← Book details Takaicin Wasu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 133 OF 176

Sashe 133

Takaicin Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nala tana kallon sa lokacin daya sauko daga motar ya je ya bude mata kofar ta dayan bangaren yakuma taimaka mata ta sauko tayi aman,har tagama yana tsaye akanta rike da goran ruwa
Can taga ya rusuna agabanta yana xuba mata ruwan tana wanke fuskan ta da bakin ta Nala Ji tayi kamar tayi bomb ta tawatse a hujajan ta zaga kasa don dukan alamu sun fara nuna mata asalin gaskiyar lamarin,sai dai bata fa gane wacace awajen a tsugune ba dan kokadan batayi kama mata da hanadi ba,taga yarinyar kamar tsiririyece ga wani uban ado da akayi mata tayi balain kyau kamar yar aljanu,dake mayafin zaira tun a motar ya xame suman kanta ne kawai ya rife mata bayanta
Sai taga nashwan yanayi Kamar zai shige jikin ta,da dukan kulawar sa yaketa famar mammanuwa da ita

tunkan nala ta dawo hayyacin ta farga taga nashwan ya mata daukar cak matar ta lafe luf akan kirjinsa a hnkli kuma ya direta a gaban motar sa,dakatawa tayi sabida yadda numfashin ta ya wani dauke mata cak,tanaji tana ganin yadda ya tsaya ata gaban seat din she knew that gyaggayra mata zaman ta yakeyi.

"Who d hell is this bitch?Cikin tsananin rawan murya da karkawa ta furta hakan azuciye tanajin kanta da xuciyarta yana harmamin tarwatsewa yana shirin bombing...

Tsaban ta rude bata ma lura da cewa har ya zago ya shiga car dinsa ya fara tafiya ba,sanda tagansu chan agaba sannan ta farga

A gigice ta koma cikin nata motarta cikin yanayin firgici ta zauna ta rufe motar da karfi,tana kama stiring ta wani ja zazzafan numfashi,fashewa dawata uban kuka mai kuna da ciwo tayi atake,a rikice ta tayar da motan ta fara binsu,batama ganin gaban ta tsaban kukan datakeyi,nashwan ne zai ci amanata?
Har Zaiyi aure bazan sani ba who is dat girl wallahy yau saina kasheta

Magana takeyi Tanata kukan kamar ranta ne zai fita ta dau wayarta ta kira baban ta bugu daya ya dauka yanacewa hello baby Ta tsare shi da balain kuka."Dad kamin alkwarin kace ni xan fara auren nashwan
I just saw him eloping with another woman now Ni dai wallahy kasan yadda zakayi da su
U fail me dad..
Tana fadan hakan ta katse wayar tana ta kuka,she is not even sure abt evrything tsabagen son datake mai har gani take kamar abunda tagani duk karya ne,ganin hanyar da suka dosa zai fitar dasu acikin garin yasa ta ja da baya kadan ta juya kan motar ta bi ta wani kwana na daban dan ta sha gabansu ta tsaresu

duk jikin ta rawa yakeyi,kifiyar sonshi da kishin sa na balain caccakar kwakwaln ta har kaman zatayi hauka da kukan jini,she just cant wait to see dat girl wacece?yar gidan uban waye?metake dashi da bana dashi meye tayi akan nashwan harya aureta kuma ya dauketa zasu bar garin,gaba daya nitsuwar jikin ta ya fara kubucewa tsabagen yadda abun yake barazanar buga mata kwakwalwa.

Tana kuwa shan kwanar motar mr mahdi ya bi bayan nata,ita batama lura ba gudu kawai takeyi tana kuka

Zaira kuwa tunda tayi aman taji daidai wani bacci mai nauyi ne ya debeta..
Sai kallon ta yakeyi da gefen idanunshi yana murmusawa thinking of yadda zata kare musu da ita in ta dawo cikin hayyacin ta tasan ita matar sa ne ayanxu,..

Da alaman baccin ya gama shiga jikin ta har wani xufa xufa yaga takeyi asaman goshin ta,dan Tsillin sumanta dake reto a sama dake neman rufe masa ganin kwaliyar saman idon yakai hannun sa akai yana neman kawarwa wani kallon fuskanta yashigayi anayinsa na shagaltuwa..
Wani karau yaji wata kara mai firgitawa tataso agaban su,burki aka ja da karfi sai da Kirjinshi ya buga a hujajen ya dago kansa yana kallon gabansan, nan da nan hannun sa ya danna full security lock sai motar ta kullu bai damu ba tunda yasan ko inanta bullet proof ce,wata jeep bakace agaban su amma baiga waye aciki ba,abunda yasa yakejin kamar bazai iya sauka ahalin yanxu ba bayason a kwatanta dauke masa matar sa ne dan kuwa bayajin in akayi hakan zai iya daurewa,nala ko kuka takeyi,kukan takeyi sosai har na fitan hankli,tsananin son shi datakeyi yaso ya fi kwalwaltn
Amma kishin nan dai bazai iya barin ta taganshi all lovey dubey da wata nadaban ba,she want to knw who is dat girl?

In har aure nashwan yay da wata na daban to tabbas ya zalunce ta,ta tuna yadda ta dawo jiya ko bacci batayi ba tsaban musun da fadan da sukayi da familynta wajen kare soyayyarsu

Duk dama taji zafim abunda ya faru dasu amma da nail ya farka taji suna maganam daukar fansa,juya musu bayan ta tayi ta basu laifi.

