← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 163

Sashe 33

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Anty chidehn ne tace mata Wai ita tafiya tsoro dayawa miye ma abin yin shocked anan sai kace yau ne tasan aka fara yin lesbian?

Tambayar ta bawa Anty mamaki sosai har hakan yasa ta d'ago idanu ta kalli Anty chidehn sosai.

Sam Anty takasa daina mamakinsu dan ganin datayi su kwata kwata abin bai wani damesu ba kamar ba abin jin kunya tasame su sunayi ba.

Dariyah kad'an Anty chidehn tasaki ganin yanda Anty ta kasa daina yi mata kallon tuhuma.

Sai ta mik'a hannu ta d'an kamo hannun Antyn atake kuwa Anty ta wafce hannunta da k'arfi domin zuwa yanzu in akwai abinda tafi kyama toh itace babbar aminiyar shawaran tata wato Anty chideh.

" come on, feel free mana mum mamud bakomai fah"
Tafad'i da dukkan gaskiyarta tana kallon Antyn ita adole in anbarta ba abin damuwa vane hakan, ganin Antyn bata kulata ba sai ta k'ara da fad'in " sucking kawai nake sata tamin when I'm in need but nothing else".

"hmm"
kawai Antyn tace tare da mik'ewa daga kan kujeran datake tace tatafi gida.

Magana taso suyi akan maganin da aka kawo mata d'azu amma wannan 6oyayyen halin Antyn chidehn data gani yau yasata fasa yin maganar ma gaba d'aya kawai ta koma gidanta.

Anty chidehn ma batawani damu ba dan tasan damuwar na yanzu ne kawai dakanta ma zata dawo kodan wani dalilin na daban.

Anty kuwa koda takoma gida tunanin abun yakasa barinta sam bata ta6a kawo hakan ga k'awartanba duk da yake ahlul kitabi ce ita amma sam bata kawo cewa rashin imanin Antyn yakai har haka ba.

Wannan dalilin ne yasa tad'an d'aukewa Anty chidehn k'afa na kusan kwana biyu, yayin da Anty chidehn tabata chance itama akan ta huce tukunna tasan cewa akan hakan bazasu rabu ba sai dai akan wani dalili daban domin bak'aramin sanin sirrin juna sukayi ba, ko wannan d'inma Anty Chidehn ta 6oye mata ne dan ganin kamar ita ba ra'ayinta bane yin hakan shiyasa bata ma bayyana mata ba.

Shima Mahmud zuwan Munira da kwana biyu yace shikan zai koma ana nemansa Daddynsa ma baya gari amma ya tattara yakoma yobe state d'in abinsa domin jiyayi sam zaman chan d'in yadaina yimasa dad'i.

Da farko Anty taso ta hanashi komawa dan ita afad'anta wai sai ya jira Abbansa yadawo tukunna.

Mahmud kuwa yak'I amincewa da batun nata don dolenta ta kyaleshi yatafi badan ranta yasoba.

A week d'in daya koma ne Munira tasake dawowa gidan amma wannan karon tafiyar kanta ce ba aike ba ne, koda tazo suka gaisa da Anty kamar yanda suka saba suka d'an zauna suna ta tad'i tsawon mintina bataga Mahmud ba bakuma taji Anty ta ambace shi ba a maganar dasukeyi d'in.

Kasa hak'uri tayi sai da ta tambaya tace " Anty ina yaronki"?

Dariya Antyn tasaki kad'an sannan tace kardai kice min tafiyar batawa bace ta Mahmud ce"?

" murmushi Muniran ma tayi tare da fad'in haba shikuma ?

" kedai fad'i gaskiya yarinya"
Yanda Antyn ta ke sakewa suyi hira da kuma yanda tayi mata magana ayanzun yasata ko shakkun Antyn ma bataji sosai ba dukda yake son d'anta yakama zuciya amma tasan dole sai dasa hannunta sannan zata sameshi inba haka ba kam tasan samunshi zai d'an mata wahala.

Sai batayi k'auran baki ba tafara sosa kanta tana sussun kuyar da kai kamar wata mumina, take sai Antyn ta gama ganota aikuwa sai tayi murmushin da kana ganinta kasan farin ciki taji har zuciyarta.

