Sashe 105
Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ummah kuwa sai da ta ganshi hankalinta ya kwanta saboda kafin yanzun hatta layukansa ma basa shiga, hankalinta duk ya bi ya tashi da rashin zuwan nasa tsoronta 'daya kar Abbas ya 'ki zuwa ne tasan mahaifinsa bazai ji da'din hakan ba, kuma idan har hakan ya faru kenan 'kiyayyar sa ga auren ya nuna 'karara wanda ita sam bahaka take bu'kata daga gareshi ba.
Gaida su yayi gaba 'daya fuskar sa normal ba yabo ba fallasa yana yi yana rarraba idanu afakaice ko zai ganta amma be ganta ba ko Hannah ma be gani ba.
Ko da ya tashi zai tafi sai Ummah ta tashi tabi bayansa awani corridor suka tsaya ta tambaye shi dalilin daya sa be taso da wuri ba tace " _harka 'daga min hankali wallahi_ _sosai na 'dauka bazaka zoba, bansan har sau nawa na gwada 'kiranka ba ayau amma duk ban same ka ba_ "
Murmushi Abbas yayi mata yace " _haba Ummah zanzo mana ai Daddy ne da kansa yace in dawo_ .
" _Yauwa Babana kayi ha'kuri dan Allah ka kar6i_ _auren nan da hannu bibbiyu, dama ai kace Fateemah amanarka ce, kai kace an baka amanarta tun abaya so kaga sai kaci gaba da kulawa da_ _amanarka cikin sau'ki tunda ta dawo 'kar'kashin ikon ka, dan Allah Muhammad karka bani kunya, karka_ _cutar min da yarinya kaji_ ?
Tabbaci ya bata da fa'din
" _Insha Allahu Ummah karki damu_ "!
Albarka tasa masa tare da yi masa zancen abinci yace akwo masa coffee ma ka'dai ya isa.
Ummah da kanta ta ha'da masa sannan aka fara cigiyar Hannah akan tazo ta kai masa coffee 'din da 'kyar aka samo ta a 6angaren Daddy yasa ta gyaran wasu kaya daga.
Hakan yasa dole sai de Teemah ce za ta kai masa tunda kam Hannah na aiki.
Tana kwance akan gado rufe ruf da blanket kanta ciwo yakeyi mata ga jikinta zafi rau amma ahakan ta aure ta mi'ke lokacin da sa'kon ana 'kiran ta ya risketa.
Hijab ta zun6ula har 'kasa kan shararar rigar da ke jikinta sai ya kasance fuskar ta ne ka'dai ake gani.
Ahaka ta kar6i coffee 'din ta taho zuwa 'dakin nasa.
Tunani takeyi na yadda Yah Abbas zai kar6e ta amatsayin mata, sannan ga Zazza6i ciwon kai da mara da yasa ta agaba tun 'dazu tarasa yadda zatayi, Hannah taso sanar mawa ko zata samo mata magani amma tun lokacin data fara jin ciwon marar bata sanya Hannah a idanunta ba.
Ahankali take tafiyar kamar bazata yi ba har ta isa 'kofar 'dakin inda tun kan ta shiga zuciyarta ya fara harbawa, ahankali ta tura 'kofar tare da yin sallama ta
shiga.
Abbas kam be amsa ba sai ma ya lumshe idanu aransa yace " _Alhamdulillah_ "
Da ganinta, dama idanunsa da zuciyarsa ba 'karamin son ganinta suke ba.
Teemah kam rashin amsawan nasa sai ya sa ta shiga ru'dani tunda tasan sarai yaji ta duk kuwa da cewa ahankali tayi sallamar amma ta tabbar yajita sai de ko in beyi niyyan amsawan bane kawai.
Shi kuwa Abbas tsayawa yayi kallonta duk da ba wani wadataccen haske bane a'dakin amma kallo 'daya yayi mata yaga canjawar da tayi afili tayi wani kyau na musamman ga haske data 'kara na gyaran data sha ya kuma sake ha'duwa dana menstrual period, daya ke idan tanayi haske yake 'kara sata ka'dan.
