← Book details Takaicin Wasu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 130 OF 176

Sashe 130

Takaicin Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaba daya ta rikitashi da jimami ga yanayin tan da saurin sa tausayi da karya zuciya, anan ma sanda sukai awa hudu ahaka tana abu daya ba sasaauci,sosai hanklin sa ya tashi
ganin Bayan kirar sunan zaira datakeyi batacewa komai sai kuka

Dalilin dayasa kenan mahdi ya kasa zanne ya kasa tsaye yakuma ki yay comunicating da nashwan tin safe..
Washe gari sassafe daya farka ya bude wayarsa yaga tex dinshi

Nan ma baiyi kasa a gwiwa ba yaje ya same wafiyya har ta idar da sallah akan wheel chair dinta tayi shiru as usual kamar tana laximi,mahdi ya rusuna agaban ta ya gaishe ta da girmamwa sannan ya mika mata wayar dan ta karanta bukatan da danta ya rubuto...

Wafiyya ta amshe wayar,Harta fara karantawa bata sa wani reaction akan fuskarta ba,sanda ta kai karshen note din kafin daddan sautin murynta ya sauko tare da tsillin hawaye,nan ta fara murmushi sosai a hnkli ta furta Alhamdullhi
Tace my zaira is getting married..

Saita juyo ta kalle mahdi da hawayen taff kwayar idanun ta, a hnkli ta shafa kansa shima kamar wani dan cikinta tace..."Mahdi.

Mr mahdi ya kasa hade idanunshi da ita barema ya amsa kirar sabida hawayen dake shirin kufce masa,he was more reliv dayaji tayi magana kuma yaga tanata murmushi sosai.

Ta kuma cewa alhamdullhi mahdi haka Allah yake lamarinsa.

Sai Kayi sauri ka cika musu alkwarin su ko?,ka bani inda zan iya in aika ma yata zaira sako,she have d right to knw who she is,who are we nd why her life is like this.

Zaira ta girma batare da tasan ita yar waye bace a duniya,i kept it from her to protect her mahdi,..

zafin rabani da akayi da nashwan bazai taba gogewa a xuciyata ba shiyasa na dade inajin tsoron na fallasa ma zaira tarihin rayuwarta dana iyayenta a duniya,yaya kake ji zanji in aka rabani da yarinyar nan?i will surely die mahdi
Im alive for my son nashwan,but who is alive for zairah?

Na dade da nauyin hakan araina amma tunda dakanshi ya neme aurenta,kayi masa auren.

But first i need to send a messge to her,koda anyi auren yau ko ba ayi ba inaso ka tabbata sakona ya isa wajen ta..dole ne in gaya mata labarin ta dana iyayen ta,zan gaya mata wacece ita..Sannan inada bukatar neman gafarar ta akan rashin kasancewa da ita acikin dukan wannan lokuta danayi harda ranar auren ta ranar da zanfi kowace uwa alfahari na kasancewa uwa agareta.

As for my son ni bana da tacewa aknshi dan nasan duk sanda yaxo wajena zaisan nice uwarsa,kaine magabacin shi uve been his evrything a friend a father a brother,his quiding angel,try to be there for him now Allah ya ma rayuwarka albarka mahdi..
Allah ya saka maka da alheri duniya da lahira,u are a frigging hero,insha Allah Alherinka zai bika har yayan yayanka.

Mr mahdi yana share hawayen shi yace ameen da kyar, yace nima nayi farin cikin dawowarki nayi farincikin samun lpyarki,ina fatan inna daura masa auren na dawo xaki bani cikakken labarin abunda ya faru daku..
Maam i really how nd how comes ure alive tare da zaira wasim dan bamu ma san anhaifeta ba

Murmushi kawai tayi tace".
Zan baka labari
We have alot to do cos I will fight for my childrens happiness.

Aseem da xuriar sa bazasu kuntata ma rayuwarmu sannan in sake basu daman kuntata ma rayuwar yaya na ba.

