← Book details Takaicin Wasu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 176

Sashe 53

Takaicin Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kallon yarta take cike da tausayi da mamakin yadda taga duk ta zama wata iri kamar ba zairah din ta ba,zaira dake makale a kafadun ta ta kankame ta kamar zata koma cikin ta tuni hawaye ya wanke mata fuska,"a hankli wafiya ta shiga shafo gefen fuskan ta tana murmushi me wuyan fassara kuma me tsananin ciwo tace,my zairah..my little princess ki gafarce ni kinji? its been too long Mama tayi kewarki sosai bazan iya daurewa bane nace ko ma yayane nidai zanzo inganki,to yaya kike?ta dago fuskarta suna kallon juna,zairah ba abunda takeyi sai hawaye dan bazata iya misalta sanyi da dadin datakeji adede wannan lokacin dataga maman tan ba , girgixa mata kai wafiyya tayi tana nurmushin ta na karfin hali data saba,ba kuka zakiyi min ba..ki tabbatar min cewa ba wani abu daya same ki mana!! Ko so kike in goyaki kowa yaji mu ina rarrashinki,kinga ai saina saka dan samarin nan daya taimaka min a matsala ko?yace min ba'a barin kowa yaxo nan ai Jiya ma naxo na dade awaje inajiranki kawai an hanani shiga ne"
Shine na jira,yau wannan samarin seya temaka min kinsan shi ko?Daga gani yasan darajar uwar sa..yana da kirki sosai
.Jin haka yasa xaira share hawayen ta ta kalle wafiyyar cikin sauri da mamaki
Tace "Mama tun jiya kika xo shine kika kwana awaje ko?wafiya tana shafo gefen fuskarta tayi shiru,hakan ya bada zairah daman gane hakan ya faru wani haushi taji sosai aranta tace wayyo Allah na,yanxu hala ma an walakntata sosai,tace mama ki amsa ni mana a ina kika kwana ro?ko komawa kikayi kika sake dawowa yau?,wafiya ta girgiza kai alaman a'a..can kuma cikin sanyin murya tana kallon idanun yar tace"I have to see you my dear..karki damu da na kwana awaje..zairah ta dan ja jikinta kadan ta runtse idanunta hawaye na fita sosai tace
"No pls mama,wallhy in har xaki zo nan to nasan zasu walakntaki bakiga koni ban sake cewa kixo ba?xan iya daukar komi amma banda cin zarafin ki mama,gidan nan fa kaf basu san darajan dan adam ba,sum of them are mean wulakanta mu kawai sukeyi..seta fara kuka ahankli kamar abun dama ya dade yana cin ta arai sosai ..cike da sigar tausaya wafiyya ta damke hannun ta sosai
Xairah Kiyi hakri Bazan iya juyawa bane nayi kewarki sosai zairah ta..
Ana walakantaki ko? waye yake walakntaki?shiru tayi tana sake ajiyan zuciya dake ta fidda abunda yake cin ta arai saitaji dan dama dama.

