← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 163

Sashe 10

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Teemah da batasan da shigowarsa ba,tafito kenan daga d'akin mummyn taganshi zaune,
Turus taja ta tsaya dan jitayi zuciyarta ta tsinke daganin nasa,dayake baya ya juya mata,so bai ga fitowar tata ba ,mummy ce dai ta lura da ita,kallonta tayi suka had'a idanu take sai tayi k'asa da kanta kamar mara gaskiya.

Dayake kuma daman da rashin gaskiyar,sai ta taho ahankali izuwa inda suke d'in.

"Ina kwana yayah "

Sai da ya d'an juya kansa sannan ya kalleta, dan bata gama k'arasowa daf dasu ba ta masa gaisuwar,

"Lafiya"ya amsa mata dashi,sannan ya dawo da kansa saiti suka ci gaba da maganar su da mummy.

Tana ganin haka ita kuwa tafice taje dakinta ta d'auko school bag d'inta sannan ta dawo zata wuce, gani tayi yanzun baya zaune awajen, mummy kad'ai ne azaune,

"Na tafi mummy"
Tafad'a sanda take gyara zaman jakarta akan kafad'arta.

"Adawo lafiyah" kawai mummyn tace mata.

Harta fita sai kuma tadawo tasake dawowa ta tsaya daga bakin k'ofa
tace
"Mummy mai na ya k'are fah"

D'aga kai mummyn tayi ta kalleta batare da magana ba.

Teemah kuwa ta juya tafita abinta don tasan ai mummyn taji me tace d'in.

Tana isa wajen motar da za akaitan aciki taganshi a mazaunin driver.
kasancewar Habibu ne yakai daddy maiduguri inda zai hau jirgi, da kyar ma in sun isa yanzu ballantana ayi zancen dawowa.

Turus tayi taja ta tsaya tana k'are masa kallo.

kusan minti biyu shima dagangan yak'i yi mata magana,sai da yaga bata da niyyan shiga ne sannan yace mata

"U ar just wasting ur time,let me tell you,ni inada abinyi"

Bai kalli inda take ba yayi maganar hannunsa d'aya kuma na kan stairy.

Ahankali ta ta ko tazo jikin motar,tana k'ok'arin bud'ewa tashiga ta tsinkayo muryarsa yana fad'in
"Habibu kika gani ne acikin motar?

Sarai tasan me yake nufi amma sai tayi kamar bataji sa ba harta bud'e k'ofar tana k'ok'arin shiga sai taji wani uban tsawan da ysa take ta firgita ta,balle daman muryarsa razana ta take.

Dawani irin b'acin rai yayi maganar "bana son rainin hankali fateema,sa' anki ne ni?

Ai tana jin muryar tasa jiki na rawa ta rufo k'ofar ta dawo gefensa tashiga ta zauna.

Wani guntun tsaki ya sake sannan yaja motar,wani uban horn yadan na tun kan su isa bakin get d'in,da gudu mai gadi yaje ya bud'e musu suka fice agidan.

Bai sarara da gudun ba har saida ya dangana da babban titi kafin nan,kasantuwar bai san inda makarantar ta ke ba,kallon ta kawai yayi sai yaji tace "NANA AISHA"

Aransa yayi murmushi dan yanda yaga tsoro kwance akan fuskarta"ga shegen tsoro ga rashin kunya,afili kuwa ko kad'an babu annuri akan fuskar tasa.

Daya ke yasan gurin sai bai k'ara ko kallon inda take ba ballantana magana har suka isa,yana yin parking ta fita da sauri tare da rufe k'ofar da iyah k'arfinta kai kace yau ta fara shiga mota,shigewa tayi ciki abinta batare da tasake ko waiwaye ba,bayanta yabi da kallo yana k'ara mamakin duk ina wannan yarinyar ta koyi rashin ji haka,komai na rashin ji salo-salo ta iya su,inbadan mummy tasani ba ma ke kinsa ne na kawo ki makaranta
(Kunji yamanta da shekarun baya😅)

Jan motar yayi ya shiga cikin gari,bai dawo ba har sai kusan 12na rana.

12:56pm
Mummy ce tsaye ajikin mota abakin makarantarsu Teemah tana jiran tashinsu,dayake cewa Abbas tayi ya kaita idan ta tashi zata bi ta 'akota tunda ita zata yi,shiyasa bai koma d'auko tan ba,hakan ma mummy tana ganin kamar ta takurashi amma bata fad'a masa yaji ba aranta ne take jin hakan.

