← Book details Takaicin Wasu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 176

Sashe 102

Takaicin Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

I will bear a ring wth her name for the rest of my life dan kowacce macen da zata aure ni daga baya tasan cewa zairah Ita kadai ce take dani..Duk wata wacce zata aureni bayan ta i will own them,thy will neva own me he look damn serious dayake fadar hakan
"mahdi yce nashwan kasan me kake fada kuwa?ni fa ban fahimce ka wai wacece ma zaka aura kwanan dakake fada
nashwan can u..
,yay saurin dakatar dashi,i knw i knw,ba nala ko hanadi bane,nima bansanta ba tukum amma im nazo aurantan zan sani,mahdi ya kada kansa yace as u wish kon,sannan ya mika masa file din to gashi kayi signing cewa alkwarin auren is valid,nashwan ya karba ya zana tambarin signaturen sa,mr mahdi ya hada duka acikin jakar sa ya mike tsaye yana duban nashwan din yace to ni zan wuce
In har kana so ka cimma nufin nail khaleepa Kayi kokri cikin gaggawa ka hadu da mutumin nan,dont waste anytime kaji,yace ok.,safe journey,mr mahdi y dau yar jakan sa ya fice.

After 30 min zaira ta dawo dauke da abincin sa harta gama serving dinsa yaci basu ce ma juna komai ba.

Yau tun 9 ta tattara ta koma dakinta
,nan har tayi bacci da mamakin rashin jin wani hayaniya ko duriyar noor agidan

Washe gari sassafe ta farka,taga gidan wayam ko nashwan din ma bata ji motsin sa ba bare noor gashi wayarta ya dawo jagwal koda tana da number sa ma lallabawa takeyi bare tace zata kirasa throuout haka tayi xaman kadaici ranan,ga wani uban sauyin yanayi da atmospher ranar tazo dashi na sanyi sosai iska yake kadawa gari yana dada rikicewa da rairayin hadari sai dai bai wani taso ya rufe ko ina ba

Fannin mayor da boss khalepa kowa nacin kafar juna amma a fili basa taba nunawa duk dama sunsan da cewa sun balain tsanar kansu..

Shida kansa ya kira mayor yayi masa zafafan habaici akan mummumar birthday partyn da su abhay suka hada dan a girgiza kima da mutuncin dansa yana mai aibata yayan south song da sunan tabarbaru marasa tarbiya,
Sosai ran mayor ya baci duk dama bai tanka masa akan hakan dayace din ba

Tin bayan partyn da suka dawo gida to bakaramin zuga nail
Abokan sa sukayi ba,musamman lateefa data san halayyar su abhay,wasu abubuwan ma nail bai lura ba amma su suka totottona suka harhada suka haukata sa da fushi da jin kishi,nail yafi kwana biyu baya iya samun bacci sabida tsaban tunanin abunda ya afku dashi a wajen birthday,kuma har yau hoton da nashwan ya musu bayan sun jefasa a ruwa shiyake yawo in major chanels,

