← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 163

Sashe 85

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da wannan damar Abbas yayi amfani ya nufi office 'din Mahmud wanda a'kage yake yaji ya Fateemah take agurin Mahmud 'din, dan shi gani yake kamar rashin son auren da Mahmud yace baya yi ne yasa shi ya kasa kula da ita, be san gidansa ba office 'dinsa yasani dan haka sai ya nufo office 'din, yana da tabbacin adai dai wannan lokacin Mahmud na office.

*****
Fateemah da Mahmud kuwa basu suka isa office 'din ba sai 9:13am
dayake ansamu ha'duwar holdup sosai ahanyar shiyasa ma suka 'dan 6ata lokaci kafin su isa.

Da isarsu office 'din ko zaman 20minutes be yi da ita ba, bayan isowarsun Mahmud ya amsa 'kira through landline 'din dake kan table 'dinsa, yana gama wayar kuwa ya mi'ke tare da sanar da Teemahn cewa yana zuwa bazai da'de ba zai dawo.

Tashi tayi da sauri tace zata rakashi itama, saboda sosai yau 'din take jin babu da'di aranta, fa'duwar gabanta kara yawaita yakeyi acikin kowani da'ki'ka.

Mahmud kuwa yadakar da ita da fa'din " _ah'ah please wait 4me mana Fateemah u ar safe here karki damu_ , yace mata files 'din da ze kai 'din masu matu'kar muhimmanci ne dole akwai wasu 'karin bayanin daya kamata shi zaiyi kafin aturasu zuwa China shiyasa zashi.

Duk tunanin Mahmud tsoron da takeji ne yasa har a office din ma takasa sakewa.

Haka ta tsaya 'ki'kam batare da tayi masa magana ba domin haka kawai yau 'din take jin wani sabon yanayi game da Yayah Mahmud 'din har bataso yayi nesa da ita.

Da fitarsa kuwa Fateemah ta 'daga hannu ta dafe goshinta, bata san dalili ba amma akowani sa'a takan tsinci kanta cikin tsananin fargaba, wanda tun da safiyar yau data' farka daga bacci ta tsinci kanta cikin wannan yanayin.

Bazata ce ga ainahin matsalarta ko damuwarta ba ayanzun ita de kawai tana ji har cikin zuciyarta ba ta da nutsuwa a hargitse take jin kanta gaba 'daya, dan haka kawai sai ta ringa maimaita _inna lillahi wa inna ilaihi raji'un, lahaula wala quwwata illah_ _billah_ acikin zuciyarta wanda yin hakan ne yake 'dan sama mata sukuni idan taji fargaban ya yawaita.

Da rigimarta sai ta wuce kan kujerar da ya ke zama a office 'din ta wani hakimce tana juyi ahankali tare da lumshe idanunta yayinda ta ringa faman sarrafa tunaninta ko zata gano babban damuwarta alokacin.

Mahmud be da'de da barin office 'din ba Teemah taji anturo 'kofar ahankali batare da annemi izinin mamallakin office 'din ba.

Dubanta takai wurin 'kofar sai ta ga wata matashiyar budurwa ce tsaye da fuskar mamaki wacce zata girme mata ahaife.

Sanye take da wata riga doguwa yellow rigar roba ce sosai kuma bawata me fa'di ba, hakan yasa rigar tabi duk jikinta ya kwanta, tare da bayyana duk wata halitta dake jikinta, kanta kuwa da wani jan mayafi ta zagaye shi, ba laifi kam ayanayin zubi da tsarinta tayi kyau sosai sai de atsarin musulunci sam bata da maki ko guda 'daya.

Kallon kallo suka tsaya yi da Teemah kowa da abinda yake sa'kawa acikin ransa, tunanin Teemah ko itama 'daya daga cikin ma'aikayar su Mahmud ne, tace wata'kila haka suka saba shigowa gurin Mahmud 'din batare da neman izini ba, sam Teemah bata san Munnira ba tunanin ta ta6a ganin ta wani guri ma sam be zo kanta ba, saboda ko lokacin dinnern auren sun akwai mutane da dama so bazata iya tunawa da kowa da ta gani awurin ba.

