← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 163

Sashe 51

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tausayi Teemahn take bawa mummy sosai zuwan yanzu ta gama harbo jirgin 'yartata sai de ga dukkan alamu ita kanta bata san me take ciki ba har yanzu, shiyasa kawai zataci gaba ro'kon Allah akan ya takaita mata yabar abin a lullu6e kamar yadda Teemahn bata gane ba Allah yasa yatafi a hakan har abada, domin matu'kar Teemah ta fara gane bambancin soyayyar 'yan uwan taka da kuma soyayyah me zaman kanta (ta aure) tasan za'a samu matsala ne,fatan ta de Allah yasa har ayi agama lafiya kar asamu problem 'din komai, tunda aure ma zatayi ai shikenan.

Domin indai Abbas ne tana ganin da kamar wuya, ko yanzun ma babu wani gaida ta da yace yanayi, ita ce mummyn dakanta tabashi labarin abin da ke faruwa a gidannasu kuma ko da ta fa'da masan ma bata wani ji alamun canji atattare dashi ba ko daga muryarsa har yanayinsa, da suka gama wayanne suna sallama sai yace" agaida mutan gidan " shine ita kuma mummy tace da ita Abbas na gaidata kuma tafa'di hakanne saboda mitan da Teeman keyi wasu lokuta akan cewa Yah Abbas ya manta da ita.

Acikin satin aka gama maganar auren Teemah harma aka sa rana sati hu'du masu zuwa.

Daddyn Teemah dakansa ya yanke wannan lokacin domin yana ganin adaidai wannan lokacin zai fi dacewa ayi bikin batare da kowa ya takura ba.

Mummy bata so hakan ba domin ita aganinta lokacin yayi kusa bata so aka yanke lokacin kwana kusa haka ba, koda ta yiwa Daddy maganar ma sai yace mata "kar ta damu ai komai lokaci ne, ba gaggawa sukayi ba wata 'kila haka Allah ya riga ya tsara lokacin bikin Fatiman yace kinga kuwa mu bamu isa muja da ikon Allah ba".

Dolen mummy taja baki tayi shiru, 6angare guda kuwa hankalinta yakasa kwanciya sam da wannan auren.Yayin da daddy shikam ba ruwansa, kusan kullum idan ya zauna sai dai kaji yana waya ya sanar da cewa lokaci kaza ne bikin Fatima 'yar wajensa, acikin lokaci 'kalilan kusan mafi yawa daga 6angarensa sun san da labarin auren kama daga kan abokansa har 'yan uwa da dangi ma duk ya sanar dasu.

'Bangaren Anty kusan hauka taso tayi akan wannan maganar gaba 'daya ta hana kowa sukuni agidan, gajiya Abbah yayi da halintan datakeyi musu akan auren, wani lokaci ya tanka mata ai kuwa kamar jira ta keyi, shi dama mahaukaci yafi so idan yana abinsa yasamu mataimaki, daga nan haukar Anty ya 'karu daddy ma ranshi ya 6aci sosai musamman yanda take ha'da ilahirin zuri'arsa ta zagesu kaf abin na masa ciwo sosai, amma sai ya lallashi zuciyar sa ya samu ya 'dan sassauto domin ji yake a ranar kamar yayiwa Antyn dukan tsiya, amma yasan haka bazai ta6a kawo gyara ba, zagi kuwa har sai da yaji kamar ya toshe kunnuwansa, munafukai takirasu yafi sau a'kirga, shikuwa yariga yayi alwashin ganin faruwar wannan auren yace ko ma miye zai faru sai dai ya faru amma shi kan be ga me hana shi 'daurawa Mahmud aure ba , mahmud dama ba ya gida tun dawowarsa daga wurin Abbas be fiya zama agida ba, wani lokaci arana sau 'daya Abbah ke kallonsa amma hakan ba damunsa yakeba, tunda dai be musa masa cewa bayaso ba ai toh "Alhamdulillah zai sau'ko ne idan ma fushi yayi.