Nail bai taba tsammanin abun ma zaiyi tasiri har haka ba Jama'a har sunyi concluding cewa nail abuge yake,kowa yafara tofin Allah tsine suna cewa tirr nail ya zama musu shugaba anan ma sosai nail yayi asaran mabiyan sa nala kan ko ajikinta daga sun fara xata fara bugamusu kirjin xata rabu dasu akan nashwan
Duk dama fada ma takeyi da nashwan din akan kin tsayawa akare partyn dashi dayayi,
Bt She got alot of expensive gifts daga wajensa wasu ma har yau bata gama bude su ba kuma duk wanda ta bude saita watsa a social media acct dinta ko dan hanadi ta gani ta haukace
,zazzafar fadar dake wakana a tsakanin su da cakke cakken maganan su ya dada tabbatar ma nail cewa eh lallai da gatse aka walkanta sa awajen partyn nala,dan har yakaiga hanadi ta gaya musu cewa trap ne kawai kuma sun fada,nala sam taki yarda amma nail yy fama da wani turirin kunya da bala'in haushin kansa,har yafada ma baban shi labarin abunda aka masan awaya ma kawai yafi sau ashirin,boss kullum acikin lallabarsa yakeyi sabida yana tsananin sonsa yana yagalgalashi
Waishi magaji,da balain confidence yake maganan sa
"Calm down my boy,
Kada ka daga hanklinka ni boss khalepa ni na haifeka jini na ne ajikin ka,ba nashwan wamako ake magana ba?ai In yasan wata bai san wata ba,yace my son, dokana ne a gidan nan kuma akanka,"daga yau duk wanda ya maka wasa da kankara kai sai kamasa da ruwan zafi...Cikin kwana uku kacal akayi wannan cakwakiyar amma saida suka cika ma nail kirji da salo salo na nauikan mugunta,har ya zamto nail baida wani babban buri ayanxu illa ya kwace north awajen nashwan koda kuwa zai yi kisan kai ne.

Fannin su abhay da su hanadi kuwa bakaramin fada suka kwasa a hannun mayor ba
Yace kuma su guji ranar da zai dawo duk se sun kwashi kashinsu a hannun sa..

Dalilin hakan yasa yace maza lady jasmine ta tattara ta dawo gida ta same su,so in 2 weeks she wll be back,shiyasa south song babu zama ko kaje ma da wuya kagansu,ga metings ga tsare tsaren duk wani abu da suka san zai cece su daga fuskatar fushin mayor,haka zasu fita aiki early su dawo vry late
Noor ne yaje taya hanadi wasu ababen tsaban yadda nata masifar yay muni,dan mamanta bakaramin azalzalan ta tayi ta taji labarin shigarsu da sukayi da kawayen ta awajen partyn ba

Kin dauka ke karamar yarinya ce?
Ko akace miki dukiya haukace?
To wallhy in baki nitsu kin kama girma da mutunci makanki ba,ko nashwan ya aureki mutanen dake karkashin sa bazasu taba daraja ki ba"..

Kullum sai ance musu kuje ku duba tarihi,mu bahaka wayewar take ba,koni nan danake son kwaras banyi yawo tsirara ba shiyasa har yau mukeda kimarmu

Hernadi ji tayi kamar zata mutu ranar,duk haushin ta hada ta sauke akan bingurl musamman data bata labarin cewa ai taga xaira ta shiga dakin nashwan adaren ranan kuma ta dade bataga ta fito ba

Abun yana ran Hanadi,amma babu yadda ta iya tasan tunda mayor ya kirasa akan hidiman partyn ma bai dauka ba to tasan da wuya in bata kwashe maruka ahannun sa inta kai masa wannan maganan Ba,kawai saita bar maganan a matsayin shara cos aranta ta bari akan cewa nashwan ya riga ya tsangame xairah,sai dai fa ita sosai Allah ya bata kishi,time to time sai ta tanbaye bingel cos she neva trust anyone if it comes to nashwan

Ga lady j tace mata tun kafin ta dawo gisa,marmaza hanadi ta sauya wardrobe kayayyakin ta kaf su dawo na mutunci
Obviously arabin gowns,turkish suits,falazos nd hijabs,and kimonos
Aikuwa babu bata lokaci tayi list ta tura dan sunsan bakaramin kura za'a tada musu in aka dawo ba.

Washe gari da sassafe zaira tana kitchen tana stir frying wani ganished chicken sauce wanda zata hada sa da basmati rice data girka.

Noor ne ya doka sallama a hankli yana dube dube ya shigo ya tsaya ta bayan ta,jin motsi zairah ta tsorata firgit ta juyo,suna hada idanu sukayi chuckling atare.

Sorry i scared u..
Yana gama fada ya kwace cokalin ya shiga tayata gauraya miyar.
Xaira tanata kallon sa tana tuna jiya Hankli ta furta
"Noorin ala noori ka tashi lpya?Murmushi yay sannan yace mai lashe abincin maza kwata kwata jiya bamu hadu ba .

