Sashe 86
Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tunawa yayi da wani toshon cable 'din daya daina amfani dashi da sauri ya tashi ya bu'de drawern yajanyo wayar ya fara nanna'de ta ransa amatu'kar 6ace kana ganinsa zaka san an ta6o shi yau 'din dan Mahmud ba haka yake ba.
Teemah ce taje dagudu ta ri'ke masa hannu dan ita tuni ma harta fara kuka saboda bata ta6a ganin tsantsan 6acin rai azahiri na Mahmud 'din ba irin yau .
" _Yayah please karka daketa kaji! dan Allah.... Yayah kayi ha'kuri._ "
ta yi maganar da muryar kuka.
Mahmud kuwa ko kulata ma be yi ba dan shi ka'dai yasan abinda yakeji azuciyarsa game da kalaman Munniran be ta6a tunanin haukarta har ya ha'da da cin zarafi da shiga hakkin wani ba.
Yana isa inda take ya sau'ke mata cable 'din abayanta, yayi niyyan yamata dukan tsiya ne na fitan hankali yanda gaba ko ganinsa tayi ahanya bazata tunkari gabansa ba ballantana hartayi tunanin cutar dashi.
Amma yana 'daga cable 'din akaro na biyu Fateema tazo dagudu ta ru'kunkume shi ta baya tana kukan itama, idan baka sani ba zakayi zaton ko dukkan su biyu yake duka.
" _Yayah........please kabari, karka daketa dan Allah Yayah kayi_ _ha'kuri.........kaifa musulmi kar kabiye sharrin zuciya_ _Yayah please kabarta ka yafe mata kaji....._
Cikin sanyin jiki ya sau'kar da hannunsa daga barin dukan nata.
Munnira kuwa gaba 'daya tabi ta rikice dana sanin zuwan ta office 'dinsa ma takeyi ayanzun, domin tunda take arayuwarta, ba'a ta6a marinta bama balle har takai ga duka da cable.
Kuka takeyi kamar ranta zai fita tana so ta fice a office 'din amma babu dama dan Mahmud sai da yarufe da lock kafin ya 'karaso ciki.
Dawo da Fateemahn yayi ta gabansa yana bubbuga bayanta alamar rarrashi yace " _yi shiru ya isa haka Fateenah, bakya ganin cutar da rayuwarmu datayi_ _ne, Fateemah wannan da kike gani babbar shai'daniya ce_ _ki bari in koya mata_ _hankali_ "
Kai Teemah ta jijjiga masa alamar " _ah ' ah_ "
Sai yace
" _okay......on one condition, zan barta amma sai ta fa'damin komai_ _data sani game da munafurcin da suka 'kulla gaba 'daya in_ _bahaka ba wallahi ba zan 'kyaleta ba_ "
Munnira kam tun kafin ya rufe bakinsa cikin sheshshka tace
" _wallahi Mahmud zan gaya maka gaba 'daya nayi al'kawari_ "
Idon su gaba 'daya suka maida shi kanta inda taci gaba da basu labari gaba 'daya.
Asirin datayiwa Teemah dashi kanshi Mahmud 'din sai da ta fa'da tace " _manufar hakan kuma shine wanzar da fitina da rashin aminta da junansu wanda_ _hakan ne zai iya yin sanadin rabuwarsu cikin sau'ki_ .Tace kuma Anty ma tasan da maganar dan ita ta'kara goya mata baya kuma itace ta ke jagorantar 'kawarta Anty Chiddy domin samun kan Fateema wanda hakan ma wani shirin ne daban a6oye.
Kasa jurewa Mahmud yayi saida ya zauna tsaban haushi da takaici.
Zaman ma sai ya gagare shi yasake mi'kewa.
