← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 149 OF 163

Sashe 149

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sau'kan su keda wuya kuwa Ummah ta ringa sau'ke masa buhun masifa da 'kyar ya samu tayi shiru, dayake dama fa'dan ba wai na zafi bane kawai na haushin rik'e Teemah da yayi ne acan da kuma wasa da hankalin ta da yayi tayi a banza.

Hannah kuwa abin nema ya samu ganin ga ta ga Teemah ga kuma tu'ke'ken cikin ta a gaba.

sai da ta gama dariya son ranta da kwatan ta irin tafiyar Teemah sannan tafara gwad'ata wai wlh cikin kyau ya 'kara yi mata tayi fresh skin 'din ta ya 'kara yellow da shai'ki, tace " sai dai kinyi bombom gaskiya da boobs sosai, har da kama baki tace "kai wannan babyn akwai wayo wallahi yana son Dad 'dinsa ya shana"
ta 'karashe da dariya.

Teemah kam bata damu ba sai ce mata tayi " soon kema ai kina hanya zan rama ne Hannah"

Hannah tace " Allah kuwa ba batun wasa anan, inaga ma shiyasa Yayah ya kasa dawo dake gida tuntuni 'din irin wannan kaya haka?, kai tubar kallah!"

Murmushi Teemah tayi tace " Hannah ke kam bazaki ta6a canza wa ba, inajin sai ranar da Bilal ya koya miki hankali tukun"
Hannah Tace
" kamar yanda Yayah ya koyar dake ba, ai naga kin wani nutsu ne duk kin canza ko dai kawai dan ana shirin zama uwa ne?".
Teemah sai tace
"Bansani ba Hannah kijira naki idan yazo kawai sai ki bani labari"

Dariya Hannah tayi tace " ai nawa daban ne da naki kema kin sani...., yauwa ni ya batun birgiman ki? Allah yasa de kin daina dan in ba haka ba yanzu kam sai dai ki koma 'dakin Yayah kiyi ta bajewar ki ke ka'dai da wannan 'katon cikin"

Teemah cewa tayi
"Zamu gani ai Hannah sai ki kore ni"

Murmushi kawai Hannah tayi ta tashi ta fita jin Ummah na 'kwalla 'kiran ta.

Washe gari Leesah tazo ta yi musu barka da zuwa, su Hannah sai sunkuyar da kai take yi ita a dole kunya, sai a bayan tafiyar Leesah ne sai Teemah tayi ta tsokanar ta wai mai kunyar iskanci bayan tana ganin yanda take satan kallon ta idan ta juya kai.

Hannah tana dariya tace " ai dan tana 'dan kama da Bilal ne shiyasa"

Teemah ma dariya tayi tana nuno ta tace " mara kunyar yarinya kawai, wato dan tana kama da Bilal ne shiyasa kike satan kallon ta".

Hannah murmushi tayi mai sauti tace " bazaki gane bane matar nan, Allah ina tsananin son Bilal fiye da yanda Yayah ke son ki ".

Ta k'arashe da zolaya.
Teemah kuwa take ta tare ta da fa'din " kar ma ki fara yaudaran kanki da wannan 'karyan, an gaya miki soyayyan Yayahn irin naku ne?"

Hannah 'kin yin magana tayi sandiyyan ganin Abbas tsaye a bakin 'kofa sai kawai ta fara 'kif-'kif da idanuwa Teemah bata san me ake ciki ba ita kam har sai da ta gama fa'din me zata fa'da ta mi'ke sannan ta ci karo da shi a tsaye.

Hannah tasowa tayi ta nufi 'kofar fita daf da shi sai tace " Ina yini Yayah?"

Da " lafiya" kawai ya amsa ta kamar yadda ya saba.

Teemah da idanu ta bi bayan Hannah har ta bar 'dakin sannan ne ta dawo da kallon kan Abbas, sanye yake da dogon wandon jeans da armless shirt, sosai kayi suka amshi jikin sa.

A hankali ya tako zuwa inda take ya zo ya tsaya a kanta batare da yayi magana ba.

Teemah 'daga kai tayi ta kalle shi suna ha'da idanu sai yayi sama da girar shi tan 'ko'karin sau'kar da idanun ta sai ya sa hannun 'daya ya 'dago ta tsaye ran'kwafowa yayi ya rungume ta baya hannun sa ya kai kan cikin ta yayin da kansa ke a wuyan ta saitin kunnan ta a hankali ya furta " na ji ana gulma ta!, laifin me na aikata kuma?"

"Ba komai"
Ta ce da shi itama cikin sanyin murya.

Kiss ya sau'ke mata a kunnan tare da fa'din " ban yarda ba "
Sai tace
"Da gaske Yayah ba komai......"
Maganar tata yankewa yayi sanadiyyan cizon dataji ya sake mata a kunnan sai ta 'karasa da fa'din
" awshh......Yayah ka cinye min kunne na".

Murmushi yayi yace " da zafi ne?"

Kai ta 'daga masa masa tana shafa kunnan tamkar zata yi hawaye.
Sai yace " tell your sister that dafin son Yayah ya zarce na kowa, bai ma da makamanci kinji?"

Shiru tayi masa kawai tana jin yadda yake 'ko'karin kai hannun sa har zuwa 'kasan ta.

Ri'ke mai hannun tayi tayi kalar tausayi tare da ro'kon sa akan " please yayi ha'kuri"

"Dalili?"
Ya ce da ita.

Sai tace " Ayyah Yayah gidan Ummah ne fah kuma kaga Hannah na iya shigowa ako wani lokaci"

Shima 'din ya san abinda ta fa'dan gaskiya amma duk da haka sai ya'ki sakin ta har sai da ya gama kashe mata jikin kafin nan ya bar 'dakin, Allah ma ya taimake ta har ta gama kintsa kanta Hannah bata dawo ba.

