← Book details Takaicin Wasu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 176

Sashe 87

Takaicin Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi kawai noor yayi yace tab yarinyar ne tana da kirki,i really want to get close to her, ina son na zamto tamkar abokin ta
Kasan ajiya dana kalle ta haka kawai jikina ya bani cewa tana da wasu baiwa
Na musamman arayuwa,she is calm,kominta a nitse takeyinshi nd think She is having deep secrets, i respect her alot to even flirt with her.
We just friends

Wani shiru naswam yayi yana mai cigaba da kallon bakin sa,
"jiya jiya kagan mutum ka fara kirkiran magangani akansa?u are mad ko?sai yaja tsaki yama ki yakarasa sauran maganan da yay niyyar furtawa ya share shi,shi dauka wa yayi noor baimasan meyake cewa ba,dan haka ya dauke kansa ma kwata kwata batare da ya tanka ba ya kara volume din tv
As usual noor baiyi shiru ba"Nashwan,
Pls Ina so in kulla alakar kawance da ita,im serious i hope its ok with u? Wani banxa dashi yy kamar baijin sa ya bata ransa sosai haka ya tsime ..
shima banza dashi din yay yacigaba da debar chapman dinsa yana kan maganansa ako oho dai"can ya kurbe sauran drink din
"..Uhmmmm KON this is amazing!..try it..ya kashe mai ido daya yana mika masa kofin da sigar wasa Hararar sa kawai yayi yacigaba da abunda yake yi
Gashi ransa ya mugun biya da qamshin drink din,cos it look delicious koda daga yadda yake qamshi ga wata rabar sanyi datake turiri duk ta mamaye glass din

****
Tun daga ranar sai yafara saka musu ido,shikuma noor ko nashwan yaso kobaiso a ko yaushe suka zauna sai yayi masa maganan zairah kuma kowani lokaci he is alwys complimenting her
Musamman inta kawo musu abinci

Itama Tun bataso harta fara yawan sake masa sanyin murmushin ta dan nuna masa tana jin dadin yabo da santin shi akan abicin ta

That her cute smiles da nashwan ya mugun tsana batare da yasan dalili ba Shi baimaga dalilin ta nayin wannan sassanyar murmushin ba

Shiyasa A kullum in tagama serving dinsu sai yay maza yace mata leave,sannan tana bada baya sai sufara fada da noor khalil

In Noor yace
I really love her warm smiles

Sai yace warm smiles ko?ina dai dada tuna maka cewa she is a maid.

Noor sai ya masa shiru alamam bai damu ba,to in yaga noor bai amsa shi ba sai ya shiga maganan zuci shikadansa yana fada dakansa

"Yes she cook well "her deserts,the cakes,omg the drink awajen sa girkin ta is one to die for,yasan shima yana mugun mutuwa ma dandanon abincin ta
Infact ji yayi ma hala bazai iya rabuwa da shi ba.

Shiidai Kawai dai baison yaga wani yana janta ajiki ne ko ana kallon ta,baison hakan har cikin ransa amma baisan meyasa ba,sai ya bari kawai akan cewa ai bautar datake masa aikin tane daya kamata tayi masa nothing special there to think abt

Saidai rashin iya daurewar sa in noor yana yabata shiyafi komi takura ma zuciyarsa ayanxu
Wani bin yanaganin yafi karfin sauke kanshi yace mata koda"sannu ne"
Wani bangare na zuciyar sa kuwa
Tambayar sa yakeyi kullum akan meyasa bashi bane yake yabawa take sakar masa wancan sasanyar murmushin?"..Ya kuma ce ma kansa meyasa ma zan yabeta?Sai ya dan lumshe idanun sa ya jingine bayan sa da chair"..naaahh im more than that..nafi karfin ta,i think she wanna use her innocence to seduce my mind!

Can ya dawo da brain dinsa daga tunanin ya dube noor,nan ya warware daga tunanin ta ya bude musu sabon shafin hirar business din dake gaban su a gobe.

Zairah tunda ta shigo dakin ta tayi sallan ishai ta lume akan gadonta zuciyarta cike fall da tunanin wannan mutumin..

A duk yadda taki amincewa da kowa she cant deny the fact that wannan mutumin mai saukin kaine kuma tsakanin sa da Allah yake bata darajarta na dan adam wanda tunda tafara aiki anan bata taba samun irinshi ba

Suna magana suna komi amma sam bata iya jure yin wata hirar minti biyar dashi,sabida
Ta lura dan anace ne shi musamman inyana bibiyarta a kitchen.

Itadai hutunta tunda yazo nashwan baiya kirarta suje wani waje tare,day by day har salon ayyukan ta nadachan suka koma yadda suke
Daga ta kimtsa wajen sai ta dafa abincin sai dan aikin waje da already ya riga ya zame mata jiki.

Washe gari sassafe suka fice danko abun kari basuyi ba,its seems the meeting dint end well dan nashwan shikadai ya kama hanyar gida ya dawo kamar yadda noor khalil ya bukace shi yayin as his therapist..

Koda ya shigo hanyar falo ya nufa Komi na gabansa bibbiyu yake fito masa tsaban baijin kansa adaidai,sosai ya fahimce cewa he has anger issures,
kawai shi baya son kuskure ne ko yaranta,kuskure kadan sai kaga yanxun nan ya fusata nd he cant even control his anger in ranshin ya baci.

