← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 163

Sashe 55

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Mummy bazan yi kuka ba, bazan sake yin kuka dan zan auri yah Mahmud ba, na miki al'kawari insha Allahu mummy"
Tana goge hawayen fuskar tata take wannan maganar.

Mummy tana nufin insoka ya Mahmud in 'kaunace ka badan komai ba sai dan saboda Allah mahalicci, dama ni ban ta6a jin bana sonka ba Yah Mahmud amma wani lokaci sai inji dama ba kai Daddy ya za6a min ba sai inji dama ya barmu a yanda muke tun farko kaci gaba da zama amatsayinka na yayana nafi feeling compotable akan haka, ban San me yasa ba amma sau da dama sai inji dama Yah Abbas Daddy yace zai aura min ba kai ba".

'Daga kai tasake yi ta dube shi, tun 'dazu data shigo ahakan yake be canja tsayuwarsa ba tsaye yake hannunsa 'daya acikin aljihu ga dukkan alamu tunani yake yi wata'kila shi yasa bata samu amsar sallamar ta data masa lokacin data shigo, Yah Mahmud bai fiya yin hakan ba yakan amsa sallama koda baya cikin yanayi na walwala sannan baya ta6a kyaleta matu'kar ta kusanci inda yake koda kuwa tayi masa abin 6acin rai baya ta6a yin fushi da ita amma ji yanzu yanda ya shareta tamkar ma besan tashigo bayan tana da tabbacin yaji shigowarta tunda da sallama tashigo, gashi ma sai taga ya 'dan rame mata 'ka'dan bakamar yanda yake ada ba, kar dai shima baya son auren ne kamar ni,? kardai maganan auren ne yasaka cikin damuwa ?

Ahankali ta 'dago 'kafafunta ta har sai da ta iso kusa dashi kafin ta tsaya daga bayansa

" _Yah Mahmud_ "!
Ta 'kira sunan shi ahankali kamar bata son yin maganan.

Be amsa ba kamar yadda be juyo ya kalleta ba haka kuma babu abinda yacanja daga yanayin tsayuwarshi.

Sai ta yi tunanin ko beji ta bane sake bu'de bakinta tayi da niyyar sake 'kiran sunan nashi
_" Yah Mahm............_

Da wannan lion voice 'din nasa ya daka mata tsawa

_"Shut up da Allah"!_
Ya fa'di maganar tare da juyowa.

*Hi every one!* 🙋‍♀

_Naga sakonninku readers da dama wasu a groups nagani yayin da wasu suka yiyyi min magana ta private, duk kanku nagani kuma na yaba da 'ko'karinku kuma ina godiya da dukkan addu'o'in da kuke bina dashi, nima ina muku fatan alkhairi.Ha'ki'ka me son ka shike iya bu'dan bakinsa ya zanzaro_ ma _addu'o'i nagartattu batare da haufi ba, duk da yasan Allah na iya amsawa ako wani lokaci, gaskiya godiya nake 'yan_ _uwana_ . *(ALLAH YA* *BAR 'KAUNA).*

*FEELING* *THANKFUL* 👏🏻

_Gareku commenters kuma inajin da'di sosai da yadda kuke bawa littafin nan kulawa harma idan kunga shiru ku tambaya ko lfy, agaskiya hakan ba 'karamin sani farin ciki yake ba, harma yake kuma 'kara min 'karfin gwiwa, as u can see last week akwai ranar da nayi posting 2pages saboda jin_ _da'din_ _ku kawai masoya na._ *( NIMA INA SONKU ADUK INDA* *KUKE).*

_Nagaji ne amma badan haka ba da na lissafo suna yenku koda ka'dan ne, sai dai duk da haka bazan manta daku ba insha Allahu nayi al'kawarin jero_ _sunayanku koda ba dukkan ku ba aduk lokacin dana samu_ _chance_ _insha Allahu._

*'KORAFI* 👎🏻

_Sai dai kuma naji wasu daga cikin ku suna ganin kamar wai ni ina team 'din_ _Mahmud_ _ne_ 🤔.