Abbas kuwa baisan dan hakane mummyn tace masa zata bi tad'auko tan ba,daya sani kuwa bazai barta ita taje d'in ba.

Bata wani dad'e agurin ba aka tashe su,tana ganin hakan sai ta koma cikin motar ta zauna saboda hayaniyar yara da kuma k'ura,kuma atunaninta ai Teemah tasan motar gidansu inta ganta ai zata ganeta.

Teemah ma bata san cewa mummy ce tazo tafiyah da ita da ba,bata fito da wuri ba sai da kusan rabin d'aliban suka wuce kafin ta fito, kuma koda ta fito data fito d'inma sai ta wani d'auke kanta daga ganin motar,dan ta zaci Abbas ne yazo yanzun
ma.

Bakin titi ta nufa da niyyan taran adaidaita amma cikin rashin sa'a sai bata samu ba,don gaba d'aya d'alibai sun tashi yanzu,kuma a irin wannan lokacin samun abin hawa wahala yakeyi,gashi ana zabga rana.

Wasu ne 'yan mata su biyu suka zo inda take tsayen,'yan class d'insu ne,suma napep zasu hau,anan suka tsaya surutu,ranar ne yafara isanta,dan tun tana jurewa harta ji inaah bazata iyah ba,da gefen ido ta kallo motar,ga mamakinta sai ta hango mummyn ta zaune aciki.

Take taji wani farin ciki ya lullu6eta........

*Drop ur comment* *nd share pls* 👌🏻

*Salmerhn ku ce* 😍
[10/2, 5:54 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_Wannan page d'in_ _naku ne ku_ _d'ai_ 👌🏻' _yan_ *CAPTAIN* *ABBAS FANS* *2* , _inajin_ _dad'in comment_ _d'inku har_ _6argona......__ 😍

*Bismillahir* *rahmanir raheem*

Worry is a total waste of time. It doesn’t change anything. All it does is steal your joy and keep you very busy doing nothing.

🅿 *11*

Da saurinta ta isa gurin motar,alokacin ma mummy hankalinta harya fara tashi da rashin ganin Teemahn,tana k'ok'arin fitowa kenan ta duba ta dakyau,sai taji muryarta ta k'ira ta

"Mummy"

Da sauri mummyn ta d'aga kanta ta kalleta kana tace

"Haba Teemah a ina kika tsaya fisabilillahi?

Karkata kai Teemahn tayi gefe tayi kalan tausayi,
Mummyn kuwa tacigaba da fad'in

"Wato dama haka kike wa Habibu idan yazo d'aukarki ko kisashi yayi ta jiranki ko?

"Ahh fah mummy ni na _d'auka_ wannan yayan ne shiyasa fah nak'i zuwa"

Haushi mummy taji dajin abin nan data fad'a d'in,gata gwanar fad'ar gaskiya bata fiye 6oye al'amarinta ba ita.

Cikin jin haushi mummy ta bata amsa da " toh ai sai ki _ajiye_ da kika ga bashi d'in bane kuma"

"Sorry my mum"
cewar
Teemh ta fad'a tana zagawa d'ayan b'angaren ta inda zata shiga motar.

"Wato ke bazaki bar raini da mugun halinkin nan ba ko?

Mummyn ta ce bayan Teemah ta shiga motar

"Shiru tayi bata yi magana ba.

"Inda Abbas d'inne kenan haka zaki shanya shi?
Waini sa'anki ne shi d'in?
"Kalli time fa Teemah kusan 1:30 amma sai yanzu zaki taho,kinsan tun yaushe nake anan d'in inaji ranki?

"Allah mummy bansan ke bace kika zo da bazan dad'e ba.

"Hmm"Allah ya shiryeki "

Kawai mummyn tace tare da yiwa motar key,sun iso daf wad'ancan friends d'in Teemahn sai Teemah tace "mummy sabon pegi" tafad'a tare da nuno su.

Tsayawa mummyn tayi,Teemah kuma tayi musu magana suka shigo dan har yanzun basu samu abin hawa ba.