Cike da zafin nama yayi jifa da malafan suit dinsa akan kujera ya wuce direct yaja daya daga cikin dining chairs din ya zauna

Wannan royal title na KON da ake so alaka masa sai yake neman ya hanasa yawan jin sha'awar daga muryan sa yana kirar ya mace daga nesa,beside arayuwr sa banda xalihar babu wacce yake iya kiran sunan ta kuma yay ta maimaitawa daga nesa.. no matter what,but yauma ji yayi bazaima iya kirar zalihar ba

Wucewa yayi kitchen ya turo kofar kamar barawo
Yana dan lekawa yaga shol baiga kowa ba kuma tamkar ba adaura komi ba"To Ina ta ke?..Allah ya sota yana juyowa yaci karo da ita abakin kofar ta fito kenan daga daki zata shiga ganin sa yasata dauke kanta kasa"welcome sir".
Wani kallo ya mata ya mugun hade rai ya wani fizge jikinshi ya wuce dakinshi batare daya amsa ba"..

Har ya kure bata dena bin bayansa da kallo ba sabida aduk abinda yakr mata sai taji jikin ta yana yawan yin sanyi,acikin jikin ta akwai wani yanayi na musamman datakeji in taga yana fushi da ita musamman ma in ba akan laifin komi bane irin na yanxu..tana shiga ktchn haka kawai sai taji ta damu

kirjinta sai bugawa yake sai ta dingaji kamar ma gajiya da aikin tayi me gaba daya kamar tana so ta bari

Rufe kofar kitchen din tayi ahankli
,sannan ta dubi agogon dake bango its just 4pm na yamma Jikintane ya bata hala yau zai so yaci abinci mai nauyi dan haka tayi masa hadadden tuwon semovita da miyar busashen kifi,dan kadan tasaka ganyen ogun ghana sannan ta shirya masa sassanyar water melon juice ta hada masa gaba daya
Iyashi haka nan ta tattaro afaranti za takai masa dakin sa
After 15 min of knoc
Akace ta shigo.

Yana ganin ta da tray batare daya tsaya ya kalle meta kawo ba ya hade rai yace whats this?
Tace ur meal sir

Kamar mai aljanu ya tashi zaune yana kallon ta...yace "Ki mayar,i want sumting else.
In a very rude manner ya fada hakan kamar yana fushi da ita sosai, batace uffan ba ta juya da abincin tayi waje

Zama yayi akan couch dinsa ya jawo system ya dora akan cinyarsa,kafin ya fara taba komi sanda ya dakata ya lumshe idanun sA ya shiga sauke
4 deep breaths kamar yadda noor yace masa in yanayi in yanajin bacin rai
Budewa lap top din yayi yafara caccakawa kamar babu gobe..

A wannan tsaikon lokaci zaira saida taci ubanta da aika,dan abinci ma kawai saida tayi kaikawo abincin yafi kala biyar yana maidata,tayi kumburin tayi saibin tayi juriya amma tun four suke abu daya har six pm ya shigo baima san tanayi ba saida yaga kamar za'a kira magrib sannan ya amince ya amshe wani fish stew sauce with french cut na yam data kawo masa a karshe..

A hnkli take takawa
For some reason she was soo emotional a lokacin,
tafarajin haushin komi taji ma komi na nshwan yana bata takaici sosai

Yau tun Kafin ta idar da sallahn magrib har yagama nan ta tahota tattara komi zata bude kofar kitchen ta aje
Wani buga babban yatsar kafarta tayi da jikin karfen kofar tsaban zafi saida ta xube kasa bata san sanda ta fashe da kuka mai karfi ba wani turus tayi akasa tanajin tagaji da komai na gidan
...kamar da wasa taga Kukan yaki yanke mata,zuciyrta saiya cunkushe harta kasa sanin akan meyema take tsanan ta kukan nata haka

Kuka takeyi da zuciyarta Ko jin alaman bude kofar batayi ba ta tsinkayi muryan mutum akanta.."Hey Whats wrong?

Da sauri ta dago kanta Ganin noor yasa tayi marmaza ta mike akasan floor din tana goge hawayen ta yace 'a' mutumiyar Kuka kikeyi ne?waya buge ki

sunkuyar da kanta cikin sauri tay Tace a'ah babu kowa..sai tayi shiru..dama na twisting kafa na ne abakin kofa,kan ta gama rufe baki taga noot har ya taho wajen da ta aje kafar ya rusuna agaban ta da sautin damuwa "oh im so sorry to ingani?noor
Yana kama wajen zairah ta firgita ta kwace kafar,wani kallo yabita dashi ya dauka ko zafi ne amma harga Allah taba tan dayayi ne bataso ba Cike da azama Tajanye jikinta a kusa dashi 'tace im fine"sai ta wuce bakin sink ta kunna ruwa ta hau dauraye kwanukan ta yanata lura da ita,new dinner oder yaso yabata amma ganin yanayin ta yasa ya danne yunwar dayakeji ya daga mata kafa aransa"..yana daf zai juya ya bar wajen sai ya juyo kadan yace
Mutumiyar pls inkin kagama ki hado min drink dinkin nan mai dadi ko?batare data juyo ba"Tace ok,sai tayi shiru..ganin ya tsaya bai tafi ba yasa ta juyo din a hnkli tace mutumin najika fa!..yay murmushi yce ok to inajiranki sai ya fice
Abinsa...wani abu taji yana tsikarar ta na damuwa da kunci aranta, Ko karar rufuwar kofar ne ko yaya ne itadai kawai tasan taji karar wani abu dayadan razanata sai kuma taga ta kara fashewa da kuka sosai harma ta dakata d wanke wanken taja gefe guda tanayi

sanda tayi mai isarta sannan ta dawo tacigaba da abunda takeyin
15mint later ta sauko falo hannunta dauke da tray din cinnamon pancake da fresh mango juice fuskam ta fayau kamar batayi kuka ba

Noor tagani zaune shi dayansa yana kallon tv.

Yana ganin ta ya fara murmushi
Thank you zaira
Yafada yana tayata ajiyewa.
Chapter 87 · 0% Book details