← Book details Takaicin Wasu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 148 OF 176

Sashe 148

Takaicin Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Zaira ta kwace jikin ta ana shi jin yadda maganunsan suke rikitata da jin tsananin sonshi da tausayinshi ta tsaya daga dan nesa baifi taku biyu ba tana kallon sa idanun ta taf taf da hawaye,she is soo confused mema zatace mashi after all ya balain bata tausayi,irin tausayin nan da bata taba jin irinsa aranta ba ma,but son shin ne bata tabbatar ba is too intense yana mata mixing da wani yanayi a kwakwalwarta so how can she even marry nashwan wamako mutumin datasha yin rantsuwar bazata taba kasancewa a inda yake ba?This Is a very hard decision for her to make bare ma ace har an riga an kullashi ya dawo alakar aure,sunata kallon juna amma ba wanda ya iya budan baki yay magana wani zuciyan ne yaketa xugata data warware auren kawai taje wani waje saitayi tunani mai kyau ta dawo,wani kuwa lallashin ta kawai yakeyi data tausaya masa ta duba uxurinsa,Kawai sai ta fasa kowanne ta juya kamar zata barshi ta koma gida nashwan ya shiga biyota abaya cikin naci yanajin ajikinshi cewa matarsa ta karbesa yace "zairah..,ta runtse idanunta tace nifa karkana biyoni,ka koma can..ya marairace yace kin tsaneni in tafi kenan?shiru tay masa tana kan tafiyarta kafufunta har hardewa suke dan sauri,zaira pls i beg u kisawa zuciyarki imani karki dandana min azaban da naji adacan baya da suka rabani da mamana,tayi shiru abunta she knw he is just saying all this out of pain nd fear of loosing her right now,tasan karya yakeyi baxai taba barin nan ba muddin in bata ce masa komi ba itakuma ahalin yanxu bata da cikakkiyar amsar da xata bashi,aira da wasu matan tagani daga can nesa suna tahowa inda suke da alaman ana nemansu Tun kan sukaraso zaira sai ta nemi waje ta tsaya,nashwan yana biyota abaya abaya aira tace "budurwa ina kikaje mama tana ta nemanku Zaira ta daure tace babu ko ina,aira bata sake kulata ba taje gaba wajen nashwan dayay fayau he look too xhausted nd bit sad,airah tanayi masa murmushi ahhkli ya mayar mata yace meye sunanki?Tace Airah daga nan zaira taga dukan yan matan sun wuceta sunje wajensa,nashwan ya riki hannayen aira sincerely,yace in baki amanarta ni zantafi ne,wata rana zaki kawomin ita ko?aira ta kalle xaira daga can nesa, bugu daya tsaf ta gane abunda take ciki,murmushi tayi tace mashi shikenan,,,sai ta jua tana hange hange can ta nuna mai wani kungurmin kusurwa kamar rami kamar riijiya da uban zurfi da duhu wnda tsaban abun tsoron sa da kayoyi da sakar gixo gixo aka killace shi
sukansu yan garin basu san meyene aciki ba,kafin aira ta jashi saida ya je gaban ramin sanda yajata sukaje gaban zaira ya kamo goshinta ya sumbata yana mata murmushi Sai uban nokewa take batako kallesa ba,Aira ta fara janshi dagsken gasken zata kaishi ta jefashi cikin kusuwar nan suna isa adaidai bakin wajen saita barsa,tace masa ya fada cikin rijiyan dan nan ne kawai hanyar da zai fice dashi garin,kallon ramin yay a tsorace dan koshi baisan dagangan aira takeyin hakan ba,aira tana barinsa awajen ta dawo wajen su zaira ta samesu tsaye zaira tafarajin kakkarfan bugun xuciya,dayan wayanda suka xo sai ta fara cewa zaira din,Allah sarki namiji zai shiga inda bazai sake fitowa ba"xaira tabita da kallon rashin fahinta irin kamar yaya?,dayan ma tace ai bama fa wanda ya taba shiga ciki,aira cikin ixgili tace ai shiyace in rike masa amanar matarsa amma kinga ni gobe aure gidan saurata waxai kawo masa ita?to hala mama dai zata iya.."To in zata iya meyasa kika turasa ya shiga wancan ramin hala mutuwa zaiyi in ya fadi,zaira tace mutuwa?sai ta juya ta kalleshi yadda yaketa kallon ramin duk ya tsorata yana daga tsaye,da sauri ta dauke kanta ta kalle aira akan me zaki turasa inda zaije ya mutu daga cewa ki rike amana saiya ce miki xai tafi ya barni?ashe ba hanya bane awajen kika kaishi?aira tayi saurin maida abun cikin xolaya ganin yadda zaira ta hayayyako da zafi
To ni me zan masa?
Ko ance miki daga gobe zaki kara ganina ne?tsaki zaira taja mai zafi tanajin batama da lokcin kulata,juyi tayi da niyyar komawa wajensa kawai taga mutum yana kokarin zare spider web da alaman zai shiga wajen da sauri ta fara daga kafa zuwa wajen,baima ganta ba,shi tunda yaga ta bi yanmatan ta share sa the more yafarajin zafin rayuwarshi the more yana damagin brain dinshi xaira ta shiga sauri sauri zata isa wajensan harta mika hannun zata dafashi sai Aira ta taho aguje ta bayansu ta wani turesa suka firgita har saura kiris ya xame ya fada cikin ramin kuma dagangan tayi hakan abunta

nashwan ya rike kafafunshi ya saki wata muguwar kara yana matsawa da baya baya yana rikke kafunshi jin yadda qayoyin suka cak cakeshi...zaira tana kallon sa ta fashe ma aira da kuka"meyasa zaki turasa?meye haka?nace miki Bana so zamu bata inkina turasa..meyayy miki

