Sashe 47
Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nasiha sosai daddy ya mata wanda ya matu'kar kashe mata jiki tare da kawo ayoyi da hadisai wanda suke nuni akan halayyar 'dan Adam da kuma bata misalai akan yadda ikon Allah ya buwayi ko'ina yace mutun ba komai ba bane shi compares to mahallici dan haka komai zatayi ta yadda da Allah da kuma 'karfin ikonsa kafin tasa tsoron wani abin halitta.
Ya 'karasa da cewa " ina fatan kin fahimceni kuma zaki bani ha'din kai"
ahanakali tace" insha Allahu".
"Yauwa, sai da safe".
Yana mi'kewa ya fa'di hakan yayinda mummy takasa amsa sai da safen dayake mata, ta dai tsaya atsaye duk tunani ya cikata, " ha'ki'ka gaskiya Daddy ya fa'da kuma tasani cewa Allah ne mafi rinjaye akan komai, toh amma abinda takasa ganewa shine kar dai ace wannan dalilin ne ya kawo Yah yusuf inda take?"
Sosai abin nan ya dameta, washe gari kuwa bata nuna komai ba suka yi gaisuwa cikin sakin fuska har suka gama karyawa sannan ne da suka ke6e da Abbah ta sake jefah mishi tambayar da ke damunta azuci inda tace " kar dai abin nan daka fa'da jiya shi ya kawo Yah Yusuf garin nan?".
" ah, ah, ah, khadeeja, kin manta me na gaya miki ne jiya hala?
Ido ta tsura masa tana kallonsa ga dukkan alamu cikakken bayani take bu'kata daga wurinsa.
Ganin hakan sai ya ci gaba da fa'din
" ba abinda yakawo shi kenan ba, kamar yanda na sanar dake ,yazo ne ya sada zumunchi sai kuma yayi katari da Fateemah sai yaga dacewa da sha'awar aurawa 'dansa ita shine yamin maganan nima kuma na amince,
kinga gara namiki gwari-gwari yanda zakifi fahimta."
Ya 'karasa da murmushi
" amma kai kana ganin bawata matsala ko? nifah gaskiya ina tsoron abinda zaije yadawo, kafa san halin Anty ba 'kaunar mu take ba gaba 'daya".
" Kin manta wannan 'dinma kenan ko?"
Kauda kai tayi gefe tare da fad'in " ban manta ba"
" toh karki damu kanki dan Allah, ita 'din ba Allah bane ya halicceta?, ki ringa sawa ranki yadda da 'kaddara kowacce iri ce, na tabbata 'kaddaran wannan al'amarin ne yakawo shi akwannan, toh kinga kuwa idan har Allah yace za'ayi toh fitinan wani ko wata be isa yasa afasa ba,dan haka ki saki ranki kinji".
"Da kai ta amsa masa, dan kasa bu'dan baki tayi ta ce komai.
Ko bayan barin sa 'dakin ma bata motsa ayanda ya bartan ba, tun yanzun tausayin 'yarta yafara shiganta.
Daddy kuwa da komawarsa wurin Abbah sai suka kammala magana inda daddy sai alokacin ne ya nuna amince warsa akan lamarin, 'karyar da yiwa mummy kuwa akan tunruni ma ya amince yayi hakane saboda ta daina sawa ranta kamar maganar zata fasu.
Yayin da Abbah ya nuna tsantsan farin ciki da amincewar daddyn harma ya 'kara da fa'din " bada wani jimawa ba zasu ji daga garesu domin baya so a'dauki dogon lokaci akan lamarin".
" bakomai ai, Allah ya nuna mana "
inji Daddyn Teemah
Zama suka yi suna 'dan ta6a hira tsakaninsu anan mummy ta tadda su, aka cigaba da hiran da ita, ranta ajagule take jinsa ,amma bata so Yah yusuf ya zargi wani abu daga 6angarenta shiyasa ma ta taho inda suke 'din, kuma ma dan kar daddy yace ta'ki jin maganarsa.