How can he not see all these secrifices
Shin bata fi kowa cancanta ta zame masa mace na farko da zai ririta a duniyarsa ba?
She is secrificing her family for him
Ita wannan din daya dauko meta ta taba yi masa?who is she?..meyasa tuntuni bamu santa ba...

Shikuwa nshwan Ganin kamar ba motsawa za'ayi ba ya kunna motar sa a yay reversing a haukace zai juya ya bar wajen,yadda ya fige kan motar ya waina da karfi yasa zaira ta tsorata ta farka, nala ma saita firgito ta wawushi stiring motar ta a gigice ta fara binshi a guje duk dama har ya fara mata nisa

Nashwan yanata mamakin kowaye wannan yake binshi gaf da gaf haka?binshin akeyi kamar zasu bar garin tare ga yamma ya kusanto sosai atare suka hawra kan gada ta inda zai sada su da hanyar xuwa range din
,kishi gaba daya ya rufewa nala idanu tukin ganganci kawai takeyi tana neman koda ta gwari bayan motar su suji zafi su tsaya sufito tagansu
,suna daf tsakiyar gadan tafara lura da jirgin sama akansu wanda tasan lallai wannan jirgin mallakin baban ta
,
cike da fargaba zaira ta fada jikinshi ta kankame shi sosai,cikin tsananin tsoro ta kasa cewa komai sai zazzare idanunta kawai takeyi, dan dolenshi ya sake stiring ya kamota jikinshi da hannun sa daya ya manneta da kirjinshi sosai hannun sa daya yana tayashi tukin Zaira har yanxu Mamakinsa takeyi Daf zasu sauka akan gadan sukaji harbin bindiga takansu inda nala ta firgita ta sake kan motarta yaje gaba da gudu ya ture nasu tayi gaba da karfi

tun kan nala tayi controlling kanta taga dakarun baban ta acan sama suna saukowa sunfi su goma kowa ya kama igiya daga saman da alaman sunyi readyn kai hari ma motar nashwan

Wani uban ihu nala ta fasa kamar zata haukace,suna sake harbin motar nashwan mr mahdi ya fara setin harba nasu jirgin in just few min karan harbe harbe ya gigita wajen,

He cant control his car sabida yadda motar nala ya tunkude su da karfi ga zaira data manne mashi ayanayin ta na firgita,jin harbin yyi yawa yasa nashwan ya gungura dasu kasa yana sauka ahankli har can can kasa kusa da wani babban teku suka zame motarsu yay dasu cikin wata jeji,suma ne kawai zaira batayi ba sai da motar ta tsaya taganta manne da kirjin sa Da alaman babu abunda ya same su Da kyar ya tashi mata yanajin yadda gefen jikin sa yake masa wani zafi zafi....
[12/12, 8:53 AM] Pretty KITTEN: *68*
bugu daya xuwa biyu yay ma glass din motar ta fashe cikin yanayin sauri sauri da kyar ya cimma glass din sannan ya tunkude murfin ta budu Duka hannun ta ya jawo ya fitar da ita waje ta tsaya sannan shima yaja jikinshi da kyar ya fito...
wani tsami tsami jikinshin yake masa da alaman ya bugu tawani wajen amma bai tsaya neman ina ne ke masa xugin ba,seat din baya kawai ya nufa ya bude ya tarkato kayansu ya kama hannun ta suka fara tafiya cikin jeji,gam gam zaira ta riko hannun san daya riketan dan bakaramin sauri sukeyi dansu bar wajenba ta wani hanya suka billa,hanklin nashwan duk ya koma kan hanyar caraf taji an cakumo mata dayan hannun ta ana janta a gigice duka suka juyo, nan sukaga wani mutum gimm agaban su kamar anjefoshi
Ko inanshi a rufe take da mask yana shirin janyota zai rabasu da qarfi wani bugun bazata nashwan ya kai masa sanda yay baya atake ya fadi kasa,nashwan yana shirin zare wata boyayyar pistol daga bayan nashi wandon sai yaga mutumin yana farfadowa tsaye,nan ya dago bindigarsa baiyi wata wata ba ya harba shi direct setin zaira inda nashwan yay saurin janyeta jikinshi bullet din ya sauka akan arm dinshi ya bulasa, wani irin kara zaira ta sake tana neman rusunawa kasa a gaban sa dan firgici
Mutumin ya mike tsaye yana wani huci ya riko bindigan shirin harbinsu na biyu,da hannun ciwon nashwan yacakame hannun ta ya daura akan bindigar sa suka rike tare daidai setin zuciyar mutumin yay da hannun tan suka harbesa hannunshin ce ta zame sabida zafin datake mai,a bazata zaira ta kuma dannawa a batasani ba ta kara masa harbin sau biyu a kirjinsa finally sai su kagansa a kasa ya fado mutacce,da sauri ta yasar da bindigan akasa duka hannun ta suna rawa sosai
Tanajin kamar numfashin ta zai figeta sama

Wani karar bindigan sukaji da alamar an kuma dauke gawar mutumin da harbi ta baya,mr mahdi ne ya bayyana agaban su yanai ma zaira alaman ta rufe bakin ta kar ajisu dan ita tunda taga ta kashe mutum ta razana tana neman zarewa kallon jinin dake tsiyaya a hannun nashwan tayi ta cigaba da hawaye sosai
Chapter 133 · 0% Book details