Nace waye yake walakntaki?tell me now..wafiyya ta fada sounding so sad nd disturbed kamar dagske zata iya daukar wani babban mataki..tuni zaira ta matsa gefe kadan dan ta kasa hade ido da ita cikin sanyin murya tace "A'ah...mama..bawani abu bane fa..aikema kinsan halayen yaran masu kudi Wani lokacin nakanji nagaji..cike da rashin qamsuwa wafiyya ta damko kafadun ta ta kira sunan ta quiet serius tace"Zairah,
Zairah tace naam mama..karki boye min komi in bakijin dadin aikin ni zan tafi dake gida yanxu...zairah ta dan yamutsa fuska a sangarce tace no mama..cikin salo ta juya akalar maganan yawwa baki gayamin labarin business dinki ba"..daga nan kaf ta gaya mata abun da umma baraka ta gaya mata..nan ma murmushi kawai wafiyar tayi batace komi ba sai alhamdullh".zairah tana dasa aya ta cigaba da matsa mata da tambayar suwaye suke walaknta ta?har ta gaji tace matan gidan ne ko ogan ki?meyake miki shi..yana miki magana?kai tsaye zairah Tace nifa bayace min komi,yana da fushi mama..wallh tsoro yake bani...dayan yarinyar sun ne bata so na mama, ta tsaneni sosai..tana tsangwama na yayi yawa nan ma dan kadan ta tsakura mata karanbattar su da hanadi,duk dai shirme shirme ta fada akan nashwan da yanayin halayen sa inda Aran wafiyya take ta alhamdullhi tunda yau dai Tafara fahimtar wasu abubuwa game da rayuwar danta hakuri ta babbata sosai ta kara mata karfin gwiwa ba dama tagaisa da yenge sabida kar a kama su,so dan abun da ta kulla a leda tazo mata da shi duk taharhada ta bata sukayi bankwana cike da kewar juna.

Sam bata san lokaci yaja haka ba Da sauri da sauri take tahowa kanta akasa saura kadan taci karo ta fadi sai taga mas'ud ne can yana tafiya da sauri kamar zai fice daga nesa tace

'Mas'u...d hey..

daga dan nesa ya kalleta saiya daga mata hannu yasakai ya fice bai tsaya ba
wani sautin kugi cikin ta ya bada dan Hakan dayayi bazai wuce yana nufin nashwan yana ciki ba kenan

Tunda taga ta kira masud bai tsaya ba ba shakka aika zaije dan shi baya wasa da aikin sa.

A hankli ta turo kofar kitchen ta shigo karaf ta buga goshin da bayan kofar,rike wajen tayi tana mulmulawa da sauri "oh ni zaira mena ke yi ne"se yanxu ma ta tuna ashe tun jiya da dare rabon cikin ta da abinci na safen ma yau bataci ba

Ta maida kofar kitchen ta rufe cikin hanxari ta bude yar kumshin ledar da wafiyya ta taho mata dasu tarkacen lemo ne da dabino sai wani tsaftacen gwangwani cikin sa duk mai mai shikuma cike yake da kitse an daddasa soyayyan namomin dayaji hadin kayan yaji aciki,spoon ta dauka tasa har jikin ta na rawa ta tsakuro guda daya ta sa abakin ta tana taunawa very slowly yana mata mugun dadi abaki sai taji kamar yana tuna mata wasu abubuwana musamman kamar yadda take kewar komi na rayuwan ta abaya musanan ma girkin wafiyya me dadi dasa kwanciyar hankli wani namar take shirin zara takai baki caraf seta tuno da ashe bata hada ma goga abincin safen sa ba,tana dubar wall clock taga goma na safiya har ya gauce a daburce ta ture ledan taga ashe yadda ta harhada ganyen spearmint a tea maker bata tafasa ba bare ta hada takai,wani sautin kuu cikin ta ya bada lkcn da
Naman data dauko ya kufce daga bakinta ya fada kasa ma bata sani ba...Cikin hanzari ta hau Tattare tattare tanayi kwalwan ta na rehearsing abubuwam data zataje ta furta agabn sa.

Tace ohni yau na shiga uku,tea din ne ko break fast?duka lokutan kaisu ya wuce gashi bata yi bama bare aje ga gyaran daki da sa ruwan wanka,gaba daya taji jikinta yayi weak Can dai ta bar muhawaran ta,ta aje komi ta fito Ko da zataji ra'ayin sa tunda ance mata bai fita ko inaba tukunna

A sadade take takunta very quietly kamar me shirin kama barawo duk fargaba ya gama nakasa ta,dede kofar falon taja ta tsaya ta dan lumshe idanun ta"Deep breath" Ta furta makan ta sanda tayi sau uku sannan tayi shahada tashigo ciki