Rayuwar auren Zaira nashwan baxai taba ginuwa acikin kunci da cin amana ba,zanyi iya bakin kokari na dan na tabbatar da hakan,cikin tsareta mr mahdi yace kenan in gaya ma nashwan cewa kin dawo kuma kina tare da shi,?"..wani mikewa tsaye tayi cikin karfin hali,shikan shi mr mahdi sanda ya razana ya tashi tsayen yana kallon ta"tace..A'a mahdi
Kar ka gaya ma nashwan cewa ka sameni,Kabari yata zaira zata kawomin shi.

Cike da gamsuwa da hakan ya amsa da toh sai ya tashi ya wuce gidansa don ya shirya tsaf,daga nan akayi documenting auren tun daga tushen alkwarin su na gaskiya da iyaye suka kulla,har gida ya kawo ma wafiyya
Tayi signing fannin neman yardan magabatan zaira..

Kaso sabain daga cikin dadadden kunci da damuwar datayi dakonsu shekaru araru aranta saiyau takejin kamar fara sauka murmushi kawai takeyi har mahdi ya wuce don ya aiwatar da auren cikin sanarda nashwan cewa komai zai yuwu

Arnd 8am na safiya zaira ta farka a gajiye but she was feeling bit relax tacikin xuciyarta sai tanajin kanta wasai kamar tama kare al'adarta ne tana bukatar wanka,nashwan yana bude kofar dakin ta tashi da kyar tana nishi kamar wacce zata xaunar da kanta batayi aune ba taji dirar mutum akusa da ita,daga ido sama tayi taganshi har ya iso daf yana tambayar ta,"are u ok?tunkan ta amaa yace zaki sha tea?
Sosai ma yake bata mamaki,tasan tana cikin zafin zazzabi da razana amma she cant help it anymore sosai takejin nauyinshi,sai taga kamar wani nauyin take daura musu da suke kulawa da ita.
Tana ta tunani aranta
He save my mum he saved me Kawai saita farajin kamar komai ma ya fita mata akai kawai gida take so ta tafi,she want to have her mum nd live this world forevr..cikin magagin zazzabin sai ta fara tambayar shi in a calm way tana cewa Ina mamanta,tace masa ita wajen maman ta zataje sabida tagaji da komai,tausayin ta ya karaji aransa musamman in yaga yadda take hawaye tana kuma saka damuwarta sosai in tana kuka,yace zansa akaiki wajenta amma saikin samu lpya ko,tana cewa sir tana shagwabewa tana dada rikitashi da sakaltacen kukan shwagaban ta,in kagansu kamar baba da fitinanniyar yarsa yar karama yana rarrashi,da kyar ta amince zatayi wanka taci abinci akan in tayi hakan yace shida kansa zai kaita wajen maman tan
Zaira tana amincewa akan zatayi wanka taci abinci nashwan ya fice ya barta a dakin san,but she cant really walk far sabida jirin datakeji sosai taso da ace adakin ta taje tay wankan yau amma ina,still dai anan tayi wankan ta kimtsa kanta fes,tana fitowa wani sabuwar jirine ya kwasota ta xube akan gadon san ta dukunkune cikin bargon san tanajin kanta da zuciyarta na wani irin muguwar sarawa.

Nashwan yana gama wani call kirar mr Mahdi ya shigo wayarsa tun akan hanya suka fara fada yanata tuhumarsa akan kin kulasa jiya da yayi
Mahdi dai baice dashi komai ba,yana gama masifar ya nitsar dashi ya gaya masa cewa yaga sakonsa na auren,sai suka fara maganan akai.

Nashwan yaji dadi kuma ya dada jin karfin gwiwa daya ga mr mahdi ya bashi tabbacin goyon baya,ata fannin mr mahdin ma ya gamsu ne ya gane cewa tsananin soyayya ce da tausayi ya sa zai auretan ba akan wani dalili ba.

