← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 128 OF 163

Sashe 128

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka rayuwar ta ya kasance agidan auren ta batare da mijin ta agida ba, satinsa uku yanzu da tafiya, zuwa wannan lokacin kuwa har ma Teemah ta riga ta saba da rashin san azahiri amma sai dai damuwar datake ji aranta koka'dan be ragu ba sai ma abinda ya 'karu musamman data ga cewa dagaske yakeyi bazai dawo Abuja dawuri ba, sau tari idan ya 'kirata takanji kamar tayi masa mitan hakan amma sai ta danne ranta dan tafi son idan suna tare burinta ma be wuci tasan matsayin ta ba, amma a yanda tasan halin sa ma tasan idan yaga dama baze ma tsaya ya saurare ta da kyau ba dan shi bai fiya son jan magana ba.

Dramar su da Hannah kuwa sai ma abinda yayi gaba musamman da har yanzu Hannahn bata fasa 'kiran ta da suna mrs dodo ba, yanzu kuwa sunan na 6ata ranta, sosai yake jin haushi idan Hannah ta 'kirashi da dodo.

Ranar da Hannah ta ishe ta kuwa ce mata tayi " _kar ta 'kara 'kira mata miji da suna dodo, tace ita mijin ta ba dodo bane koma miye ne ita a hakan yafi birgeta_ "

Hannah ido ta zaro da zolaya tasake fa'din " _iyeeh, kice abin yafi najiya bansani ba, yi ha'kuri toh matar Yayah bazan sake ba"_

Teemah a tsare tace da Hannah
" _Daya fi miki_
_in bahaka ba kuwa in tona miki asiri awurin Ummah ince kina da 6oyayyan saurayi bata sani_ _ba_ "

Cikin ko in kula Hannah tace
" _Toh miye aciki ban kai nayi saurayin bane?_

" _kin kai harma kinfi, karki damu yarinya zaki gani zan baki mamaki ai_ "!

Da sauri Hannah ta dakatar da itada fa'din
" _Ah'Ah baiwar Allah abin be kai haka ba, wasa fah nake yi miki, indai mijinki ne ai nace na bar zancen sa ko, da Allah rufe wannan_ _chapter 'din bana so Yayah yasan ina da wani saurayi dan da kaina nace masa makaranta zanyi kinga kuwa ai_ _idan yasani na 6allo ruwa_ "

Teemah cewa tayi
" _Sai ki kiyaye bakin ki in kina so nima na rufa miki asiri_ "

Hannah ma da sauri tace
" _Kwantar da hankalin ki matar Yayah wannan shi yafi komai sau'ki_ "

" _Dayafi miki_ "
Fa'din Teemah daga 'karshe.

Murmushi kawai Hannah tayi tace
" _ni kaina ya kulle fah Allah, wai yaushe yafara yi miki ne_ ?

Atakaice Teemah tace
" _Jiya da safe_ !

Hannah ma sai tace
" _Ai kuwa ba mamaki gaskiya, amma fah kin ban tausayi wallahi, abin yakama ki da 'karfi sosai_ ?

Ringing 'din da wayar ta ta 'dauka ne ya katse musu hiran, Hannah kam naganin me 'kiran sai tayi murmushi tare da 'dagawa.

*****
Tun ranar da Abbas ya cika sati hu'du da tafiya be 'kiran ta ba tun daga ranan, itama kuwa bata damu ba dan halin san yanzun tafara sabawa dashi, itama batayi tunanin 'kiran sa ba kamar yadda bata sanar da Hannah meke faruwa ba, wasa-wasa har suka kwana biyu amma shiru ba labarin sa, ranan na ukun ne abin yafara damun ta sosai, tanaso ta 'kira shi taji me ya faru amma sai zuciyar ta ta rabu kashi biyu, inda 'daya ke bata 'karfin gwiwan ta'kira shi yayin da 'dayan ke bata shawaran ta 'kyale shi itama, kamar yanda yayi 'din wata'kila tana damun sa ne shiyasa.

Wannan 6angaren tunanin ne yayu tasiri azuciyar ta har ma sai ya rinjaye ta gaba 'daya.