Satin Abbas 'daya a Abuja sannan ya koma Rivers, ranar daya koma kuwa a ranar Teemah ta bar 'dakin sa ta koma na Hannah bisa umarnin Ummah.

Sosai Teemah ke jin kewar sa musamman lokacin da tazo bacci, dan ta saba bacci ajikin sa yanzun kuwa sai take jin ta wani iri, in bama maganar da Hannah tayi mata akan birgima ba ai ita tuni ta mance da cewar tana yi, dan kullun yanda ta kwanta ajikin sa a hakan take tashi bata ganin ta canza wuri saboda baya raba jikinsa da nata har gari ya waye, so ta ina zata samu damar yin birgima a hakan, yau da gobe kuwa yasa har ta saba da bacci a nutsen especially ma idan tana jikinsa dan ko fa'da sukayi da shi kuwa wannan yanayin baccin nasu baya ta6a canzawa ko ta'ki ma dole sai ta ha'kura saboda ba barin ta zai yi ba.

Aranar da 'kyar bacci ya 'dauke ta da tunanin sa a ranta har kuwa cikin mafarki sai da ta ganshi.

Washe gari da suka tashi Hannah da yake bakin ta baya shiru sai tace " gaskiya Yayah ya iya displine kin koyi bacci mai kyau, da ai har ina fargaban ki danne ni da wannan 'katon cikin naki".
Teemah cewa tayi " ke de kika sani Aku uwar magana, ina nan in da raina watarana sai na rama insha Allahu".

Hannah murmushi kawai tayi bata yi magana ba tana tuno cewa wai itama watan watarana sai gata ga ciki. " hmm" kawai ta furta a fili with smile on her face.

Zaman Abuja yayi wa Teemah da'di, dan sosai Ummah ke bata kulawa tare da bata wasu addu'o'i tana karantawa kullum, bata da damuwar komai yanzu face tunanin mijin ta da kuma fatan Allah ya sau'ke ta lafiya.

Shima Abbas 'din suna waya akai-akai dashi dan a'kalla suna waya a rana kusan sau biyar in dai yana da lokaci baya gajiya da 'kiran ta.

Tun lokacin da watan haihuwar ta ya kama sai ya kasa jin kwanciyar hankali, kullum baya bacci mai kyau da dare haka zai 'dau lokaci yana yin sallah yana ro'ka mata ubangiji sau'kin na'kuda, haka ma Mummy ba'a bar ta a baya ba tana iya 'ko'karin ta.

Da yamma kullum sai sun fita cikin compound 'din gidan ita da Hannah su 'dan zaga tana warware ga6o6in ta, ko ina kuwa zata da ruwan ta a hannu take tafiya, dan yawan shan ruwane da ita akai-akai yanzun.

According to her EDD an ce haihuwar ta zai kama ne zuwa kwanaki takwas masu zuwa ko kuma 'kasa da haka, sannan kuma zai iya haura hakan it's depends basu da tabbaci, kuma duk ba matsala bane.

Dalilin haka ne yasa yanzun Ummah sam bata nutsuwa kullum hankalin ta na kan Teemah, hatta baccin dare ma bata yin shi gaba 'daya, ta ringa zarya kenan a 'dakin su, haka ta hana Hannah ma dogon bacci duk wai dan kar wani abin ya taso kuma basu sani ba.

*****
Ranar wata lahadi ne wanda ya kasance kwana na biyar cikin kwanakin da aka gindaya mata, kenan idan aka bi lissafin da aka tana da sauran kwanaki har uku kafin cikin EDD 'din ta, shiyasa ma bata damu ba koda taji marar ta na 'dan haura mata da ciwo ka'dan-ka'dan, zaton ta ko zai daina kamar yanda ya saba yi mata dan haka sai bata sanar da Hannah halin da take ciki ba ganin tana baccin ta, shiyasa ma ko motsin kirki ta 'kiyi dan kar ta ta she ta.

Zirga-zirgan zuwa bathroom ta fara dan yawan fitsarin dake matsata, in ta je 'din kuwa ba wani abin kirki take yi ba sai dai ta dawo tana cije baki tana tafiya da 'kyar kuma a hankali saboda azaba.

Gajiya tayi da yawon zuwa bayin ga ciwon marar nata na k'ara tsanani kawai sai ta sanya kuka a hankali ta dur'kushe daga bakin gado dai-dai farkawan Hannah ha'de da turo 'kofan Ummah a lokaci guda.

Da hanzari suka yo kanta Ummah kam sai ta daka wa Hannah tsawan rashin hankalin datayi inji Ummah da yake ta mata warning akan kar ta yadda ta ringa yin dogon bacci saboda irin hakan.

Take sai Hannah taja gefe tana rarraba idanu tayi kicin-kicin da fuska.

Ciwon Teemah kam kamar jira yake yi yaga idanuwa sai kawai ya tashi gadan-gadan, Hannah ma kuka ta sanya ganin halin da y'ar uwar ta ke ciki kafin kace kwabo har hawaye ya wanke mata fuska gaba 'daya.

Ummah fita tayi da sauri taje ta d'auko wayar ta da mayafin ta bata dawo 'dakin ba sai da ta fita waje ta yiwa driver magana, Allah ma cikin ikon sa yasa yau 'din agidan su drivern ya kwana saboda daren da yayi bai koma gida da wuri ba shiyasa kawai ya kwana be tafi ba.

Hannah kam sai aikin sannu take ta yiwa Fateemahn gwanin ban tausayi idan ka gansu.

Ummah na dawowa sai ta umarci Hannah data ta 'daukowa Teemah mayafi su wuce asibiti.
Chapter 149 · 0% Book details