Da lokacin tafiyar Abbah yayi sosai ya musu alkhairi daga mummyn har Teemah, ya bawa kowa kyautan ku'di daidai yanda yayi ra'ayi saboda acewarsa be taho musu da komai ba wai suyi ha'kuri da wannan sai in ya 'kara dawowa.
Teemah da bata san abinda ke faruwa ba taringa bashi 'sakon gaida Yah Mahmud kusan sau hu'du tana maimaitawa jitake kamar tabishi su tafi, shikiwa Abbah sai amsa mata yakeyi yana murmushi da jin da'di, sai da mummy ta banka mata harara kafin tayi shiru ta daina magana.
Da daddy suka tafi domin shima akwai abinda zai kashi can arean Lagos 'din harkan kasuwancinsa.
*LAGOS*
Koda Abbah ya isa gida Mahmud ne ka'dai ya nuna farin ciki da dawowar tashi, dan tun da yaje 'dauko shi a airport yake washe ha'kora, wannan na 'daya daga cikin burikansa dayake son ganin faruwarsu, sai kuma gashi hakan yafaru, ba 'karamin da'di yaji ba da Abbah yace zaije Yobe , da farko ma yace zai bishi suje tare amma da Anty ta azalzale shi a'daki tayi masa masifah tare da fa'din matu'kar ya 'dauki 'kafa yabi Abban nasa toh yasani _babu ita_ _babu shi_ "
Dajin hakan sai ya ha'kura da tafiyar saboda duk yanda yakai da rashin ji sam baya son mummunan kalma daga mahaifansa, ha'ki'ka iyaye iyayena kuma duk girmanka da ikonka yazame maka dole kabisu kodan samun rabauta awurin mahallici, amma be sanar da Abbansa abinda yafaru ba sai kawai ya nuna masa cewa akwai abinda yataso masa ne shiyasa ya fasa zuwa, amma insha Allahu zaizo yaje ko daga bayane.
Abbah be wani damu ba yace " toh shikenan ba matsala, kai ai daman 'dan can ne ko bakaje yanzun ba matsala, da'ace baka ta6a zuwa ba ne toh da 'kafata 'kafarka amma yanzu kam ka fansheku, Allah ya nuna mana lokacin dazaka sake zuwa 'din "
"Ameen"
Mahmud ya amsa wa Abbahn dashi, be damu da _yah_ _fanshe sun_ da Abbah yake nufi ba sam ma abin be zo kansa ba, Abbah kuwa nufinsa shi Mahmud 'din da Antyn sa.
Sai kawai ya 'kyale Mahmud 'din yayi tafiyarsa shi ka'dai, domin koshima bazai so bakin uwa yakama 'dan sa 'daya tilo da Allah ya mallakawa ba.
Abinda Mahmud be sani ba shine duk abinda Anty ta fa'da kaf yaji ta, kuma wannan dalilin ne yasa ya 'kara saka himma wa tafiyar tasa.
Koda yatafin kuwa basuyi waya ba har yaje ya dawo gida ko fatan sau'ka lafiya bata yi masa ba ballantana taji yanda ya sauka shine ma ya gwada kiranta sau 'daya dayaga bata 'dauka ba sai be sake 'kiraba yace inhar ba da gangan ta'ki 'dauka ba toh intaga missed call zata kirasa, ilai kuwa yaji shiru, bata 'kirashin ba kamar yadda shima be sake 'kiranta ba har ya dawo sai dai suyi wayarsu shi da Mahmud.
Ko yau 'din ma da zai dawo Mahmud kawai ya 'kira ya sanar dashi ,shi kuwa be sanar da Anty ba kawai yaje ya 'dauko shi.
Anty bata ma gida lokacin da Abbah ya dawo tatafi yawace-yawacen ta acikin gari ita da 'kawarta Anty chideh.
_Comment_
_Vote_
_Share_
*Salmerh* 😍
[10/2, 6:00 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕
By
*Salmerh MD*
Luv story😍
*Wattpad @*
*Serlmerh-md*
💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO* 😍
*Salmerh nayi muku* *fatan alkhairi*
*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*
Remember the 5 (five) simple rules to be happy, Free your heart from hatred.....Free your mind from worries...... Live simply.......Give more and Expect less.