*SUGGESTION* !👌🏻

_Azahiri bahaka ba ne kar ku manta fa ni na kowa ne dukkan su ina son su babu wanda bana so aciki, kuma ai ba lallai bane arayuwa ace wanda kafi so kuma shi yafi tara dukkan abubuwa in dai hakane ashe za'a iya cewa 'dan Adam_ _batara yake ba yacika goma cif-cif, ba dole bane ace Star 'din littafi shi yafi iya komai acikin littafin tunda kowa ma mutun ne, kuma kowa nada tashi irin baiwar Allah yayi masa kunga dole sai ansamu similarities da difference sannan asamu best_ *.(hakane)* ❓

_Dan haka karku manta wannan littafin sunan shi_ *CAPTAIN* *ABBAS* _kuma star_ ' _dinku a_ _littafin sunanshi_ *oga* *ABBAS*👈🏻😃

_dan haka_ 👇🏼

🤞🏻 *ACIGABA DA*. *GASHI KAWAI* ................... ❓

_Comment_
_Vote_
_Share_

*Salmerh* 😍
[10/2, 6:01 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

_Dedicated_
_2 all masoyan_ _cApTaIn_ _AbbAs._ 😍

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

_If you don’t care about what people think about u, you already passed the first step of success._

🅿 *46*

Cikin firgita Teemah ta matsa baya ka'dan tare da furta _" Yah Abbas "_ asaman la66an ta.

Ganin yanda idanuwan sa suka koma tare da irin kallon da yake mata ma ka'dai abin tsoro ne ballantana kuma irin ihun da ya daka mata aka.

'Kasa tayi da idanuwanta da har sun fara 'ko'karin tara ruwa shikuwa sai ya tako ahankali zuwa gabanta tamkar wani abin arziki zai mata sai kuma yasa hannu ya 'dago habarta zuwa sama dolenta ta 'dago kannata batare da taso ba dan ita yanzu tsoro ya Abbas yake bata sak ya juya mata wani irin halitta daban mai abin tsoro.

Rintse idanuwan nata tayi da 'karfi jikin na rawa saboda lokacin da ya 'dago kannata tayi zaton sau'kar mari zataji amma kuma sai taji shiru.

Shikuwa Abbas kallon fuskar tata ya tsaya yi, sosai yaga yarinyar ta rame masa amma be tsaya yabi takan ramar tata ba sai hankalin sa ya tafi ga rintse idanuwan da tayin, haushin hakan yaji, shi tunaninshi tayi hakan ne dan bata so taga ko da fuskar ne while bahaka bane ita ta rufe idanun ne saboda tsoronsa, tsoron ha'da idao takeyi dashi.

Sake mata fuskartata yayi sai yacigaba da 'kare mata kallo, be kawar da idanun sa daga kannata ba yace _" lover girl !_, _" kin zaci saurayin ki ne yazo ko"?_

Be jira jin amsarta ba yajuya mata baya ya fara taku ahankali hannunsa 'daya har yanzu na acikin aljihunsa kamar an ce kuma yajuyo, sai ya dawo inda take tsayen ya cira hannunsa yaja hannunta da 'karfi.

Be zame ko'ina da ita ba sai a wajen kujera ya wani jefata da 'karfi ya tsaya akanta yana huci, ita kuwa sai ta kudun dune jikinta wuri 'daya yayin da hawayen da ya taru acikin idanunta 'dazun yasamu damar gangarowa abinsa, ci gaba tayi da zubda hawayen helplessly kanta acikin tafin hannunta.

Sau'kan duka kawai take jira awurin yah Abbas 'din dan zuwa yanzun gaba 'daya ta saduda da wannan alamarin, bata san laifin data yi masa ba, dan ita bata masa laifin komai ba a iya saninta amma ga dukkan alamu ranshi a6ace yake da ita.