A falo ta same sa yana zaune akan one sitter yana baza wata muguwar qamshi jikinsa a tsaftce da casuals as usual farin body wamer da dogon bakin wando mai laushi kamar kasa hannun kayi ta wasa da suman kanshi tsaban yadda sukaji gyara sukayi kyau suna wani kyalli,i dont knw why he loves black nd white colour kayan sa daddaya zaisa baka same kala daya daga cikin su ba
"zuciyarta ne
ya furta hakan ayayin datake karasowa tana kkrin doka sallama cikin gaggawa,baiko juyo ta inda take bama bare taji kamar zai amsa, Kallo ma yakeyi da remote control a hannun sa da alama yau ba lallai ya fita aiki ba

"Good mrning sir.katashi lpya

Shiru taji ba'a amsata ba

Dakanta tasha jinin jikinta tayi shiru can seta fara bada hakuri."Kayi hkri bansan lokaci yaja haka ba Dama dama naxo inji ko da akwai abunda zan iya girka maka yanxu.Yadau kusan mintina uku kafun ya dago kansa ya kalle ta ya kare mata kallo up nd down
" And did u care to xplain wher the hell u are?Shiru ta danyi yi dan bata san me zatace atake ba,can tace
I....i..dama inata waje ne
Tsaye ya mike kamar wani tsohon soja fuskan nan a murtuke giving a blank stare irin kalon nan me matukar kada hanji da razanarwa.

Atake taji gwiwanta sunyi kasa gaban sa tana kneeling jajayen idanun sa gaba dayansu fixed suke akanta

Can kasa ta maida kanta sosai zuciyarta kamar zai fita ya balla kirjin ta tsaban gudu

Kika fita waje..
Whith whose permison?

Yadda yayi maganan gwanin ban tsoro yasa takasa ma iya dago kanta ta amsa shi kasan tiles din kawai take kallo...kurwan tane ya furta soryy din ko gangan jikin tane ita duk bata gane ba dan bata ma cikin hayyacin ta.

Listen nd listen carefully
Ya fara magana cikin iko "ni ba abokin wasarki bane..i dont look like a joke to u..dake dani har abada ajinmu bazai zama daya ba.

Na lura dake kin mance me yakawo ki nan,amma zan tuna miki..zaki gane cewa na wuce duk yadda kike tsammani Zaki kuma gane ke kike min aiki bani nake miki aiki ba.

I also have power to decide for ur miserable life,zan iya batar dake abanxa kuma har abada banxa ta bata..

Zaira bata san sanda hawayen ta yafara saukowa ba

Wani kazamun kallo yake mata daga gani zuciarsa na kona,"next time do ur job kafin ki tafi yawon gantalinki acting asif u own urself around here
Ke ba komai bace
Illiterate..Kuma Karki sake inji wani sautin kukanki anan..u disgusting little brat and
When u finish foaming an ocean with that miserable liguid coming out frm ur eyes u can get up and serv ur purpose.

Yana gama furta hakan ya wani jifa da remote din akasa yayi waje,remote ya twarwatse akasa kaca kaca itama zairah din sanda ta karkace tsaban ta razana bata iya motsawa anan ba sai bayan wasu seconi,can ta goge hawayen ta ta mike cikin rudani bata san ya zatayi takuma tambaye sa me zaici ba dan daga zarar ya mata tsawa ko tsiwa sosai takejin tsoron sa ya kama xuciyar ta

Ranar haka tayi ta rakube rakube gashi tun bayan nan bata kara ganin sa ba har dare kuma ko abincin ta yau bai taba ba,haka ta dawo daki jikinta a sanyaye yaukam tasan gangncin ta ya jawo mata d only time dataji sauki aranta shine intayi juyi takan tina cewa yau tayi ido hudu da maman ta wafiyya nd that alone its realy soothing her....

Kalaman wafiyya yana saka mata kwanciyar hankli
Chapter 53 · 0% Book details