Sashe 13
Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
masoyan_ _CAPTAIN ABBAS. Kusani ina yinku irin sosai sosai d'innan,Nagode da_ _irin kyawawan_ _addu'o'inku_ _gareni.Nima ina_ _sonku sosai_ 😍
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
Free your heart from any hatred. Free your mind from any worries. Live simply. Give more. Expect less.
🅿 *13*
Da malaman suka ji ya fad'i haka sai suka ce toh shikenan daman hakkin addini ne kuma dan gudun siga hakki ake son sauk'e shi,amma tunda yace haka shikenan,Allah ya k'ara musu hak'urin rashin dasu kayi,amma duk da haka sai sunji daga bakin manyansa tukunna,wasu daga cikin y'an uwan baban haushi sosai sukaji dan aganinsu Yusuf bak'aramin bak'in ciki yayi musu ba,amma da sukaji za'a tambayi manyansa sai suka d'an ji dama-dama dan sun zaci za'a samu sa6anin harshe ne.
Sai dai basu yi sa'a ba,dan da aka tambayi ummahn suma cewa tayi
" _a'a yanda idonta yaga jinin Baban ya zuban nan ko da sun kar6i kud'in gani zasuyi kamar jinin baban suka fansar,tsautsayi da k'addara ai abokan tafiyar dukkan wani halitta ne,babu wanda ya isa ya gujewa k'addararsa,Allah ya riga da ya rubuta inda ajalinsa yake kenan dan haka su basu da wani abin fad'a fatansu kawai Allah yah kyautata makwancin Baban"
Ummah tana hawaye take wannan maganar,kusan kowa dake zaune agun sai da ya share hawaye,duk da zuwa yanzun abin yad'an bar zuk'atansu,sun riga da sun dangana tsakaninsu da Baban yamzu addu'a ce kawai.
"Allahu akbar",
"Allahu akbar"
"Allahu akbar"
Babban malamin dake zaune agun ne yafad'i hakan tare da jijjiga kansa,d'ago wa yayi ya kalle su gaba d'aya sannan yaci gaba da cewa
"Hak'ika wannan kad'ai baiwa ce da Allah ya riga ya halicci ahalin wannan gidan dashi,kalamanku su suka bayyana hakan,ga dukkan alamu ba wani k'arfi ne daku ba amma wannan furucin naku yah tabbatar mana da cewa wadatar zuci abokiyar tafiyar ku ne,Allah kad'ai kuka dogara dashi,Hak'ik'a agurin Allah ku masu arzik'i ne da yardarsa,Allah ubangiji ya saka muku da mafificin alkhairi ya kyautata rayuwarku gaba d'aya daga yanzu har yaumul sa'a.
"Ameen-Ameen"!
sauran dake gurin suka amsa masa dashi,amma kowa jikinsa ya matuk'ar yin sanyi.
Sake kallon Ummah yayi dake faman goge hawaye tun d'azu,sannan yace
"Kuyi hak'uri insha Allahu mutuwar malam hutu ce agare shi muna mishi fatan alkhairi insha Allahu,malam mutum ne da kowa yaji wannan mutuwar tashi ta matuk'ar ta6a zuk'ata da yawan gaske,amma dukkan mu yazama mana dolene muyi hak'uri,addu'a itace gatansa ayanzu"
Babban malamin ne yasake juyowa ga ragowar ahalin Baba yasake tambayarsu,suma da wuri suka amince sai bakinsu yazama d'aya dukkansu.
Da haka taron yawatse amma har aran Alhaji Muhammad ji yayi ya kasa hak'uri da wannan lamari ji yake bazai iyah kyalesu a haka ba
amma bai yi magana awurin ba yadai bar abinsa aransa ne kawai.