Yana huci yace
" _Ai kuwa kinyi kuskure, Munnira munafurcin ki beyi tasiri ba koka'dan, domin Fateema bata_ _san ma tana da wannan_ _matsalarba balle har ta 'daga min hankali akai, har yaushe......Munnira_ _har yaushe zaki tsaya 6ata lokacinki akan yarinya_ ' _karama irin wannan, ko angaya miki ma ko na rabu da Fateema zan aureki ne?, wallahi_ _ko babu mata aduniya Munnira bazan ta6a auranki ba........._
_Kuma aurena da kike gani ni da Fateema auren zobe ne in bakisani ba ma yau ki sani, Allah_ _ne ya ha'da kuma shika'dai zai iya rabashi ba de ke ba kam Munnira_ ".
Yana kaiwa nan yayi Wulli da wayar ya ja hannunta zuwa gabansa wanda hakan ya tilasta mata tashi tsaye tare da fasa wani 'kara, zaton ta ko wani dukan ze kuma mata.
Teemah ma da sauri tace
" _Yayah please........_
Juyawa yayi ya kalli Teema sai ya sake kallon Munniran, fasa fa'dan abinda yayi niyya yayi sai kawai yaja hannunta suka nufi 'kofar fita.
Be damu da takalmanta da mayafinta dasuke jefe a'kasan office 'din ba haka yajata suka ratsa cikin Companyn har zuwa inda yayi parking, yana zuwa yaturata abaya yarufe sannan ya zagayo ya shiga driver seat.
Teemah ce cikin sauri ta tattaro sauran tarkacen Munniran ta ri'ko ahannunta da gudu tabiyo bayansa amma kafin ta iso har yaja motar da 'karfi 'kuran bayan motar kawai ta tarar.
Zuwa lokacin kuwa hankalin dayawa daga cikin ma'aikatan yadawo kansu dan ko lokacin daya bar cikin companyn ma wasu nata mamakin dalilin daya sashi hakan.
Umar ne da shigowansa kenan ya 'dan fita waje yasamo Teemahn tsaye hannunta rike da wasu kaya.
Mamakin dalilin hakan yayi sai yanemi ji daga bakinta.
Amma bata sanar dashi ba sai ma ro'konsa data fara yi akan ya taimaka yakaita gida wata'kila Mahmud can yanufa da Munnira.
Tana cikin ro'kon Umar sai ta hango Abbas na 'kokarin giftasu, gaba 'daya sai hankalinta ya koma gurinsa.
Hatta Umar sai da ya juya ya kalloshi dan yanda hankalin Fateemah ya 'dauku izuwa kallonshi dole tasa Umar ma yabi gurin da kallo.
Take ya gane shi domin sun ha'du wajen 'daurin auren Mahmud a damaturu duk da be da'de tare da su ba amma hakan be sa Umar ya manta da fuskarsa ba.
" _Yah..... Abbas_ !
Ta fa'di sunansa da tunanin shi 'din ne ko kuwa wani ne me kama dashi.
Cak kuwa ya tsaya duk da be gama tantance shine ake nufi da 'kiran ba ko waninsa, amma muryarta ba ze ta6a mantawa ba ko a ina yaji ta.
Hakan ne kuma yashi waigowa ahankali sai caraf idanunsu ya sar'ke cikin na juna.
Teemah kam kasa juran hakan tayi dan haka sai ta meda idanun nata 'kasa ta taho ahankali zuwa inda yake kayan Munnira rungume a 'kirjinta.
Mamaki Abbas yakeyi ganin Fateemah a harabar companing su Mahmud kuma batare dashi ba.
Tana isa inda yake sai taji idanunta na 'ko'karin tsatstsafo da ruwan hawaye ahankali tasake 'daga idanu takalleshi amma kwarjininsa ya hanata sakewa.
" wai ke faruwa ne? Ina Mahmud 'din?
Ya tambayeta cikin sauri.
Daidai nan Umar ya iso ya mi'ka masa hannu suka gaisa sai ya sanar dashi cewa yana zaton Mahmud 'din be jima da fita ba saboda wata 'yar matsala dake faruwa yace shima yanzu yake so ya sau'ke ta agida.
Tare suka koma motan dukkan su inda Teemah tashiga baya sukuma Abbas da Umar na gaba.
Rintse idanu yayi yana sake recalling mafarkinsa wato dagaske Fateema na bu'katan taimako, in bahaka ba meyasa yaganta haka tana kuka?
