← Book details Takaicin Wasu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 168 OF 176

Sashe 168

Takaicin Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mayor yayita kirarsa akan yabar maganan lauchng din nan yajirashi ya dawo sai bai daga wayar ba,daga bisani har kararshi yayi wajen manyan garin masu fada aji amma haka yaki fir yaki xuwa, wayanda ma ya daraja su yaje ma sai dai yajisu amma ko uffan baya cewa kuma bai fasa abunda yayi niyya ba,ya riga ya san in ya jira mayor zasuce ayi louching din in a grand way dan ya sake kwadaita ma talakawa maganan bmf shikuma bata nan hanklinsa yake ba kuma baison a sauya masa ra'ayi akan komi.

Lady jasmine kamar
Xatayi hauka wajen tada bori da masifa,da kyar ma nashwan yazo gidan dan tunda su abhay
Suka cilla england suka same noor bai kara taka kafarsa gidan ba,tayi ta masa masifa hartana kumfar baki
,Irin ta haukace masan nan da mita koda zai sassauta ya bar maganan louching din,ta kawo wasu zancen ta na cewa basu shirya ba as a family menenen ta babu yadda za'ayi subarshi yayi making babban move arayuwarshi a lalace cikin ganin damar sa ko akan maganin nan ma saida ta tuhumesa wai meyasa bai gaya musu yanada team of scientist ba meyasa zaiyi komi batare daya fada ba
Haka ya gama jin ta tana gamawa ya tashi tsaye ya fetsa mata walkantacen dabiar rashin da'arsa yace mata shi ba danta bane shi baisan ta bama kuma ita ko mijinta basu isa dashi ba bare ya zauna mata bayanin komi in zaiyi arayuwarsa,
kaca kaca ya mata ya nuna mata cewa bata kai ta tuhume sa akan rayuwar sa ba..irin kayi reminding din mutum cewa kasan fa ba sonka yakeyi ba dalili ne yasa akr zaman tare,nashwan yace mata yadda ta tsane shi tun farko shima haka ya tsaneta so is bettr su cigaba da tolerating juna karta sake ya fara nuna mata nashi tsanar a fili dan yasan bazata so abunda zai mata ba

Tsaban bacin rai Babu irin tsine masa da zaginsa da lady j batayi ba shima kuma ramawa yakeyi akan idonta ko ajikinsa dan ko kadan baijin kunyarta ko tsoron ta,haka sukayi yar watsi bazaka ce zasu sake yin magana ma juna ba har duniya ta nade cos he said many terible things to her masu zafi..

Washe gari tana ji tana gani ya bude anguwar sa ya sa aka saka mutane aciki tsanarsa sosai ya ninku a xuciyarta ta farajin da tana da iko ko yartan da ake so abashi da bazata taba bayarwa ba hanadi babu yadda batayi donta rarrasheta ba amma ina,sanda tayi kwana biyu tsaban fushi bata magana da kowa sanda mijinta mayor ya zo ya kira su a waya kafin taji dama dama.

Mayor yace ta barshi karta kara ce masa komi yana shiri zai dawo ne kuma in ya dawo komi za'a gama shi.

*1 month leave*

Komi ya lafa sosai sakamakon shirun nazari da kowa yayi boss khalepa anash fannin yanata bincike ne sosai akan case din wancan cutar haka ma mayor yaketa bincike yana son yasan wayanda suke taimaka ma nashwan apart frm mr mahdi..

Nashwan tuni ya koma zama wajen mamanshi tana tarairayar sa with honour nd pride najin dadin yadda akayi komi yadda take so da yadda baiya tsallake dokar ta musamman in tace kar yayi abu..

Rayuwar sa mai dadi sukeyi duk dama ya matsa mata sosai akan zaije inda matarshi take,wafiya tace masa ya dan jira mr mahdi ya dawo tukuna dan wancan satin ta aike mr mahdi daular sun amma bata gaya ma nashwan din ba

Nashwan duk ya babbata labarin new life din su abhi,yace mata ai har sun siya babban gida makansu abhay yana runing companies dinsa daga can amma ya koma makaranta zai karanta law under islamic jurisprudency altho basu da islamic background su a fodder class aka ma fara sakashi in da za'a koyar da shi dokokin da tushen addinin sa for 6month,abhi kuma matsala yaketa shiga da superiorz dinsa tun dayace musu yana so ya bar aikin ganin dagaske yakei sai suka hanashi takardan sallaman sukace sun bashi hutu duk sanda yaji na dawowa zasu karbe shi,daga nan share kashin su yayi ya fara bibiyar noor shima yana neman mafita ma rayuwar sa,within these period sosai rayuwar sa ya sauya kamar basu ba sabida passion din da suka sa aransu na son cimma hakan,da suport din nashwan da noor dake azama su uwa uba suna samun kyakwar kulawar lpyar kwakwalnsu ta hanyar therapy daga noor Thy live not far away from each oda dan gidan sun baya da bambamci dana noor sosai,an nemi abhay a industryn su na waka har angaji anyi shiru daga schl sai gida sai wajen noor basa kuma waya da kowa sai nashwan..
Sosai wafiyya taji musu dadi dik dama haryau nashwan bai gaya musu yana tare da maman shi ba most time in suna wayar video call sukance ya nuna musu zaira su gaisa amma haka zaiyita wainasu har ya gaya musu cewa sai sunxo masa dukansu kafin ya nuna musu ita

After a week kuwa suka masa ziyarar bazata batare da sunje ss ko sun sanar da kowa ba,da noor da abhi da abhay suja sauka a gidansa sai basu same sa anan ba,nashwan yanajin labarin xuwansun yace ace musu yana xuwa haka yaje ya fada ma mamanshi wafiyya cewa sun iso,Shidai yana da trust issures gani yake hala noor zai fada ma su lady j cewa ya same maman shi,shikam tsoron hakan yakeji ransa tuntuni...
wafiya kuwa ta riga tasa aranta cewa muddin sunsan wahalar da yasha na rashinta basu masa haka ba Itace .a ta dada bashi go ahead din kawosu nan inda take..

