← Book details Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 163

Sashe 1

Captain Abbas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

[10/2, 5:43 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

Luv story😍

By
*Salmerh MD*

💫 *DA BAZAR MU* *WRITER'S ASS* 💫

We are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are best among all....... *DA BAZAR* *MU MUKE* *TUN'KAHO.*

Dedicated to
*Safiyya Aliyu wakili*
(Masoyiyar asali)... marubuciyar
*MASAUQIN SO* da
*SHI NAKE JIRAH* ....on point.......
Allah ubangiji ya saka miki da mafificin alkhairi
(AMEEN SUMMA AMEEN)👏🏻

*Bismillahir* *rahmanir raheem*

Littafin Captain Abbas ba na ku'di bane, kuma ni.ban ce asiyar ko asiya ba duk kuwanda yayi kuskuran aikata hakan toh yaci da gumina kuma na bar ahi da fitowar rana da fa'duwansa.

🅿1

'Yan makaranta naga suke ta wucewa da alamar tashin su kenan daga makarantar,
daya ke yara qanana ne shiyasa mafi yawancinsu kafin ma su tashi ake zuwa zaman jiran daukan su,
wanda inka duba zaka ga motoci ne awurin suka fi yawa sai da tsirarun 'yan adaidaita,
wasu kuwa daba nisa ne dasu ba sae suke qarasawa da qafafunsu da alamar sun riga sun gane hanyar gidan dakansu basai anmusu jagora ba,
kadan daga cikinsu kuwa musamman ake xuwa dan aqarasa dasu gida koda qafan ne
,hakan yana nuni dacewa ba'a so ne suka mo hanyar
gidan su kadai......

Wata yarinya ce nagani atsaye bazata wuce shekara takwas ba,tsaye take da lunching box din ta kalar pink mai kyau ahannu.....

Atsayenta ta ke bata da alamar motsawa ko ina ga dukkan alamu itama jira take azo atafi da ita gida,

Har yara sun fara watsewa sae kuwa naga wani kyakykyawan yaro matashi ne wanda bazai haura 15 yrs ba yazo tabayanta ahankali ya lalla6o karab yarufe mata idanu,

Kokadan banga alamar razana atattare da ita ba sai ma dan dariya data yi irin nasu na yara.
sannan tadago hannun daman ta ta saita hannun daya rufe mata idon dashi ta sa ke mar mintsini mai shiga jiki

take ya bude mata idanun sannan yafara yarfe hannu

Kai ,

kai,

kai

"Haba ke kuwa dan Allah yafada kamar zaiyi kuka.

Dariya tafara yi masa tana qara kallonshi.

"Gaskiya yarinyar nan muguntarki ta shahara

Wama ya koya miki irin wannan abin ne dan Allah."

Ya fada yana qara kallon cikin idanunta
Da alamar mintsinin yashige shi sosai

Kamo hannunta yayi daniyar su fara tafiya,zuwa gida don yasan daman bayaga dariyan toh ba magana zata sake yimar ba

Al'adarta kenan ita inde tamar mugunta toh sae de tayita dariya amma ko me zai fada bata ta6a bashi amsar maganrsa

Mu wuce gida toh"
yace da ita

Na kusan yin maganinki ae badae ni kike rainawa ba.

ah ah yayah
Bakai ne karufe min ido ba"
sai yanzun ta budi baki tayi magana tana me turo bakin gaba

Toh dan na rufe miki ido sae akace kuma ki gutsure min fatata?

Kalli fah yanda kika yimin!

fuskar tausayi tayi dan ganin gurin yayi jaa sosai

Sorry yayah
bazan sa ke ba!!

Kima sake kiga wanda zai ringa dawo da ke gida.

Yitayi kamar zatayi kuka,ta tsaya da tafiyar

Miye kuma ya faru?

Bakai bane?

Toh yi haquri taho abinki daddy's angel kinga yau akwai rana,muyi sauri muje gida kar rana ya dafa mu.

Tafiya tafara ahankali
ganin hakan yasa shi yah qara kamo hannunta tare da kar6ar lunchbox din dake hannunta

Nace kiyi sauri wannan ranar fah tafara damuna.

Wae ma ni kekam da ba ke kadai kike dawowa bane?

Wato dan nazo sau daya na rakaki gida kuma shikenan kema kika daena tahowa dakanki ko?

