← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 163

Sashe 109

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana fitowa kuwa sai ta ganshi tsaye ransa duk a6ace, a hankali ta 'karasa ta 'karasa bakin gado zata zauna, kafin ma ta zauna sai taji ya kama hannun ta kafin ta yun'kura kuwa taji yaja hannun dole tabi bayansa.

A parlour kan dinning 'dinsa na marowatan nan in jita ya ajiyeta, ganin warmers da plates harma da spoons akan table 'din sai ta 'daga kanta ta ta dube shi , " Oyah eat" yayi maganan tare da nuna mata warmers.

Abinci ne kala biyu tagani harda pepper soup 'din kayan ciki, ita kuwa duk basu mata ba sai ta bu'de ledan data gani a ajiye shima, fruits ne a ledan tana ganin haka kuwa ta kauda warmers 'din ta janyo fruits 'din ta tafara sha, dama bata jin da'din bakin ta sosai hakan yasa abu me mai ' ko sam bata sha'awar sa.

Fruits 'din taringa ci tana za6an masu 'dan tsami tana sha, haka duk ta bi ta lalata kusan rabinsu dan in dai ta ta6a taji ba tsami toh ajiyewa take yi ta 'dauki wani.

Tana cikin hakan sai ta ganshi tsaye akantsa hannun sa ri'ke da tea cup.

Sosai ta tsorata dan ta zaci ze yi mata masifan 6arnar da tayi ne amma ga mamakin ta sai ta ga ya mi'ka mata 'daya hannunsa, kar6a tayi sai taga magunguna ya 6allo mata kafin tayi wani yun'kuri sai ya mi'ka mata tea cup 'din.

'Kamshin da tea 'din keyi ne yasa ta sha'awar shan sa, aikuwa taringa sha a hankali tare da maganin da 'da'd'aya har ta shanye su.

Abbas kam beyi mamaki ba dan yasan halin ta dama da jarabar son fruits shiyasa ma ya sa aka kawo, yazaci ma zata 'danyi sha'awar peper soup 'din amma sai yaga bata ko kula shi ba.

Yana ganin ta gama da maganin ya juya ya abinsa koma bedroom.

Data ga ya juya ne sai tayi saurin dakatar dashi da fa'din " _Yayah toh tsaya ka rakani mana, na gama fah_ !
Ko kulata Abbas beyi ba yayi shigewar sa ciki.

Teemah kam bata tashi ba sai da ta gama da shayin ta dire cup 'din, tayi zaman jiran sa na mintina, 5, 10 zuwa 16 mins zaton ta ko zai fito ne, ganin shiru har yanzu sai kawai ta mi'ke itama.

'Kofan taje ta duba sai taga ya kuma sake saka lock, inda taga ya 'dau key 'dazu nan taje ta duba amma bata ga komai ba dan haka itama sai ta koma bedroom 'din ta same shi.

Ganin sa tayi kwance yayi 'da'd'daya agado, haushi yasa ta isa gabansa da sauri kamar wacce zata 'dau wani mataki amma tana isa kansa sai taja ta tsaya tace " _Yayah_ !
_Yayah dan Allah ka tashi ka rakani mana, su Ummah fah zasu_ ta _nema na, haka ma Hannah"!_

Shiru yayi tamkar beji ta ba sai tafara bubbuga 'kafafu a'kasa.

Tashi yayi ya zauna, da taga haka sai ta sake fa'din " _Nifah Yayah bacci nakeji kuma ka'ki ka rakani ni atsaye zan kwana_ _ne toh_ ?

" _in zaki iya kwana atsayen bismillah ai ban hanaki ba_ "

Hawaye tafara tana 'ku'k'kuni 'kasa-'kasa.

" _banji ba_ " yace da ita yana kallon ta.