Gaban sa tazo ta ajiye 'karamin tray 'din bata mi'ke ba sai da ta gaida shi tukun na.
Abbas amsawa yayi yana kallonta dan tuni ya shagala da sha'kan da'd'da'dan kamshin dake tashi ajikin ta, 'dakin bawani haske sosai illah hasken television da ke aiki kawai a palourn shi 'din ma be wani wadaci 'dakin ba dan wani guri idan aka nuno yakan yi duhu ne gaba 'daya hakan kuwa sai ya sa 'dakin ya kasance ba shida maraba da wanda babu hasken ma gaba 'daya.
Lokuta da dama tana mamakin sa yanda yake son kasance wa a cikin duhu shi, kamar wani marar gaskiya.
Tana 'ko'karin mi'kewa sai kamar an matsi bakinsa yace " _tafiya zakiyi kuma_ ?
Fasa mi'kewan tayi sai ta koma kamar yadda take tsugunne da farko.
Zazza6i takeji sosai ga ciwon kai sanadin haka kuwa har yanasa idanun ta tara ruwa.
Data rasa me zatayi sai kawai ta 'dauki cup ta tsiyaya masa coffee 'din tare da mi'ka masa.
Hannu ya sa ya kar6a tare da fa'din " _I thought kin manta ne ai_ "
Maganar tasa bata bu'katar amsarta dan haka sai ta yi shiru.
" _Wai meke damunki ne_ ?
Yasake tambayar ta yana kallon ta.
Tambayar kuwa sai ya sa ta sakin hawaye, da sauri ta kai hannu ta share hawayen wai dan kar ya gani amma
ina yariga yagani.
Zaro idanu yayi yace " _me aka miki_ ?
_Ko yau 'din ma ba'a son ranki kika zo ba, nifa bance dole sai ke zaki kawo_ _min abu ba!_
_Ko wani abu na miki yanzun_ ?
Girgiza masa kai tayi alamar " _ah ah_ "
Hawayenta naci gaba da zuba.
" _So kukan fah na_ _menene_ ?
yasake tambayarta.
Cikin in i nan kuka tace " _Kai...kaina ke min.. ciwo_ "
Abbas be yi mamaki ba dan lokacin data mi'ka masa coffe 'din yaji 'dumin da jikinta ya 'dauka dama yasan za'a rina.
Ajiye coffee 'din yayi yakai hannu ya ta6o fuskarta sai yaji zafi gau take yace
" _Sabhanallah tun yaushe yafara miki?_
" _D'azu_ " tabashi amsa atakaice.
" _Kinsha magani ne_ ?
Ya sake tambayarta.
" _ah 'ah_ "
tabashi amsa tare da jijjiga kanta.
Mi'kewa yayi yace mata
" _tashi muje_ "
Yayi maganar yana fita daga 'dakin, itama Teemah sai ta bishi abaya a hankali dan har jiri takeji yana 'dibanta, hatta haske bata son gani dan sai taji idanunta na mata zogi sosai.
Wurin driver ya wuce ya kar6o key sannan ya nufi gurin motar har ya bu'de zai shiga kuma sai ya tuna wani abu.
Jiranta yayi sai data iso sannan yace mata " _zonan wato dana tafi bakya cin abinci sosai ko_ ?
Shiru tayi masa tana rarraba idanu.
Tsaki ka'dan yaja sannan ya juya ya shiga motar tare da tada ta.
Teemah ma shiga tayi yaja suka fita daga gidan.
Sai da yabi da ita wani eatry yasata dole sai da ta 'dan ta6a abinci tukunna kafin suka wuce inda zasu.
Wani 'karamin private clinic dake kusa dasu ka'dan ya kaita.
Suna zuwa kuwa suka samu wata nurse ce a duty dan haka itace ta duba Teemah.
Abbas kam kamewa yayi akan kujera yace Teemah tafa'di abinda ke damunta wa nurse 'din.
Nurse 'din itama murmushi tayi tace " _meke damunki ne_ _'yan mata_ ?