Zanyi maganinki ae yarinyah kwanan nan.......

Bata kula maganar daya ke yi mata ba.

Sai ji yayi tafara cewa yauwa yayah yau apple xaka siyamin tana fada tana tsalle irin na farin cikinnan tana kuma nuna mai teburin fruit din dayake junction din shiga unguwar tasu.

Ke nifah yau banfitoh da kudi ba......

Take kuwa tafara kuka tana mar ihun ita kam dole sai ya siya mata bai kulata ba suka cigaba da tafiyah.

Aikuwa suna zuwa daidai gurin mai kayan fruits din ta kwace hannaunta daga cikin nasa ta qi wuce wa takafe awurin tana kwa6a fuska.....

Yasan ko mai zai ce da ita ba yadda zatayi ta bishi batare da ta ga abinda takeso din ahannunta ba.

"Maiyah"

yace qasa qasa sannan yawuce wurin mai fruits din ya kar6o mata aleda sunkai guda biyar akan anjima zai kawo masa kudin.

Dayake sun saba da mai fruits dinma sosai so bashida matsala da yaran yasan kudinsa zasu zo cas ba ragi shiyasa bai damu ba

daman kullum idan akazo daidai mai fruits din zakaga ta fara tsalle tana fadin abinda takeso asiya mata

Wataran tace pineapple,wataran watermelon,wataran kuma tace babana,ko kuma apple kamar yanda tayi nayau kenan.

Lemu ne kadae bata sha ita kwata kwata bata sonshi ma kokadan.

Kuma kullum Indai suka zo wucewa sai ya siya mata abinda yake ao din inkuwa bae siyaba toh kuwa zai sha rigima
sosai aranar

Sallama yayi apalourn kafin yatura qofar yashiga,ganin bakowa apalourn yasashi zama akan two seatern dake cikin palourn.

Ita kuwa ciki ta wuce dagudunta uniform kawai tacire ko kaya bata saka ba tasake fitowa da sauri ta nufi ledar da apple dinnata ke ciki.

Bai lura da ita ba harse data dau ledar tanufi kitchen kafin ya hango ta

"Teemah"
Yace da qarfi

Na'am ta amsa mai

Yayah wankewa zanyi neh a kitchen"

Ta tafada mar dan ita azatonta akai ne yake qiran nata.

Dawo nan
Yafada tare da miqewa xaune"

Dawowa tayi da ledar ahannunta tazo gabanshi ta tsaya

Hannu yasa ya kar6i ledar ya ajiyeh agefensa sannan yadaga hannu yakamo kunnanta daya

"Stubborn girl kike so ki zama ko"

Kuka zata fara
Ya daka mata tsawa

" oyah jeki sa kaya my friend"

yafada sannan ya sake mata kunnan nata.

Ban hanaki zama da pant ba ne acikin gida?

Wuche kije kisa kaya ni inbahaka ba zanga mai baki apple din ai.

Yarinya sai rashin jin tsiyah"

Dakuka tajuya dakin nata, taje tasako wata riga mara kauri iya gwiwanta tafito

Duk ta qagu taganta tanashan apple dinta .

Tana shigowa sae kuma ga fanni (house maid) dinsu ce itama tashigo.Kusan sa'ar sa ce itama amma zata dan girme masa kadan

"Fanni kunna min AC pls."

Yafada da dan guntun tsuka da alama zafi Ya ishesa sosai.

Ha 'ah kun iso kenan?
Matar dake shigowa ta wata qofah daban ta ke fadi

Ehh mundawo mummy tun dazu ma"
Matashin yaron ne yabata amsar maganar tata

Murmushi tayi

Sannan tace

ai kuwa najiyo hayaniyar ku dazu ina shirin tada sallah ne shiyasa ban fito ba

ehh nida wannan mara jin ne ai yafada yana kallonta.
ita kuwa ko ajikinta sai faman kokuwa ta ke yi da apple din dake gabanta.

Toh yau din kuma za aji kanku kenan"
ceawr mummyn nasu sannan taqara da cewa

"Yanaga hannunka kamar ciwo yayi ja.

Kallon Teemar yayi yaga ko ajikinta kamar bada ita ake maganar bama.

Bugewa nayi mummy

Ayyah sannu Abbas"

Shiga dakina akan mirror inaga akwai man zafi Kasamu kashafa awurin da wuri.

