← Book details Takaicin Wasu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 176

Sashe 2

Takaicin Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani Rawa jikinta ya somayi da kyar ma ta juyo ta dube tsoho dake rigingine batare da ta duba yanayin sa ba ta iso daf garesa Ta tambaye sa ina danta..taji shima yayi mata shiru sanda ta taba sa tukun ta gane cewa he is no more,cikin sassanyar yanayin lumshe ido ta ja dabaya tana jin wani abu me zafi da firgitarwa yana tsargan mata tun daga zuciyanta har kwakwlwanta yana mata tsananin zafi da zugi bata kara minti daya ba ta rusa a guje cikin kaduwa tana kwala kiran danta.
IS NOT FREE Contact me 08060712446 to acesss full story please read the disclaimer...
_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence!_
Wannan labari kirkirarre ne and is strictly fictional,a gaske bai faruba dan haka banyi alkawarin rubuta shi dan in nuna wani al'adan malam bahaushe,tarbiyan sa ko addininin sa ba,this story is full of detailed show offs and exerggerations,shawara shine in ka fara bi kaga tsarin bai maka ba sai ka ajiye sa,as this time arnd thy are no vacancy and space for nit-pickers and super board of directors,duk wani walakancin dayazo ya biyo baya im sorry sai kayi kuka da kanka!wannan shine GARGADI NA.
[10/17, 6:35 PM] The DUTCHESS🌟: *♡TAKAICIN WASU🌺*
_the destiny untouched.._

_A nigerian historical fiction_ _*WATTPAD SURAYYAHMS*_
_Brilliant writers association_

_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence!_

*02.*
Numfashinta kamar zai bar jikin ta ayayin da zuciyatta da kwakwalta yake garari cikin wani yanayi me wuyan fassarawa,sama da kasa duk ta birkita tana dubawa tabi mafaka mafaka ta tambaye kowa babu
Wanda ma ya wani kulata

tafiya takeyi a hnkli tsaban yadda takejin zuciyatta na bugu"..Nashwan,nashwan,nashwan,wani tafasashen kukane ya kufce mata batare data tsaya ba ta cigaba da bin duhun daren tana neman sa cikin tsananin tsoro tashin hankali da damuwa

Ganin taci rabin camp din a kafa bata ji duriyar sa yasa ta gurfana bisa gwiwar ta ta sake wata tsumammiyar kuka me tarin baqin ciki da karayar zuciya da jajayen idanun ta ta kure sama zuciyan ta na tsananin neman temakon Allah.

Strange movement dake tinkaro ta yaso ya dawo da ita hayyacin ta a daburce ta dago kai sedai hasken tochlight daya hasku dau a kwayar idanun ta shi ya hanata ganin komai

But still present din yaron ta datayi feeling ajikinta yasa ta isowa gare su cikin sauri

Maza biu ne karfafa sanye da green uniform din forest rangers tare da su akwai wata kibabbiyar mace,baqace me madaidaciyr tsawo sede siffar ta bai yi dibi dana musulmai ba,dan asalin low cut ne ma aknta fusknta fayau kuma a murtuke kunnen ta babu dan kunne saidai wannan ba damuwar wafiyya bane ganin danta n baccinsa hankali kwance a hannun matan shi yafi daga mata hankali

Cikin sauri ta iyo gabansu tanaji aranta cewa Allah ne yaji adduatta ya maido mata danta
Cike da godiyar Allah da zakuwA irin na uwa ta kira sunan sa a hankli

hannu Ta saka
zata amshe sa taji dirar wata tsawa da hantara cikin nuna iko gami da nuna mata kan bindiga da maxan sukayi..

"Stop,Ure very stupid who are you?'...

Muryan matan ne ya bijiro mata cikin kunnenta kamar wata dakakkiyar tsawa kakkausan sautin muryanta irin me razanarwa ne cike da tsoro wafiyya tayi nuni da yaron,ta matso kusa da shi har yar yatsar nata na rawa.

"I am wafiyya..He is my son nashwan.

Bata gama rufe bakin ta ba taji saukar wani mari tassssssss

Makaryaciya!!!!!

U bloody lier..
wannan ba danki bane ki fadi gaskiya kona sa a harbe ki

"Wallhy Dana ne..
Cike da rawan murya ta furta ido matan ta tsura mata kamar zata cinye ta danye,babu bata lokaci ta soma mata bayanin abun da ya faru daga farkon daren har iyanzu ta karashe da rantsuwar cewa tabbas wannan danta ne

Matar tayi shiru sanda ta gama sauraron ta Sannan tace"

"Kiyi mana shiru anan,makaryaciya..I said Shut up..Kin raina makanki hankali.

..wani identity card ta ciro ta nuna mata rai a murtuke take maganan.

"Sunana rotarian binta moses akuyam,ni babban jamiar kare haqqin dan adam ne daga babban kungiyar human right,drug abuse and childtraficking na duniya baki daya

And righ now ure under Arrest for identity fraud,child abuse and suspect traficking...nd im taking the child with me... ta juyo ta kalle sojojin,inta ki zama ku mata duka gobe zamu bincika muji asalin gaskiyar ta

Wani kukan bazata ne ya kufce ma wafiyya a mugun gigice ta rude ta fada kasa taname qaskntar da wuya cikin rudani tace
madam na roke ki da kiyi mini rai..na rantse miki da ranan mutuwa ta babu karya a labari na wannan yaron nawa ne..ki bani shi in ya farka zakiji yace min mama..i swear to god he is my son.