Aira ko ajikinta,taga ma kamar fushi xata tsayayi bazata duba masa inda kayan ya cakeshin ba,ta wani taho tana wani langwasa zata kama kafafunshi xaira ta tureta da haushi,."dan wannan ciwon kaima saika zauna kana nishi nishi,ni ka tashi mutafi..ta farajan hatsalellen tsaki tanai masa masifa
"Katashi,nashwan bai iya motsawa ba dan har jini inda kayar ya cakke shi yayi,tsugunawa agaban sa tayi tana dubawa,bata ko lura da abunda aira take gaya masa da sauran yan uwanta da idanunta ba..

zaira tana shashhafe masa wajen nashwan ya dada birkicewa kamar an saka masa barkwano ya fara mannuwa da ita kamar zai shige jikinta ,..."wayyo Allah kafa na..Su aira ma suka fara tayashi riritawa suna mishi sannu sannu,zaira tana ta famar dubawa dan ita bata ga wani abun kirki awajen ba kamar zatai kuka tace,"to ka tashi mu tafi..ya langwabe wuya yace bazan iya ba fa sai ragwaf ya kwanta akan krjinta kamar dan karamin yaro.. haka ta dinga sassaita shi,Dake dama hade bakinsu sukayi sai dayar wacce bata ce komi ba tuntuni tace in baka taka yanzu ba toh bazaka sake iya tafiya ba fa..aljnu sun tafi da kafarka kenan Dukansu suka dago suka kalleta,zaira tace aljanu?Aira ta langwabe kai kamar dagaske ta sa fuskar bada hakuri,/tace budurwa dan Allah kiyafe ni bansan fa zai shiga wajen ba dama can da wasa na masa
canfa Dakin aljanu gashi har qayansu ya cakke shi shikenan namiji bazai sake iya takawa kin dawo matar gurgo,xaira ta mike tsaye tana kallonta da mamaki Kikace wasa?meyasa zaki masa wannan wasan shi ina yasan miki dakin aljanu anan?aira ta sunkuyar da kai kasa ai naga kamar bakya sonshi ne kuma fa koda ban ce ya shiga ba mutuwa yacemin zaiyi in ya bar garin nan garin ahaka,toni meye laifi na
,,zaira taji kamar zata tsinka mata mari ni nace maki banason shi?kawai kice dai kin cuceni da wasar banzanki
..sai ta dauke kanta a fixge ta dawo gabansa ta kama kafar tana jujjuya tanata masa tofin addua akai har kamar abun dariya

,mutumin dayaga duk ta daga hanklinta sai yafara langwabe mata sosai,tun tana masa rarrashin da masifa harta koma lallabar sa tana shasshafa shi,aranshi bakaramin dadin abunda su aira sukayi masa yaji ba.
Yasan a rude take bazata taba gaya masa amsar sa ba
Haka kuwa tayi fushi da su ta ja hannunshi suka koma gida takai kararsu direct wajen mamansun hartana kuka,sosai ma take bashi mamaki,
sanda aka raba case kafin taje ta kwantar dashi,
ananma kafin ta dawo ta samu duka sun hade mata baki,
Matar ce kawai tace mata ai xasu san yadda zasuyi su warkan dashi,amma zaira sam taki ta kwantar da hanklinta daren ranan gaba daya ajikinta yayi baccinsa abunsa tana duddubashi

Kwanan su biyu anan zaira ta dawo normal tana kulawa dashi sosai zuciyan ta tuntuni ya riga ya zaba mata amsar rudanin ta Tausayin shi da sonshi ne yanxu yake mata dabaibayi musamman da ta gane asalin damuwar shi
Da boyayyr kuncinsa

Sassafen qashe garin ranan nashwan yana bacci akaje musu wankan tsumi na karshe,yaune za'ai kai dukan yan matan nan gidan sarki dan haka suka dinga yi ma juna bankwana inda aira da sauran yan matan suka dinga yi mata fada suka tona asirin abunda sukai mata ranar da cewa tabi mijinta su koma tunda dai tasan tana mutuwar sonshi.. basarakiyar nan tace koda baki gama gamsuwa da hukuncin da xuciyarki ta yanke akan sonshi ba kisa aranki kemai iya xanja muguntar sa ne ya dawo muku alheri,tace kiyi shahada wajen ganin kin cimma hakan,..hade da guntun nata feeling din duk saita karaya ta farajin ta qamsu da hakan kawai.

Rana na fitowa suka shirya tsaf dan sudin za'a fara rakawa su fita agarin,matar taja xaira dakin ta mata hayaki sannan ta kawo wasu jigidar sirri masu balain kyau rubu goma ta damka mata tace mata tasa wata rana zasuyi mata amfani
Chapter 148 · 0% Book details