🅿 *40*
Koda ta dawo ta ganshi agida kuwa 'dauke kai tayi tamkar ma bata ganshi ba, shima Abbah sai ya'ki yi mata magana yasan da kanta ma zata kulashi idan nata ya 'debo ta.
Kwana biyar bayan dawowarsa sannan ya 'kira Mahmud tare da Anty, yayi musu bayanin abinda ke faruwa, yayin da hankalin Mahmud yakai 'kololuwa wurin tashi rasa yadda zaiyi ma yayi hakama Anty.
Ita kam tsaye ta mi'ke da gama jin abinda Abban yagama fa'di tace "banji abinda kake fa'da da kyau ba, 'dan sake maimaita pls".
Murmusawa Abbah yayi, yana kallonta har kamanninta sun soma sauyawa atake, be damu ba ya sake mai maita mata akaro na biyu duk da yasan ta ji shi da kyau, kawai sha'kiyanci ne ke damunta shikuwa yana daidai da ita awannan karon.
Kwankwaso ta kama da hannunta 'daya jikinta har rawa yakeyi tsabar masifah.
"Amma kai ko kunyar fa'da ma bakaji?
Kallon ta Abbah yayi wannan karon sai ya koma baya jikin kujera ya zauna ya jinginu yana binta da kallo yana murmushi dama yasan sai ta masa rashin hankali shi kuwa me sashi barin maganan nan se ikon Allah kawai sai yace mata.
" abin kunya nayi ne da har zanji kunyar fa'di"?
"Dakata dan Allah Alhaji, inaga kamar ka manta da maganar da akayi kwanaki agidannan ko, inace kai da bakinka kace zakayi bincike bayan yaro yasanar dakai ga abinda yakeso shine zakaje ku wani 'kulla 'kulle-'kullenku daga zuwanka, ka zo kace ga abinda za'ayi, kai aganinka kayi adalci kenan,? Toh ya kuma kake so ayi da ita waccen da take s.....da Mahmud 'din yake sonta?
Da wuri ta daidaita harshenta dan kar ta kwafsa.
" kinje kin tambayo auren ne"?
Abban ya tambayeta hankalisa akwance domin shi baya jin yana da damuwa koka'dan saima wani farin ciki dayakeji, yayin da masifar da Antyn keyi yake 'kara masa kwarin gwiwa dan ganin yacika Burinsa.
" haushi tambayar tasa ta bata, take kuwa ranta ya 'kara 6aci tafara masifa kamar ta ari baki
" taya za'ayi kace ko na tambayo aure dama mace tana tambayar aure ne?
"Ni na sani ne ko akanki za'a fara"!
yasake fa'da cikin kwanciyar hankali .
" Wallahi Alhaji karka ga nayi shiru akan wannan maganar ka zaci ko maganar ta fasu ne, dama na fahimci take-takenka tun farko so kake ka'ki sa baki amaganar shiyasa ka tsiro da wani batun bincike, toh wallahi bari kaji ba rantse da Allah ko zan tafi tsirara ne sai naga Mahmud ya auri Munira, kuma bari in tabbatar maka wani abu da baka sani ni 'dana bazai auri wata 'kazama wai Fatima ba ko da kuwa mata sun 'kare a duniya toh sai sai ya zauna ba mace amma bazai ta6a auranta ba ,akai kasuwa".
Tana gama fa'din hakan tayi waje tana ta sababi.
Binta da kallo dukkan su sukayi har Mahmud 'din wanda yake zaune akan 'kafafunsa tamkar gunki tun lokacin dauaji bayanan Abban nasa na farko be 'kara jin komai ba, masifan da Anty tafara na 'karshe shine ya dawo shi cikin hayyacinsa saboda da 'karfi tayi maganan.
Sai data 6acewa ganin su kafin suka dawo da kallon su ga juna suna ha'da idanu kuwa Mahmud yayi 'kasa da idanunsa.
Bayyanan niyar murmushi Abban yayi sai yace " Mahmud kaima baka so ko"?