Nashwan yana isa gidansa ya same su har sun babbaje sun kwanta suna jiran sa,sunfi awa guda suna barkwanci da tsokana kafin yace musu su biyoshi shima ya hada musu babban suprise a wani waje

Abhay ya fara quesing hala nashwan yay parking secrtly ya koma wani gida ne da amaryanshi za'akaisu suga sabon gidan amarya
Noor ya fara tunanin hala ko zaira tana da ciki ne yake so yayi shocking dinsu,abhi kuwa damuwar sa naga abinci ne,minti daya saiya tambaye shi ince dai matrka tana dafa mana kai harda kuma abinci?
A mota daban daban suka dau hanyar dukansu suka isa akan lokaci.

Nashwan ya rike hannun noor kamar dan yaro suna tafiya sai abhi da abhy da suke biyosa abaya suna zazzare ido jin inda gidan ya dau wani irin shiru..

Haka ya rinka jan ransu yana wucewa da su falo falo,karshe ya fitar dasu can ta kofar baya inda suka ga wata hadaddiyar garden,wafiyya ce a tsaye tana jejjera cutleris ita daya agaban 10 chaired outdoor dinning table,table din round ne inda kowa zaina facing kowa,ta sa kayanta mai kyau zubinsa da tsayin sa kamar alkyabba
Batama ji karar shigowar su akan lokaci ba sabida yadda dukansu hanklin su ya koma kanta ganin basu taba ganinta arayuwar su ba,noor ya fara tunanin ko mahaifiyar zaira ce..

Yana kokarin zare hannun shi nashwan yaki ya sake shi har sanda taji motsin su ta juyo,wani kayatacen murmushin ta mai sanyaya ta sake ta tarbesu,inda nashwan ya mika mata hannun noor ta rike anata tana ta kallonshi tana maaa murmushi yace mama,ibrahim kenan..ga su abhi.. atake suka rusuna kasa cikin rudani zasuyi gaisuwa wafiyya tace musu ta yafe su taho kan table su zauna tukuna,suna zama ta sassaka musu ruwa mai sanyi a kofi kowa ta bashi a hannun shi cikin kulawa,tana basu tana tambayar su lpyarsu da na harkokin su tana dada welcoming dinsu,kan su duk ya daure ya basuga zaira ba?thy tot ai wajenta zasu zo, nashwan kamar zai fashe tsaban dariyar rudewar fuskokin su da tambyoyi dake cinsu ta ciki..

Nashwan yanata ce mata mama mama suna jinshi noor kam ya gama sawa aransa maman zaira ne Kai tsaye wafiyya ta deddeba musu lafiyayyun abinci ta umarce su da suci.

Abhi ne dama bai saba da flako ba amma ganin yadda take bawa nashwan yana ci kamar dan yaro sai abun yake dan daukar hanklinsu..
Wafiyya bata ce musu komi ba sanda ta lura dadin abincin ya shigesu sun fara aika ma juna funy gestures musamman ma noor da nashwan sannan ta fara musu magana a nitse..

Ta fara da noor cikin tausasahiyar kalamin daya saurin bayyana masa godiyarta agareshi altho bai fahimce mai ya taba mata arayuwa datake saka masa wannan albarkan ba..

Hakama su abhay,daga yanayim su kawai ta gane cewa abhi is the weakest one dan haka shi tafi bada eye contacts data fara magana da su akan rayuwa,the place was so quiet jin yadda take tausasa su da kalaman samun karfin gwiwar cigaba da rayuwar su yadda ya dace wanda da tunda aka kawo su duniya basu samu mai gaya musu irin wayannan maganan ba..
Tana gamawa nashwan ya amshe maganan,inda ya basu mamaki ayayin da yake musu godiya akan tolerating din halinshi da suka dingayi da yadda amanan su da damuwar su ya dawo dasu tamkar yan uwa,he stood up yanata kallon fuskar noor shima hawaye cike da nashi idanun yace guys i knw u most be wondering who is she?noor cikin breaking silence dinsu yace "mahaifiyar zaira ce ko?..wafiyya tayi murmushi..nashwan yace yess,..BUT i will like yo all to oficially meet my MUM...she is mrs wafiyya wamako..
My mum..my world my queen my life
Yan biyun in shock suka dago idanunsu atare suka dire akanta,noor ya mike tsaye cikin rudew yace"ur mum? Uhmmm wnnan itce Wafiyya wamako?
ya fada a rude nashwan yana tare hawayenshi da suka ciko idanunshi yace "yes,"i found her" she is alive...bai gama karasa maganan ba yagan su duka uka agaban ta har sun zago sun mamayeta da idanu kowa da kalar gaisuwar sa da rudewar sa,bayan sun sata hawayen kalaman su na barka da dawowarta har sanda taci dariyar musun da suka tafka awajen kowa yana cewa dama jikinshi ya bashi da kyar noor ya fadi gaskiyan cewa shi ya dauka ma maman zaira ne

Its become the most amaxing day of thy life,suda suka zo da niyyar komawa gobe gobe sai gashi sunyi ma wafiyya kwana biyu Abhi ya farajin kamar karya bar gidan tsaban gatan data babbasu kullum sai tayi dariyar comedynsu kamar zata yi fitsari
Chapter 168 · 0% Book details