Gaida mummyn suka yi ta amsa musu cikin sakin fuska daganan ta d'auki hanyar sabon pegin,ba hanyarsu bace amma haka sai da ta kaisu har k'ofar gidan su da taimakon kwatancen da suke mata,har suka isa,godiya sukayi mata sannan suka shiga ciki dan dukkan su 'yan gida d'aya ne.

Daga nan mummy ta juyo ta nufo hanyar gidansu dake Nyanya Quaters gujba road Damaturu.

"Allah mummy gwanda da kika zo,d'azu da wannan yayan yamin wani tsawa har sai da naji fitsari.

"Wataran ma ai har dukan ki zaiyi inde kika ce juninki rashin jine"

"nifah babu abinda namasa mummy"

Bata kulata ba,dan tasan koma me zata ce toh 6ata bakinta takeyi abanza kawai dan Teemah baji takeyi ba.

Horn mummy tayi aka bud'e mata get d'in tashiga.

Da sallama suka shiga parlourn,babu kowa aciki dan haka kowa yanufi d'akinsa.

Teemah na shiga ta fara ciccire kayan jikinta,sai da taga tacire komai sannan tafad'a kan gado tare da fad'in

"wash wallahi nagaji"

takai tsawon mintina biyu akwancen kafin ta mik'e tsaye

Towel ta d'auka akan k'ofar bayinta ta d'aura sannan tayi unhooking bra d'in jikinta ta ajiyesa,ta nufi k'ofar fita,harta kusan fita daga d'akin sai ta tuna abinda ke jikinta dawowa tayi sai kuma ta tsaya ta fara kwalla k'iran Baabah Lami,bakinta uku taji shiru babu amsa sai ta d'auki hijab d'inta ta saka sannan ta fito,kitchen ta shiga ta d'auko ruwan goran c'est,garin fita daga kitchen d'in ne ta had'u da Baabah Lami ita kuma tana k'ok'arin shigowa kitchen d'in.

"Baabah Lami inata k'iranki kika k'i kulani"

"Yi hak'uri fatee,naje wurin hajiya ne,

"Owk dama ruwane kuma ma kinga na d'auko abuna"

"Babu wani abinda kuma kike buk'ata?
Baabah Lami d'inne ta tambayeta da dukkan kulawa.

"Ah ah bakomai "
Teemahn ta bata amsa.

Daganan tawuce d'akinta da ruwan ahannunta,tun kam ta k'arasa cikin d'akin sai ta cire hijab d'in ta rik'e a hannunta, zama tayi akan side drwaer d'inta ta d'aga goran ruwan takafa abakinta,dan ko kofi ma bata d'auko ba,sai data sha kusan rabi kafin ta rufe ta ajiye
"Gaskiya yau kam masha Allah akwai zafi"

Wanka ta tashi ta shiga kusan 20mins tana bayin sannan ta fito,wajen dressing mirror ta nufah tana goge jikinta,sai yanzu taji d'an dama dama,domin ruwan sanyi tahad'a tayi wankan dashi,shiyasa take so tad'an shafa mai koda ak'afarta da hannunta ne dan kar suyi mata wani iri.
Har taje ta tsaya gaban madubin sai kuma ta tuno ashe man nata ya k'are gaba d'aya,ai kawai sai ta fito ta nufi d'akin mummy ahakan datake,shaf ta manta da batun wani Abbas agidan shiyasa take al'amuranta cikin sake wa kamar yanda tasaba.

Sallah tasamu mummyn nayi take ta tuna ashe fah batayi azahar ba itama.

Zama tayi tajira mummyn harta idar sannan ta tambayeta batun man shafuwan.

Mummy cewa tayi "aini mantawa nayi ma gaba d'aya,ki bari da yamma zan aika asiyo miki"

"Toh"
tace sannan tamik'e da niyyar fita daga d'akin,

"Teemah"Mummy tak'irata tana daga zaune akan sallayar datayi sallahr.

"Na'am"ta amsa tare da juyowa

"Kindai san yanzu bamu kad'ai bane agidan nan ko?

"Kai ta d'agawa mummyn alamar "ehh"

"Toh ki daina fita da irin wannan shigar dan Allah."

"Toh mummy yan zunma mantawa nayi ne kuma dana fito ma ban had'u da kowaba"

"Ki dai kiyaye"

"Uhm"
Teemahn tace sannan ta fito daga d'akin.
Chapter 10 · 0% Book details