Kauda kai tayi gefe tace " _Allah Ummah fah da su Anty zasuyi ta nemana_ "

'Dan 'karamin tsaki yaja dan harga Allah rigimartan yafara isan shi sai ya fara
'Ko'karin sake kwanciya tare da fa'din
" _Idan bazaki kwanta ba ki kama hanya kiyi tafiyar ki dan ni babu inda zani_ "

Yana gama fa'din haka ya koma yayi kwanciyar sa tare da juya mata baya.

Tsayuwan mintina sun kai ishirin tayi ahaka sannan a hankali ta shiga bayi, wani sabon brush data gani ba'a bu'de ba ta 'dauka tayi amfani dashi sannan ta fito.

'Dayan 6angaren gadon ta kwanta nesa dashi sosai tawani 'dosa na jikin ta kamar ace fita ta zura da gudu.

Abbas kuwa be kula ta ba ko da yaga ta kwanta 'din ma sai da ya bata tazarar kusan rabin hour kafin ya tashi bayan yaji ta sauke ajiyan zuciya .

Kakkashe dukkan hasken yayi sannan ya dawo gaban gadon, ganin har ta fara birgima yasa shi fa'din " _fitinanniya kawai_ "

Space sosai yabada atsakanin su sannan ya kwanta.

👎🏻
*HA'KURIN NAN DAI DANA SANKU DASHI SHI NAKE SO KU 'KARA YIMIN, NASAN KUN SHA JIRAN GANIN POSTING AMMA KUKA GA SHIRU, NI KAINA KUNA RAINA....BA NUFI NA IN BA'KANTA MUKU BA KOKA'DAN, PLZ AYIMIN UZURI SABODA ALLAH*

_Comment_
_Vote_
_Share_

*Salmerhn ku ce* 😍
[10/2, 6:03 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

*Bismillahir rahmanir raheem*

_If couples who ar in love ar called *LOVE BIRDS,* then couples who always argue should be called *ANGRY BIRDS*..........._

🅿 *77*

Abbas kam ko daya kwanta 'din ma bacci kasa 'daukan sa yayi har kusan 'karfe 12:00 na dare.

Tashi yai yayi alwala ya dinga jero nafilfili tare da addu'o'i sosai sannan ya kwanta.

'Bangaren Teemah kuwa bacci ya mata da'di sosai har bata san lokacin da ta gangaro jikin captain ta shige jikinsa ba.

Har alokacin kuwa baccin be 'dauke shi ba, ganin ta dawo jikinsa ne yasa shi sakin ajiyan zuciya, kanta akan hannun sa ta 'dora, sai hakan ya bashi dama yake sha'kan dadda'dan 'kamshin da jikin ta ke fitarwa da kuma gashinta, a haka bacci yayi awon gaba dasu gaba 'daya.

Da asuba Abbas ne ya rigata farkawa ganin bata motsa ba sai ya sau'kar da kanta dake kan hannun sa ahankali ya mayar mata kan 'karamin sweet design pillow dake kan gadon madadin hannun nasa sannan ya tashi.

Alwala yayi ya wuche masallaci domin gabatar da sallar asubah.

'Karfe biyar da rabi ( 5:30am) Teemah ma ta farka.
A hankali ta bude idanun ta sai taga ita 'daya ce a 'dakin, tashi tayi da sauri ta nufi bayi ta 'dan kintsa kanta a gaggauce sannan ta fito da sauri ko mayafi bata tsaya nema ba ta fice abinta.

Allah ya taimake ta kuwa daya fita abu'de ya bar 'kofan hakan sai ya bata daman fita cikin sau'ki.

Har a lokacin gari be gama yin haske ba amma a hakan da duru-duru ta nufi 'dakin su.

Hannah na kan sallaya bayan ta idar da sallan asubah sai taji an turo kofa an shigo, waigawa tayi sai taci karo da ita
kamar an koro ta ta shigo kanta ko 'dan kwali ma babu.

Tashi Hannah tayi da sauri ta tareta tana murmushi tare da zaro idanu tace " _Ah'ah amaryar Yayah ya haka da sassafen nan kuma kamar an koro ki_?

