← Book details Takaicin Wasu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 176

Sashe 6

Takaicin Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bahiyya Tace nima wasim ya bani labarin abunda ya afku tsakanin mazajen mu wafiyya
Nidai babu abunda zance sai Allah ya sassauta mana
shikuma Aseem Allah yasa ya gane..ya cuci kansa yaci amanan abokansa dn badai mu ya cutar ba.
Wafiyya We must get intouch da lawyar dayace zai bincika miki inda aka aje nashwan dole ne musan dukanin wayanda suke bibiyar rayuwarmu dana yayan mu da sharri

Gyada kai kawai wafiyya tayi batace uffan ba..

Daga nan Sosai sukan zage sukayi kukan bakin ciki mai tafe makokin mazajen su da uwa uba rudanin rashin sanin mafita da makomar rayuwar su Sunfi sati guda cikin jimami da sassaita zuciyan juna har Allah ya sa abubuwan suka zo sukayi musu sauki.

Bayan wata biyu bahiyya ta yaye yarta zairah daga nono inda wafiyya take gwawarmayan samo musu labarin asalin abunda ke afkuwa daga bakin lawyar qwamnati
,akan haka sunsha wuya sosai,dan sai kusan bayan shekara guda suka san asalin meke faruwa ahakan ma da kyar suka samo kan labarin rayuwar mazajen sun wanda tunda sukaji ya haddasa rashin kwanciyar hankali mai tsanani a zuciyoyin su..

MAFARIN LABARI.
_Kerala bhavanam the dark millatary jungle Early:1963 in old columbia!_

Baqin Jejin kerala bhanavam jeji ne wanda ake masa lakani da jejin baqar mutuwa,ba a masan ainihin mazaunin sa a duniya ba amma a canki cankin masanan geography da kimiyya sukan ce ana samun sa a daidai kan 00000.1000°NE of the earth imaginary line on the slighest corner of the world eqota in between kasashen colombia da mexico wani bin wutsiyar jejin yabiya har cikin kasashen india,brazil da korea,shinfide yake a cikin kasa can kasar hanyar magudanar babban ruwan tekun pacific ocean inda in dan adam ya tsinci kansa aciki to tabbas baya kara saka ran dawowa duniya da ransa,acikin wannan jeji babu komai illa halittun Allah wayanda mutum baisaba ganin irin su ba,bishiyoyin su da ciyawai da dabbobin da kwarin da suke rayuwa a wajen basa kama da wanda idanu ya saba gani,thy are xtremely dark green vegetations,very soft,succulent and huge,some r deadly poisonous wani ganyen ma kana tabawa mutuwa zakayi atake
,hakama cixon kwari dabbobin su babu maganin sa sai tsananin azaba da mutuwa,shiyasa jejin ya tara sunaye da inkiyiyo kamar "the devils palor,ghost well,
evilsanctuary,and death forest,. domin duk wanda yaje baya dawo har karshen rayuwar sa.

A Da can ba a ma iya shiga jejin kwata kwata sai dai kallo daga nesa ta naurar leken asiri irinsu locomotive chips da high grade drones.

Amma naci da bincike irin na turawa yasa aka zo Wani zamani da gaggan sojojin duniya wanda suka kai makura wajen sanin sirrrin aikin su, masu tsananin ilimi,fasaha, karfi da jarumta..nd most of them are marine
raiders,army comandos,superior navies da dangerous mayors daga sassa sassa na na kafafen sojoji daga kasashen duniya daban daban.

Acikin jejin suka kafa base base inda
Kowanne kasa take da cibiyarta da makafarta.

Anan ake hade haden world most dangerous war deals,deadly ammunition exercution hatta yaki da aliens wanda bai shafi mutanen duniya ba anan ake hada shi.

Shiyasa duk wani sojan daka gansa a jejin yakai ne kuma ka dauka kawai babu mahadin sa
Kayan yaki nauoriri Bindigogi da bomabamai dake jejin babu iyakarsu wajen inganci hatsari shiyasa awajen kowa yake amfani da ilimi da kwalkwala..