Da abin Anty yayi yawa ne sai Abbah ya yanke shawarar sanar da mahaifinta halin da ake ciki, beyi 'kasa agwi wa ba ya shirya yatafi kano musamman ya je domin yakai 'karanta agurin mahaifinta Alhaji Muhammad, abinda be ta6a faruwa ba kenan tun farkon auren su sai awannan lokacin.

Yanzun ma yaga abin nata yayi yawa ne shiyasa, dan ko kunya bataji ballantana tsoron Allah take furta maganganu marasa kan gado ciki harda alwashin kisa akan wai inhar suka yadda auren nan yayiwu.

Ran Alhaji Muhammad ba 'karamin 6aci yayi ba da yaji abinda Abbahn yagama zayyano masa, tun ma kafin Abbah yabar wurin yafara masifah yana nunawa mahaifiyarta illar rashin hankali da kuma 6ata rayuwa da halayyan yaro tun bai je ko'ina ba, yace wannan rashin hankali har ina, maimakon Abbah da za'a bawa ha'kuri sai ya zamana shine ke bawa Alhaji ha'kuri gashi girma ya kamashi yanzun sosai harma baya fita harkan kasuwancinsa sai de a jagoranceshi,maganar ma da 'kyar yake fizgota yakeyi tsabar ranshi daya 6aci da Antyn.

Da 'kyar suka samu ya sau'ko daga dokin fushin da ya hau, mahaifiyar Anty har sai da hawayen ta ya 'diga tsabar yanda taji hankalinta ya tashi domin fa'dan Alhajin kakaf kanta ya tattara ya dawo afa'darsa wai ai duk laifin tane.

Koda Alhajin ya sau'ko sai ya bawa Abbah ha'kuri sosai tare da cemishi idan yakoma yaturota tazo yace mata yana nemanta inda hali ma su dawo tare.

"Abbah yace bakomai za'ayi kamar yadda ya keso"

Alhaji Mahammad yayi yayi da Abbah akan ya 'dan kwana musu biyu amma Abbah ya'ki amincewa yace yana so ne yaje yaga 'yan uwan mahaifinsu"

Alhaji Muhammad dayaji haka sai ya washe baki yace " ai babu komai hakanma yayi, yace daman ma yanaso ya tambayeshi ko yajeshi 'din ashe ma abin nacikin ransa, Sai Alhajin ya 'kara jan hankalin Abbah akan kyautata mu'amala da kuma ri'ke zumunchi yace zumunchi ba'abin yarwa bane akula da ita sosai..

Fatan alkhairi yayi masa shi Alhajin daga nan Abbah ma yayi musu sallama yafita agidan yana me 'kara yiwa Alhajin godiya tare da yi musu alkhairi sannan yayi tafiyarsa.

A waya sanar da Anty sa'kon mahaifin nata inda ya 'kara da fa'din " nan da kwana biyu tasamu ta je domin yace karta 6ata lokaci"

Batayi magana ba illah wani dogon tsaki da ta ja sannan ta kashe wayan, Abbah kuwa be damu da yanda tayin ba dan shi fiye da hakan ma yasan zata aikata, transfern ku'di yayi mata a account 'din ta kafin ya maida wayar cikin aljihunsa wanda
yasan zai isheta duk wani shige da ficenta har taje ta dawo.

Koda Abbah ya isa gurin 'yan uwan mahaifinsa sun yi farin ciki da zuwansa sosai, 'dai 'dai ku daga cikin su ma sun rasu yayinda ma'danda suke rayen ma duk 'karfin su yakasa ayanzun, wasun da suka rasu Abbah yanada labari wasu kuwa be sani ba sam dan ba wani communication sosai ne atsakaninsu ba, tausayinsu yakeji sosai duk 'kinsu dasukayi abaya be damu ba yasan ko ada 'din ma ba laifinsu bane giyar talauci ce tasa su sukayi yadda suyi rayuwa dasu.