Teemah ko kula Hannah batayi ba ta wuce kan gado ta kwanta tare da jan blanket ta rufe jikin ta dashi, tana shirin juya wa Hannah baya sai Hannah ta dakatar da ita da fa'din " _Haba Amarya har da nine a fa'dan amarcin_ ?

Sai yanzu Teemah ta bu'di baki tace
" _Hannah plz ni ki 'kyale ni, Allah bansan damuwa ki barni nayi bacci na, ina kam jiya 'kin_ _zuwa nema na kika yi dagangan kika barni na kwana acan bayan sarai kin san halin Yayah da masifa ba rakoni zaiyi ba_ "!

" _Yanzu dana barki kika kwana acan din me yasame ki? Baga shi kin 'debo lada ba, ke dama zaku tafi tare da shi toh miye abin fushi dan kin kwana 'daya awurin sa_ ?
Hannah tace tana kallon ta.

"Bazaki gane ba ne ai Hannah dan ba ke bace"

" _oh o o'oh barni da Bilalu na ni kam kuje can ku 'karata keda wannan dodon mijin naki_ "!
Hannah tayi maganar tana kokarin tashi tsaye.

" _ai naje amma Yayah ya hana ni ganinki sai ma ya wani ce dani bacci kike yi irin ke ga me mijin nan.....nima ai barina kika_ _yi anan 'din na kwana ni ka'dai bayan kinsan su Rauda ba kwana zasu yi anan ba_ _amma kika tafi, in hakane nima nayi fushin mana_ "

'Kasa-'kasa tace
" _Sai kije ai ki gaya masa wannan kuma, dan nima tsintar kaina kawai_ _nayi acan_ "

Juyawa Hannah tayi tana wa Teemahn murmushi irin na tura haushi tace " _may be sace ki yayi babu wanda ya sani_ !"

" _Mtheww_ "
Teemah taja tsaki tare da gyara kwanciyar ta da kyau.

'Karfe shida cif Abbas ya dawo sai ya tarar bata nan, amma be wani damu ba dan dama yasan matu'kar tasan cewa 'kofa abu'de yake toh bazata zauna a dakin ba.

Kai ya jijjiga kawai lokacin da ya ga yanda ta tafi ta bar gadon batare da ko gyara shi tayi ba, yasan duk cikin saurin barin 'dakin ne yasa ko tsayawa ta gyaran batayi ba.
" _Allah ya shirya_ "
Yace a zuciyar sa, da kansa ya kintsa akin sannan ya koma parlour ya 'dau ko wayar sa da tun jiya ya barta anan.

Ogansa ya 'kira suka gaisa inda yayi masa murna tare da sanya masa albarka acikin auren da yayi.

Ya 'kara da fa'din be samu ya halacci bikin ba lokacin yaje duba yaron sa ba lafiya ne shiyasa amma yayi ha'kuri. Godiya Abbas yayi masa dan ya tura masa sa'ko musamman yasa aka kawo mishi.
bayan haka ne suka yanke 'kiran.

Daddy ya kuma 'kira suka gaisa shima yayi musu ban gajiya tare da fatan alkhairi wa auren da suka je 'daurawa.

Yana shirin ajiye wayar sai ga 'kiran Saleem kamar yasan yana kusa waya a dai dai lokacin, domin tun jiya yake 'kira amma Abbas 'din be 'dagawa.

Yanzun kuwa 'dauka yayi ya kai kunnan sa tare da yin shiru dan yasan meze biyo baya, ai kuwa Saleem 'din cewa yayi " _Girman ka ne yalla6ai ,gaskiya najinjinawa zumuncin ka_ "

Shi kansa Abbas yasan be kyauta ba amma sai ya basar yace dashi
" _Ya akayi ne Saleem ka 6uya fah?_
Ya fa'da a wani tsare.
Chapter 109 · 0% Book details