Kansu a matukar hade yake,duk halin da ake ciki bakinsu daya ne Duk da banbancin kasa aiki matsayi da yare da launin fatarsu.
Anan sojoji sukanyi shekara da shekaru basu fito ba sabida ba abu mai sauki bane shiga jejin bare kuma fita.

Har akazo Wani zamani da ilimin kimiyya da fasaha ya bunkasa, hanya ya bude ajejin sosai aka samu sassaucin shige da fice,sai dai daga nan kuma amana ya soma yin karanci,cin hanci da rashawa ya wanzu, sojoji suka soma saida muguyen bombs,naura da bindigogin su na sirri ma mugaye masu tada tsaye a duniya.

Zamani ne yaxo musu mai wuya amma yawancin sojojin dake nan ta hannan harkan ne sukayi kazaman kudi sunyi arzikin da hankali bazai ma iya daukawa ba.

Sun mance da amana da alkwarin da sukayi ma Allah na kare kasashen su,kowa ya gina kansa da rashin gaskiya,abu daya ne ya rage musu na nagarta wato Hadin kai,dan duk tsiya anan jejin soja da soja basa cin kafar juna saidai in araba abunda aka samu tare ko ayi mutuwar kasko

Tsawon lokaci ana tafiya ahakan har Allah ya kawo sauyi ma wanann yanayi sakamakon shigowar wasu jajirtaccun mayors guda uku.

Na farko shine 8 stared army Mayor Alhakeem sultan wamako.

He is a kabardian.

ya fito ne daga yankin North caucasian daga cikin hadaddiyar kabilar circassian.

Alhakeem wamako dan musulmi ne,practising one, wanda ya samo Tushe daga zuriar sultan wamako from an old nigerin tribe na jarawa,Allah ya albarkaci zuriar wamako da tsananin ilimi, rike amana,nagarta fasaha,basira da dumbin arziki.

da sana'ar Noma na(comercial agriculture) aka fi sanin su dashi tun zamanin da chan kafin suka zo suka surka da electric power generation inda suke da gaggan power industries,energy canals da electricity generation dams

Talaka a zuriar wamako shine wanda ya mallaki a kalla $200 million euros wanda daidai yake da billiyoyin kudi in za'a juya sa a kudin yan africa.

Zuriar Suna da matukar rike amana da gaskiya uwa uba ruko ga addinin Allah shiyasa sukeda dumbin arzikin da sukan su basusan iyakar su ba sai dai Allah bai wani basu tsawon rai ba

Mafi tsawon wanda ya rayu azuriar kaf shine wanda ya mutu yana da shekara 58,hakan yasa hakeem wamako ya taso babu iyayen sa da sauran danginsa altho saida ya girman har yayi aure ya auri budurwan sa na yarinta wato wafiyya ahmet wacce sanadiyar kai ziyaransu gidan marayu ya sameta ita ba taba sanin tushen ta taba amma u can easily tell that she is a swabian musamman daga yanayin Alemannic dialect dinta.
Intana magana seka na ji kamar ita balarabiya ce da yaren ya gama cinye mata baki

Ita da shi har sukayi aurensu babu wani matsala daga baya mahaifiyar sa maysam wamakon itama ta rasu.

Shi hakeem wamako Baije ko jamia ba amma yayi karatun special courses na sojoji kuma tun yana shekara 7 ya iya harbin bindiga.
Aikin sa shine Baiwar sa, dan bayan mutuwar famlyn sa hakem ya kasance cikin jajirtaccun sojijin nan na special troop da tunaninka ma bazai kai wajen ba.

Tun zuwan sa aikin soja hakeem baida abokan da ya wuce mutane biyu wato
Mayor Aaseem Assidique da mayor
Wasim kaita ..
Kamancecceniyar sunan su har yasa ake kiran su"the tripplet military falcons"Komin su atare sukeyi, wani irin strong solidarity bond da amana mai karfi shiya ya daure abokantakn su hakama matsayin aikin su iri daya ne duk dama aikin sun daban daban ne.