Tashin farko sai takamo hannun muniran sannan ta bata assurance akan cewa karta damu indai Mahmud ne kamar tasameshi tagama tadaina ma damun kanta."

Wannan albishir d'in ne yasa Munira ta rungume Antyn da k'arfi tana murna da godiya kamar bazata daina ba, tana sake Antyn kuwa ta tashi ta zari key d'in ta da gudu ko kunya bataji tayi waje wai bari takaiwa mummynta albishir mai dad'i.

Da murmushi Anty ma tarakata yayinda tana fita itama Anty ta zari mayafi ta tafi gidan aminiyar ta Anty chideh shab ta manta da batun lesbian d'in tsabar farin cikin datake ciki.

Kuyi hak'urin rashin jin update da dawuri da bakuyi ba pls abubuwane suka min yawa.

Vote, comment and share pls🤞🏻

*Salmern ku ce* 😍
[10/2, 5:59 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

By
*Salmerh MD*

Luv story😍

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASS*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* * *MUKE TUNK'AHO*

_Dedicated to_👎🏻 😍

*Salmerh nayi muku* *fatan alkhairi*

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

When people walk away from you, let them go. Your destiny is never tied to anyone who leaves you, and it doesn’t mean they are bad people. It just means that their part in your story is over.

🅿 *30*

Koda Anty chideh taganta murmushi kawai tayi, daman tasan dolene zata dawo kodan yanda sukayi sabo sosai ma.

Haka Anty ta kora mata bayanin abinda yafaru tare da nuna tsantsar farin cikinta afili.

Dama tun asali tafison ita taza6awa Mahmud matar aure da kanta sai kuma akayi sa'a fad'uwa tazo mata daidai da zama Munira ta nuna tana ra'ayinsa.

Munira y'ar k'awar Anty ce dasuka had'u sanadiyyar maganin mata.

Domin duk wani nau'i na magani da suke anfani dashi ita da Anty chideh Mahaifiyar Munira ke musu order daga sokoto kuma sunajin dad'in maganin shiyasa suke shiri sosai.

Anty tana gani kamar samun Munirah amatsayin matar d'anta wata dama zata samu dazai sa zumuncinsu da mahaifiyar Muniran ya d'ore sosai.

Anty chideh ma sai tayata murna tare da k'arfafa mata gwiwa akan hakan.

*****
Mahmud kuwa koda yakoma bai wani dad'e agidan ba yawuche inda aka turashi awani d'an k'auye ne zaiyi bautar k'asan.

Da farko Teemah murna takeyi sosai data ga yadawo d'in dan azatonta yanzun agida zai zauna amma sai yace mata ai shi tafiya zaiyi take sai murnar tata ta koma ciki.

Dayaga haka sai ya mata alk'awarin zuwa duk weekend yana dubata sai da taji haka kafin tad'an sake fuska.

Haka sukayi ta dashi aranar daya sauk'a d'in kuma duk hirar bata wuce ta Abbas ba.

Shima sai ya ringa biyeta ganin hakan tafi buk'ata.

Harda yayi niyyar k'ira mata Abbas d'in su gaisa amma sai ya fasa daya tuno cewa Abbas d'in yanzu yana bakin aiki ne.

Haka suka gama hirarsu suka rabu, yana komawa d'akinsa kamar Abbas d'in yasani sai ga k'iran sa ya shigo.

D'auka Mahmud yayi yana murmushi yace " d'an halak"

"Allah ko"?
Cewar Abbas d'in slowly

Mahmud ne yaci gaba da fad'in wallahi nake gaya ma yanzu muka gama hirarka da lil sis harfa da zan k'ira layinka in had'a ku sai kuma nayi tunanin ko kana aiki ne"

" hmm ai gara ma baka k'ira ba, bayanzu zanyi magana da ita ba tukunna da sauran lokaci"

Mahmud na dariya yace
"Kai oga Abbas hukunci ne wannan ko kuma ra'ayine?

" duka biyun" Abbas ma yafad'a atakaice.