Matar tana shiru sanda ta kare mata kallo sosai, Tsaki taja ta bar wajen bata sake kulasu ba

Sosai wafiyya take kuka ayayin da mazan suka killace ta a gurd room har safiya tana jeka ka dawo cikin tsananin damuwa da fargaba

Basu tashi budeta sanda gari ya waye waje yayi tarwal ahakama jamian tsaro wanda bata taba ganin su ba sune sukayo kanta suna hantararta Basu tsaya ba Saida sukayi da ita cikin camp din bakin anan har wani gaban teburi aka akaita Inda bazata iya cewa ta gane kowa ba se daidaikun masu basu aikin gini and she cant even say inta taba maganan minti biyar mai kyau dasu tsaye tayi sauran suna xaune, duk hankalinta baijikinta sabida Bata ga shigowar matar ba bare taga danta

Tayi Shirin da ta saba,Wanda inda xaa duba yadda xuciyanta yake a disashe da damuwa ba tantama Mai imani dolene ya tausaaya Mata..

"Good morning director"

Can cikin gestures masu nuna girmamawa taji ana furtawa Nan danan ta daga idanun ta sai taga kowa ya mike tsaye ayayin da wannan matar ta shigo hannun ta rike dana nashwan

Fuskanta a matukar daure Blond and Blue humanatarian uniform ne a jikinta Wanda ya dada sawa tayi kama da tsohuwar soja yanayin ta Sam Babu fara a ko hayaniya Wanda acikin dakikan mintina biyu
Wafiyya ta Gama kare mata kallo daga Nan ta maida kallonta kan danta
Daya tsura mata Ido sosai rungume da pure milk shake da banana biscuit he look helpless da alaman Yana so xaixo wajen ta Amma yanayin da ake ciki already ya gama gigita sa

Ranta ya sanyi sanyi da bataga yana kukaba probably bcos of Madara da biscuit din da aka rudesa da shi cos dama yunwar ita dama tafi axabtar da su anan tun xuwan su nashwan Bai taba cin wani Abu Mai dadi Kamar na yau ba

"Mammmy....ya firta so slow yanata kallonta ayayin da muryan kukan sa take Shirin ballewa.da sauri wafiyya ta matso xata taba sa wani uban tsawa aka dakata Mata sanda ta ja baya Babu Shiri ..

Cikin bacin Rai da fada ta ficcike jikin ta

"He is my son pls let me have him.

Nashwan ya fashe da kuka ganin mamansa na Neman birkicewa

Nan aka hade Mata baki cikinn Sauki ana me nuna mata cewa yaro ba nata bane Sato shi tayi kota ke sonyi Kuma Sharia za'ayi da ita ma sannan a tabbatar

Kuka takeyi sosai dan Tabon hankali ne kawai Bai kama ta ba iya rantsuwa iya bayani tayi musu amma koda mutum daya Bai nuna ya gamsu ba Tasha mamaki matuka da har wayanda ma take musu aikin suka santa da yaron tsawon shekaru biyu Basu bada sheda ba Ga wani Dan uban yunwa na cin hanjinta ga yaron ta nata kuka xaixo wajen ta an riko sa an Hana su sakat ance karya take wai itake ta bude masa ido shiyasa yake kukan.

Agaban ta aka rubuta takarda aka rantaba hannu wai tafiya da ita za'ayi can gari wajen hukuman secret service agents da cids ayi bincike da cewar intana da sheda ta Nemo lawyanta Sai akai maganan kotu in bata yarda ba

Tana kuka tana Kiran danta"
nashwan nashwan,kahra...kahraman..duk jikin ta na karkarwa abar tausayi shima yaron Yana kukan sosai Yana Mika Mata hannuunasa cikin kuka Yana firta mummy a yanayin da duk Wanda ya ci Karo da yanayin su saiyaji ya karaya sosai,iya roko da magiya tayi koda ma abarta ta taba Dan yatsan sa Amma Ina tanaji tana gani kowa yaa juya Mata baya suka rufe ido sannan tasha mamaki kwarai ace cikin dukanin wayanda tayi Zama da su a kangon Babu Wanda ya Bada shedan cewa nashwan dantane and it even hurt her more to know tht mutum daya data San inda Yana Raye baxai karyata taba ya Riga ya mutu jiya.

Gaban mota aka tunkudo ta Kamar baiwa ta tana tafiya tana maganganu Kamar zata hadiye ranta ta mutu babu abunda yake memetuwa a kwakwaltan face maganganu mijin ta mayor alhakeem wamako da ya mata na karshe

"Run far away wafiyya..

karki taba Basu daman cutar min daku..Babu abunda zai min illa Bayan mutawa na kaman hakan.inkin amince cewa Tunda nake daku Bantaba gaxawa wajen kare ku da kulawa daku ba se yau aranan mutuwa ta to ki tashi ki gudu da nashwan ki bar Nan wajen wafiyya imm now helpless..I just wish I can protect u even after ny dearth my love..

"Ina neman alfarmanki daki taimaka min kimin alkwarin xaki Kulamin da Abunda na bari a duniya kinji?"Ke... Da nashwan u two r everything to me..pls protect Our kahraman..our love..wafiyya pls go away...kinji?..har yau datake tuna wayannan kalaman she can still remember clearly the beam clouded expression in his face in his last moment..
"La illa ha illa muhammdurasullillah swa
And that was his final word..sai Allah ya karbi ranshi

"mummy,mumma mmmaaama..
Muryan nashwan dake calla ihu cikin raxannnen yanayi ya dawo da ita duniyar mutane a gigicee ta juya taga Ashe batare da shi xata bar wajen ba ta juya a raxane ta fasa ihu me kara wanda sautin sa yake tamkar zai tsaga zuciyarta tace
"NASHWAN!!!!?....
A gigicee ta fincike zata balle ta je wajen san wani irin saukan wani Abu me nauyi taji akanta me tsananin radadi cikin gushewar hankali ta dago taga bindiga aka doke ta da shi.
Chapter 2 · 0% Book details