Amma ba ze iya bu'dan baki ya tambayeta ba.
Ganin da Umar yayi kamar abin ya sar'ke zuxiyar Abbas ne yasa shi sake tambayarta abinda ke faruwa.
Zuciyarta na tsananin bugu ga damuwa da suke son suyi wa zuciyarta yawa amma haka ta daure tayi musu bayani atai'kace dan muryarta shaking yakeyi sam bazata iya dogon magana ba ahalin yanzun.
Abbas jiyayi tamkar zuciyarsa zata fito waje tsabar haushi ba'kin ciki dan Teemah batun Anty Chiddy ka'dai ta sanar dasu bazata iya fa'da musu 'dayan maganar ba.
Jikin Abbas har rawa yake yi saboda yanda ransa ya 6aci amma ko 'kala be ce ba shi de yayi shiru Allah ne ka'dai yasan yanda yakeji azuciyarsa wato Mahmud zuwa yayi ya watsar da ita har wasu banzayen 'yan iska suka samu daman shiga rayuwarta da haukarsu.
Jiyake da zaiga mutanen awannan lokacin dashi ka'dai yasan abinda ze musu.
Da wannan tunanin suka isa gidan Mahmud amma baya nan, Abbas ne yayita gwada 'kiransa amma kusan missed call uku yamasa be 'daga ba.
Hakan kuwa ya 'kara tunzira zuciyar Abbas aciki yake jin ciwo da 'kunan abin.
Shiru Umar yayi duk da be gama fahimtar abinda yafaru duka ba amma ayanayin labarin da Fateemah ta basu ya fahimci cewa ran Mahmud yagama 6aci ayau 'din. Tunanin inda zai samu Mahmud yake a dai-dai wannan lokacin, ina yanufa da yarinyar da Fateemah tace yafita da ita.
*****
Mahmud kuwa be zame ko'ina da Munnira ba sai gidan Anty, yana shiga kuwa ya hangota tana shirin shiga mota itama ga dukkan alamu fita zata yi.
Ko gama parking beyiba ya fita tare da jawo hannun Munniran yakawo ta gaban Anty da tun shigowar motan ta tsaya saroro tana ganin ikon Allah dan ayanayin daya shigo ka'dai ma sai da mamaki ya kamata balle data ga Munnira ahannunsa wujuga wujiga ai shikenan tunaninta ya tsaya cak.
Yana isowa yatura Munniran kamar kayan wanki ta fa'di agaban Anty tana kukan fitan rai.
Azuciye yace
" _saurari yarinyar nan Anty kiji abinda take fa'da, Anty bana fatan abinda_ _naji ya kasance gaskiya domin hankalina baze iya 'dauka ba._
_Anty wai dake za'a ha'du acutar dani da rayuwata, Anty idan ma kina_ _gadaran 'danki ne ni toh ita Fateemah fa?,miye yarinyar nan ta tsare miki_ _aduniyan nan da har zaki nemi sata a mummunan harka irin ma'digo_ , _Anty_ _bakya tunanin alhakin Allah ne_ ?,
_Kun hana yarinya rayuwa me kyau agidan aurenta kun hanata sakewa, kun sanya tsoro yazama abokin tafiyarta duk meyasa hakan Anty dan kawai kin tsaneta, wallahi ni cewa kikayi insake ta takoma wurin iyayenta daya fimin da wannan alhakin!!_
_Itan fa jinina_ _ce......Fateema_ _dangina ce da ko ba aure atsakanin mu ni me iya ri'keta ne_ _awajena, banda haka ma Anty_
_me kike so ingayawa mahallici na idan ya tsaida ni akan amanarta_ _dana kar6o a hannun iyayenta ?_ _Anty_
_bakya tunanin ranar da Allah ze tuhume mu gaba 'daya_ .........
" _Ya isa haka ni Mahmud_ ......
Anty ta daka masa tsawa tare da 'dago Munnira ta jingina ta da jikinta.
Taci gaba da fa'din