Kafin Mahmud yasakeyin wata magana sai Abbas d'in ya k'ara fad'in yaushe ma kadawo ne bansani Mahmud?

" Yau-yau d'in nan na iso amma inajin gobe ko jibi ma zan shiga wani k'auye"

" owk Allah ya kaimu"

da " Ameen" Mahmud ya fufe maganar sannan sukayi sallama da juna.

Washegari da yamma Mahmud yawuche yabar Teemah da kewa.

Amma wannan karon bata wani damu sosai ba dan zuwa yanzun tafara sabo da irin hakan. Tafar gane cewa dole ne irin hakan sai ya faru tunda suna da 'yan uwa kuma dole a ziyarci juna.

Bazai yiwu ace kowa yazo sai ta yi kewarsu ba saboda ba kowane zai zo yakuma zauna mata agida ba dolene atafi tunda kowa nada muhallinsa koma badan hakan ba kowa nada abinyi.

Haka tacigaba da zuwa makarantar ta harsun kusa kammala S S 2 d'in sai Daddynta yace waec zata rubuta kawai bazatayi SS3 ba.

Itama dataji datayi farin ciki sosai dan dama tagaji da zaryar zuwa makarantar nan.

Shikuwa Daddyn ganin girman data ke k'arawa ne yasashi yanke wannan hukuncin, dan Teemahn akullum kamar hurata akeyi haka ta k'ara k'iba dukta cicciko.

Yayinda Mummy sam hakan bai mata ba, inda asonta taso Teemahn ta kammala gaba d'aya kafin sai ta rubuta waec d'in, amma koda ta gwada sanar da daddyn Teemah k'i yayi ya amince dan acewarsa bata da hujhan da zai sa dole sai anyi hakan, dolenta ta hak'ura ta zuba musu idanu.

Ana cikin hakan ne wani matashi yabi ya uzzura ma rayuwarta yahanata sakat.

Akullum inta fita zuwa islamiyah sai ta ganshi yasha gabanta da niyyar yimata magana.

Itakuwa kokad'an bata so daya takurata ma sai ta daina zuwa da k'afan datake zuwa dayake dama itace tace zata na zuwa dakanta bama sai ankaita ba, amma dataga matsin yayin yawa sai ta ce Habibun yaci gaba dakaita kawai.

Amma me.....gudun gara take ganin kawai tayi domin tana fitowa zata ganshi tsaye ajikin motarsa yana rarraba idanun ta inda zai ganta.

Rashin sa'an datasake yi kuma shine wani lokaci Habibu baya isowa da wuri har sai an d'an fara watsewa yayinda wasu lokuta kuma har jiranta yakeyi tatashi kafin su wuce gidan.

Aduk ranar da Habibun bai iso dawuri ba haushi sosai Teemah keji kamar tayi fiffike yayinda ga matashin kuma abin farin ciki ne dan yana samun chance d'in zuwa kusa da ita harma yayi mata magana, dukda bawani kulashi takeyi ba amma dai yana jin dad'in hakan sosai.

Ranar kuwa da bai samu daman mata magana ba yakan bisu abaya har sai sun shiga kafin yake wuchewa shima.

Sai dai bai ta6a gangancin shiga musu gida ba yakanzo ya tsaya na tsawon wasu lokuta a k'ofar gidan daga d'an nesa batare daya nemi kowa ba shidai akullum burinsa yaganta koda sau d'aya ne.

Yau ma takama ranar Sunday, koda Habibun ya sauk'eta gida yakoma suka fita da mummy kuma basu dawo dawuri ba har aka tashi a islamiyar dan siyayyar mummy baya k'arewa matuk'ar tashiga kasuwa shiyasa suka 6ata lokaci sosai.

Tsaye take ak'ofar makarantar tana ganin duk kowa na tafiya amma ita sam ba Habibu babu alamarsa, zuciyarta nagaya mata cewa tabi ayarin masu wucewan itama suwuce tare sai dai tana tsoron kar kuma waccen mayen yabiyo su abaya abinda ta tsana kenan.
Chapter 33 · 0% Book details