Sai ya ha'da yayi musu ta'aziya gaba 'daya yakuma yi wa iyalansu kyaututtuka sosai wanda zata anfane su tareda wa'dan da suka rage arayen daga yayu da 'kannen mahaifin nasa dukka ya ha'da yayi musu alkhairi.

Da ya sanar dasu ma batun auren Mahmud ne yatashi sunnuna farin cikin su sosai harma da dama daga cikin su suka rin'ka zubda hawaye suna masu neman yafiya daga gurin Abbah akan abinda suka aikata musu abaya.

Shima kusan kukan suka saka shi domin idan yagansu akowani lokaci tunowa yakeyi da mahaifinsa amma dole ya daure ya hana nashi kukan tasiri ya ta basu baki yana nuna musu cewa ai tuntuni komai yawuce shi agurinsa be ri'ke su a zuciya ba komai yafaru ai mu'kaddari ne kuma rubutacce ne awajen mahallici.

Kwanan sa uku tare da dangin mahaifin nasu kafin Anty ta iso wai a hakan ma sai da Abbah yayi mata 'karyan a kwana biyu mahaifinnata ke nemanta amma duk da haka sai da ta 'kara akan yanda ya sanar da itan.

Be tafi aranar ba sai washe gari sannan yayi sallama da kowa yakama hanya.

Alhaji fa'da yayi wa Anty sosai harma ya jajjada mata cewa matu'kar tace bazata kwantar da hankalinta ta zauna lafiya agidan aurenta ba toh kar tayi tunanin tana da mahaifi aduniyan nan.

Yace kuma datake wani borin hana auren bata tunanin cewa shi Mahmud 'din da ita 'yar gidan Khadijan sun fi kusa akan wata daban da takeso 'dan tan ya aura, yace wata daban 'din ma girman cikin garin lagos.

Shi aure mu'kaddari ne kuma lokaci ne, idan Allah ya riga ya tsara abu toh babu wanda ya isa ya canja shi, sannan ba'a jayayya da qaddarar ubangiji koma ayaya tazo maka u must have to accept it, karta bari shai'dan yayi galaba akanta akan abun da ba ita keda ikon sawa ko hana yiwuwarshi ba, yace da ace son ran mutun ne dashi dakansa bazai barta ta auri Yusuf alokutan baya ba saboda yasan halinsu da bambamci , amma miye dayake Allah yariga ya rubuta sai sunyi auren yace bagashi ba , ni ban isa na hana ba, kamar yadda kema kika yi ka'dan ki hana dan haka tun wuri ki maida hanakalinki ki san me kike ciki, idan har kika kuskura na 'kara jin kinyi irin abu makamanciyar wanda naji ayanzu toh wallahi Maryam kisani zamu raba ala'ka dake ,saboda ni kinga ban aurar dake ga wannan bawan Allahn dan ki ta 'daga masa hankali ba, yace wallahi da yasan abinda zata aikata kenan ma da tun farko ba zai amince da batun auran ba, amma bakomai wannan duk cikin 'kaddara ne kuma babu wanda ya isa ya gujewa tasa 'kaddarar matu'kar tazo.

Da nasiha ya kammala maganar tasa ga dukkansu tare da 'kara bawa Abbah ha'kuri yace ya 'kara akan wanda yayi tayi abaya.

Godiya Abbah yayi masa daga nan suna idar da sallahr azahar ya kama hanya ya koma lagos.

Anty kuwa kusan Satin ta 'daya a kano bayan komawan Abbah, duk da bawani da'din zaman takeji ba amma wani lokaci takanji cewa zama agidan yafi mata wai ko zata hita da taahin hankali, gashi tana ji tana gani abu na nema yafi 'karfinta abanza kuma takasa 'daukan mataki.
Chapter 51 · 0% Book details