sake kallon shi.

Ganin be motsa ba kuma be kulata ba yasa ta sake maida yatsan ahankali tana latsawa.

Abbas sai ya kai hannun sa ya ri'ke nata hannun dake masa yawo a fuska.

Yana cire hannun sai ya sake gyara kwanciyar sa akan cinyar tata.

Teemah sai ta tura bakin haushin ya hana ta ta6a dimple 'dinsa bayan ya'ki amincewa ya kaita wurin Zahran sa.

Zuba masa idanu tayi cike da takaici, da ta rasa abin yi sai ta fara jan 'kafar ta tare da fa'din " _''daga min kafata nima tagaji Yayah_ "

Be ce da ita ko 'kala ba sai ya maida kan nasa yayi matashi da pillow kamar yanda yake da farko tare da juya mata baya.

Teemah ma tashi tayi ta ajiye masa wayar a kan drawer sannan tafice zuwa 'dakin ta fuska babu walwala, wanka tayi cikin sanyin jiki.

Yau ko kwalliya ma batayi ba powder kawai ta shafawa fuskarta, cikin rashin kuzari take yin komai dan tun barowar ta 'dakin sa take jin 6acin rai nataso mata, ga tunanin Zahran sa daya tsaye mata a zuci, bata san me yasa take jin haushin ta ba, sai taji bata 'kaunar ta ma sam, tasan wata'kila da Zahran ce ai da bazai hanata ta6a mai fuska ba.

Yau kam bata fita ba zaman ta tayi a 'daki ko lokacin da door bell yayi 'kara ma tanaji amma ta'ki fita, Abbas ne yaje ya bud'e 'kofar wanda tun da ga jin yanayin gaisuwar su ma ka'dai yasa tagane ba Hannah bace yau takawo musu breakfast 'din.

Sai lokacin ma ta tuna ashe yau monday ne Hannah nada lectures a makaranta.

Ashe kuwa ya taho mata da tarkacen wayoyin ta da sauran kayan ta na anfani ciki kuwa harda wayar Mahmud aka ha'do.

Dama ta sanar da Mummy cewa wayar ta na gida Hannah ta taho mata da wayar idan zata zo.

Abbas da kansa ya kawo mata har 'dakin ta ko daya ga tana wani shan 'Kamshi ma sai ya share ta shima ya fice abinsa dan yasan mecece matsalar ta.
Chapter 116 · 0% Book details