Yayinda Munnira aranta take jinjina kyaun da ta ga Teemahn ta 'karayi, duk da yake ta ganta alokacin hidiman bikinta kuma kwalliyar biki daban yake dana kullum amma duk da haka bata ga aibin Teemah ba koka 'dan sai ma wani fresh data 'karayi tayi kyau bayaga haka bata ga wani abu daban ba, take kuwa tsantsan kishin datake ji azuciyarta game da Teemah ya motsa, amma duk da haka sai da ta 'dan yi dariyar mugunta wanda ta 'dan cije ta maida shi murmushi yanda Teemah bazata fahimci manufarta ba.

Ahankali take takowa izuwa gaban Teemahn yayinda takalmin dake sanye a 'kafafunta yasamu daman bada sauti 'kwas.....'kwas me 'dan 'kara ka'dan saboda yanayinsa.

Teemah sam batada niyyan kulata ko yi mata magana ba duk da taga cewa ta tunkaro ne, ita tun ganinta nafarko ma yarinyar bata birge ta ba koka'dan ganin cewa girmanta be sa tasan muhimmancin yiwa mutun sallama ba sai de ta tsaya kallonta.

Komawa tayi ta jinginu da kyau da jikin kujerar ta kwantar da kanta tare da 'dora 'kafa 'daya kan 'daya harda lumshe idanu tana juyi da kujerar ahankali tamkar itace mamallakiyar office 'din, sai tayi kamar irin ba matsalarta ba ce zuwan Munniran.

Idanunta alumshen ta tsinkayo muryar Munniran akusa da ita tana fa'din
" _Amarya me da'din_ _tuwo!!!_
muryarta cike da murmushi tayi maganar.

Ahankali ta bu'de idanunta ta sau'ke su akan Munniran daga idanun kuwa bata motsa koda 'yan yatsun ta ba.

Kallon a ina kika sanni tayiwa Munniran tare da 'dan zaro idanu ka'dan ta juya su.

Murmushi Munniran tayi itama ta zuba wa Teemahn idanu,
Idon su cikin na juna Munnira ta'kara fa'din
" _soyayyan be 'kare agida ba kenan shine kuka kawo sauran a office ko mrs Mahmud_ ?
_Sai de kuma naga ai angon naki ba me amfani bane........ko de akwai wani sirrin ne bayan wannan?_

Teemah bata kulata ba saima mamakinta daya 'karu tambaya ta fara yiwa kanta shin wacece wannan haka sam Teemah ta tsani shishshigi.

Munnira tagama fahimtar Teemahn da abinda ke cikin ranta dan tasan dama Teemah da wuya tagane ta dan haka sai ta gyara zama tare da yin murmushi tace
" _kina mamakine amaryar mijina?Ki kwantar da hankalinki 'yan_ _mata kinsan fah Mahmud shine rayuwata kinga kuwa dole insan_ _abubuwa da dama game da rayuwarsa, saboda in 'karfafa soyayyata wanda nake tunanin shi_ _kansa ma 'kila be san da su ba, amma inke kina so ki sani zan iya sanar dake bawani_ _abu_ ! "

Ganin da tayi Teemahn bata tanka ta ba har yanzun illah idanu data ke binta dashi yasa tayi murmushi, murmushintan da aduk sanda tayi shi tana jin izzah ne aranta irin kamar tagama dasu 'dinnan.
Kamar an matsi bakinta ta furta.

" _kin san wani abu amarya_ ?
Bata jin cewar Teemahn ba taci gaba.
" _ni 'din nan da kike gani babbar_ _masoyiyar mijinki ne tun ranar farko dana ganshi naji wani mahaukacin_ ' _kaunarsa yakamani amma cikin rashin sa'a sai Mahmud_ _yayi watsi dani da_ _bu'ka'ata ta duk da kuwa yasan ina matsanancin son shi hakan be sa yayi min duban_ _masoyiya ba koda kuwa sau 'daya ne tak, nayi 'ko'karin ganin na fahimtar dashi 'dimbin_ ' _kaunar danake masa amma sam yakasa bani dama, ana cikin haka_ _sai maganar aurenku ya 6ullo daga bakin mahaifin sa, Anty ne tasanar da_ _Mamina komai, nayi 'ko'karin ganin na hana auren yiyuwa amma hakan ma befaru_ _ba, saboda ance auren Mahmud dake zanannen 'kaddara ce da dole sai ya faru,_ _Malamin mami na ne ya fa'di ne yafa'di haka, badan naso ba na ha'kura har aka 'daura_ _auren ki da Mahmud............ Fateemah kina ganin zan iya ha'kura naga_ _rayuwar farin ciki_ _na wanzuwa atsakaninku ne dukda tarin ba'kin cikin da Mahmud ya 'kunsa min_ ?

