← Book details Takaicin Wasu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 176

Sashe 12

Takaicin Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ina so kisa ido sosai ki dube yarinyar nan
Zairah tayi saurin buge yatsan ta dake shirin nuni da hanadi..

"Metayi?..zairah ta mata tambaya a miskile tana duban bakin ta dake Allah Allah ya furta kalma
Ta nuna hanadi da baki tace
"Wallhy She is fake
All fake fake fake...ki duba dai wallhy duk plastiv surgery ne up and down ajikinta,hmm
Allah kadai yasan ya asalin halittar ta yake wayasan ma single hamamace me kunkukumin akuya ni duk cikinsu baga wanda ta caza min kwakwala kamar wannan ba..

Sake kai yatsa tayi zatayi pointing din hanadi zaira ta buga hannun ta kasa da karfi

"Are u mad?
Pls dont point at her,wayace miki ana nuna mutane, muna gaba gaba ne fa meye haka afiyya.

Da karfi afiyya taja tsaki ta kwace yatsan ta cikin masifa"Ke ni ki kyaleni an nuna tan.. ai gaskiya na fada ba fake din bace?ke fa ranar kika nuna min ire iren alaman surgery da nake musu akan hallitar jikin kim kardashians,nikuma tun ranar nake gane wa and this girl is fake in gaya miki Babu abu daya nata wanda ba surgery ba..

Shiru zairah tayi ta kau da kanta tana me cigaba da kallon dayan jerin 5 cars da ba'a bude ba inda hakan ya bada afiyya takaici sosai,tsaki tayi mai sauti a duk dama sun saba yar hakan tun suna yara
..ita zairah sam bata amsa irin wayannn small talks din, magana in bamai kama hankli ba saidai ta saurare ka tayi shiru amma bazata ce ma uffan ba ita kuma Afiyya ko abakin kura take
Sai tayi gulma da kokkawfi koda bazaka amsa din ba.

Tun tsaywar ta agefen zairah Sai mutsu mutsu take da idanun ta Tana faman tura bakinta tana gatsine,tsaban damuwa da damuwar wani har zuciyan ta na bugawa tanajin tamkar zata balle ta shiga filin ta samu hanadi ta gaya mata she is fake har wani haushin ta takeji haka kawai dan bakaramin tsole mata ido tayi,tsaban neman abun fadi ababu abu har ta kirga yawan surgeries din dake jikin ta,and As far as she can tell dogon hancin dake fuskan hanadi bana Allah bane she has goten a nose job,ta kalle nonowan ma tace duk breast implant ne,ga liposunction a lips shima ya fallasa kansa,dake ita hanadi ba suit tasa ba sai ta bar straihgt hair dinta ya sauko so ko dankwali ma batasa ba,anan ma har lifted hairline afiyya tagani wanda akeyin shi to get rid of flay away hairs sai kaga suman kan mutum ya tafi zirr ya mike super smooth ko iska baya iya jajjansa kamar dai an jona sa akan mace da engine,ga tummy tuck cikin hanadi is super flat,cheek implant,ba a bar bum lift da chin augementation ba
Ga uwa uba botox,Afiyya tayi kwafa aranta she was like."Ohh no wonder she looks peefect halittar hanadin yayi mugun kama da wanda babu kuskure ko gyara aciko, koman ta seems authentic ashe duk na engine ne..

wani jijii da kai afiyya takeyi tana tsit da yawu cikin bankama, ita daya tana hura hanci aganin ta tun da ita kadai ce ta gane hakan ai tagama cinyewa Tasan dai mutanen kauye sun nan na ka duk jahilai mabarata ne to wama zai fahimta?ashe kuwa yau ita za tafi kowa bada labari me zafi..

Daga yanayin yadda hanadi take shan qamshi take taku daidai behaving so poorly da maids din dake biye da ita..

Basu ma yi nisa ba taja ta matse taki takawar saita tsaya a tsakiyar fili ita batayi gaba ba kuma batayi baya ba sukuma maids din suna biyeta mata suna wani yagalgalata kamar sunga yar fir'auna toh tun anan zakasan cewa hanadi tana da giggiwa.

Hanadi irin matan nan ne masu muguwar son girma son girman ma irin na kwanta in taka ka...

Sanadiyar hakan taja hanklin jama'a da kin motsawar ta,dan sam taki taje mazaunin ta tana jiran lallai abude motar NASHWAN su taka tare,irin su jera din nan ita dai tagansa a gefen ta acikin jama'a..

Nashwan dan Saurayi ne kerarre dan shekaru ashirin da bakwai wanda yayi kyam yana zaune a owners coner sanyin Acn benzan sa na ratsa shi cikin nitsuwa da kwanciyar hankli

Kansa ya lafar a bayan seat din extremely black mercdez maybech dinsan,doguwar hira a wayar dayakeyi looks pretty important da alaman baima saka ranar saukowa ba

italian Designer Aldo bianchi yaci wankan sa up and down with xception of agogon rolex kirar submariner silver and black dake hannun sa and bayan wannan
Komai na jikin sa is fashionably
Pampered, well tailored and xtremly classy...

He look damn healthy Komai na halittar jikin sa is remixed,halittar mahaifin sa da mahaifiyar sa babu wanda ya aje agefe.

Shiyasa yau zakaga skin colounsa pure carribean white irin kamar an goge sa da zuma da madaran nan gobe kuma in ya fito sai ka gansa fari dau kamar dan bature.