Dangin Baba kuwa haushinsu k'aruwa yayi akan nada, ji suka yi kamar su rufe ummah da duka lokacin da ta ke nata bayanin,koda aka zaga yo kansu da tambayar kuwa suma dan dolensu suka amince badan ransu yasoba,dan de kar aga zak'ewa da zilamar su ne,shiyasa basu canja baki ba,tunda bau wanda yasan meke acin ran su sai kowa ya yabawa wannan zu'ri'a ta mariga yi masu sanin ya kamata da girmama k'addarsu, inka d'auke mutune biyu dasuka kasance su d'in k'anne ne ga Baba,Mal.Hadi da mal.kallah sune kad'ai suka yi maganar datake har cikin zuciyarsu ne badan komai ba sai dan saboda Allah kawai, amma saura daga ciki duk bada son ransu suka amince ba,dansu aganinsu a irin yanayin talaucin da suke ciki kud'in ba k'aramin taimaka musu zaiyi ba,basu sani ba ashe irin kud'in nan baya kawar da buk'atar mutum dan tafiyah yake kamar ana hure shi,daga k'arshe ma karasa ya akayi ne ma yak'are gaba d'aya,inkayi wasa da tunani kawai zai barka,amma bansani ba kodan basuga yadda k'arshen d'an uwan nasu yakasance bane shiyasa tsoron rayuwar bata shigesu ba,domin kafin su iso har an sada baba da makwancinsa na har abada.
Mal.kallah kanin marigayi Baba ne da suka kasance uwa d'aya su kad'ai mahaifiyar su ta haifah inda tarasu tun awajen haihuwar Mal.Hadi haka yataso baisan mahaifiyarsa ba da dad'i da wuyah haka de ya girma ahannun kishiyoyin uwa shida wansa,kuma sun kasance y'a'ya k'anana daga cikin y'ay'ayn da mahaifinsu ya haifa,dan mahifiyarsu itace ta k'arshe acikin matan mahaifin nasu while mal.Hadi kuma uba suke d'aya.
Mahaifinsu ma masha Allah,dan ya mori duniya sosai,shekarar sa baifi uku da rasuwa ba yanzuh,tsufa yayi jigib cikin ikon _buwayi_ har baya gane mutane,kafin Allah ya kar6i abunsa.
*****
Alhaji Muh'd wanda yakad'e baban kenan kayan abinci yaci kasu dashi sosai iya iyawarshi,sannan yaci gaba da zuwa akai akai yana dubasu,kuma bai fasa yin azumin da shari'ah ta d'ora kansa ba.
Dangin mahaifin nasu kuwa tun daga ranar suka fita daga harkar su,basu k'ara waiwayarsu ba,kowa gudun d'awainiyah yake yi saboda yanzu sun zama marayu,mahaifiyarsu kuwa dama y'an cirani ne,ba'a san inda danginta suke ba tunda ta auri baba shikenan rabuwarsu da ahalinta.So basu san kowa daga 6angarenata ba.
Haka har Lokacin tafiyar Yusuf tayi,yatafi service d'insa,a Taraba state batare da wani fargaba ba,dan yanzu Alhamdulillah basu da matsalar abinci,domin sosai suke samun tallafi daga al'umma dan wani lokaci mutane basa tuna su taimaka maka koda sun san baka da k'arfi har sai sunga ka kwanta dama,alokacin ne zakaga zuciyar taimakon ta motsa, inkayi sa'a zuri'ar ka bazata wahala ba ko bayan baka,sannan ga Alhaji muhammad ma bai ta6a mantawa dasu ba,yanayin iyah k'ok'arinsa akansu wani lokaci har suna tausaya masa,na ganin kaddarar mutuwar baba tasa wani nauyi ya hau kansa batare da ya shiryawa hakan ba
sannan sunyi-sunyi dashi akan yad'an huta da d'awainiyar sam yak'i,sai dai yace musu shi saboda Allah yakeyi badan komai ba.
Kafin yah gama azuminsa rama yayi sosai kamar wanda yayi wata ka'aramar jinya,Addu'a kawai kawai suke binsa dashi dan itace kad'ai sakayyar da suke ganin zasu iyah masa,hak'kik'a yacika mutum managarci,ba kowa keda irin halinsa ba acikin mutanen mu na yanzu.
Sau kusan biyar yusuf yazo ganin gida acikin shekara d'ayan da ya yi a taraban.
Yana dawowa kuwa Alhaji muhammad ya bashi jari,akan ya fara kasuwancin kansa da kansa,da kyar ya kar6i kud'in dan gani yake kamar sun d'orawa Alhajin wani nauyi ne na daban akan k'addarar da kowa bai isa ya tsallake ta ba,amma Alhajin yace sam dole sai ya kar6a,da yaga Alhajin yafisa baki sai yace toh yah rage yawan kud'in nan ma Alhajin yace shi abinda yayi niyyar bayarwa kenan so baze rage ko kada'n ba,haka dan dolensa ya kar6a,godiya kuwa shi kansa sai da ya rasa adadin daya ambace su,daga k'arshe ma Alhajin barin d'akin yayi ya barsa shi kad'ai aciki rik'e da kud'i,yana hawaye ya fito daga d'akin shima,karo suka ci. da y'ar Alhajin tana k'ok'arin shigowa itama,binsa tayi da kallo har ya fice agidan,dan take taji ya kwanta mata.