Bata 'kira shin ba amma kuma sam nutsuwa ya'ki zuwa mata, haka ta wuni wata iri da ita, hatta wayar ma yau ko bi ta kanta batayi ba tsaban yanda tunani ya yawaita a brain 'din ta, 'dakin nasa ma yau ko bu'de shi batayi ba acikin nata 'dakin ta wuni.

*1:13pm*
Ta tashi tafara rage kayan jikin ta a hankali dan so takeyi ta watsa ruwa ko zata 'dan ji dai-dai, ga mararta ma dake 'dan mur'da mata ka'dan-ka'dan wannan karan period 'din ta yayi mata jinkirin kwanaki dan kuwa wata har yawuce da kwanaki amma bai zo ba, jin mur'dawan da yake yi mata sama-sama ne yasa ta saka ran zuwan sa daga yanzun zuwa kowani lokaci, ga tsoron ciwon maran dayake tasan baya yi mata da wasa, sosai yake damun ta.

Tana tsayen sai taji 'karan door bell tasan Hannah ce dan haka sai ta 'daura hijab kawai akan skirt 'din dake jikinta, dayake tariga ta cire riga sai bra ne ka'dai yarage asaman ta shiyasa ma tasa hijabin, a haka ta nufi 'kofan ta bu'de batare da tunanin komai ba dan tasan bayaga Hannah bata tsammanin kowa.

Turus tayi ha'di da wani bugu da zuciyan ta yayi har sai da yasata 'dauke wuta na 'yan seconds kafin ta dawo dai-dai, kallon-kallo suka tsaya yiwa juna na 'dan lokaci kowa na ayyana irin yanda yaga 'dan uwansa ya canja, kowa ji yayi aransa babu da'di ganin duk da irin 'kuncin da zu'katansu ke ciki amma be hana 'dan uwansa yin wani sihirtaccen kyau da 'kiba azahiri ba.
Teemah kam harda mamakin ganin sa ma duk suka cikata.

Abbas ne yayi gyaran murya sannan Teemah ta bashi hanya ya shigo, bata sake kallon shi ba ta tura 'kofan ta rufe sannan ta dawo ciki itama, haka tawani 'dauke kanta gefe tana tafiya tace dashi " _sannu da_ _zuwa_ "
bata ko jira taji ya amsa ba balle tayi tunanin kar6an jakan sa talkless of welcoming nasa da abin sha ko kuma wani abu daban ba ta wuce ciki abinta.

Abbas ma be amsa ba sai ya bita da idanu kawai, tana shigewa 'dakin ta sai ya jijjiga kansa tare da nufan hanyar nasa 'dakin, amma sai ya jita akulle, beyi mamaki ba dan haka sai ya koma nata 'dakin har yanzu da jakarsa akan kafa'dan sa.

Ga mamakin sa kuwa yana shigowa tana fa'dawa bathroom ga dukkan alamu wanka zatayi.

Jakar tasa ya sau'ke ya ajiye sannan ya zauna abakin gadon nata, he wish yasan inda ta ajiye keys 'din da bazai tsaya jiranta ba 'daukan abinsa zai yi ya.

Zaman sa keda wuya sai kuma yakoma ya kwanta rigingine akan gadon yayiwa kansa matashi da hannayen sa biyu dake bu'de kuma sarke da juna, 'kafar sa 'daya na lan'kwashe akan 'dayar yayin da 'dayan 'kafar ke tsaye yana faman jijjiga su.

Teemah tana bayi tayi zaman ta sarai tasan yana cikin 'dakin nata amma haushin irin wannan zuwan dayayi matan yasa ta share shi duk kuwa da tasan cewa 'dakin sa a kulle amma hakan be sa tayi tunanin tayi hanzarin fitowa ba.

11mins ya 'dauke ta a bayin kafin ta fito d'aure da towel ajikinta, koda ta fito 'din ma idanun ta kansa suka fara sau'ka amma sai ta 'dauke kanta tamkar bata ganshi ba, shirin ta ta hau yi a tsanake tayi light make up tare da zura wata doguwar riga da hijabin sallahn ta. Sam Teemah 'dauke hankalin ta tayi daga kansa tamkar bata san cewa akwai wani abu mai rai dangin halittar mutun acikin 'dakin ba.