Fatar jikinsan babu tabo bare illar rana is alwys looking
natural,mattified and shiny,ga wani elegant million dollar saje da gemunshi daya masa kyau bana wasaba,suman kansa xtremly black nd shiny yalolone irin na sadaqa yallah yasha askin zamani yanata sheqi,hrt shape lips dinsa shiba pink ba shiba pitch ba dai normal one and ofcous dogon hancin sa zak na maman sa wanda hakan ya kara masa girlish look ata nan.

yanada gajiyayun brown eyeballs wanda a karo na farko in kuka hade ido dashi zakace ya cake ne but no ko maltina bayasha bare giya ko wani abu mai bugarwa,
eyes dinsa is naturally clumsy sumtimes yana wara su suna kwacewa kullum kama suke da kamar yana jin bacci,but dake sun kasance round kuma gwalagwala ne sai hakan ya bashi wani sigar rigimaman salo.

To me he look and behave like that columbian singer wato maluma the best latin artist in the world.

Kana kallonsa kaga balaien rigima,ji da kai,tattalin kai da shan qamshi uwa uba sangartacce ne na kure tunani.

Sabida yanayin kammanin uwa da uba daya hada yasa zakayi saurin rudewa wajen karantar personalityn sa
Sumtimes kamar macce,dan yanada dan banzan rigima da kwainane hakan ya sa ake kasa shi a jerin sexy and high atractive guys,ko a inda yayi rayuwar sa a europe bai dawo ba sanda yayi suna sosai wajen iya saurin jan hanklin yan mata.

and some times kamar namijin yake namijin ma babban soja,he act bold confident stern ga uban daure fuska da iya shariya da jefa baqar magana.

Idan ya saka sutura yau ya fito taro toh komin tsadar sa baya sake maimaitawa and belive me if you want to talk to him u most have degree in sacarsm dan Allah ya bashi baiwar iya cakka bakaken magana masu karya zuciya kuwa.

5 black mercedec maybach ya biyo,
kai zakace shima maids din ne suka masa rakiya amma ina,gogan shi daya yake tafe infact duka motocin sa empty ne daga drivers sai wanda shikansa yake ciki ana jansa.

Koda wasan wasa baya son wani tarkacen gurds bare maids a kusa da shi musammam ma dayake yasan halayen sa tun yana karami bamai sauki ba nd he highly daubt in akwai wanda zai iya zama da shi bare tolerating dinsa.

Abhay ne ya taso yana tafiyar sa a nitse har ya karaso gaban hanadi..ya tsaya kamar wanda zai dora hannu a kwankwaso amma bai daura din ba yamata kallon 2 scnd sannan yay gyaran murya

"C'mon Hanadi ...its time ki wuce mutafi.
Tayi shiru Bata ko kalle sa ba Ta galla wata gatsine cikin sautin taurin kai kasar wuyarta tace
"No bazan xo ba..sannan
Ta juya ta kalle shin a dakile dake tasan halin sa yanxu sai yayi kokarin jawo ta dan ta wuce su tafi.

A dame Yace Dan Allah sis ki zo mu wuce..

Ta bata rai Tace A'a Zan jirashi

"Hanadi muna cikin mutane ne kuma kinsan halin nashwan koya fito ma ba kulaki zaiyi ba, shiru kawai tayi..

"He is even on a call wallhy dawuya ya fito nan bai dizga ki ba"kamar bata jinsa haka tayi banxa da shi...can ya rankwafo wuyarsa kamar zai mata gulma cikin rada yace akauye fa muke,and all eyes is on you kinsan kinfa hadu sosai,i do not want u to spoil ur mood anan wajen

Wani juyi tayi da kanta a hankli taja karamar tsuka mai tafe da blush me nuna tana son ayabe haduwantan
..
"Cikin jan masa rai ta daga kafada tana sauke murya kasa "ohhhhh Abhay dafa ka barni kawai wallhy i want to walk along with NASH kasan fa ina son hakan.

..abhay Baiyi wata wata ba ya tabe baki cikin murmushin takaicin ta yace shikenan ok,tunda publicity stunt kike so to ni na tafi..tunkan ta dago kai ya kama hanya ya tafi ya barta a tsaye awajen kuma haka taci tsayuwar jiran nash daga karshe she have no choice ta hakura ta wuce wajen zaman ta dan dole.

ALokacin Afiyya ta gama cika ma zairah ciki da surutu duk motsawar da hanadi tayi saita kalubalance shi da mummunan fassara
Tsaki akan tsaki kamar wata tsaka.

Msww tuntuni Ita fa take bata ma mutane lokaci..

Mswww to meye na wani tsayawa atskiyar fili bayan yan uwanta duk sunje gaba ita ta tsaya tana leke leken meye?

To uban waye ma take jira haka mschewwww

Uban waye ne ma a motar dayaki fitowa?mchewwww

abuntan yanata bada zairah takaici da mamaki itadai batace kala ba
..afiyyar ma batayi shiru ba ta cigaba da mita tana tambaya "To waye a motar?msww shima ya fito ma dan fi'ilin tsiya,Tana gama furta hakan sai wutar placard dinsa ta kawo dau sanda wajen yayi wani irin shiru kamar mutuwace ta gifta.

"K.O.N....?

Wani matashi ya furta da karfi inda tuni wajen ya amsa da wannan kalmar wasu har suna fadawa kasa kansu bisa wuya tamkar wani sarki ne zai sauko

"KON..KON... KON ..
Harmoniously wajen ya wani amsa da muryoyin mutane maza da mata da yara wayanda basu ma san ma'anan abun ba kuma ana kiran sune da wani kalar shaukin da zai tabbatar maka al'umma suna tuna wani abu ko qarni daya shude mai dadi kuma muhimmi a tarihin rayuwrsu wanda bazasu taba iya mancewa ba
Chapter 12 · 0% Book details