Dake awaya ne so dan kadan suka tattauna akan maganan project din north da aka daura mas'ud din ayau,Nashwan was very confident akan mas'ud,tunda yaga dukan project dinsa yayi masa su batare da cin amana ko algus ba..

Mr mahdi ma ya yaba sosai da halayyar mas'ud duk dama ya fara tunanin neman sanin wayeshi kuma suwaye asalin iyayen sa..

Bisa umarnin nashwan ne yasa mahdi bai karaso gidan ba,ya nufi inda zai tara shedu dan aje masallaci a daura musu auren..
So nash ya amince cewa auren its gonna happen in an idda sallahr jumua
Dan yace shima yanaso lallai yaxo wajen yay witnesing daurin auren sa

Zaira datayi kwanciyar ta dade tana jin jiri jiri da ciwon kan amma bataga shigowar nashwan ba,can arnd 11 na safiya ta farka, Wata mata na dabance ta shigo mata tana mata hidima ita ta kawo mata abincin ta taimaka mata tayi sallah dan tayi wankan sallar daxu,kayan jikin ta dai ta mayar ta koma ta kwanta dan sosai ne batajin dadin jikintan..
But matar was so gentle with her,wani yagalgalta takeyi kamar yar sarki,komi tace tana so sai taga ankawo kuma bata barinta ita daya koda na minti dayane

Zaira tun tana matsewa harta fara jin ta damu ganin sha biyun rana ya wuce bataji duriyar nashwan ba,hakan yasa tama ki taci abincin da aka sake kawowa,bayan sun gama magana da mahdi Mayor Aseem ne ya kirashi sharp sharp babu jira ya fara masa zancen cewa yakamata su dawo da maganan BMF tunda abunda yay jiya yasa talakawa sun kara kimantasu
Kuma darajar sa da sunan ya kara daukakuwa

Acewar mayor lallai nashwan wamako ya dau wannan damar ya kuma shirya speech inda xai bayyana ma talakawan sa cewa nan da wata biyu thats bayan an kammala gina north
Dashi da mayor Aseem din zasu hada kai sutada hidimomin BMF.
Tun jiyan ashe Nashwan yana nan yana fama da zaira ne amma acan sauthsong lady jasmine da yarta hanadi da mayor aseem har sunyi video call meeting jiya cikin dare akan cewa,in mayor ya tursasa nashwan ya amshe magamn tada BMF in 2 mth time za'ayi yin auren sa da hanadi Shikenan burin su ya gama cikawa

Agabar meeting dinsun na jiya sosai suka dada hasassa ma hanadi son jinta aure nashwan.
Musamman ayanxu da talakawan gari suke rubinshi suna jinshi untop a zuciyoyin su

In a Qaddara ya amince da maganar BMF din kowa acikinsu yasan in yay hakan he will be unstopble wajen farin jinin jam'aa dan za'a kimanta sa ne fiye da kima and hanadi is dyieng to be by his side awannan lokacin..

Hanadi tana barin wajen mayor ya dada jadadda ma matarsa cewa in har nashwan bai amince ba zasu karya shi ne da shirin da suka kirkira domin yinsa akan banafsha
So evrything seem achievable to them sosai hankalinsu ya kwanta...

Da yau da safen da mayor ya kirashi Tsaf ya nitsu ya gama jinshi Amma ko kadan bai dauki maganan sa guda daya ba.

Shi damuwar sa aynxu naga auren dazaiyi ayau din ne da kuma burin neman ma matarsan farinciki ita da mahaifiyarta ba xancen BMF fa.

Haka suka gama waya da mayor baice ma mayor eh ko aa ba,kuma bai yi tunanin saka kowa a shirgin hidiman auren sa ba
Banda mahdi dazai zame masa uba ko masud dayasan ya yadda dashi bai gaya masa cewa aure zaiyi ba bare su abhay da babban abokinsa noor
Chapter 130 · 0% Book details