Ko kuma cewa da taji akeyi anawa sojoji allura wata'kila gaskiya ne, gashi yau tashiga hannunsa Allah ne ka'dai zai 'kwace ta yau ahannunsa, ahankali cikin kukan ta fara fa'din _" Yah Abbas... dan Allah.....dan Allah kayi ha'kuri, wallahi bazan sake ba, dan Allah karka dake ni, in ka dake ni_ _mutuwa zanyi Yah_ _Abbas........"_

Ahankali take maganar dan in ba akusa da ita kake bama bazaka ta6a fahimtar me take fa'di ba saboda cikin shashsheka tayi maganar.

Shi kanshi Abbas yanda tayi sai da ta bashi tausayi amma sam yakasa jin nutsuwa acikin azuciyarsa, yakasa bawa kansa ha'kuri akan abinda yakeji, aganinsa ai shi rani masa hanakali kawai take shirin yi kamar yanda tasaba abaya, azahiri shikanshi be san laifin data yi masa ba she looks innocent, amma shi aransa ji yake tamkar wani babban laifi tayi masa da babu wanda yata6a aikata masa irin laifin akaf fa'din duniya.

Da 'kyar yasamu ya 'dan sassauto ya 'daidaita nutsuwar shi, sai ya yun'kura da niyyan zama agefenta akan kujeran daya jefa tan.

Teemah kuwa na ganin haka ta zamo da sauri ta dawo 'kasa akan carpet kusa da kujerar taci gaba da rera kukanta.

Gira 'daya Abbas ya 'dage da mamakin abin da tayin yana kallonta.

_"meke nan wai "?_
Ya tambayi kansa azuciyarsa.

Teemah kuwa tana sau'ko wa taci gaba da bashi hak'uri " _Nifa banyi laifin komai ba Yayah dan Allah kabarni na tafi, inbaka yadda ba ka tambayi mummy kaji Allah banyi mata laifi ba "_

Rashin sanin amsar da zai bawa tambayar tasa yasa ya watsar da tambayar kawai ya dawo da dukkan hankalinsa gareta yaci gaba da sauraransa ha'kurin nata tana dasa aya yayi murmushin takaici tare da 'dan rankwafo da kansa daf da ita
" _Fatima_ " ya 'kira sunan ta cikin natsuwa.

Shiru tayi bata amsa ba duk da tayi mamakin hakan domin ayanda taganshi 'dazun batayi zaton zai sau'ko so soon haka ba, yau de _" Allah kai ka'dai zaka fitar dani_" ta fa'di aranta sai ta 'dan 'dago kanta ka'dan amma bata kaiga duban fuskarsaba.

Shima be takurata ba wannan karan dan zuwa yanzun ko ba'a fa'da ba dakansa yafara fahimtar irin tsoratan da tayi dashi, ya gane cewa duk abinda takeyi atsorace take yinsa.

_" Waye yace miki bakiyi laifi ba"?_

Shiru tayi masa wannan karan ma dayaga bazata yi magana ba sai yaci gaba da tashi maganar _" anyway,_ _ki bani_ _labari"_.
Yayi maganar yana duba agogon dake 'daure da tsintsiyar hannunsa sai kawai ya 'kara da fa'din

_" ki ban labarin yanda kike so auren ki yakasance"!._

Ko yanzun ma shiru tayi batayi masa magana ba, kawai sai ta 'kara maida kanta 'kasa kamar yanda yake da farko ko ka'dan bata yi alamar zata bashi amsa ba _" toh_ _me yake so_ _ince masa, har akwai wani yanda nakeso aure na ya kasance ne?.

Muryarsa tajiyo yana fa'din _" idan nayi magana banason ashare ni Fatima wata'kila kin manta da wannan ko?"_

Yayi maganar tare da komawa baya ya jinginu da jikin kujerar tamkar wani basarake.

Kai tayi niyyan jijjiga masa amma da tuno da warning 'dinsa daya ta6a mata abaya akan hakan shiyasa sai ta bu'di bakinta da 'kyar kamar ma bazata yi maganar ba tace " ban manta ba".

Shirun shima yayi idanuwansa nakan la66anta datayi maganar, kukan da tayi gaba 'daya sai yasa suka zama jajir, zuba mata idanu yayi shi ka'dai yasan me yake sa'kawa aranshi.
Chapter 55 · 0% Book details