← Book details Takaicin Wasu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 176

Sashe 16

Takaicin Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

all thy life basa iya jure zaman lpya a tsakanin su,tun akan maganan arziki suka fara dan banzan competing da juna suna caccakar juna suna buga kishin jahilci sannan duk abunda daya tayi sai daya tayi wanda ya fishi kayan sawa gwalagwalai motoci da jirage kwarkwasa da kwalisa abun ma har ya zama kamar zasu illata kansu dan yau idan hanadi taje plastic surgery aka ja kumatun ta to gobe zakaji nala taje anja goshin ta.

Sai kamannin dirin halittar su ya dawo kusan daya xak zak dukan su in sun bada baya bazaka ma tantance ba sai dai wanda sukeyi dominsan bai ma san sunayi ba
But is still to nala's advantage dan sosai yake kawance da ita,nashwan yana son kula nala sosai sabida arayuwa yana son abinda kowa baya so a familyn sa kuma yakan tsani abunda kowa yake so a familyn hakan tasa hanadi bata iya daurewa in nala tana waje itama tana nan to dole ne suyi fada.

Fannin nashwan kuwa tunda incident din kauyen nan ya faru yakejin kamar wani abu yadan sauya ajikinsa amma rashin bada muhimmcin ma abu naturen sa ne so baima bada hanklin sa wajen son ya gane komai ba,kwana biyu kawai dai zaka gansa so quiet kuma baya son shiga hayaniyar jamaa,sau dari za'a aje abinci a dinning dinsa sau goma za'a dawo a kwashe bai taba komai ba

Abun ya dame kowa amma babu wanda yake da liver tunkarar sa dan ko banafsha daya sake ma yasan ita sam bata iya takura masa ne intaga yayi shiru sai tayi shiru in taga ya damu sai ta kawo abun nishadi tasa shi dariya duk shakuwar sun nan bata hirar minti talatin da shi tana gamawa sai ta tafi abun ta.

This time ita ma shirin partyn take shiyasa baya ganin ta sosai kuma sosai abubuwa suka cunkushe masa a zuciya, babban damuwar sa shine baima sam menene mafarin abun ba
Shi kawai jinkansa yake a mugun dame hanklin sa yaki kwanciya,kwana biyu ko business dinsa bai duba ba and Sabida mood dinsa bai cika barin wayar sa a kunne ba.

Kowa yayi noticing hakan sosai amma ba wanda ya tambyesa dalili sai bayan kwana biyu da hajiya fulani tayi shahada ta kawo masa ziyara har dakin sa ta same shi yana kwance akan kujera yayi shiru..

"Bayan tayi sallama A kusa da shi ta xauna fuskan ta dauke da murmushi irin na yarta banafsha mai saurin kama nitsuwar sa gyara kwanciyar sa yayi yace"Ina yini hajiya..
Batace uffan ba Ta fadada murmushin kan fuskarta can Tace KON ranka shi dade,at same time tana mika masa wani haddaden kwaryan pure milk na asalin tatsar fulani madarar fal ya cike kwaryan wanda yaji zanen gargajiya yay balain kwankwasu wa ya fito ras dan karami qwanin sha'awa.

nashwan baiyi wata wata ba ya mike zaune ya karba ya kauda faifayin
,tsafta da kaurin madaran ya balain ja masa rai dan shiya sashi yayi bismilla cikin zakuwa ya kai bakin sa ya hau kurba,its taste good.dan ko ita data san yanayin cin abinci sa kullum a taba sama sama yau taga bambanci dan sosai yasha wannan madarar.

Tanata kallon sa yana sha,Haka kawai taji ya matukar bata tausayi shiru tayi daga bisani ta kamo ytsun hannun sa a nitse Cikin sassanyar murya tce "Nashwan?yace uhm"tace Are u ok?i mean kwana biyu kamar naga baka sakewa,".our kon u look so worried,zaka iya fada min fa karka manta,
yanayin fuskan damuwa data sa yasashi yai kwafa kamar dai zaiyi murmushi sai kuma ya fasa ya tabe bakin sa a miskile yace"...dama Abunda ya kawoki kenan?wani garas taji dirar maganan amma sai ta daure ta amsa Tace eh.

hannun ta ya riko abazata yace
Hajiya fulani kincika damuwa,ni lpyata lau bana cikin damuwar kome I am fine"

Tayi shiru batace komai ba kuma bata kalle sa ba haka shima,dan shiru ne ya gifta wajen can wani karamin murmushi ya subuce masa aransa yace wato mutanen nan bazasu barni bako?

"Yace to tashi mana ki tafi kinsan bana son surutun ki..ta kalle sa a saukake amma sam bazata iya boye damuwarta akan sa ba, ba musu ta mike zata fitan.Yace Here..ya mika mata kwarya da sauran milk din dan kadan aciki
,hannu ta mika tana karba ya dan rusuna kai yace "thank you..i like it"

It mean alot to her dataji ya furta hakan so har ta bar dakin tana jin dadi aranta duk dama bataso rashin gaya mata damuwar sa da yayi ba.