Mayor Wasim mesut kaita shiba land army bane,acibiyar navy yake aiki amma dake kusan sa'ar su daya ne da abokansa hakan bai taba raba su.

Mayor Wasim mesut kaita ya fito ne daga zuriar wani babban sarki mai suna king mall mesut,ba'asan tushen sa ba but thy speak pure qurayshian arabic daga can wani yanki a yankin saudi arabia.

Dabiu da nagartan Kabilar mayor wasim mesut basu da wani kwakwarn banbanci dana zuriar hakeem wamako duk dama su familyn sarauta ne, sannan babban sana'an su shine tatsa da safaran gwalagwalai da saida man fetur,so arzikin su is mainly base on oil boom and precious stones economy

Wasim yana da shekara 20 a duniya aka masa auren dangin da wata cousin sistersa Mai suna princess bahiyya oumran mall.

bahiyya yar sarkin kudancin yankin sune auren gata aka musu amma bakaramin son juna sukeyi da mijin ta wasim ba har zuriar iyayen su tazo ta shafe,thy kingdom bcom null and lost aka bar wasim da dumbin arziki inda ya dau matar sa suka ya maidata wani kasa,shiyana aikin sojan sa tare da abokan sa.

Na ukun sun shine mayor Aseem assiduque Daga zuriar mimiko ya fito kabilar data fito daga yankin yemen wanda ta hade yare da bakaken labarawar somalia,mimikos empire yayi kaurin suna sabida mugayen mutane ne karfafa wanda basu da saukin kai sosai
Shi mayor aseem assidique ya fito ne a wani shaharren familyn drug lords wato masu safaran miyagun kwayoyi da bindigogi da boma bomai sai dai kusan tsarin rayuwar su iri daya ne da abokan sa amma shi jami'in sojan marine shikam bada wuri yayi aure ba,ya aure matar sa mai suna "Jasmine aboubakr"

ita jasmine cikakkiyar somalian beauty ce wadda ta hada yare da asalin hausawa gaba daya familynta gaggan yan siyasa ne aurene ya tarkato ta itama ya dawo da ita garin mijin ta.

Sai ya kasance Acikin su su ukun nan mayor Aseem shine yake da abun fadi marar kyau sabida wannan safaran miyagyn kwayoyi da saida bindigogin da kakar sa yayi tayi ma mutanen da bai dace ba..

Tun assidiq wato mahaifin aseem din baya son abun har dai yazo ya rinjaye sa shima ya fada,amma dansa mayor aseem yaki ya jona harkan kwata kwata hakan yasa arzikin sa bai kai na sauran aminan sa bunkasa ba, mafi akasari kudin aikin sa ne dukiyar sa,shi sam baya son kudi daya fito daga zuriar sa duk dama suna da shidin sosai.

Mayor hakeem
mayor wasim da mayor Aseem su ukun nan sunyi tarayya acikin tsananin abota,
son juna,yarda kuma amanar dake tsakanin su ya zarce tunanin kowa.

Komai tare sukeyi arayuwar su ban dauke bacci cin abinci ibada da aiki ba, atare suka gina kansu sukayi wani irin tsinananen karfi da suna, cikin tsananin amana da yarda da kara mai girma babu wani babban makafan sojoji da makafan criminals a duniya sa ba san sa zaman abokai ukun nan ba

Wasim hakeem da Aaseem su suka kawo karshen tabarbarewar sojojin dake cikin jejin kerala suka kuma kawo karshen cin amanan kasa cin hanci da saida miyagun bindigogi..

Hakan ya sa suka dawo tamkar icons,heros kuma ake mutuwar jin shakkar su da tsoron su, dan har suka kammala aikin sojan su babu wanda ya tabayin tunanin karawa da su.
Chapter 6 · 0% Book details