Toh mummy.

Yace da ita....
Sannan yamiqe daniyar zuwa dauko maganin

Bayan fitarsa ne mummy tadawo da kallonta ga Teeman
tace da ita

"yau Teemah ko kulani ma bazakiyi bako kinsamu apple ya dauke miki hankali"

Dagudu ta taso tazo ga mummyn tana da dariya dan zuwa yanzu taci iya wanda zata iya ci daga ciki kuma ya isheta,daya da rabi ta cinye rabin kuwa sanda mummy ta mata magana ne ta ajiyeshi ta taho gareta
Qoqarin hawa jikin mummyn ta ke yi
mummyn ta dakatar da ita da fadin

"a' a dakata daganan mamana bakiga hannunki bane"

Maza jeki fanni ta watsa miki ruwa sae ki zo ina jiranki
kinji "
Da gudunta tafita ta nufi wurin fannin"

Dai dai nan shima ya dawo dakin yana me qarasa shafa maganin ahannunsa

Zama yayi a inda yatashi dazu

Yarinyan nan akwai rigima mummy......

Wani abin tamaka ko?
Mummyn tafada tana me tattaro hankalinta garesa

Nan yabata labarin
abinda Ya faru dazu awajen me kayan fruits

suka danyi dariya dukkansu.

Shiyasa ai naga ta nutsu ta bata hankalinta akai Ashe rigima tayi akai sosai.

Inka ci abinci sai ka zo ka miqa masa kudin nasa.

Uhmm barin ci abinci tukunna.

Abbas din yafda sannan ya miqe ya nufi daining side ya dibi abincin dai dai yanda xai iya ci,ko takanta bai bi
Dan yasan tunda tasha wannan abin toh ba qara waiwayan abinci zatayi ba.

*Wannan kenan*
👌🏻

*Interested* ?🤔

*Pls keep following* *me* .........

Akwai cakwakiyah fah agaba😃

*Salmerh md* 😍
[10/2, 5:48 PM] Ummiyo: 💕 *CAPTAIN ABBAS* 💕

💫 *DA BAZARMU* *WRITER'S ASS*
💫

We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all........ *DAZARMU* *MUKE TUN 'KAHO*

Luv story😍

By
*Salmerh md*

*Alhamdulillah* !,
masoya. *CAPTAIN* *ABBAS* haqiqa naji dadin yanda kuka nuna soyayyar ku ga wannan littafin.hakan yasani matuqar farin ciki marar misaltuwa........kusani in sha Allahu *ana tare* 🤝

*HAPPY JUMMA'AT* *2 ALL MUSLIMS* 👏🏻

*Bismillahirah manir* *raheem*

🅿 *2*

Mintina goma ya dauka agurin cin abincin,cak ya miqe tsaye
Dakinsa ya shiga ya watso ruwa yayi sallah Sannan yayi zaman shirya jikinsa da kyau.

Abbas yaro ne shi amma sam bashi da wauta ko hayaniya irinta yarintan nan anatse yake komansa kamar wani babba.

Haka idan yayi gayu har mamaki zai baka don irin yadda ya iyah zama ya gyara jikinsa tsab kamar bashi ba.

Fitowa yayi da niyar zuwa gurin mummy,sai kuma yaganta a parlour tana kallon wani hausa movie.

Mummy dake zaune acikin parlourn

kallon inda taji motsin tafiya tayi,sarai tasan Abbas ne dan jiyo irin qanshin turaren dayake amfani dashi da tayi.

murmushi ne ya su6ce mata sanda ya bayyan aidanunta

Aranta ta ke jinjina irin tsabta da kula da kai da Abbas din
yake dashi.

Qaraso wa yayicikin parlourn amma tunkafin yayi magana sai mummyn tariga shi dacewa
"harka shirya kenan"

Murmushi yayi mata batare dayayi magana ba.

'Karaso wa yayi ya zauna agefenta

Sannan yace
"barka da hutawa mummy"

Amsa masa tayi da "yauwa dan albarka"

Sannan tajeho masa tambaya tana qara kallon inda yake zaunen daga gefenta.

"Yanzu zaka miqa kudin mai fruits dinne?"

Kai Abbas din yadaga mata alamar
"ehh"

cewa tayi
Chapter 1 · 0% Book details