Ahankali Teemah ta bu'di baki tace " _Zazza6i nakeji da ciwon kai da....da kuma...._
Kasa 'karasawa tayi sai ta 'dan saci kallon Abbas sai taga shikan idanunsa nakan wayar sa ne.
Muryar Nurse 'din tasake ji tana fa'din
" _inajinki, da me kuma?_
Sai da sake kallonsa kafin ta fisgi maganar tace
".... _da...Menstrual_ _pain_ "
Tana gama fa'di sai ta wani rintse idanu da 'karfi.
Abbas kam murmushi yayi ganin akan wannan abin take wani jan magana.
Nurse 'din ma murmushi tayi mata tace
" _kina jin kunyar_ _Yayah ko_ ?
Bata kulata ba sai ta kauda kanta gefe.
Tashi Nurse tayi taha'da mata magungunan da suka dace, taso tayi mata allura amma Teemah tace bata so, harta fara lalla6ata sai Abbas yace abar alluran kawai tunda bata so.
Koda suka koma gida kuwa be barta ba sai da ya tabbatar tasha maganin ta tukunna , tana shiga 'dakin su kuwa ta tarar da Hannah tsaye da waya a hannunta Anty ma na zaune a gefen gado ta zubawa Hannah idanu.
Sallamar ta ce ta dawo da hankulansu gareta Hannah harda ajiyan zuciya Anty kuwa da sauri ta zo ta tareta.
Hannah ce ta jefa tambaya tace
" _Teemah ina kika shiga dan Allah duk kinbi kin 'daga mana hankali_ _gashi mun ta 'kiran wayarki bakya 'dagawa har 'dakin_ _Yayah naje fah ban same ki ba?_
Teemah da dafe kai tace.
" _Wayar na nan 'ka'kashin pillow ne kuma tana silent_ "
Anty ne ta taho da sauri ta ri'ke ta tare da fa'din
" _Fateemah meya faru kuma naji jikinki da zafi_ _sosai_ ?
Ledan magungunan ta 'dago ta bawa Anty a hannunta tare da fa'din "
_Anty clinic mukaje_ _da Yayah_ "
daga nan ta basu labarin zazza6in daya dameta 'dazu.
Anty kar6a tayi da mamaki tace " _Ya akayi baki sanar da_ _kowa ba toh_ ?
Tana shirin yin magana Anty ta dakatar da ita da fa'da akan shirun da tayi bata sanar musu halin da take ciki ba, tace karta sake yin irin haka
yanzu ba dan shi Abbas 'din ya lura ya tari abin ba da tasan meze faru ne? Su suna can suna shirin biki while ita wacce akeyi domin tan kuma tana nan tana fama da jinya ina anfanin haka?
Ha'kuri Teemah tayita bawa Anty tace bazata sake maimaita irin haka ba.
Anty bata bar 'dakin nasu ba sai da ta tabbatar da sassaucin zazza6in kafin nan taje ta kwanta itama.
Abbas kam da kansa yazo ya duba ta lokacin 'karfe 11:48pm su suna ma bacci basu san yazo ba, ganin tana bacci yasashi jan 'kofar ya rufe ahankali tare da hamdala dan yasan zazza6in ya sau'ka kenan tunda har tasamu tayi bacci, yaso ya shiga ya ta6a yaji lafiyar jikin amma saboda kasancewar Hannah na 'dakin yasa kawai ya juya batare da ya shigan ba.
*****
Washegari yakama ranar Friday wanda ya kasance aranar jama'ah da dama suka shaida 'daurin auren Muhammad Abbas Al'hassan tare da amaryar sa Fateema Kabeer inda yasamu hallatar alummar musulmai da dama dayake a masallaci aka 'daura auren bayan an idar da sallah juma'ah.
Abbas kam farin cikinsa ba ze ta6a misaltuwa ba domin shi ka'dai ne zai iya fassara irin yanayin daya shiga alokacin daya ji an sar'ke sunansu waje guda, godiya kawai ya ringa zubawa mahalicci dan bashi da abin da zai iya furtawa bayan haka.
*Wash Allah na nagaji sosai............Dan Allah readers ku taimaka inga ruwan comments in ba haka ba ni daku sai jibi ko ma monday wallahi.*