Tace ai nasani tsoron kuliya ne ya hanaka fitowa,"cikin basarwa yana murmushi yace nop
Tsokanan ki nakeyi amma bana tsoron kuliya, kamar yadda kike tsokanta cewa bakijin haushin dan uwana..,gyara tsayuwarta tayi agefen sa salon rashin ganewa tace amma waye dan uwanka danai ma haka?yay shiru yana ta stir frying dinsa sanda miyar ya fara kamawa zaira
Ta rage wutar kasa kasa tace scary cat inajin ka fa?tasha mamakin ganin yadda ya sauke ajiyan zuciyar sa kamun ya dasa mata serious looking eyes dinsa anasa.

Zairah u are one of my best friends now inma baki sani ba.
Se wayanda na shaku dasu nakuma yarda dasu suke sanin ina tsoron kuliya..

Yakamata kidena boye min damuwar ki haka nan

,abubuwanda ya faru shekaran jiya tsakanin ki da nashwan banji dadi ba am a therapist u knw,kuma nasan kina cikin damuwa"..Na lura dake komi sai kina shanye wa acikin zuciyarki but
U cant help urself alone, Nidai na yarda da ke Kuma a matsayin yar uwata abokiyata na kwarai na ajiye ki In har zaki iya kibani matsayi daya a zuciyarki,matsayin dan uwa ko abokin ki,in zan samu duka kuwa zan jira koda nan da shekara dari ne,bt pls can u share ur prblem with me?

Jikin zaira yayi sanyi ta sauke ajiyan zuciya da kanta kasa tana kallon kasan tiles da yanayin damuwa a yanayin ta

"No no,karki takura kanki sai kin fada min if its personal,i also have trust issures kowama yana dashi Is very normal to have secrets sabida kowani dan adam a duniyarsa yanada bukatar sirrinta damuwarsa da nasarar sa.

Amma kisani cewa Nafi ki sanin waye nashwan,tare muka tashi dashi har muka mallaki hanklin kanmu.,i knw Its must be vry hard for u to work for him sabida yanayin sa.. u have to tell me sumtin
.atleast..Nidai Ina son in cire zargi araina na cewa nashwan bai daya daga cikin wayanda suke sakaki cikin damuwa..dan Allah ki tabbatar min da haka?ya riko hannun ta yana ta kallon ta dagasken gaske,wani sanyi qasaita ne mai cike da natsuwa yake tattare da yanayinta ayayin da noor yaji dadi da yaga yau bata kwace hannun tan ba,gwala gwalan idanun ta masu haske tasa a nashi dan kuwa bakasafai noor yake nitsuwa haka in zaiyi mata magana ba.,ganin kamar har cikin zucuyar shi yake furta wayannan kalaman yasa ta tsaya na yan mintina tana ta kallonshi,can ta sauke da idanun ta kasa cikin sanyin murya ta fara masa magana a nitse cikin sanyin murya tace"Nagode da jin haka friend,Kuma insha Allah zan fada maka damuwata no one has eva cared abt me this much like u do'..Jan ajiyan xuciya tayi...sai kuma tadanyi shiru,jin takasa cigaba da maganan yasa shi kara nitsuwa yadada maida hanklin sa kanta,she look restless duk tunanin ta kar ta fadi komi azo a asamu rashin fahimta ne,what if nashwan yaji haushin kalamanta akansa ya koreta?koda can ma tasan most of abubuwan dake faruwa da ita awajen nashwan in aka bibiya mafi yawancinsu ita take jangalowa,wani wulkancin san duk da laifinta aciki.

Gashi yau bataso Ko kadan tarasa aikinta,a wannan lokaci tayi alkwarin tara wasu kudaden da zai cika mata burinta akan samun lpyar maman ta ne.
Chapter 102 · 0% Book details