Labarin visit din kaf ta kwashe ta gaya ma kakarsu hajya turai so Bayan kwana biyu suka hada kai suka sake masa irin madaran sukaje dashi suka dame sa sosai har saida ya amayo zancen

Yace hajiya nakasa mancewa da ranar
Bawai ina tuna wani abu bane amma tun da abun ya faru naji hankli na ya ki kwanciya im so worried for nothing

Calmy suka saurare sa,so bayan ya gama Atare suka hadu suka nitsar da zuciyar sa da kalamai masu dadi

Hjya fulani tace kawai ya mace komi yashiga hidaman shirye shiryen party kamar yan uwan sa

Ita kuma hajiya turai tace ya rinka fita a site dinsa yana shawagi a waje ko a garden yana shan iska cos zaman kadaici da shiru ne yakan kara masa damuwa.

Shidai baice musu komai ba har suka fice ya koma yayi kwanciyar sa abunsa.

Fannin zaira kuwa wahalan yau daban ta gobe daban duk dama BMF basu daga maganar ba amma yan kauyen
Su sun matsata,thy make her life so difficult a boye ma afiya take taimaka mata da abinci suci da wafiyya duk an nace ana so lallai alaka musu sharrin maita dan a walakan tasu.

Zaira batajin dadi sam,wafiyya tana ta lura da yanayin ta kwana biyu is asif she is depressed ta gaji da duniyar aganin ta meye amfanin wahalar neman ilimin datayi a birnin in bazai amfane su ba.
Maman ta data sha wahalan bara ta biya mata karatun gata nan yau sati biyu har ana neman shiga na uku bata samu ta nemo mata magani ba.most time In ta dubi wafiyyar sai taji tayi loosing appetite din ta komin yunwa dake cikin ta sai taji tama koshi.

Wafiyya kuwa tana ta kokarine ta danna zuciyar ta tayi calming kanta koda ma zata warke amma ina abun yaki,ita tunda taga danta ya girma ya zama cikakken namiji lafiyyaye sai ta soma dora burin duniyan nan akan sa,sai dai intayi tunanin kullum abun karewa yake abanza tanada tabbacin in har tayi kuskuren nuna knta ma mayor Aseem to ba shakka seya kashe su ita da danta,so she became hopelessly sad sai zazzabi yayi ta shigarta yana nakasa ta.

Gashi sam Bata san abunda zai taba mata zairah amma wannan abun yaso yaci karfin ta,wani bin tana gani zaira din zatayi ta buge buge agefe agefe dan ta lura kamar Afiyya tana da gulma da baki most time zairah is not happy ko da ta taimake su,Amma dai suna tare dan sosai take amfani da ita tana neman aiki acan cikin gari ta birni nesa da kauyen dan burin ta ne tayi kudi ta dauke maman ta subar nan.

Acan southsong mansion kuwa komai daidai yake tafiya face nashwan daya yayi banza da shawaran da tsoffin nan suka basa akan ya rinka fita.

Hakan yasa duk aka masa taron dangi a gidan harda mumyn su lady jasmine akan cewa ko body gurds da maids abari asaka a site dinsa ai ko babu komai zai na jin motsin mutane kuma giving oders here and there ai zai sa shi surutu

Tsaf suka gama kulla hakan kowa ya amince harda banafsha,hanadi kam tunda akace za'a sa maid a site din nashwan ta nada kanta wakiliya
Har tana da female candidate din ta wanda ta zaba a cikin maid din ta data fi yarda dasu.

There is this particular maid da ake kira da suna
BINGEL a shekaru zatayi ashirun da biyu to wannan yarinya ita ce babban shakikiyar hanadi a masu aikin gidan,bawai dan ta iya aikin kula da ita ko goge goge ba,tana da kazar kazar din amma bingel kwararriyar shedaniyace wajen iya gulma da munafurci da bin diddigi,tun hanadi tana kin halayen nata harta tazo ta saba sabida bingel ce take gaya mata labarin abunda ke faruwa da kowani mutum a gidan in full details komi daki daki take fada kamar a gaban ta aka yi sannan tana da banzan halin kyashi da fadi ban tambaye ka ba.

Wasa wasa hanadi ta saba da bingel komin ta bingel,itama bingel uwar jakuna duk inda hanadi take zakagan ta tana sunne da bakin idanun ta wai tana fadanci,altho bashi yasa take ragar mata ba,hanadi ta iya taka mutane badama taga maid to aika akan aika she do oder bingel nan da can kuma dama duk mace me mugun son girma tana da walakanci ga tsinannen rigima ko hausan ta ma da slangs yake fitowa in bingel din zata kira sai kaji tana sinne murya tana
Cewa "BINGURL"
BINGIRL seka rasa shin suna ne ko kalman turanci..

Ita kuwa bingel abun dadi yake mata takan dauka bingurl da hanadi take fada sunan ta da turanci kenan kuma dama tana son rayuwar karya da fafa shiyasa ta iya babatu ita sam bata je makaranta ba tanan dai jahilin wala niyyar karatu.

Tun da akace za'a lankaya ma nash body gurds da maid a dan dole hanadi ta fara yi ma bingel training da kwaje kwaje tana koya mata abubuwa

Duk wannan kullin ana tayi ne amma nash kam bai sani ba,abhay da abhi ne ke dan tsakurar sa da gulma dake suna dan wasa sosai in abun ya taso,duk tsoron abunda zaije ya dawo ya sa ba'a same wanda zaiyi jarumtar gaya masa maganan boro boro ba.

Ana saura sati guda mayor aseem ya dawo domin ayi partyn shirye shirye ya tsanan ta kan kowa yayi zafi.
Dan ba partyn kasuwancin su bane kawai,Party ne da zasuyi amfani da shi su cimma muhimman abubuwa arayuwan su nan gaba
Chapter 16 · 0% Book details