Dadduma ta 'dauko ta shimfida ta tada sallah abinta.

Duk abin nan dake faruwa Abbas na kallon ta shima be tanka ta ba, iya gudun ruwan ta yake so yagani, ganin ta fara sallah batare da ta ko kalli inda yake ba yasa yatashi a hankali ya zauna yana kallon bayan ta dayake yana daga bayan ta ne, kamar an tsikare shi kuma sai ya mi'ke, daukan jakarsa yayi ya juya yafice agidan ma gaba 'daya.

Sai da ya tsaya a masallaci ya sallaci azuhur kafin 'dan adaidaita ya sau'ke shi a 'kofar gidan mahaifinsa.

Teemah koda tayi sallamah bata juyo da wuri ba sai data 'dan 'dauki lokaci tana ro'kon ubangijin ta bu'katun dake gabanta sannan ta shafa ta tashi, taji motsin fitar shi tana sallahn amma batayi zaton gidan yabari ba, tayi zaton ko parlour ya koma ne.

Tana na'de daddumar taji aranta cewa bata kyau ta ba dan haka bata 6ata lokaci ba tafito parlourn sai kuma taga empty babu kowa, da mamaki tajuya zuwa 'dakinsa nan ma adatse yake tun rufewar ta na safe, 'dakunan gidan duk tabi ta dudduba amma bayanan arikice ta dawo 'dakin ta da tunanin inda ya shiga.

Wayar ta ta 'dauka ta ta 'kiran layin sa amma baya 'dagawa.
Take taji komai ya tsaya mata cak.

Abbas kam ga mamakinsa gani yayi kowa dake gidan su na farin ciki da zuwan sa tun daga kan ma'aikatan gidan har mahaifiyar sa gaba 'daya, sa6anin ita waccen yarinyar da ko kallon arzi'ki ma bai samu daga wurinta ba.

" _Toh me ya faru ne_ ? _Me ke damunta?_ ya tambayi kansa.

Wani 6arin zuciyarsa ne yabashi amsa da fa'din " _babu komai iskancin ta ne kawai yau 'din ya motsa mata_ ".

Firgigi yayi lokacin daya tsinkayi muryar Ummah ya daki dodon kunnan sa da 'dan 'karfi, ga dukkan alamu ba farkon maganar ta kenan ba " _Muhammad meke faruwa ne wai_ ?
Yaji ta fa'da da kulawa ganin ya shiga 'dan guntun tunanin daya yi saurin tafiya da hankalinsa gaba 'daya, sosai hankalin Ummah ya tashi da ganin hakan, mussamman ma da yake yanzu isowar sa bata san kuma da me yazo mata ba.

Abbas bai bata amsar tambayar ta na farko ba sai data 'kara maimaitawa kafin ya kauda kai tare da fa'din " _bakomai Ummah_ "

Kafin Ummah tasake yin wata magana sai taji 'karan wayar ta, dayake ma wayar na gefen ta shiyasa tayi hanzarin 'dauka ta sada shi da kunnan ta.

Abbas baya yayi ya jinginu da kujera tare da 'daga kansa sama ya lumshe idanu kamar mai tunani.

Gaisuwar da ake yi mata daga 'dayan 6angaren ta amsa tare da fa'da'da fara'ar ta, afili zaka fahimci matsayin me 'kiran awurin ta musamman idan kayi duba da yanda ta bada hankalinta sosai tare da 6acewan damuwar dake kan fuskar ta tashi guda.

Bayan gaisuwar sai Teemah ta tambayeta a 'dan kunyace inda tace " _Ummah Yayah yazo ne_ ?

Sai da Ummah ta juya ta kalleshi kafin tayi dariya ka'dan tace da ita " _ehh yazo, gashi nan ma agefe na, inaga anan yafara sau'ka dan na ganshi da jaka!, bakuyi waya bane_ ?
Chapter 128 · 0% Book details