Shikenan tun daga ranar ta nace masa mahaifiyar ta ma ta goye mata baya,har se da taga sun sami had'in kansa kafin nan ta sami salama.
Ga Alhaji muhammad kuwa bawai ba yason auren bane a'a shima yana matuk'ar farin ciki da kasancewar yusuf d'in sirkinsa dan ya yadda da tarbiyarsa sosai,
matsalar kawai maganan mutane yake gudu,kar wasu suce shi ya lik'a masa y'ar sa adole dan yaga basu da k'arfi,ko kuma dan basu da wani akansu yanzu.
Amma da malamin daya wakilci auran ya fahimtar da shi cewa shi aure had'i ne na Allah,shiyake tsara abunsa aduk yanayin da yaso a kuma duk inda yaga dama,hakade malamin yata nusar dashi muhimmancin da hakan ke dashi, take kuwa shima yayi na'am da zancen,aka yi bikin lafiya aka kawo amaryar gidansu da suke zaune bayan gidan yasha kwaskwarima sosai.
Kuma Alhajin ne ya d'au nawin komai na bikin danma kar yusuf ya ta6a wani abu daga cikin dukiyar da ya bashin sai ya kar6e ya ajiye agunsa sai bayan bikin ya maida masa da abinsa.
Ganin yawan k'ud'in ne yasa yusuf yaje ga mahaifiyarsa neman shawarar sana'ar data dace yayi,cemasa tayi yayi kowanne ma inde yaga ta kwanta masa bata da matsala dashi matuk'ar yasan bazai sirka dukiyarsa data haramun ba toh yaje ya za6i duk sana'ar data mishi yayi.
Godiyah yayi mata tareda alkawarin insha Allahu zai tsaya akan iyaka halak d'insa ne bazai wuce hakan ba izinin Allahu.
Da addu'ar samun sa'a tabishi.
Rasa yanda zai yi da kud'in yai kwata kwata daga k'arshe sai ya k'ira abokinsa da suka yi makaranta tare mai suna kabiru dan yaga kamar su d'in ma harkar kasuwanci mahaifinsa yake yi,so aganinsa zai fi samun clue daga bakinsa.
Abokin nasa kuwa d'an albarka sai ya had'asa da mahaifinsa ya fara juya masa kud'in,watansu shida tare sai mahaifin kabirun ya ware ma yusuf iya tashi dukiyar tare kuma da ribar da suka samu akai,daganan ya k'ara ha d'asa da manyan y'an kasuwa da suke harka tare yace ya cigaba da harkokinsa shikad'ai dan sha'anin dukiyah wuyah ne da ita.
Yin hakan baifi da sati biyu ba Allah ya yiwa mahaifin kabirun rasuwa,Sosai mutuwar ta ta6a su gaba d'aya satin yusuf guda cif a Gombe wurin ta'a ziyar mahaifin kabirun sannan ya dawo gida cike da alhini,dan bazai ta6a manta karamcin mutumin ba,sai fatan Allah ya kai haske kabarinsa.
Ana raba musu gado kabiru ya taho kano yasamu yusuf suka yi shawarar yin kasuwanci atare,kabiru yanada k'anne biyu mace da namiji Sunan macen Zahra kuma itace ka'rama sai namijin mai suna Hassan 'yan biyu ne shi amma d'ayan bai rayuba shekara ukune tsakaninsu da Hassan d'in,ko lokacin da aka raba musu gado ma kowa karbar nashi yayi danshi hassan tun shekarar data gabata yayi aurensa,auren gida Hassan d'in yayi shikuma kabiru ya tsaya yin karatu,Zahra ma tana gama secondary Mahaifinta ya aurar da ita rana d'aya da Hassan,alokacin da mahaifinta ya rasu ma ciki ne da ita.
Sun fara kasuwanci lafiya lau kuma suna ganin haske aciki,Kwatsam sai suka wayi gari babu mahaifiyarsu Allah ya kar6i abinsa,tun daga lokacin kuma sai khadijan tashiga wani hali dan har alokacin ma bata k'are secondary ba,shekara kusan goma sha d'aya ne tsakaninta da yayanta Yusuf.