Kai ta jijjiga tace
" _sam bazan iya ba, bazan iya juran ganin wannan ranar_ _ba............._
_"Inajin kamar inasonki ne shiyasa nake gaya miki wannan...."_

Dai dai nan Teemah ta hango Mahmud tsaye abakin 'kofar office 'din ganinsa kawai tayi bata san tun yaushe yake wurin ba, dayake Munnira data shigo
ganin Fateemah yasa bata tura 'kofar da kyau ba hakan ne kuwa yabawa Mahmud damar gani da jin kalamanta da kyau ba batare da wani tangar'da ba.

Teemah ce ke saitin 'kofa dan haka ita ka'dai ce ta hango shi sai yayi mata ido akan ta 'dauke kanta akansa ta daina kallonsa hakan kuwa tayi sai ta meda hankalinta da idanunta wajen Munniran dan kalaman data gama furtawa yanzun yasa ta ji tausayinta sosai harta fara jin cewa dama Yah Mahmud be mata haka ba tunda tana tsananin son shi daya daure ya aure ta, Munnira bata san da zuwan Mahmud ba, dan haka sai taci gaba da maganarta kanta tsaye, Teemah kuwa taci gaba da sauraro bata 'kara kallon 'kofar ba koda asace.

" _Tun kafin auren ku nake ta neman hanyar da zan hana auren ku ya'duwa tunda hana yiyuwar_ _auren ya gagareni, nasha fama sosai da 'kyar nasamu hanya_ _wacce itace ta 'dan sanyaya min zuciya har tasa na rage damuwata domin na yadda da aikin_ _danayi_ "

Ido 'daya takashe wa Teemahn tana murmushi taci gaba da fa'din,
" _ba sai na tuna miki ba nasan kinsani tunda ke ke fama da matsalar......._
Cikin izgili tace " _ya kike yine idan jarabar ki ta tashi cikin dare? ai an gaya min cewa da dare ne kawai kike da damuwa da rana kina rayuwarki ne kamar kowa_ "

Dariya ta yi ita ka'danta sannan taci gaba da fa'din
" _ranar dinnern aurenku da nasa Anty ta shirya shi nasamu nasaran_ _aiwatar da niyyata akanki... zaki iya tunawa dani kuwa_ ?

Goshi Teeemah ta ha'da tare da kawar da kanta gefe alamar ita ta manta.

" _Ai nasan bazaki iya tunawa ba, yanzun ma inajin fah kamar inasonki ne shiyasa na_ _ke fa'da miki wannan maganar dan kinsan sirri ne_ _babba awajena fiye ma sirrin dake_ _tsakaninki da Mahmud.Kuma kinsan wani_ _abin birgewa aciki mother in-law 'din ki ce take 'kara min_ ' _kwarin gwiwa akan komai wanda har hakan yasa tayi kyautar ki gaba daya wa 'kawarta_ _musamman saboda farin cikina.........._

Sau'kar mari kawai Munnira taji akan kuncinta wanda yakusan gigita ta kafin ta gama fahimtar ta inda marin yazo sai ta sake jin wani marin, sai da ya mata mari lafiyayyu guda hu'du wanda yasa har takai 'kasa ta zube tana kuka tare da dafe kuncin nata da hannayen ta duka biyu.

Kalle- kalle yafara yana neman abin duka kasancewar ba belt ajikinsa jumpa ya saka shiyasa shi neman abin, haka ya gama kalle-kallen sa be ga komai ba.
Chapter 85 · 0% Book details